Author : Maman Khadija Category : Hausa Novels 001
[2/26, 4:57 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: DR. AHMAD*
1
*NA MAMAN KHADIJA.*♀
*HASKE WRITERS ASSO.*
(Home of expert & perfect writer's)
Kusan a jiga ce ya shigo gidan idanun shi duk sunyi ja sabida masifar tafiyar daya shawo
fatan shi kawai ya jishi yana watsama jikin shi ruwan sanyi, "Assalamu alaikum." ya furta cikin
siririyar muryarshi.
"Wa'alaikumussala na Maman shi ka dawo kenan, sannu da zuwa kawo jakar in ta yaka d'auka
kaji Allah yayi maka albarka insha Allahu wataran za kayi alfahari da wannan wahalar da kake
sha kaji?"
Cikin jin dad'i ya mika mata jakar littatafan sannan ya d'auki bokitin ruwan dake cike wanda
dama ya san nashine kullum ya kan dawo ya tadda ruwan wankan shi Mama ta zuba ta ajiye
mai. Ya jima yana wankan sannan ya fito kallon d'aya zakai mishi kasan cewa yanzu ya dawo
hayyacin shi ba kamar d'azu daya shigo ba.
Saida ya shiga d'akin shi ya gama shirin shi sannan ya nufi d'akin mahaifiyar tashi cikin shi nata
kukan yinwa. gaida ta yayi sannan ya amshi samirar da take miko mishi ya faracin shinkafa
damai da yajin dake cikinta, kamin yace
"Mama ina aminu yayine naji banji motsin shi ba?"
Tace "iko yanzu khadija tazo nemanshi wai Maman ta zata aike shi."
"Babana ya karatun naka ina fatan lafiya lau ko?"
"Alhamdulillah wallahi mun kusa shiga aji shidda ai ni sonake kawai inganni cikin jami'a Mama."
"karka damu na Maman shi insha Allah kamar yaune kai-dai kaci gaba da maida hankali domin
zaka zama duk abinda kakeso a rayuwa idan har ka dage."
"Mama bari in d'an kwanta kamin la'asar saina leka wajan d'inkin."
gadon shi ya haye wanda yaci gadon shi bayan mituwar mahaifinshi babu wata katifar kirki
ammafa yaji gyara domin saika rantse ba kwana akeyi kanshi ba. tabbas bacci yaso yayi
idanunshi cike suke da bacci da gajiya saida yana hawo godon yajishi cikin wata irin
matsananciyar bukatar mace, nan da nan ya fara juye- juye jikin shi yai wani iri cikin kasala ya
tashi ya koma kan dardumar shi dake k'asa shimfid'e ya kwanta tare da dukunkune jikin shi
waje d'aya. Tun yana jin wani mugun sanyi har ya samu da temakon addu'o,in da ya keyi wani
barci yayi gaba dashi.
Saida ya kuma watsa ruwa sannan yafice masallaci bayan ya gayawa Maman shi cewa zai
wuce wajan d'inki daga masallaci domin Ahmad ya kan yi d'in kuna awani shagon abokinshi
dake cikin unguwar aduk lokacin da ya dawo makarantar boko.
********
"Kai babana idan ka gama sharar ka bar wanke bayin nayi idan nagama abinda na keyi
kajiko? kai maza kazo ka karya ka tafi kadda ka makara kasan dai tafiyar dake gabanka ko?"
"Mama ki bari na gama miki kuma ni azumi na keyi yau, kai Aminu zoka amshi kud'in tara ka
wuce."
kusan da mamaki take kallonshi bayan ta isa gaban shi tace "kai babana bani son sakarci yau
yaushe?"
Sadda kanshi k'asa yayi kamin yace "Mama yau laraba."
"To me yasa ka tashi da azumi yau tunda kasan alhamis da litinin kawai na amince kayi azumi
iye?" kiyi hakuri Mama bawai nasab'a umarninki hakan nanba wallahi ba haka bane kawa gani
nayi azumin shine mafita agareni shi yasa na tashi dashi amma kiyi hakuri bazan Kara ba."
