KUDIN ALAJABI Book 1 Complete littafin Yaki by Mansur Usman Sufi .txt

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Hausa Book Store

Chapter   4 / 4

9K to 10.2K   out of 10.2K words

ɗago da kanshi cikin ladabi ya ce "ya shugabana na rantse da ƙabarin kakana Marganun-uƙub ba zan dawo gare ka ba face na samu nasara shiga fadar bokaye.
Koda gama faɗin hakan sai Jauharul-Layal ya shimfiɗe gadon bayanshi,
Nan take Raudatul-Abyad ta ruga izuwa inda mahaifinta yake ta faɗa kan ƙirjinshi tana mai fashe da kuka, Abu-Raudat ya rungume ta, na wani lokaci daga bisani ta janye jikinta daga nashi ta dube shi cikin alamun matuƙar tausayi lokacin da idanuwanta suka ciko da ƙwalla ta ce "ya abbana haƙiƙa na shaƙu da kai ainun tsawon shekaru tun ina yarinya ƙarama, ban san kowa ba sai kai, yau ga shi zan tafi nayi nesa da kai inda bana da tabbacin zamu sake saduwa da juna ba";
Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai mahaifinta ya dube ta lokacin da ƙwalla ta cika mashi idanu ya dube ta ya ce "ya farin cikin rayuwata kuma sanyin idaniyata kiyi sani cewa na fi ki jin zafi da raɗaɗin rabuwa dake, domin a halin yanzu na rasa komai na jin daɗin rayuwa, dukiya, mulki da SADAUKANTAKA.
A halin yanzu yanzu shekaru na sun ja a Kowa ne lokaci ajali zai iya riskata, domin koda a halin yanzu bamu rabu ba, tabbas akwai mutuwa. Kin ga dole na zaɓa miki abin da zai inganta rayuwarki kuma ya ba ki farin ciki.
Wasiyya ta a gare ki ita ce duk sa'adda rai da rabo suka kai ki izuwa birnin Madinatul-Aswaj ki cika burin zuri'armu na ɗaukar fansa akan sarauniya Jauharat.
Lokacin da tsoho Abu-Raudat ya zo nan azancen shi sai duk biyun suka fashe da kuka mai tsuma zuciya suka sake ƙanƙame juna.
Al'amarin da ya sanya na ji ƙwallar tausayi ta zubo min, domin rabuwa da masoyi babu daɗi, duk da dake War zuciya irin ta aljani Jauharul-Layal sai da ƙwalla ta zubo mashi.
Tsawon daƙiƙa hamsin suna cikin wannan hali sai daga bisani ne Raudatul-Abyad ta janye jikinta daga na mahaifinta ta nufi inda nake, ba tare da wani ɓata lokaci ba ni da ita muka hau bisa Jauharul-Layal muka zauna.
Jauharul-Layal ya yunƙura cikin zafin nama irin na GWARAZAN JIYA ya buɗe manyan fuka-fukan shi ya tashi izuwa sararin samaniya ya fara keta giza-gizai. Tun Abu-Raudat na iya hangen mu har muka ɓace mashi da gani, ana fara wannan tafiya sai na cika da matuƙar mamaki bisa ganin irin matsanancin gudun da Jauharul-Layal ke yi, domin a iya tsawon rayuwata ko a tarihi ban taɓa jin aljani mai matuƙar gudu a sararin samaniya tamkar shi ba.
Sai da muka shafe tsawon sa'a bakwai a sararin samaniya muna tafiya babu sassauci ba tare da mun yada zango ba, lokacin da sa'a ɗaya ta sake shuɗewa ne, Jauharul-Layal ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuuh! Ya sauka a bisa turba.
Inda aka saukar ya kasance daji mai tattare da dogwayen bishiyu, duwatsu, ƙoromu da sarƙaƙiya. Ko iya shirun da ya wanzu a dajin ya isa ya jefa razani a zukatan duk wata halitta.
Cikin alamun matuƙar damuwa na dubi Raudatul-Abyad na ce "ya sarauniyar kyawawa shin bakya ganin cewa yada zango a wannan daji a haɗari sosai, ki duba ga ki ga yadda yanayin shi yake ?
Har Raudat ta buɗi baki da nufin ta furta wani abu sai sarkin matasan aljanu ya yi caraf na tari numfashin ta ya ce "ai an kare zai yi cizo ake siyo shi a kiwata. Domin koda akwai abubuwa masu cutar a wannan daji dole ne mu yada zango domin mu samu ƙwarin jikin da zamu tunkari fadar Sarkin bokaye".
