Author : Fatima S Umar Jajira Category : Old Hausa Novels
sosai saita gano tsakanin su.
Izzatu na tafiya, me gadi ya sha ciki da salama.
Amsawa Nafisa ta yi
Ya mi a mata kayan ya ce
"Gashi inji wata, wai kin siyi kaya kunta."
Tana ansa ta duba ta ce
"Eh kayana ne na siya, zaka iya ta fiya."
Tashi ya yi yana cewa
"To Hajiya a huta lafiya."
Itadai Nafisa tabayi magana ba, sai bu e ledar da ta yi.
Kayane less masu kyau, sai wani abu a jakar.
Waya ta ako, ta kira Izzatu.
"Hello, naga kaya na mene?"
Daga can Izzatu ta ce
"Kaya na wane, abunda ke jarka kuma jini ne."
"Me? Mezanyi dashi kuma?"
"Dashi zamuyi anfani ki baro gidan, arin ciki zakiyi na bogi."
Mamaki ne ya kama, Nafisa ka fin ta ce.
"Idan ya kira Nasir fa?"
"Bazai same shi ba."
"Sabuda me?"
"Sabuda kema ba samunsa kike ba."
Kai ta gyada cike da gamsuwa ta ce yanzu ya zanyi, nan Izzatu ta labarta mata yadda zasuyi, sukayi salama ta kashe wayar.
Bayan minti 20 da yin haka, Nafisa ta fito daga aki da gyar tana nishi.
Anwar dake kan kujera ya taho gurinta yana cewa
"Ummi meyake damunki?"
Cikin wahala ta ce
"Kiramun Sada (Megadi)."
Da sauri ya fice, ya kira Sada.
Tare suka shigo falon da Anwar, ya fa a jikin Ummin tasa yana kuka ganin yadda taketa zubar da jini.
Hankalin Sada a tashe ya ce
"Sannu Hajiya, dama baki da lafiya?"
Tana juya kai ta ce
"Ina tunanin ari zanyi, ka ako waya ta, zakaga number kanwata Izzatu, ka kiratu muje Hospital."
Ta arasa maganar tana nishi da arfi.
Hankalin Sada ne ya ara tashi ya ce
"Bari na kira Alhaji na sanar dashi."
Da sauri Nafisa ta ce
"Aa karabu dashi tunda baya nan, ka taimaka mun zanmutu."
Ta cigaba da murkususu.
Koda Sada ya ga haka sai ya fala lalubar number Alhaji Nasir.
Zagaye suke da matar a kusa dasu ida nuwanta sun koma blue colour ta kalli Nasir, da wata irin murya ta ce
"Lalai ka aikata mumunan laifi kuma sai dodo ya hukunta ka, ita kuma yariyar da kake batu ta gudu, zata kawo kanta har cikin gidan nan, sai muyi abunda muke so muyi cikin sauki dan ya zama dole wannan aikin ko duk ta shafemu."
Shiru duk sukayi shi kuwa Nasir kansa yana asa ya kasa magana.
Wata kwarya ce ta bayana a gabanta, ta ce
"Kallo nan."
Nasir ya kalli cikin kwaryar.
Khadija ce zaune a tsakar gidan su Yusuf tayi tagumi.
"Khadija!.
Matar ta kira sunanta, a firgice Khadija ta kallo su.
" Khadija! Kizo nan yanzu."
Ko gama rufe baki batayi ba, Khadija ta taso da sauri ta ta fito ko takalimi babu............
Sharhi ko arin haske 08166077167
Comments
And
Share
By
*Zahara*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 15
Ba kowa a tsakar gidan, dan haka ba wanda ya ga fitar ta.
Sada yai ta kiran layin Nasir amma a kashe, ga Nafisa kwance male-male cikin jini, tana faman murkusu da rike ciki.
Bashi da za i ila yai abunda ta ce, dan haka ya ako wayar tata ya kira Izzatu kamar yadda ta ce.
"Hello Nafisa dama kuna duniya."
Izzatu ta ce lokacin da ta aga wayar.
"Aa ba ita bace, bata da lafiya gata kwance cikin jini kizo a taimaka ma a kaita Hospital yanzu."
"Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un, okay ganinan ku jirani."
Kashe wayar ta yi, shikuwa Sada ya cigaba da jerowa Nafisa sannu.
Yau me gari Usmanu da kansa ya je police station, ya dage aka bashi belin Haliru ya taho dashi gida.
Haliru ko zama baiba yai wanka ba, ya fito kangon su inda suka saba zama.