Jinjina kanta tayi sannan tabar wajan zuciyarta cike da tausayin yaron nata ammadai ta d'auki
alwashin jin damuwarshi yau idan ya dawo daga makaranta domin ba taso wata lalura ta
kamashi.
Cikin biyayya ya duka ya amshi kud'in kamin yace "yayana nagode Allah yasaka maka da
Alkhairi kuma jiya aunty khadija tace tana gaida ka." cewar Aminu kanin Ahmad wanda ke
sanye da kayan primary na gwamnati.
murmushi Ahmad d'in yayi kamin yace to madallah ina amsawa kai maza katafi kaji ko banda
wasa me kakeso in siyo maka idan zan dawo? "Aminu ya washe gibin dake bakin shi daya ke
yafara famfara kamin yace "yaya alawa me tsinke."
Dariya Ahmad d'in yayi kamin yace "to wawulo sai naga idan kayi karatu sosai sannan nikuma
zanyo maka tsaraba."
"Babana baza kazo ka tafi ba ka biye ma Aminu da surutin shi ko?" cewar Mama daga cikin
d'akin ta domin tana jin duk maganar da su keyi.
*****
Lafiya lau yaje ya dawo babu wani damuwa cikin ranshi fatanshi arayuwa be wuce yaga ya
zama wani abuba kodan dangin mahaifinshi wa inda kullun burunsu be wuce ganinshi
awukance ba.
Suna zaune suna tattauna halin rayuwa bayan gama cin abincin su na dare yayin da Aminu tuni
ya bingire ajikin Ahmad d'in yana barcinshi sabida shi indai cikin shi ya cika to babu abinda ke
biyo baya sai bacci.
cikin nutsuwa ta kalleshi kamin tace "babana ina son kabani duk nutsuwarka anan yanzu sabida
bani son ka boyemin damuwarka domin duk duniya baka da kamata kanaji ko? sabida haka ka
gayamin banda karatu menene damuwarka??"
marairaicewa yayi kamin ya kalleta sai kuma ya kuma sadda kanshi k'asa yana wasa da dogon
hancin aminu wanda keta bacci abinshi.
"Ina jinka babana
a hankali kamar me rad'a ya furta kiyi hakuri Mama wallahi aure nake bukata wallahi nayi bakin
kokarin ya kice tunanin araina kodan karatuna sannan ba wani karfine da muba amma na kasa
shi yasa nake ya waita yin azumin.....
_TIRK'ASHI......_
*MAMAN KHADIJA*♀
[2/26, 4:57 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: DR.AHMAD*
2
*NA MAMAN KHADIJA.*♀
Edit by *Hajja ce*
*HASKE WRITERS ASSO.*
(Home of expert & perfect writer's)
Wata irin zufa ce taji ta fara karyo mata lokaci guda tunanin mahaifin shine ya taso mata
idanunta ta zuba mishi tana karantar duk wani yanayin daya ke ciki kamin ta sauke ajiyar zuciya
tace,
"Babana tun yaushe kake son auren?"
kanshi a k'asa yace "tun shekaru biyu da suka wuce Mama na rasa yadda zanyi dan Allah
Mama ki temakeni."
Lissafin shekarunshi ta fara yi inda lissafinta ya nunamata yanzu yana shekara ta cikin goma
shabakwai.
"To tashi kaje ka kwantar dashi kaima sai ka kwanta da safe za muyi magana."
A sanyaye ya kai Aminu kan shimfid'arshi kamin ya bar d'akin yana cike da tausayin mahaifiyar
tashi dan yasan ba k'aramin tashin hankali yasa ta ba.
kusan kwana yayi yana gayama Allah damuwar shi duk da cewa shi Allah masani ne abisa
dukkan komai na fili dana b'oye, amma yana so ka kwantar da kanka gareshi ka kai kukanka
gareshi bawai dan be san halin da kake ciki ba. yaso ya kuma tashi da azumi sai dai sam baya
san damuwar Maman tashi domin ita gani ta keyi kamar cutar yunwa zata iya kamashi.
kanshi a k'asa yake gaidata bayan dawowarshi masallaci kamin yace "Mama me zan dora
yanzun?" d'an murmushi tayi kamin tace "ah'ah babana so nake zaka huta yau."