Raudatul-Abyad ta ce "kwarai kuwa zancen ka dutse ya sarkin matasa, domin haka sai mu kasance cikin shirin ko ta kwana".
Koda gama faɗin hakan sai muka nufi wata itaciya, bayan mun zauna a ƙarƙashin ta sai muka fito da abin guzuri muka shiga kimtsa cikinmu, bayan mun kammala ne sai muka kishingiɗa domin mu huce gajiyar dake tattare, shi kuwa Jauharul-Layal sai ya shiga yin rangadi a wajen domin tabbatar da cikekken tsaro.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wata kyakkyawar budurwa ta bayyana a wajen.
Budurwar ta kasance doguwa mai kyawun diri da sura.
Hancinta dogo ne mai lankwasa da kyawu a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur, wuyanta mai kyawu ne dogo tamkar na barewa, kirjinta cike yake kuna a tsaye ƙyam! Ba su ranƙwafa ba, sai sheƙi suke tamkar nunanniyar gwanda, gwanin ban sha'awa, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya buɗe ya yi tudu ta yadda koda kofin lemu aka ɗora akai zai zauna daram, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi da fatar su ta kasance luwai-luwai tamkar ta jaririya sabuwar haihuwa, sanye take cikin tufafi na fatun dabbobi tun daga ƙasa har sama da suka kama jikinta ainun duk wata sura da zata ja hankalin namiji ta bayyana.
Wohoho! Haƙiƙa babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kwaɗaitu da sha'awarta
Sa'adda muka yi arbda da wannan kyakkyawar sura sai muka miƙe tsaye zumbur! Aka fara kallon-kallo tsakaninmu, a iya tsawon rayuwata ban taɓa ganiko jin wata 'ya mace mai kyawu tamkar budurwar ba. Duk da irin kyawun diri na Raudatul-Abyad amma budurwar ta zarce ta matuƙa ainun.
Tsawon daƙiƙa hamsin muna cikin wannan hali sai daga bisani ne kyakkyawar budurwa ta buɗi cikin wata irin zazzaƙar murya tamkar ana busa sarewa ta ce "yakai Matawus ibn Raziwan tare da Raudatul-Abyad bintu Abu-Raudat ku yi sani cewa tsawon shekaru huɗu ina jiran dakon samun ku domin na mallaki taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar domin cimma burina na ɗaukar fansar ran mahaifina a hannun sarakunan duniya huɗu na kuma mulki duniya baki ɗaya. Fatana na cikawa abbana burinshi na mulkar duniya baki ɗaya,
Saboda haka kira na a gare ku ku gaggauta damƙa min taswirar fadar cikin ruwan sanyi, idan kuwa kuka ƙi ta lumana azabar KAIFIN TAKOBI na zata tabbata a gare ku".
Koda jin wannan batu daga bakin kyakkyawar budurwar sai na dube ta cikin matuƙar fushi na ce "ya ke wannan AZZALUMA kiyi sani cewa haƙiƙa rafkananniyar zuciyarki ta yaudare ki da ta bayyana maki cewa za ki iya yi mana fashi da makami, wato ƙura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi.
Kuma ina so kiyi sani cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne, ko ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza" kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Zamu ga yadda za ki karɓe taswirar daga hannunmu."
Koda jin wannan daga bakina sai kyakkyawar budurwar ta fusata ainun, idanuwanta suka kaɗa suka yi jajur, har ƙwalla ta zubo mata ta dube mu ta ce "haƙiƙa rashin sani ne ya sanya har ka amba ce ni da azzaluma, amma akwai buƙatar na sanar da ku labarina a takaice.




Mu haɗu a littafi na biyu domin jin cigaban wannan kayataccen littafi.


Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da koyaushe.


Mansur Usman Sufi
08137237071

4 / 4