MATAR MAHAUKACI END Book Complete Document Writing Mrs Sadauki .txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   2 / 19

3K to 6K   out of 55.1K words

gaya mata ɗin zai iya zama matsala mi zai hana mu jira mu ji abinda Dr ɗin zai ce?"Abbasi ya girgiza kai yace "a'a gwara a sanar da ita dan tunaninta zai iya bata ko fita yayi"Ado na shirin magana Dr ya fito ya kira Abbasi .




Ɗakin da Mahomet ke ciki suka shiga,a zaune suka tarar da shi kan bed ya ƙi barin a saka masa ƙarin ruwa saboda a samu ƙarfin jikinsa ya dawo.Da lalami Abbasi ya ciyo kansa a ka saka mashi ƙarin ruwan da bai ɗauki minti goma ba ya ida,"ya kamata a cire masa wannan jallabiyar tunda ta jiƙe kar mura ta kama shi"cewar Dr Abbasi yace "ok yanzu da mun isa gida za'a cire"ordonnance Dr ya bashi ya jawo hannun Mahomet suka fito suka shiga mota Ado ya ja su.






A bakin get suka tarar da Ammi ita da mai gadi ya na yi mata bayanin abinda ya faru,ajiyar zuciya ta sauke ganin Mahomet ya fito daga mota bisa ƙafafun sa.
"Ammi ga mu mun dawo mu je ciki"cewar Abbasi,Ammi tace "eh yanzu mai gadi ke faɗa min,yaya jikin na sa?"Abbasi na riƙe da hannun Mahomet ya amsa mata da "alhamdullah"su na masu shigewa part ɗin ta.








★★★ *MAI JAN GERO*




Banda murƙususu da matsar ƙwalla babu abinda Maryam ke yi tun safe,ta rasa yadda za ta yi ciwon ciki mai azaba ke damun ta shiyasa ma ta tafi makaranta ba ta daɗe ba ta dawo gida ta tarar kuma Inna ba ta nan ƙila ta shiga makwabta kasancewar ba ta rufe gidan ba sai ɗaki.






Ta na nan kwance taji marar ta haɗi da cikinta sun murɗa lokaci ɗaya,da sauri ta ɗauki buta ta shige banɗaki ta fara zawo🤣 zuwa can kuma ta fashe da kuka ta kiran ta shiga uku sakamakon ganin jini da tayi sai zubowa ta ke.
Ta na kuka haka ta wanke ta fito,ciwon ma sai ta neme sa ta rasa sai tunanin yadda za ta cewa Inna ta ke.Tashi tayi ta koma banɗaki ta duba pant ɗin ta tare da shafowa ,jinin ta kuma gani ai kuwa ta ƙara sautin kuka ta fito ta fara zagayen gida sai da ta gaji ta zauna ta rabka tagumi.Tsawon lokaci ta na zaune sai taji damshin ruwa kamar ya jiƙata,tashi tayi ta kwance zane nan ta shiga tashin hankali ganin ya ɓace wani uban ihu ta buga wanda yayi daidai da shigowar Inna.
Da sauri ta nufo ta tana cewa "ke lafiyar ki?"
"Wayyyo Inna shikenan nayi abun kunya na haifi ɗan shege, wayyyo Inna na haihu amman ban ga jaririn ba"
Ƙirji Inna ta dafe sai kuma idonta ya sauka kan zanen da Maryam ta jefar ƙasa,da sauri ta ɗauke sa tace "jinin mine ni ke gani?"baya Maryam tayi tace "wlh Inna nima haka na gan shi tun safe ni ke jin ciwon ciki shine yanzu na haihu"mi ina za ta yi in ban dariya ba saboda ta gane jinin al'ada ne Maryam ta fara......






