Author : AYSHERCOOL Category : Top Hausa Novels 2025
Sadik yake iya shegensa, Hakimi be tofa komai ba, se a wannan karon da ya bi Sadik ɗin da kallo shima.
Nana ta fito tsakar gida, tana bawa magunan Inna Abinci, kasancewar Innan kamar kiwon su take.
Sun kai su kusan bakwai magunan se tsalle tsalle sukeyi.
Faruk ya zo ya sameta a gurin, yace "wannan magunan fa kyawawa Masha Allah?"
Nana tace "Na Inna ne, nake basu Abinci, ni kaga nawa nan wannan farar da wannan ɗan beutyn"
Faruk yace "Wow, gasky ne they are cute"
Sadik na gefe, ya shirya Fitowar Abba kawai yake jira su tafi, yana zaune yana harar Nana da zarar sun haɗa ido.
Nana tacewa Faruk "kaga wancan muzurun, me tsigaggen gashin nan, ya fiye fitinar tsiya, ga rawar kai gashi bashi da kunya, shiyasa gashi nan mummuna, ko fara'a ba ya yi, sunan sa Autan Mother"
Faruk ya ɗaga kai ya kalli Sadik, wanda ya zubowa Nana ido, dan yasa wannan cin fuskar da shi take, wato muzuru ma ta sawa Autan Mother, hadda ce masa mummuna.
Tunanin abunda zewa Nana yake dan ya huce, sega Abba ya fito a shirye, da alama tafiya za suyi, abun mamaki sega Hakimi ma da ƙafafunsa ze rakasu mota tare da Inna.
Sadik yai saurin miƙewa, dan jinsa yake kamar akan ƙaya.
Hakimi ya kalli Sadik sannan ya kalli Abba yace "Wannan abokin nawa a nan zaka barmin shi"
Abba yai murmushi dan zatonsa Hakimi da wasa yake yi.
Sadik kam ya fara zoma kai gaba, yana jiran su Abba su wuce ya biyo bayansu.
Suna zuwa zaure na biyu, Hakimi ya kalli wani dogari yace "kar a bar wannan abokin nan nawa ya ɗaga ƙafarsa daga inda yake, a nan za'a barmin shi" yai maganar yana nuna Sadik.
Abba ya kalli Hakimin yace "Alhaji kana nufin a nan ze zauna?"
"Eh, ko ban isa bane?"
Abba yace "wane ni ja da maganar ka"
"A nan za'a barmin shi, kuma daga yau bana buƙatar ka sake zuwa, tunda naji sauƙi Alhamdilillah.
Aikuwa Sadik ya gigice, ze taka yabi Abba, a kai sama da shi aka mayar da shi cikin gida, yana kurma ihu yana kiran Abba!
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
Ko ku tuntuɓe ni ta wannan lambar
Ayshercool
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Jiki a sanyaye Abba yai gaba, yana jiyo yadda Sadik ke ƙwala masa kira yana ihu.
Duk da shi kansa Abba beji daɗin abubuwan da Sadik ɗin ya dinga yi ba a gidan, amma se yaji beji daɗi ba amma ba yadda ya iya.
Shi kansa Faruk, se yaji tausayin Sadik ya kama shi, yasan yadda Sadik yake a sangar ce ba ƙaranar wahala ze sha zama a garin nan ba.
Gashi Hakimi yace kar Abba ya sake zuwa garin. Se da wani ƙwaƙwalwa Dalili.
Har mota suka raka Abba da Faruk, sukai musu Sallama.
Nana kuwa da taga an saɓo Sadik a kafaɗa an dawo da shi, se abun ya bata mamaki.
Inna na shigowa Nana tace "Inna wai ya naga an dawo da shi? Ba tafiya za suyi ba"
"Kakansa yace a nan za'a barshi" Inna na faɗin haka ta shige ɗakinta.
Sadik se kiran Abba yake kama wanibɗan yaye, ya kuma nufar ƙofar da gudu ze fita amma aka kuma hankaɗo shi aka hanashi fita.
Hakimi ne ya shigo yana takunsa cikin nutsuwa, yaga yadda ake dambarwa da Sadik akan lallai seya fita.
Ya kalli dogarin yace "ka ladabtar da shi idan ya kuma yunƙurin fita"
Zare ido Nana tai jin abunda Hakimi ya faɗa, aikuwa aka ɗakko zumgureriyar bulalar dukan doki, Sadik na ganin wannan uwar bulalar ya shiga taitayinsa.