Murushi kawai yayi har lokacin be kalleta ba domin samun kanshi yayi da wata irin kunyarta, jin
yayi shiru ya sata cewa "taliyar murje zaka dafa mana yau saika zabi kalar wacce kakeso ta
manja kota mangyad'a kayi mana akwai komai na bukata na ajiye cikin kitchen."
Gidan ya fara gyarawa kamar yadda ya saba kamin ya d'ora girkin yana yi yana bin sautin
karatun Alqur'ani a cikin wayarshi k'aramar nokia a gidan wani Redio da akasan ya.
Yana ta zullumin zatai mishi magana sai yaga sab'anin hakan domin har yayi mata sallamar
tafiya makaranta beji tace mai komai ba.
Bayan tafiyar su makarnta ne ya sata d'ora tuwon masara wanda ta juyeshi cikin kulla sannan
miyar ma haka, shiri tayi cikin riga da zani na atamfa da dogon hijabinta sannan ta rufe gidan ta
nufi gidan aminiyarta kuma matar aminin mahaifin su Ahmad gida hudune kawai tsakanin su.
Murna kamar zasu cinye junansu kai kace watanni suka d'auka basu had'u ba. Bayan sun
gaisane Maman Ahmad tace "uhum Maman khadija nifa tafe nake da magana bakina Allah
yasa malam yana nan yanzu?"
Maman khadija tace "aiko yana nan sabida yanzu ya dawo daga gidan gaisuwar malam iliya,
wanka ya keyi yanzu Allah yasa dai lafiya?"
Mama khadija ta tambaya cikin jimami "To bari dai malam d'in yazo kyaji yaron kun wallahi ke
son d'auko min magana..!!!"
Saida malam Mamuda ya gama shirin shi cikin d'akin shi sannnan ya taddasu sunata hirarsu.
Bayan sungaisa ne yake tambayarta lafiya ko Maman Ahmad?
Tace "Eh to malam dama akan babana ne."
Malam Mamuda ya gyara tsayuwa tare da cewa "To to naji dai ina jinki ainasan Ahmad beda
wata illa arayuwa kuma insha Allah bamafatan yasa meta nan gaba meya faru dashi d'in?
Tayi shiru ita kanta maganar nauyi take mata tajima cikin yin shiru sannan tace "Tun watan nin
baya naga ya dage da yin azumi kusan kullun to shine naimishi fad'a sosai sabida ina gudun
kadda cutar yunwa ta kamashi (olsa) toh kuma dai be dena ba tun yana yi alhamis da litini duk
sati sai naga yanzu duk sanda yaga dama yi yake, to jiya na turke shi da tambaya shine yace
min wai bukatar aure ke damunshi to nikuma naga babana duka nawa yake da zai san wannan
abin shine nace bari nazo naimaka magana ko zaka ganar dashi ya bari sai nan gaba karya ja
mana surutun mutane."
Malam Mamuda ya ajiye asuwakin shi gefe kamin yace "ikon Allah to Alhamdulillahi tabbas
wannan lamari dole mugode ma Allah domin Ahmad yana da nutsuwa sosai kuma tunda ya
nuna yana so to insha Allah baza mu tauyeshi ba domin gashi yana da kokarin ganin ya kare
kanshi daga sab'awa Allah ta hanyar yin azumi, dan haka dole mu samami shi mafita tun kamin
abun yafi karfin shi a zo ana da ansa ni."
"Maganar karatu kuma wannan babu abinda zai gagara insha Allah zai kai duk matakin da ya
keso ya kai." cikin farin ciki Maman khadija tace "kin ga shike nan sai mu aura mishi kanwarshi
khadija hankalin mu kwance ko malam?"
Shima cikin farin ciki yace "Nima tinanin da nayi kenan sabida haka gobe kije ki shaidama
dangin mahaifin shi sabida afita hakkinsu sannan ki shaida mishi cewa yazo su gaisa da kanwar
tashi Allah yayi mana jagoranci cikin lamarin."
