Chapter 3 Reading Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf Arewa Novels

Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf

Author :  Fadila Lamido Category :  Hausa Novels 001

Chapter   3 / 16

6K to 9K   out of 47.9K words

ce.

yaran masu kudi ne ke zuwa gun safna duk da cewa SS 2 safna take ayanzun amma ita
ummi barin ta kudi.

yauma kamar kulum safna na zaune ita dawani saurayin ta a harabar gidan ,halal ya
faka motar sa bayan yafito yakalli gurin da su safna ke zaune, sultan ya gani zaune agefe sai
dai yarinyar be gane ko wacece ba amma fah Allah yayi halitta agurin nan, azuciyar shi yake
tunani me ya kawo sultan da budurwar sa tadi gidan su, inda wani shashi na zuciyar shi kecewa
Ina ma ace ya mallake yarinyar nan, dawan nan tunani ya shiga gida, yana shiga ya samu
ummi zaune a falo , zuwa yayi ya kwanta ajikin ta.
ummi tace yaya dai yaro, lfy naga jikin ka a sanyaye?
ummi wata yarinya nagani ita da sultan awaje.
murmushi ummi tayi tace jalal safna ce baka gane ba.
jalal tashi yayi ya zauna yace ummi kina nufin safna ce ke tadi da sultan?

ita ce mana ai safnar tamu ta waye sultan ya rikice akanta, ummi bata gama fadan
maganar bakin taba taga jalal ya mike cikin fusatan da bata taba ganin shi cikin saba, itama
mikewa tayi tana fadin me ya tada maka hankali ne jalal.
waje yayi da sauri ummi bayan sa tabi tana kiran jalal jalal.
amman ina besan ma tayi ba sai da ya isa gurin ya kare mata kallo riga da wando ne jikinta
sun kamata sosai tabas kamanin ta basu bace masa ba, cikin fada yace da sultan malam tashi
ka fita agidan nan.
sultan cike da mamaki yace ban gane na fitaba ai ba gurinka nazo ba.
eh koma gurin wa kazo karna kara ganin ka gidan nan, cikin tsawa yace ke tashi kishiga gida.
cikin sauri tamike zata bar wajen, sultan ya tashi ya rike safna yana fadin babu inda zata sai
mungama maganar da muke.

duk abinda suke ummi na daga kofa tana kallon su, jalal ji yayi ya kara kulewa waton
sultan ya saba rike safna kenan, jalal jiki na rawa ya fara kaiwa sultan naushi
[7:41PM, 11/26/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜


Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed

16-18


ummi karasowa tayi da gudu ta rike jalal tana fadin jalal baka da han kaline ,me yayi maka, da
ker ummi ta janye jalal daga jikin sultan, hancin sa har ya fara fitar da jini.

ummi matsawa tayi kusa da sultan tace sultan jeka gida zan zo na same mamar ka, yace
ummi amman dai kin ga abinda yayi min ko?
na gani kuma zanyi maganin sa, ka kwantar da hankalin ka.
sultan girgiza kai kawai yayi, ya shiga motar sa yabar wajen.

Jalal na tsaye sai huce yake yi , safna kuwa dama tun da taga fada ya kaure ta ruga da gudu
ta shiga gida

ummi ce ta juyo ta kalli jalal dake tsaye ban da huce babu abin da yake yi, tace muje ciki,
gaba ya shi ga ummi nabin sa a baya.

suna shiga ummi tace me kake nufi da kake koran ma safna saurayi.
sai da ya dukar dakai sannan yace ba abin da nake nufi ummi kawai tarbiyan da akama safna
ne ban ji dadin ganin ta ahaka ba, kuma ummi be kamata abarta tana kula samari ba, ummi
sultan fah ba mutumin kirki bane lalata yaran muta ne kawai yake yi.