Nana kuwa ta tuntsure da dariya tace "yau naga ƙarshen taurin kai da raina mutane" ta dinga dariya yayin da Sadik bata ta yake ba, yadda ze ya gudu kawai yake tunani.
Daga Abba har Faruk su kai jugum jugum a mota, ba wanda yake magana, kowa da abunda yake saƙawa a ransa, can Abba yace "Faruk kaga abunda ƙaninka ya jawa kansa ko? Da ya daure beyi wannan ƙaƙale ƙaƙalen nasa ba, da babu lallai Hakimi yace a barshi amma kaga abunda ya jawa kansa"
Faruk yace "wallahi kuwa Abba, Sadik yana da matsala halinsa se shi, ni kaina na nusar da shi amma yaƙi ganewa"
"Ai shike nan, kaga gobe ba ya kuma ba, kuma idan yace ze rashin ji jikinsa ne ze gaya masa, ni rigimar mahaifiyarku nake tunani, yanzu idan muka koma babu shi haka za tai ta sababi"
"Hakane kam, za tai mita sosai amma ai shine ya jawa kansa"
Haka suka cigaba da tafiya suna maida zancen.
Wasa wasa Sega Sadik yana hawaye, saboda shi ganinsa an zalunce shi idan aka ce ya cigaba da zama a nan, garin da babu wani abun more rayuwa a cikin sa.
Ya nemi guri yai zaman direshen a tsakar gida, se lokacin salla, ze tashi yai alwalwa yai salla a nan tsakar gidan.
Ba wanda ya kuma bi ta kansa, kowa sabgar gabansa kawai yake yi.
Ganin ba kowa a tsakar gidan yasa ya miƙe cikin sanɗa ya nufi hanyar fita, amma yana zuwa ya tarar da dogarai a soro na biyu riƙe da manyan bulalai.
Dawowa yayi kamar ya ɗora hannu a ka yai ihu, akai Abincin rana aka kawo masa, amma ya barshi a gurin be taɓa ba, har ƙarfe uku na rana yana tsakar gida a zaune kamar maye.
Wajen la'asar sannan su Abba suka isa gida, Mother najin tsayuwar motarsu ta fito, cike da burin ganin yaranta da aka kwasa a ka kai mata ƙauye suka kwana, mussaman Annurin zuciyarta wato Sadik.
Tana nan tsaye suka firfito daga mota, ta ƙarasa in da suke tana faɗin sannunku da zuwa, ina ɗan Autana?"
Abba bece komai ba yai gaba abunsa, Faruk ma ƙoƙarin barin gurin yake, ta kalli motar ta tabattar ba kowa a cikin ta, ta kalli Faruk tace "ina Sadik ɗin?"
Faruk yace "Ki tambayi Abba"
'ban gane in tambayu Abba ba, kai ka gayamin mana"
"Mother am pressed, i want ease myself" yai maganar tare da nufar BQ.
Mamakk ya kanainaye Mother tabi bayan Abba, tana zuwa yana shiga toilet ɗauro Alwala.
Ta samu guri ta zauna tana jiransa, ko da ya fito kuma ya nuna mata salla zeyi ta ƙyale shi.
Ba ta gaji ba ta nemi Guri ta zauna dan jiransa ya idar da sallar, taji ba'asin in da aka baro mata ɗa.
Abba ji yai kamar kar ya idar da sallar nan, saboda be san ta yadda ze fara mata bayani ba, dan ya san ba ƙaramin haurawa za suyi ba.
Aikuwa yana shafa addu'a tace "Abba nifa baku cemin komai ba, ina Sadik ne?"
Abba ya kalleta yace "zan siyar da Sadik ɗin ne? Idan ma siyar da shi nai ai dai ɗana ne ko?"
"Eh naji na kuma yadda ɗanka ne, amma Yakamata in san in da yake, kun tafi kun dawon ba shi dole in tambaya"
Abba ya ɗan haɗe rai, cikin basarwa yace "mun baro shi a can"
"Can ina?" Tai maganar tana zaro idanuwa.