Tsabar farin ciki yasa Maman Ahmad sakar musu kuka domin tabbas wa innan mutane sun cika
mutane sannan kuma sun rike amanar zumunci da sanin hakkin makotaka.
Da kyar suka lallashe ta sannan tayi musu sallama.
sai kuma zullumin yanda dangin mijin nata zasu amsheta idan ta je musu da zancen. A hanya
ta had'u da khadija tun daga nesa take karema yarinyar kallo lokaci guda ta kalli kirjinta babu
komai na daga dukiyar kirjin kai daka ganta kasan yarinya ce sharaf innalillahi ta furta kamin ta
kauda tunaninta akan abun tana amsa gaisuwarta tace "Mama zanzo na tayaki hira yau tun da
babu islamiyya."
Cikin jin dad'i Maman tace "To d'iya ta dama gashi yau mutuminki nayi da ranarnan tuwo sai
kinzo sai kici ki koshi."
"To mama sai nazo wanka da salla kawai zanyo in taho gidan ki......"
[2/26, 4:57 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: DR.AHMAD*
3
*NA MAMAN KHADIJA*♀
Edit by *Hajja ce*
*HASKE WRITERS ASSO.*
(Home of expert & perfect writer's)
Da sallama ta shiga gidan nata sannan ta d'auki buta bayan ta rataye hijabinta akan kyauren
kofarta har yanzu mamakin irin k'irkin mutanen take yi tabbas sun jima suna yi mata halacci
tana fatan itama Allah ya bata ikon ganin ta kyautata musu kamar yadda suma koda yashe
burunsu suga hankalin ta ya kwanta.
Ta jima cikin sujjadarta ta karshe da kyawawan adduo'i ga mijinta da iyayenta sannan ya ranta
guda biyu kacal wanda Allah ya azurtata dasu. Tun kamin ta gama lazumin da ta keyi Aminu
yayi sallama hankalin shi nakan kulolin abincin dake ajiye kowa dai ya san yanda ake dawowa
makaranta da yunwa da kyar ya zare takalman sandal d'in dake kafafunshi ya zauna sai kallon
Maman tashi yake da alama jira yake kawai yaga ta mike ko tayi mai nuni tace ya d'auka.
"Mama ki tashi ki zuba min yunwa zata kasheni." dariya tayi kamin tace "Toh rago kai kam
Aminu baka wasa da cikinka ba kamar yayan kaba kaje ka wanko hannu kamin nan na zuba
maka."
Yanaci tana kallon shi sosai take ganin kamar da yayi da ita bakamar Ahmad ba wanda yake
kallo d'aya zakai mishi ka gane agwai ne.
Sai wajan biyu da rabi sannan ahmad ya shigo gidan kai tsaye d'akin shi ya shige sai da ya
kwale kayan jikin shi sannan ya nufi d'akin Maman, "Mama sannu da gida na dawo."
"Yauwa babana sannu da dawowa ga ruwan wankan ka can ka farayi saika zo kaci abinci."
Saida yayo wankan ya kintsa sannan ya nufi d'akin nan ya tadda Aminu zaune yana kallon tv.
Gaishe ta yayi sannan ya zauna shima yaci tuwon hankalin shi kwance lokaci zuwa lokaci yana
kallon Maman tashi sabida yaga sai murmushi ta keyi.
"Mama ki gaya min mana ta samu ne naga kina tayi min murmushi?"
dariya tayi kamin tace "kawai dai ina cikin nishad'i ne sabida yarona zai ajiye iyali."
Kusan da gudu yabar d'akin yana dariya kamin ta bud'e miryarta itama tace "kaje babanku na
kira idan ka huta...!!"
Saida yaji anfara kiran sallar la'asar sannan ya tashi kayan ya saka sannan ya fito waje dan
d'aura alwala.
Da khadija ya fara cin karo cikin doguwar riga ta material tayi kyau sosai tayi acuci da gashinta
Aminu take yan kema farcen shi sabida ta fishi wayo da dabara tana ganin shi tace.
"Lhha ya Ahmad sannu da tashi tun d'azu nazo Mama tace bacci kake yi ina yini?"