Suna ganin sa duk suka mi e suna gaidashi ana murnar dawowarsa.
Fuska ba annuri ya ce
"Yau lahira zatayi bako acikin garin nan kowa ya shirya."
Ihu duk suka saka, ya fara yin gaba suka bishi a baya suna a aga makamai sama suna ihu.
Mintina ka an Izzatu ta zo, suka kama Nafisa, aka sata a mota, har zasu tafi Nafisa ta ce
"Izzatu kije akin Nasir da ku i masu yawa duk ki kwaso mana su."
Ba musu ta koma ciki
A jaka ta zubo duka ku in ta kamo hannun Anwar suka shiga motar Sada yaja suka tafi Hospital.
Suna shiga Hospital in Nurses suka amshi Nafisa, sukayi ciki da ita.
Rufa musu baya Izzatu tayi suka dakatar da ita ta ce
"Kuyi hakuri, dole ni zan yiwa Doctor bayani."
Barin ta sukayi ta huce ciki.
Doctor Maryam ta zo dan duba Nafisa, Izzatu ta ce
"Doctor lafiyar ta lau."
Da sauri Doctor ta kaleta zata yi magana taga Nafisa ta tashi zaune cikin tashin hankali ta ce
"Ki rufa mana asiri Doctor mijina azabtar dani yake ya rabani da kowa, ya hana kowa zuwa inda nake, shiyasa na nemi nayi ciwan wasa na gudu."
Girgiza kai Doctor ta yi ta ce
"Gaskiya baza'a ha a baki dani ayi mugun abuba kuyi hakuri."
Magiya Izzatu ta ringa yi mata amma ta burje bata yarda ba.
Nafisa sa ce ta amshi jakar hannun Izzatu ta ciro ku i masu yawa ta ce
"Dan Allah ki mana wannan taimakon, kati kawai zaki rubuta mana ki mi awa, wanda ya kawo mu kice ya je ya siyo magani yanzu, mukuma zamu gudu ke kuma kice anan kika barmu, ga dubu ari uku ki taimaka.
Amsa doctor ta yi ta ce
"Shike nan amma sabuda Allah zanyi."
"To mun gode."
Rubuta magani doctor Maryam ta yi kamar yadda suka bu ata, ta fita.
Sada ta samu a waje ta ce
"Dan Allah kaje a samo wannan maganin da ruwa da sauri."
Amsa ya yi jiki na rawa ya ce
"To in sha Allah."
Da sauri yabar gurin.
Komawa ciki ta yi ta ce
"Na turashi ya siyo maganin da nasan bamudashi a nan saiya fita tafiya me nisa zaku iya tafiya."
Godiya suka mata, da sauri suka fito dan su gudu.
Wata hanya doctor ta nuna musu dan subi ta gurin.
Har sunzo fita Nafisa ta tsaya ta kalli Izzatu ta ce
"Ina Anwar?"
Sai lokacin suka kula ba yaron.
Izzatu ta ce
"Ki taho kawai mu tafi."
Harara Nafisa ta watsa mata ta ce
"Baki da hankali an nawa zan bari."
Kasa magana Izzatu ta yi
Sai Doctor Maryam ce ta ce
"Ki fita ki tare muku abun hawa nida Izzatu sai mu dubo shi."
Da farko in yarda Nafisa ta yi, saida Doctor ta tabbatar mata zasu samu yaron.
Komawa sukayi ciki ita kuma ta fita ta tare me kafu babur.
Shiru Mama Lube tai tanajin fa an da Baba ya ke tayi.
Da ta gaji ta ce
"Haba Malam, yanzu ni na hana Khadija zuwa gida ko ya?"
"Ai kinsan inda take aure ki kaini da kaina naga halin da take ciki mana."
"Kaga malam nifa bansan gidan Khadija ba."
"To gidan ubanwa aka kaimun ata, ai ke kikasan mutumin wallahi ko ki fito mun da ita konayi ararki gurin hukuma."
Mi ewa Mama Lube tai ta ce
"Ni nasa ka saida artaka da zaka ringa agamun murya."
"Haka ma kika ce ko? To zakiga matakin da zan auka a kanki."
Daga haka ya fice daga gidan, mama Lube ta rakashi da harara.
Doctor Maryam suna komawa sukaci karo da Sada da Anwar a hannu.
Tsuru-tsuru sukayi zatonsu ya ganosu sai ji sukayi ya ce
"Naje Pharmacy ban samu maganin ba, bari na fita waje."
"Okay kawo Anwar in sabuda rana."
Mi a mata shi yai ya ce
"Bari naje to."