"Can ƙauye mahaifata, gidan Hakimi"
"Amma meyasa zaka baromin yaro a can, kasan fa ba iya zama ze ba"
"Saboda nima da na rayu a can ɗin kan ki haɗu dani a birni, ban mutu ba, dan haka shima baze mutu saboda zaman ƙauye ba se lokacinsa yayi"
"Haba dan Allah, ai ba ka haɗa rayuwar da kai da wadda ze ba, haba Abba, Sadik be taɓa nisa dani na kwana biyu ba, duk in da yake muna tare, ni da Faruk ka bari ba zan damu ba, amma Sadik be saba ba baze iya zama ba, dan Allah in laifi yayi ka baro shi kayi haƙuri ka ɗakkon ɗana"
Abba ya numfasa yace "bani yaiwa laifii ba, bana ce kai tsaye ga abunda yai ba, amma zan iya cewa koma mene shi ya jawowa kansa, tunda mukaje yake wasu irin abubuwa na nuna ƙyama ga garin, kuma bani na yanke wannan hukuncin ba, Hakimi ne yace a barshi a garin"
"Amma maimakon ka basu haƙuri, ka san Sadik baze iya zama ba wallahi, ai seka basu haƙuri amm ba ka baro min shi a can ba"
"Kinga Hauwa'u ki kiyayeni, ba zan bijirewa iyayena dan in faranta miki rai ba, yadda kike son ɗanki haka nima suke sona, kuma ba za suyi abunda zasu cutar da abunda na haifa ba"
"Amma duk da haka se a duba yaron nan, tsakani da Allah baze samu yadda ya saba a nan a can garin ba"
Ganin Mother na neman sake ɓata masa rai yasa ya miƙe, ya koma sashinsa ya rufe ɗaki.
Wasu irin hawayen takaici ne suka taru a idon Mother, sam ba ai mata adalci ba, koma me Sadik zeyi ai bekamata ai masa wannan hukuncin ba, wannan uban ƙauye ina Sadik ze iya zama a cikin sa.
Wayarta ta ɗakko ta kira Mummy, wato Maman Khairat, seda ta kusa katsewa sannan Mummy ta ɗaga Tare da faɗin "Afuwa Please, salla nake ne ya gida ya yaran?"
"Gida lafiya ƙalau"
Mummy tace "ya naji Muryar ki haka ne?"
Cikin ƙufula Mother tace "kin san kuwa abunda Baban yaran nan yai min?"
Mummy tace "to yau kuma ke da sweetheart ɗin ne? Meyafaru?"
"Wai daga zuwa duba mahaifinsa a ƙauye, ya ɗaukar min Sadik ya tafi da shi, wai se dawomin yai daga shi se Faruk kawai, wai ya baro shi a can"
"Kamar ya ya baro shi a can?"
"Wai kakanninsa ne sukace a barshi a can, saboda yana nuna wa garin ƙyama, tsakani da Allah an min adalci kenan, inyi magana ace bani da haƙuri, ta yaya Sadik ze iya zama a garin nan fisabilillahi? Tsabar abu kuma ina masa magana ya tafi part ɗinsa ya rufe ɗakinsa"
Mummy tace "Subhanallah, ai riƙon mahaukaci se sarki, waze iya riƙe wannan yaron naki ɗan hutu in ba ke ba, Sadii baya son wahala da takura, gaskiya ba'ai miki adalci ba, amma karki ce zaki matsa ki bi Komai a hankali, kiyi ta lallaɓa shi har ya ɗakko miki ɗanki, kar kice zaki fushi kin san zaki kuma janyowa kanki matsala ne, dan haka kiyi haƙuri na san ba'a kyauta miki ba"
Mother tace "shikenan Yanzu a can ze kwana? Wannan wane irin abu ne, ni na san halin kayana wahala ze sha a garin nan wallahi be saba ba"
"Na sani Hauwa'u, amma dai kiyi haƙuri dama kin san yadda Akuyarki tai kuka a dangin mijinki, dan haka karki ce zaki matsa ki ƙara baƙin jini"
"Wallahi ji nake kamar in ɗau mota inje in ɗakko shi, sedai ai duk wadda za'ai"
"Ke karki kuskura, garin son ɗa da neman gira ki rasa idanu, shi dai baban nasu zaki cigaba da lallaɓawa"
"Shikenan Mummy, ki gaida su Khairat"
"Bakomai za suji amma ki kwantar da hankalinki".
"Shikenan se an jima" ta katse kiran.
Mummy tace "Ikon Allah, wannan kakannin na su Faruk sun fiye Matsala wallahi"
Khairat dake kusa da Mummy a kwance ta ɗaga kai ta kalleta tace "Wai Mummy Sadik aka kai ƙauye?"