Jikar Rabo ce 😎
[06/02 à 14:49] Mrs SADAUKI 💫: *MATAR MAHAUKACI*🙆🏻‍♀️
```Destiny
Love
and
Romantic story```


Dedicated to *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR* 🇳🇪 ina alfahari da ƙasa ta✊🏻






*☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*


```MRS SADAUKI 💫✍🏻```


_______________________




Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*




*PAGE* 5-6




Asubar farin ma aikatan gidan suka shiga aikin gyare-gyare yayinda Ammi ta shiga kitchen da kanta domin girkawa mai gidan nata abinci da kanta.Mahomet na falo ya na kallon Ball ya ƙurawa tvn ido kai kace ya na fahimtar abinda ake yi,ya na nan zaune sai ga Hajiya Atine ta shigo da sauri ya tashi jiki na mashi rawa.Wata banzar harara ta watsa masa tare da jan tsuki kafin ta samu waje ta zauna ta na taunar cingam kamar wata tsohuwar karuwa.Mahomet cikin muryar rauni yace "Ammi!"da ɗan ƙarfi ta yadda za ta jiyo,daga can kitchen tace "ya dai Mahomet ko ruwa kake so?"jin yayi shiru ya saka Ammi fitowa.Ja tayi ta tsaya ta na kallon Hajiya Atine sai kuma ta share dan ta san bai wuce makircinta ganin Alhaji zai dawo kuma ta san direct nan zai shigo tunda ba ita ke da girki ba.
Da sauri ya nufi mahaifiyar sa ya koma bayanta ya na leƙon Hajiya Atine kamar yaron da ke leƙen abun tsoro,"sannu"Ammi ta furta ta na kallon Atine sai da ta taɓe baki kafin tace "ciwo ki ga a jikina koko cikin mawuyacin hali kika ganni?ga wanda ya kamata ki jerawa sannu nan mai fama da cutar da babu magani"
Sosai maganar ta baƙanta ma Ammi rai amman ta danne zuciyarta tace "Allah mai girma bai taɓa hallitar ƙwayar cuta ba fa ce sai ya fara yin makarinta ko wane ciwo a duniya da maganin..."Hajiya Atine tayi saurin katse ta da "ah kice maganin da likitoci suke ɗirka masa na banza ne tunda sun kasa warkar da shi kawai ɓarnar kuɗinmu mu ke yaro sai ƙara haukacewa ya ke na san nan gaba ma duka zai fara"ta ida maganar ta na mai yi masu kallon masheƙan hatsi.
Kafin Ammi tayi magana Allah ya baiwa Mahomet damar furta "Ni ba MAHAUKACI ba ne Ammi da hankalina ban san miye ya sa..."sai kuma yayi shiru jin kamar an tsikare sa da kwanya,dariya Hajiya Atine ta tirtse tace "au!da mi za ka ce hhhh"Ammi ta shafi kumatunsa tace "sha kurumin ka takwaran Manzo domin kuwa alƙawalin Allah gaskiya ne da kansa yace «BA MU SAUKAR DA ALƘUR'ANI BA FA CE DAN YA ZAMO MAKU WARAKA»shi littafin Allah mai Tsarki dukkan sa rahama ne ga al'umma sannan in shaa Allah cutar kamar gobe za ka samu lafiya"
Hajiya Atine ta ja tsaki tace "ayi mu gani in tusa na hura wuta,aikin banza aikin wofi yaro ya yaje yayi shaye-shayen sa za'a liƙawa aljannu ina ce kwanaki gangaren Unwala aka samo sa ya na sha wiwi wa ya sani ma har da yaran mutane ya ke ƙwaƙulewa"ta na gama faɗa ba ta ida rufe bakinta ba Ammi ta wanketa da mari daidai nan kuma Alhaji Issufu ya sallamo tare da kunno kai Abbasi na take masa baya.






Hajiya Atine abun nema ya samu daman hakan ta ke so ta faru kawai sai ta ɓare baki ta na kuka,tare da cewa "Ammin Mahomet ni kika mara?daga faɗin gaskiya ?ai shawara na baki ban ce doli sai kin yi aiki da ita ba kuma Allah na gani ba da wata niyya na kira Mahomet mahaukaci ba sai dan takama doli amman ba komi"ta ida maganar ta na sharar ƙwalla tare da ƙoƙarin fita.






Alhaji Issufu wanda fuskarsa tayi ja saboda ɓacin rai yace "Hajiya je zauna"babu muso Atine ta zauna,ya maido dubansa ga Ammi wacce ta ke kallonsa "ke kuma ina son sanin mi tayi maki kika mare ta saboda na ji ƙarar marin balle ki ce sharri tayi maki"babu tsoro ko shakka Ammi tace "eh ƙwarai kuwa na mareta saboda ba zan bari ta tozarta min Ɗa ba tare da yi mashi sharri mafi muni "da sauri Hajiya Atine tace "miye na sharri daga nace jiya Abbasi ke faɗan ciwon Mahomet kamar shafar aljannu shine fah na zo mata da batun Malamin nan da ya yiwa Ramlatu aiki ya fitar da aljannun da suka hanata aure yanzu haka fah an yi auren har da albarkar yara shine Ammin Mahomet ta rufe ni da masifa wai ɗan ta ba MAHAUKACI ba ne da na matsa kawai sai ta kwaɗa min mari"ta ƙarashe ta na fashewa da wani irin kuka kai kace mutuwar uwa ko uba aka shaida mata.