Cikin farin ciki Doctor Maryam ta ce
"Kai sauri fa."
"To."
Ya ce ya juya ya fice.
Godiya Izzatu taiwa Doctor da gudu ta fice ta ayar kofar.
Kafu babur in ta shiga da Nafisa ta ke suka tafi.
Sunyi nisa Nafisa ya amshi Anwar ta rungumeshi a jikinta ta saki kuka me tsuma zuciya, ita da gidan Nasir har abada tunda ta samu ta fito.
Cikin tausayawa Izzatu ta ringa rarrashinta harta samu tayi shuru, suka arasa gida.
Gayar da Haliru ya ibo kai tsaye gidan su Yusuf suka nufa.
Zuwansu yai dai-dai da fitowar Khadija a firgice.
Da sauri Haliru ya ce
"Ku kamo mun waccan bakuwar da taketa sauri."
Da gudu sukafi Khadija, wadda bamata cikin hayacinta...............
*Zaku iya samun complete ducment na ABDULFATAH da TAURARI BIYU da AURAN JARIMI akan fashi me sauki.*
*Guda aya #200 guda biyu #400 guda uku #500*
*Zaku iya tuntu ar wannan number 08166077167 domin malakar naku, karku bari a barku a baya.*
Comments
And
Share
By
*Zahra*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 16
Batasan abunda akeyi ba balatana ta gudu, har yaran Haliru suka risketa.
Rirriketa sukayi har oga Haliru ya zo gurin, ganin irin fusge-fusgen da ihun da take ya ce ya kule masa ita.
Nan take yaran nasa suka aiwàtar da abunda ya sa su, sukaja Khadija sukabar gurin da ita.
Har sukaje gida, Khadija tana wani irin fusge-fusge da ihu, hakan tasa Haliru ya farajin tsoro ya ce asata a aki a kule.
Yusuf ne ya fito daga akinsa.
Har zai fita sai ya fara kiran Hauwa,
Amsawa ta yi ta fito ta ce
"Gani."
"Ina Murja ne?"
"Ai Murja sun tafi da Hassana awarta dubiya."
"To Khadija fa?"
Saida ta turo baki ta ce
"Tana aki."
Kirayomun ita aiki zasumun.
Juyawa ta yi ta nufi akin, amma bataga Khadija ba, har akin Inna amma bata nan.
Dawowa tai ta ce
"Wata kila ta fice yawo dan bata nan."
"Khadija ce take fita yawo?"
"To ina tashiga inba yawonba tunda dai gashi bata nan."
"Mtssss."
Yusuf yaja dogon tsaki, ya fara kiran Khadija yana duba gidan amma shiru ba ita ba alamarta.
Hankalinsa ya gama tashi sabuda tunu wautar da tayi ranan nan.
Fita yai yana cigiyar ko akwai wanda yaga inda tayi.
Wani tsoho da kulum yana ofar masalaci a zaune ya kira Yusuf.
Har asa Yusuf ya du a ya gaida tsohon.
"Yaro naga wannan tantirin an me gari Haliru yazo har nan, ya tafi da wata yariya harda aureta da igiya."
A tsorace Yusuf ya ce
"Baba wane irin kayane a jikinta? Ko sufarta."
"Yarinyace dai amma da hijabi me ruwan asa a jikinta."
"Inalilahi wa'ina ilaihiraji'un!"
Abunda Yusuf ya iya furtawa kenan yaiwa Baba tsoho godiya ya koma cikin gida.
A gidan Izzatu suka sauka, Nafisa tai wanka ta gyara jikinta, sannan suka zauna a falo.
Cikin kulawa ta kalli Izzatu ta ce
"Kinsan me yasa nace ki ibo mana wannan ku in?"
"A'a."
"Sabuda bazan koma gida ba, nasan halin su Baba, zasu iya maidani wannan gidan, wanda da zamansa gara zaman kabari, bazasu duba wahalar da nake sha ba, suna ganin kudi shike nan."
Gyada kai Izzatu tai cike da gamsuwa ta ce
"Gaskiya ne, yanzu kinga za'a iya bincike ace dasa hannu na kika gudu, kuma in mijina yaji bazaiji dadi ba, dan haka dole mu shirya wata dabarar da zata futar dani."
Shiru Nafisa tai kafin ta ce
"Hakane amma me yakamata muyi?"
"Zaman gidan nan bazai fishe kiba, ki dole zaki koma wani gurin ni kuma duk yadda zanyi na kare kaina zanyi."
"Amma ina kike tunanin zanje yanzu."