"Wallahi kuwa, baki ji muryar babarsa ba ina ga ma kuka take, kai Allah ya jarrabi Hauwa'u da son 'ya'ya mussaman Sadik"
Khairat tace "gaskiya ba'a kyauta ba, wallahi ze sha wahala ne kawai amma kin san Sadik da son hutu"
"Aikuwa yanzu se ta Allah, wannan ƙasurgumin ƙauye ina ze ga wani hutu".
Wasawasa har la'asar Sadik yana zaune a tsakar gida, ya ƙi cin abinci kuma ya ƙi tashi ya shiga ɗaki, da fari Nana dariya ta dinga yi masa, amma daga bisani kuma se ya fara bata tausayi, ganin har taje ta dawo daga Islamiyya amma yana zaune a tsakar gida, haka kurum rana tsaka a bar mutum a in da be saba zuwa ba, alhalin da uwarsa da ubansa a raye, se taga ba'a kyauta masa ba.
Idanunsa sunyi jawur, saboda tsabagen yunwa ga kuma baƙin taurin kai irin na Sadik.
Aka yi sallar magariba, yai salla a in da yake ya nemi guri ya zauna, aikuwa sauro ya fara ɗawafi a kansa, saura ya fara zagaye baƙar sumarsa, ga yunwa dake sakatar cikin sa kamar ze ci babu.
Nana ta fito daga ɗakin Inna, ta tarar da shi a zaune yana kore sauro da hannunsa, ga network ɗin wayarsa sam yaƙi harbawa.
"Ka taso daga nan ka koma ɗakin da kuka kwana jiya, in ba haka ba sauro se ya kusa halaka ka a gurin nan"
Banza yai mata kamar be ji me tace ba, daga ɗaki Inna tace "ke ina ruwanki da shi? Waye yace ki masa Magana se kunzo kuna faɗa ko?, Ki ƙyale shi yai ta zama a gurin, idan saurayen suka gama tsotse masa jini, ya tashi ya bar gurin, ai bari ba shegiya bace da ubanta.
Sadik a ransa yace 'wannan tsohuwar yadda ta tsaneni ba ta ƙi in mutu a gurin nan ba' dan haka ya miƙe ya tafi in da suka kwana jiya ya kunna fitilar wayarsa yana sake haske ɗakin.
Ɗakin ƙasa ne na gaske, an masa sumunti da ƙasa aka kawo farar ƙasa aka shafe ɗakin da shi.
Se wata 'yar taga 'yar ƙut a sama kamar gurin kiwon tattabara, ɗakin ɗauke yake da ƙatuwar katifa da manyan matasai.
Ga shimfiɗar buzu a gurin, wanda akeyi da fatar dabbobi, wanda warinsu kawai damun Sadik yake.
Ya ajiye wayoyinsa akan katifar ya nemi guri ya zauna, yai tagumi yana jin yadda cikinsa ke wata irin juyawa.
Ganin ba kowa a tsakar gida yasa Nana ta nufi ɗakin Hakimi.
Ta tarar da shi yana kan sallaya yana jan carbi.
Wata tasa taje ta buɗe ta ɗebi gurasa, har zata fita Hakimi yai gyaran murya.
Ta waigo tace "Ci zanyi, yau ba zanci tuwo ba"
Tana gama maganar tai waje, ɗakin da Sadik yake ta nufa, tana yi tana waige kar Inna ta kamata, ta ɗebo ruwa a kofin silba ta shiga ɗakin.
Ta tarar da Sadik yai uban tagumi, kamar wanda yake jiran wani mummunan saƙo.
Ta dire masa tace "gashi nan in ka ga dama kaci, in baka ga dama ba kai ta zama da yunwa bame lallaɓa ka yace se ka ci, sedai ka mutu da yunwa"
Tana gama maganar ta juya ta fita, yayin da Sadik ko kallonta be ba, ya cigaba da taguminsa.
Wunin nan guda yau be wanka ba, ya nemi guri ya kwanta akan katifar nan, ga tunanin Mother ga na Farhan, ga Faruk ɗinsa shima yana missing.
Kawai yaji zuciyarsa na raya masa yaiwa tsofaffin nan Allah ya isa, saboda a ganinsa abunda su kai masa zunzurutun zalunci ne, saboda tsabar mugunta a dole se sun azabtar da shi.
Jin sa da yake kamar ze mutu saboda yunwa yasa ya tashi zaune, ya janyo kwanon gurasar nan ya dinga danna ta haka gaya ba miya bakomai.
Ya nayi yana shaƙewa yana korawa da ruwa, gashi ta fara bushewa, se yayi kokawa da ƙyar take haɗiyuwa, kamar yana cin takadda.