Ammi tsaye tayi ta na kallon Atine ta na mai jinjina ƙarfin makircinta da yadda ta iya drama kai kace ƴar wasar kwaikwayo, Alhaji ya dubi Ammi yace "miye laifinta a nan dan ta nuna maki hanyar alkhairi?zo ki rama marin da tayi maki"da sauri Abbasi ya matso yace "Daddy kar ayi haka tunda ta riga ta faru kawai abar zancen ka yi masu nasiha kawai,kai fah shugaba ne in kace ta rama to wata masifar ce za ka kuma kunnowa sulhu ya kamace ka"
Atine ta miƙe ta na jin wani gululun baƙin ciki dan ta san tunda Abbasi ya saka baki to fah maganar sa Daddy zai ɗauka "Ni na tafi Abbasi ka karɓan abincina tunda dai a tare mu ka yi girkin balle a hana ni"ta faɗa ta na mai ficewa Abbasi ya dube ta da kallon mamaki dan ya san ƙarya ta gilla saboda a part ɗin ta ya barta lokacin da zai tafiya ɗaukar Daddy aéroport.






Kitchen Ammi ta shige dama jus ne ta ke ɗurawa a budo dan ta gama komi.Mahomet wanda tun ɗazu ya kasa yin komi ya kalli Daddy da idonsa da ke nuna zallar tsoro,gajiya da kuma begen mahaifin na sa.Hannuwa Daddy ya buɗe kamar wani ƙaramin yaro ya ƙarasa inda ya ke tsaye tare da faɗawa jikinsa, Daddy ya zagaye bayansa da hannuwansa ya na sake saka sa ƙirjin sa.Sanyayar ajiyar zuciya Mahomet ya fara saukewa ya na jin wata nutsuwa na shigar sa kafin wasu hawayen farin ciki su zubo masa ,a zuci yace "Allah kai ne abun godiya ina sake gode maka bisa ni'imar da ka yi min wacce ba kowa ka baiwa irin ta,ni ɗin na kasance tamkar ruwa da ƙanƙara ne wani gun nayi tauri wani gun kuma da taushi.A baɗini na sani mai lafiya ne kamar kowa amman a zahiri mahaukaci ne ni wanda kai kaɗai ka san miye sirrin da ya ɓoye wanzuwata a ruwa biyu."ƙara rungume mahaifinsa yayi wanda duk duniya bai da kamarsa,saboda sai in ya na tare da shi ne kawai ya ke sanin ainahin shi ɗin wanene ya ke kuma samun nutsuwar yin tunani daidai da na masu cikakken hankali.






"Mu je ka faɗan yanda ka yi kewata"cewar Daddy ya na zame sa daga cikin jikinsa ya zaunar da shi kan salon kafin shi ma ya zauna ya kamo tafukan hannun Mahomet.
Murmurshi yayi ya dubi mahaifin sa yace "Daddyna..."sai kuma yayi shiru ya ɗaga kai ya kalli Abbasi wanda ya ke tsaye rataye da jakar Daddy ya harɗe hannuwa ya na kallon su.Kamar wani ƙaramin yaro Mahomet ya turo baki ya na kallon Abbasi wanda ke masa dariya,wacce kuma ba ta rasa nasaba da yadda sangartar Mahomet ɗin ta motsa.
Daddy ya dubi Abbasi yace "Abbasi ba mu wuri za mu yi magana da farin cikina"Abbasi na dariya ya ajiye jakar ya shiga kitchen ya tarar da Ammi tsaye ta na sharar ƙwalla.A gabanta ya tsaya ya marairaice fuska yace "please Ammi ki yi haƙuri dan Allah ni na san sharri Hajiya tayi maki,dan Allah ki ƙara haƙuri ki bar biye mata "kai kawai Ammi ta jinjina tare da ɗaukar plate ta zuba masa abinci.