"Akwai wata anwata wadda muke uba aya tana aure a Yobe state, munyi magana da ita mijinta yana America zaki iya zuwa can ki gama kwanakin kima bai dawo ba, kinga saikinfi sakewa mijinta baya nan."
Gyada kai Nafisa tai cike da gamsuwa ta ce
"Gaskiya ne, nagode Izzatu, bani da bakin da zan miki godiya saidai fatan alkairi."
"Karki ji komai awata mun riga mun zama aya."
Nan suka cigaba da tsara yadda zasuyi dan a asuba Izzatu take so Nafisa tabar garin gaba aya.
Cirko-cirko sukayi a tsakar gidan, Kawu ya ce
"Gaskiya lamarin yaron nan ya fara yawa, dole sai mun dauki mataki tsatstsaura akansa."
Inna da tai tagumi ta ce
"In banda abun Haliru me wannan yariyar ta masa ita da bata san abunda ke faruwaba."
Murja da kuka take ta ce
"Allah Inna dan yaga ba'a hukun tashine shiyasa yake taka duk wanda ya so."
"Idan yafi karfin hukuma aimu baifi karfin mu ba, gani yake kamar tsoransa akeji shiyasa yake wa mutane wannan iskancin, ni yau zanje mu raba raini dashi."
Yusuf yana gama fa in haka ya juya yabar gidan da sauri.
Hauwa da taketa tabe baki ganin ya fita ta ce
"Amma Kawu ku dakatar dashi kar su masa wani abun."
Kawu ya ce
"Yaga zai iyane kar wanda ya dakatar dashi."
Kuka Hauwa tasa, ta shige aki harda ora hannu aka tana cewa
"Shike nan na mutu na lalace, takaba ta kamani."
Sunajin tanata hauka ba wanda ya kulata.
Har kangon da suke zama yaje ya shiga ciki
Kamar yadda yai tsamani Haliru yana ciki da yaransa sunata shaye-shaye.
Har gaban Haliru ya tsaya yana huci ya ce
"Ina ka kai ar mutane?"
agowa Haliru ya yi, yana ganin me magana ya mike zunbur ya sa ihu ya ce
"Hhhhhh wai yau Akuya ce ta shigo ramin kura."
* * * * * * * * *
A tsora ce ta yaye jan mayafin da ta rufa a jikinta, Idonta suka koma red ta ce
"Akwai matsala."
"Wani yana kokarin tar watsa komai namu, ya daure yariyar nan a gidan sa, duk da akwai bakin aljani a jikinta ta kasa fitowa."
Tsuru-tsuru duka sukayi ganin lokaci guda komai yana son lalacewa.
"Dole ne mu kawo karshen komai tun kafin tsafin mu ya daina tasiri akan mu."
Shiru yai yana tuno wani abu cike da firgici ya tashi ya fice daga gidan.
Duk da kallo suka bishi na mamaki ganin yana so yaja da ikon dodo ana zama ya fita...............!
Sharhi ko arin haske 08166077167
Comments
And
Share
by
*Zahra*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 17
Bai bi takan kowa ba ya hau motarsa ya baro Kaduna.
Taron nasu kuwa tashi yai sabuda wanda akayi domin sa ya bar gurin, dan haka suma suka watse tunda shi fushin dodo zai hau kansa.
Mi ewa yai ya tsaya gaban Yusuf, yana huci, shima Yusuf din hucin ya keyi.
Yaran Haliru kuwa sun zagaye su da maka mansu a hannu.
Haliru ne yai kukan kura ya cakumi wuyan Yusuf, shima Yusuf cakumar tasa yai.
Yaran sukayo kan Yusuf.
Yusuf yai saurin shake Haliru ya zaro huka a jikin Haliru ya saita wuyansa ya ce
"Idan baka dakatar da suba wallahi zan yanka ma ogaranka."
Ba shiri Haliru ya ce yaran suja baya, suka ja da baya.
Yusuf ya ce yaje ya nuna masa inda Khadija ta ke.
Kamar ra umi da akala haka Haliru yakai Yusuf inda ya kule Khadija.
Aka budeta, sabuda rashin iska har ta suma acikin d'akin.
Ran Yusuf ya baci sosai dan haka yana ganin halin da Khadija ke ciki yasa hannu yaiwa Haliru wani wawan duka, saida Haliru ya zube a gurin ba nunfashi.
Fita Yusuf yai ya samo me mashin ya taimaka suka dauki Khadija suka tafi gida da ita.
Yan gidan kowa yai mamakin ganin Yusuf lafiya kuma gashi da Khadija.