Be tsaya duba wane irin ruwa bane, haka ya sha ruwan nan dan samawa kansa mafita.
Da ya gama ci saboda tsabar takaici yai cilli da kwanukan a tsakar ɗakin yana huci.
Ya hau kan katifar ya kwanta, zuciyarsa kamar ta tsaga ƙirjinsa ta fito dan baƙin ciki.
Ba wuta, ba fanka ba sanyin AC, ɗakin se uban zafi, ga ba fitila se fitilar wayarsa da ya kunna.
'wannan ɗaki ko kabari ne se haka' ya furta yana tsaki.
Ya dinga juyi amma ya kasa bacci, saboda ƙaiƙayi da jikinsa ya dinga yi, beyi wanka ba, ga sauro da uban zafi da ya addabe shi.
Tashi yai zaune zaman dirshan, ya rasa abunda ze yi dan yaji daɗi.
Farhan kam ta ɗan damu, dan yadda sukai da Sadik a Ranar zasu dawo, amma har yau Lahadi babu message ɗin sa tsawon wuni guda, tun saƙon da ya tura mata cewar a can za su kwana, tai ta kiran wayarsa amma ba ta shiga, haka ta haƙura ta kashe wayar ta maida ita in da take ɓoye ta.
Tsakar dare Sadik ya kasa bacci sam, be san lokacin da hawaye suka fara bin idanunsa ba, hawaye ɗaya bayan ɗaya.
Tsakar gidan ya fito yana ƙarewa gidan kallo, hasken farin wata ya haske ko ina, kawai se yaga gidan somehow look scary to him, toilet yake son shiga amma tsoro da fargaba suka hana shi hakan.
Inna da take salla taji motsi a tsakar gida, ta ɗaga labule, taga yadda Sadik yake tsaye yana rarraba ido.
"Me kake a nan gurin?" Maganar da Inna tai seda Sadik ya kusa zurawa da gudu, saboda jin maganar yai from no where.
Se da ga baya ya fuskanci Inna ce, ya tsuke fuska yace "wanka zan na kasa bacci"
"Wanka a tsohon daren nan, maza cigaba da tsaiwa a gurin kar kaje ka kwanta, akwai mayu idan suka fito suka lashe ka shikenan"
Zare ido Sadik yai, be san takamaimai meye maita ba, amma dai yasan tabbas maita wani abune nau'i na tsoro, aikuwa cikin hanzari ya kwasa da sauri ya koma ɗakin da yake.
Inna ta saki labule tace "ba dai kace kai baka ji ba, zaka ga tsiya ai ja'iri"
Sadik sosai ya dinga kuka, kamar ƙaramin yaro me shan nono.
Se wajen Asuba sannan bacci ya saci Sadik, Asubar fari aka zo aka tashe shi, yai Alwala zuwa masallacin cikin gidan Hakimi.
Yana shirin ya miƙe yaje ya samu ya kwanta ya koma bacci, saboda rashin baccin da be samu ba jiya.
Aka ce ba in da za shi za'a zauna karatun Alqur'ani.
Aka rarraba Alqur'ani, amma Sadik ya ajiye nasa yace ko yayi ba lada dan be niyya ba, saboda haka baze ba.
Ana ta karatun Alkur'ani, ya jingina da bango yana baccinsa, baccinsa ya fara nisa yaji an tsula masa carbi a ƙafa, ya buɗe ido a gigice.
Wani dogari yace "ka buɗe idonka ka dena mana bacci"
Tsaki Sadik yai, dan yaji zafin dukan carbin nan, dan se yace Allah ya isa.
Haka Sadik ya zauna yai zuru yana rarraba ido.
Mother kam baccin dare gagarar ta yayi, saboda tunanin halin da ɗanta yake ciki, ta san babu Lallai Sadik ya iya bacci a wannan garin, yadda ta ga dare haka taga rana, zuciyarta cike da tunani da tausayin ɗanta.
Se kusan ƙarfe bakwai na safe aka tashi daga wannan karatun, Sadik ya tashi idonsa har mannewa yake saboda tsabar baccin da yake ji.
A tsakar gida ya tarar da Inna da Nana, ba wanda ya gaisar ko ya kula a cikinsu ya wuce ɗakin da ya kwana.
Ya haye kan katifa ya fara bacci, ƙafarsa na ta zugin dukan da aka masa da carbi.
Ji yai an watsa masa ruwa, ya tashi firgigit.
"Ka taso ana kiran ka"