A falo kuwa murya ƙasa-ƙasa kamar ta munafuki Mahomet ya fara magana "Daddy nayi kewar ka sosai,a kullum idona su na kan hanya da tsumayen ganin ka,zuciyata ta raunata sai ni ke ganin tamkar in babu kai babu Mahomet wani sa'in kuma sai naji tamkar kai ne innuwata wacce zan raɓa na ji sanyi"shiru Daddy yayi ya na kallon farin cikin na sa don duk duniya babu abinda ya ke so sama da Mahomet in ka fidda Inna ita ma ɗin dan ta kasance uwa mahaifiya gare sa.




Rasa mi zai ce yayi kawai sai ya jawo sa zuwa jikinsa,lamarin Mahomet na basa tsoro sosai haɗi da mamaki.Bayan Daddy babu wanda Mahomet kan iya yin fira da shi tunda wannan cutar ta same sa,in kaji yayi magana to ba mai tsawo ba ce.
Ammi ta fito ta dire tray bisa table tamkar babu abinda ya faru ta tsiyaya lemu ta zuba a cup ta ɗan duƙa kaɗan tace "sannu da zuwa Abbansu fatan kun sauka lafiya?"murmurshi Daddy yayi ya karɓi kofin yayi Bismillah ya fara sha ya na jin sanyi biyu na ratsa zuciyar na farko yadda Ammi ta kasance mace tagari komin suka yi faɗa ba ta hana shi abinci ko kuma haƙin kwanciya,na biyu kuma daɗin ɗanɗanon lemun gami da sanyin sa.
Sai da ya kai rabi sannan ya ɗora kofin a bakin Mahomet ,sannan yace "alhamdullah uwa tagari"Abbasi ya kalli yadda Daddy ke mu'amula da su Ammi ba kamar yadda ya ke yi ba in ya je can part ɗin su wato ɓangaren Hajiya Atine.A zuci yace "baƙin halin Hajiya ya sa haka"a zahiri kuwa cewa yayi "Ammi zan wuce ina abincin Hajiya ɗin?"miƙewa Ammi tayi ta koma kitchen ta zubo masa a kula kafin yayi sallama ya fita.






Tamkar wasu sabbin aure masu ɗan jinjiri haka suka saka Mahomet tsakiya su na cin abinci cike da soyayya da ƙaunar juna.






★★★ *MAI JAN GERO*




Cikin gunguni Maryam tace "Ni fah na gaji da wanke pant da tsumman nan ,sabida Allah kamar wata ƙazama kullum cikin wankin jini"ta ida maganar ta na matse wani ƙyalen atamfa wanda Inna ta bata ta na yin ƙunzugu da shi.
Ta na gama wankan ta fito ta ɗaura alwala kafin ta wuce ɗaki,pant da ƙyalen ta shanya bisa ƙarfen gado sannan ta ɗauki wani busashen ƙyale gami da pant tayi ƙunzugu kamar yadda Inna ta koya mata.
Tapis ta shimfiɗa ta saka hijabi,har ta fara iƙama taji Inna na cewa "au!wai dama ba ki gama jinin ba shine na gan ki ɗazu ki na sallah asubahi?"da sauri Maryam ta juyo ta na kallon Inna wacce ta dawo daga gidan buki.
Rau-rau tayi da ido tace "har yanzu ya na zubowa"Inna tace "shine kuma kike sallah ba tare da kin gama ba?"Maryam ta ɓata fuska tace "in ya na zubowa ba'a yin Sallah?" "Eh mana sai ya ɗauke kin yin wanka tukunna sannan ki koma yin Sallah"
"Shine kuma kika ƙi faɗa min kika bar ni ina ta aikin banza?"cewar Maryam ta na zare hijabi.
Inna tace "ah toh ni na san digin garin wai baƙuwa da tayi kashi cikin moɗa,na zata kin gama ne da na ga kin yin wanka da asuba zan ce ko na tsarki ne kika yi"
Maryam tace "wankan tsarki?"Inna ta ce "ungo dubala da jus in kin canye sai na yi maki bayani"karɓar ledar tayi ta ajiye kan gado tace "a'a yi min yanzu"
Inna ta fara yi mata bayanin daga lokacin da mace ta fara yin jinin haila ta girma kuma in namiji ya taɓata ciki za ta yi,sannan in an gama ana yin wankan tsarki nan dai ta koya mata komi.....