sai da ummi ta karewa jalal kallo san nan tace, jalal ni fah na haifeka kar ka manta kamin
alkawarin babu aure tsakanin ka da yarinyar nan , to meye naka na tada hankalin ka dan ka
ganta da wani, to bari kaji na fada maka daga yau babu ruwan ka da safna sultan auren ta zai yi
kar na kara ganin kaje kusa da su , inhar kana son azauna lafiya.
amman dai ummi ai be kamata ace za,a mata aure yanzun ba.
babu ruwanka ba abinda ya shafe ka, suna cikin haka suji sallaman hajiya baturiya
mahaifiyar sultan tana rike da hannun sultan, jalal be sauri me zasu ce ba, ya nufi dakin kairat
ya samu safna kwance sai kuka take, ya dade tsaye akanta bata ma san ya shigo ba, sai da ya
kare mata kallo sannan yace safna, da sauri ta dago ta kalleshi. Ya sake cewa safna kina kuka na korar miki saurayi.

gargiza kai tayi tace ba haka bane yaya ni fada ne bana son naga anayi.
Jalal murna ta kama shi ashe dai tana da hankali.
yace safna daga yau karki kara zuwa gurin sultan , ba auren ki zaiyi ba kamar yadda ummi take
fada, in na kara ganinki da sultan ranki zai baci, ya sake kwantar da murya yace ko kina son
sultan din ne?

Shiru tayi, tayi kasa da kai dan jalal ya mata kwar jini da yawa, dan gani tayi ya kara mata
kyau duk wanda tayi dace ta samu jalal a matsayin miji ta more.
Jalal sake maimaita tambayan sa yayi safna nace ko kina son sultan din ne.
kanta akasa tace ni dama ummi ce take tura ni.
dadi yaji sosai ban da shi akwai wasu da ke zuwa gurinki ne? eh tace dashi.

to daga yau koma wanene yazo karki Kara fita, kuma safna me yasa kike fita waje a haka, har
ki zauna kina hira da wani dubi jikin ki fah duk awaje yake, kanki ko dan kwali babu, haba safna
sai kace ba yar musulmai ba, baki da hijjab ne ko gyale.

safna ta kalli jikinta gaskiya jalal ya fada kwata kwata be tace ba, tace ina dashi yaya amman
ummi tace na dai na sanya hijjab idan zan fita.

Jalal shiru yayi nadan wani lokaci san nan yace karki kara saka irin wadan nan kayan, mijin
kine kawai ya kamata ya ganki da su, kuma inzaki fita ki sanya hijjab ko gyale , kinji ko?

juyawa yayi zai fita safna ta bishi da kallo har ya kule.
lokacin da jalal ya fito ummi kadai ya samu a falon dan haka besan me suka shirya ba,
zuwa yayi ya wuce ummi da sauri ya shiga dakin sa,
ummi binshi tayi da kallo ta mike ta shiga dakin safna, wani mugun kallo ta mata sannan tace
jalal nan ya shigo?
eh.
me yace miki?
cikin in ina tace ba komi.
saukan mari taji a fuskar ta ke dan ubanki ni zaki ma karya zaki gayamin ko sai na miki illa.
safna tana kuka tace cewa yayi karna kara fita gurin wani.

Lallai kuwa ashe ba zaman lafiya kinzo har gida zaki rabani da dana, to baki isa ba

Bayan kwana uku da yin haka jalal yasa ma safna ido sosai dan yanzun yana zama agida
sosai .
yau ko ya kula ummi shirye shiryen fita takeyi, ya name guri ya zauna afalo duk da cewa
ummi fushi take dashi, ba kamar da ba.

kalon shi tayi taga bashi da niyar tashi tace yau bazaka fita bane?
zan fita amman sai an jima.
tabe baki tayi ta kira safna tamika mata wata leda tace kaya ne aciki maza ki sa kizo mutafi, ta
karba ta juya.
jalal ko jira yake yoga wani irin kaya ne.
ummi ta gaji da jira, ta sake daga murya tace wai me kikeyi har yanzun.
cikin sauri tace ummi ganinan zuwa ta kara kasa da murya ummi yaya jalal fah yace na daina
yawo a haka.