Murmushi yayi kamin ya amsa da "lafiya lau ya makaranta?" Murmushi kawai tayi wucewa yayi
yana mamakin rashin maganarta wani lokacin yana k'okarin fita yace.
"kuce ma Mama na fita masallaci Aminu naga ta fara sallah."
A dawo lafiya su kayi mishi sannan ya fice.
A masallaci suka had'u da malam Mamuda ganin irin kallon da yake bin shi da shi ne ya sashi
jikin shi yin mugun sanyi domin yana jin mutumin kamar mahaifinshi tabbas idan be yarda da
bukatarshi ta aureba to zai hakura yaci gaba da danne abinda ke taso mishi.
Hannun Ahmad malam Mamuda ya rike a haka har sai da suka je gidan shi sannan ya tsayar
dashi a zaure. Lokacin jikin shi harya fara rawa sabida be san me zai faruba.
"Ka kwantar da hankalinka Ahmad insha Allah zan tsayamaka akan duk abunda kake so
matukar be sab'ama shari'aba d'azu Mamanka tazo min da sakonka shine nace me zai hana ku
dai-daita da kanwarka duk da dai tayi kan kanta da yawa ammadai nasan zata iya ragemaka
wani abun sannan kuma kaga kaima kayi yarinta da yawa yanzu duk gun wanda naje
nemamaka auren abin ma surutu zai zama koba haka ba?"
Cikin wani mugun jin nauyi jikin shi na rawa zuciyar shi na bugawa yace "haka ne baba." Malam
Mamuda ya gyra tsayuwa kamin ya fara yi mai nasiha sosai, Ahmad ya d'ora dayi mishi godiya
kamar bakin shi zai sakko k'asa.
"kadda ka damu Ahmad ni mahaifinka ne zan yi komai dan farin cikinka, yanzu zaka iya hakuri
har karshen shekara kokuwa kana ganin a d'aura auren alabashi daga baya idan angama
gyaran inda zaku zauna sai kawai ku tare?"
Shi dai Ahmad shiru yayi sai yatsun shi daya keta faman murza. murmushi malam Mamuda yayi
kamin yace "to tashi kaje zamu yi magana da Maman ka Allah yayi maka albarka ya kuma k'ara
tsareka ka jika ko? Allah yaji kan mahaifinka."
Tsabar kunya ta hana shi karasawa cikin gidan ya gaishe da Maman khadija d'in a kunya ce
yabar zauren, yayin da malam Mamuda ya bishi da kallon kauna yana murmushi tare da
godema Allah da samun siriki kamar Ahmad.(sai kace wani babba)
******
Dafaffar gyad'a ya gani a hanya ya tsaya ya siya sannan ya nufi gidan su yana mejin kunyar
ganin khadijan.
Yajima tsaye yana kare mata kallo tun daga yatsun kafarta har zuwa gashin kanta tallabe
kumatun shi yayi da hannu d'aya yana tunanin shiko me zaiji ajikin khadija wadda da alama ko
kirgen dangima kila bata faraba shida ya kejin bukatar kasan cewa da mace.
_Abin da dariya koshi Ahmad d'in nawa yake da har yake raina wani.?_
Saida ya gaji da tsayuwa sannan yayi sallama ya shiga gidan sannun sukai mishi sannu shi
kuma kai tsaye ya wuce d'akin Mama da ledar a hannunshi.
Zama yayi tare da furta "washhhhh Allah na....!"
kallon shi tayi kamin tace "sannu daga ina haka?" Yace,
"Mama wajan baba naje munyi magana dashi amma kuma yayi min maganar khadija Mama me
zanji ajikin khadija dan Allah haba...?" idasa maganar yayi cike da yarinta da shagwab'a tare da
nuna shifa babba yake SO. kauda kanta tayi ga barin kallon shi kamin tace "kayi hakuri da ita
itama babu abinda ba zata iyaba indai ka lallab'ata kuma ka bata kulawa, gobe insha Allah
zanje tsaranci in gayama dangin babanka."
Gyadar ya juye a kasa ba tare daya kula da maganar data yiba ya faraci itama faraci