*Ga masu son yin payement ƙofa a buɗe ta ke, 200₦ ƴan Niger 300f duk wacce ta san ba ta shirya saya ba dan Allah kar ta min magana*
+22795045822






Jikar Rabo ce 😎
[07/02 à 12:44] Mrs SADAUKI 💫: *MATAR MAHAUKACI*🙆🏻‍♀️
```Destiny
Love
and
Romantic story```


Dedicated to *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR* 🇳🇪 ina alfahari da ƙasa ta✊🏻






*☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*


```MRS SADAUKI 💫✍🏻```


_______________________




Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*




*PAGE* 7-8




Fitowarta daga wanka kenan taji sallamar bakin ƙofa,bokitin ta ajiye ta gyara zaman hijabinta kafin ta leƙa.
A tsaye ya ke hannunsa riƙe da fararen zomaye🐿️ mata da miji,ya na ganinta ya washe baki yace "Mairo ta ai na zata ba za ki fito ba"sai ta ɗan sunne kai tace "ah haba miyasa za ka yi wannan tunanin?" Rabe ya miƙo mata zomayen yace "wlh Mairo sai ni ke ganin kamar Inna ba ta son soyayyar mu da ke shiyasa ni ke jin tsoro"kallon zomayen tayi tace "Ni fah tsoronsu ni ke,ina kuma ka samo su?"yace "sayo su nayi domin ke,kin san yau sallar masoya shine na kawo maki cadeau"har ga Allah Maryam taji daɗi hakan yasa ta miƙa hannu ta damƙi cikin ɗaya da sauri ta saki jin taushi.
Rabe yayi dariya yace "kunnuwa za ki kama saboda Zomo duk jikinsa tsoka ne babu ƙashi"ta ɗan ja da baya tace "to in fah na katse masa kunnuwa ,a'a ni dai gaskiya ba zan iya riƙewa ba"dariya yayi yace "to mu je na kai maki su cikin gida sai na saka maki su cikin akurkin kazar da na baki kafin na kawo kajin"hanya ta basa ya shigo ya saka su cikin keji wanda ainahi dama shi ya kawo shi da yayi mata alƙawarin kaji sama da shekara ɗaya kullum yau gobe zai kawo.






Ya na saka su ya rufe yace "zuwa an jima zan kawo maki karas da salati sai ki basu"Maryam tayi murmurshi tace "na gode sosai matuƙa Allah bar zumunci"Rabe har ya washe baki jin ƙarshen furucinta yasa ya gimtse yace "zumunci kuma Mairo?ko har yanzu ba ki fara sona ba?"
Ƙofar shiga ɗaki ta nufa ta na mai cewa "yanzu dai sai an jima kar Inna ta tarar da kai ka sa ta doke ni"ba don ran Rabe ya so ba ya bar gidan cike da zullumi.




Gefen gado ta zauna ta fara shafa mai ta na mai cewa "ah yo toh ina dalili ka sa ni yin ƙarya sabida Allah a rubuta min zunubi,ban sonka amman ba zan faɗa ma ba kar ran ka ya ɓace amman nan da ɗan lokaci zan bar ma garin gaba ɗaya Allah dai ya bani BEPC ina samu zan koma gidan Kawu Issufu"ta na gama shafa mai ta saka kayanta ta haye gado ta fara tunanin rayuwar da za ta yi a Maradi.
"Ko yaya zan kuma kasancewa?an ce jarabatu bai da lafiya yanzu ƙila ba zai takura ni ba mtws da wasu ido na sa irin na kwartaye"Maryam ke sambatu ita ɗaya sai kuma ta bushe da dariya tace "oh Maryam ko ina kika taɓa ganin idon kwarto?"sai kuma tayi shiru ta na tunani "kamar dai irin na Mahomet masu shegen kaifi sai yayi ta kallon mutane kamar maye"ta faɗa ta na mai lumshe ido.








★★★ *MARADI VILLE*




Alhaji Issufu wato Daddy shine hakimce bisa kujera ta alfarma ya na latsa waya yayinda matan sa su ke zaune ɗaya waje suna jiran jin abinda yasa ya kira su.
Sai da ya ɗauki lokaci ya na aiki da wayar kafin ya ajiye ya dube su cikin bada umarni yace "an kammala gida an yi komi zan turawa

2 / 19