ummi tsaki tayi, ki fito kina bata min lokaci, ta mike ta fita, jalal na zaune saiga safna ta fito ta
matse riga da wando ne jikin ta sai wani dan kamin gyale, a tsorace ta wuce shi ya bita da kallo,
har ta fita yaga bazai iya jurewa ba ya mike yabi bayan su
Lokacin tuni ummi ta shiga cikin mota,itako safna kokarin shiga take, jalal yace safna karki
sake ki shiga cikin motar nan.
cikin fada ummi tace wai kai jalal Ina wasa dakai ne ko ni abokiyar wasan ka ce,
ummi wlh safna bazata fita tsirara ba
[8:04PM, 11/27/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜

Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊
19-21


Bude murfin motar tayi ta fito, ta zagayo ta rike safna tana tura ta cikin motar, jalal ma riketa
yayi yace ummi ki dai na irin wannan babu kyau fah, cikin tamke fuska tace sake ta jalal idai ba
kana son ranka ya baci bane.
ummi dan Allah kibari ,ta canxa kaya sai ku tafi.

zuwa tayi gaban shi tace wlh wlh in baka sake yarinyar nan ba ranka zaiyi mummunan baci,
kasake ta kawai.
dukar dakai yayi ya kara rike gefen rigar safna ciki tashin hankali ya dago ya kalli ummi ya
sake dukar da kai.
Safna na tsaye tsakiyar su tayi tsuro tsuro, ummi ta sake cewa ba dakai nake magana ba,
gani tayi ko motsi ba yayi dan haka ta taho gadan gadan ta kwashe shi da mari.

da sauri jalal ya saki safna ya dafe wajen dan shi atunani shi babu wanda ya taba dukan
shi.

jalal kallon ummi yayi cike da mamaki, yace ummi nine fah, jalal dinki ne fah.
ummi bata saurari me jalal yake fada ba ta tura safna mota suka bar wajen.
binsu yayi da kallo yana bakin cikin wai mahaifiyar shice take wannan dabi,a wai yaushe
ummi ta canza , shi dai yasan ummi na son farin cikin shi.

Yana nan tsaye drive ya dawo da kairat daga makaranta, tana fitowa ta hango jalal da gudu
ta karaso ta rikeshi, gani hawaye tayi yana bin kuncin sa tace yaya waye ya dake ka.

Jalal da besan hawaye na fita ba yasa hanu ya shafa idon sa yace idona ne yake ciwo,
riko hannuta yayi suka shiga gida, kairat taso ta bishi dakinsa yace mata bacci yake ji.

tunda jalal ya shiga daki yasa key, yau dau ki waya ya kira mahaifin sa har ta katse be
dauka ba, ya ajiye wayar ya kwanta ,da matsa nan cin bacin rai yau da ummi ba mahaifiyar shi
bace da sai ya dauki mumunan mataki akanta, shi bema san me yake damun saba illa dai
kawai yasan yana matukar kishin safna wanda ko mace yar uwanta baya son yaga ta cika
kallon ta da yawa, bare kuma na miji.

su ummi basu dawo ba sai wajan 9:00 shiko jalal tun yamma zazzabi ya rufe shi dan ko

sallah ma a daki yayi ta.

ummi na shigowa hara bar gidan taga motar alhj tace wai nikam me yasa alhj yake min
haka, inzai dawo bazai sanar dani ba saidai na ganshi kwatsam.

da sauri ta fito safna ma ta fito ummi tace ke dakata duba cikin ledan cen ki dau hijjab ki
sanya, safna ta juya ta dauko wani zumbulelen hijjab har kasa ta sanya.