Tabarma Inna ta shinfi a aka kwantar da Khadija.
Murja ta samo ruwa aka shafawa Khadija.
Nan take ta sauke nunfashi
"Alhadulilah."
Kowa yake furtawa.
Amm abun mamakin shine, tunda Khadija ta farka take wani fusge-fusge da ihu tana neman ficewa daga gidan.
Kawu yana ganin haka ya kalli Yusuf da yake cikin ru ani ya ce
"Daga gani wannan shafar junu ne, ka kira liman yanzu ya mata addu'a."
Ba musu Yusuf ya fita ya kira Malam liman
Nan Malam liman ya ringa yiwa Khadija addu'a aljanun basuyi magana ba, amma da sukaji wuya sun gudu.
Rubutu da tirare, Malam liman ya bada yace abawa Khadija ta ringayi in sha Allah, ba wani aljani da zai sake shiga jikinta.
Godiya suka masa, ya koma masalaci.
Sai dare Khadija ta tashi shima abunci kawai taci ta koma ta kwanta.
Washe gari.
Tunda asuba Izzatu ta raka Nafisa tasha ta hau motar yobe state, saida ta tabbatar sun tafi sannan ta koma gida.
Nasir da yaga dare ya masa a hanya, bai koma gida ba, ya kama hotel ya kwana sai da safe ya koma gida.
Tunda ya shiga gidan yaga duk ma'aikatan gidan jiki a sanyaye kuma duk a tsorace yasan akwai lauje cikin na i.
Yana shiga falo yaga Sada ya biyoshi jiki a sanyaye ya zauna ya ce
"Ranka shi dade, bayan tafiyarka an samu matsala, Hajiya ta bar gidan nan."
"What! Me kake nufi?"
Nasir ya ce, cike da tashin hankali.
Muryar Sada na rawa, ya zayanewa Nasir komai abunda ya faru.
Ajiyar zuciya, Nasir yai ya ce
"Tashi ka bani guri."
Kamar jira Sada yake ya fice daga falon.
Shiru Nasir yai yana nazarin abunda Sada ya sanar dashi, yanzu ta ina zai fara? Neman Khadija da Yusuf da sukaci amanar sa ko neman Nafisa?
Da arfi ya gatsa le ansa jikin sa na rawa.
Sai 2:17pm su Nafisa suka sauka a Yobe, mota suka hau da kwatance aka kaisu gidan anwar Izzatu.
Da salama Nafisa ta shiga gidan, wata datijuwar mata ta amsa mata salamar da fara'a.
Murmushi Nafisa tai wa matar, matar ta amshi jakar Nafisan tashiga da ita ciki.
A falo suka zauna matar ta shiga da kayan ta sanar da Maryam matar gidan zuwan Nafisa.
Itama Maryam kamar Izzatu tanada mutunci. Da fara'a suka gaisa da Nafisa, tana mata sannu da zuwa tasa Mama Karime ta kawo musu ruwa da lemuka da abunci.
Sunaci suna hira, bayan sun gama Mama Karime ta auki Anwar suka shiga akinta dashi.
Da murmushi Nafisa ta rakasu ta ce
"Da alama Mama Karime tana son yara."
"Sosai ma kuwa musaman mata, nasha kamata tana kuka idan ta auki yariya ta, na tanbayeta dalili ta ce bakomai."
"Allah sarki, wata kila ta ta a haihuwa a baya yaran sun mutu."
"Hakane kam."
Hira suka cigaba dayi kamar sun jima da sanin juna.
Da dare Nafisa tana zaune a akin da aka bata, Mama Karime ta shigo da Anwar ta kwantar dashi tana kallon fuskarsa.
Nafisa ce ta kaleta cike da kulawa ta ce
"Amma Mama Karime kin ta a haihuwar yara a baya ko?"
Hawaye Mama Karime ta share ta ce
"Tabbas inada yariya mace amma yanzu bansan inda take ba, amma wannan yaron naki yanamun tsananin kama da wani an uwana a katsina ya rasu can da darewa, amma yanada yaro Nasiru bansan inda yake a halin yanzu ba."
A matukar tsorace Nafisa ta kalli Mama Karime ta ce................!
Sharhi ko arin haske 08166077167
Comments
And
Share
By
*Zahra*
*WATA RAYUWA*
Na
Fatima S Umar Jajira
Free book
Episode 18
"Nasir sunan mahaifinsa kenan."
Itama Mama Karime tayi mamaki ta ce
"Ban sani ba ko sunana ne yazo aya amma nawa an