suna shiga alhj na zaune afalo ya rufeta da fada, kwantar da kai tayi tai ta bashi hakuri,
safna kuwa sumi sumi ta shige daki.

sai da yagama zazzaga bata sannan yace ina abduljalal tare kuka fita?
a,a mun barshi gida.
toh ina yaje kuma sunce kwata kwata yau beje office ba wai me yasa yaron nan yanzun duk
yabi ya rikice ne, shifa ya matsa sai na bude mai kamfani kuma dan me yanzun zai sanya wasa,
dazun nakira shi wayar shi kashe take, wai me yaron nan yake nufi ne.

ummi tace haba alhaji sai faman fada kakeyi kayi hakuri duk ma inda yake nasan hankalin
sa na gida.


*********

barin zancen sukayi suka kama wata hirar, kairat ce ta fito tana dari daddy daman kadawo shine
baka kirani ba.

cikin murmushi ya rike ta yace kairat na rude ne har yanzun abduljalal be tadawo gida
gashi wayar shi kashe take.
cikin sauri tace daddy dazunfa an daki yaya jalal a office din su yana ta kuku, amman sai
yayi min wayau yace wai idon shi ke ciwo kuma yaki bari na bishi daki wai shi barci yake ji, cikin
shagwaba ta karasa zance ta.

ummi kuwa
Cikin ta kara ya fara dan bata zaci zai dau abin da zafi haka ba.
alhj ko kallon ummi beyi ba yatashi ya nufi dakin jalal ya tura kofar yajita kulle , juyowa yayi ya
kira ummi yaron nanfah bashi gidan nan, cikin rudewa tazo ta wuce alhj ta isa kofar ta fara Kira
yaro yaro shiru, jalal jalal nanma shiru kuka ta saka tana fadin nashiga uku, alhj ya daga murya
yace abduljalal, da sauri ya amsa na am daddy.
yace zoka bade min kofa.

yana rawan sanyi yazo ya bude kofar rige rige suka fara kowa na kokarin kai hannun shi jikin
jalal komawa gado yayi ya kwanta .

alhj ya dafa jalal yace me ya same ka, waye ya tabaka dan waye agarin nan, ka gaya min
waye uban sa.

ummi ce ta kawo hannu zata tabashi, yace daddy kace mata karta tabani daddy kace ta fitan
min adaki.
alhj yace jalal ummin kace fah wai baka cikin hankalin kane.

ina sane daddy cikin hakali na nake kawai bana son ganin ta ne.
tsawa alhaji yayi wa jalal mahaifiyar ta ka kake cewa baka son gani kar na kara jin wannan
kalman abakin ka.

shuru jalal yayi yana kuka kasa kasa ummi na makure jikin bango , alhj ya dago yace to ya
isa dai na kuka sai kace ba namiji ba lallai ummin ka tayi laifi, abduljalal gayamin me ummin ka
tamaka da zafi haka har kake zubar da hawaye.

Jalal juyar da kansa gefe yayi sannan yace daddy ummi nasa safna nayin shigan banza tana
fita waje, kuma nayi magana ummi ta mareni.
mari ? zaliha ke kika mari jalal akan me, alhj mikewa yayi ya daki kirjin shi yace dana kika
Mara



07014197556âœ
[7:59PM, 11/28/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜


Story
&
Written
Fadeela Lamido
MmnYazeed📊




*Gaisuwa zuwa gare ki Faty afreen marubuciyar* 🎾NIDA SOJANA🎾 *bansan taya zan mika
godiyata a gareki ba saidai nace Allah yasa kifi hakaí ½í±í ¼í¿»*


*Jinjina agareki*
*Ummi Ridwan*

*da duk daukacin* *members na* _Precious writer's porum_
*kuna burgeni😘*

22-24

Akan wani dalili kika mare shi ?
ciki sanyi murya ummi tace alhj mun shirya zamu fita da safna har nashiga mota amman

3 / 16