Author : AYSHERCOOL Category : Top Hausa Novels 2025
abunyi a kai Yaushe? For how long zan jira ka nemo mafita, idan kuma aka gano ni a gida fa"
"Wait, ki dena wannan kukan dan Allah, babu me ganowa har ayi abunda za'ai, zanje in bincika abunyi zuwa gobe in Allah ya kaimu, amma dan Allah karki gayawa kowa Lilly"
"Ni ba wanda zan gayawa, damuwata shine in rabu da cikin nan, zamansa a jikina kusanta ni da bala'i yake koma ajalina, dan babana baze barni da rai ba idan ya gano ni Allah" tai maganar hawaye na gangarowa daga idonta.
"Nasani Lilly, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki shiga toilet ki wanke fuskar ki, seki koma aji dan Allah karki bari asirinmu ya tonu"
Ta jinjina masa kai ta fice daga Office ɗin.
Guri ya nema ya zauna, yana yakice gumi a fuskar sa, yana jin yadda zuciyar sa ke wani irin bugawa saboda tsabar tsoro da fargaba, be taɓa tunanin a karon farko haka Lilly zata ɗau ciki ba.
Ajin su Sadik kuwa, an haɗu suna ta hada hadar su, wasu na ciye ciye wasu na danna waya.
Nas ne yace "Allah sarki, wallahi missing ɗin abokin mu nake"
Amin yace "kai dai bari bro, wallahi tun da Sadik ya bar school ɗin nan ta dena min daɗi, babu wani show na Musamman, gaskiya anyi missing wallahi"
Taslim tace "ai ba'a cewa komai, Sadik duniya ne gayen yayi, he's very jovial yana bamu nishaɗi sosai"
Amin yace "gaskiya Nas Yakamata mu kai masa ziyara gidan su"
"Hakane, ni zata ma ze dinga zuwa school ɗin nan ko dan saboda beb ɗin sa, amma naga sau ɗaya ya zo daga nan be sake zuwa ba"
Amin yace "kai Sadik ɗan bala'i ne, wallahi wani aka samu ya kira shi ya gaya masa Mubarak yana bibiyar Yarinyar nan, se gashi kamar an jefo shi, seda suka kusa bawa hammta iska fa ranar da ya zo, ni tsoro ma naji karsu dambace dan ka san Mubarak na yawo da makami"
Nas yace "wallahi fa, kuma idan ya illata Sadik se yayi prison, dan babansa ba shi da kuɗin da ze ƙwace shi a gurin baban Sadik"
Meenal tace "se cin mutuncin saurayin Taslim kuke a gabanta ya haka ne gayu"
Taslim tai murmushi tace "saurayina na wucin gadi ba, ni ina ruwana dalili ne ya haɗamu kuma ya raba mu dan haka suyi ta zaginsa"
Amin yace "kai Taslim, duk soyayyar da ku kai?"
"Taɓɗijan, ai banda dalili ba abunda ze sa in saurari Mubarak, kai ka san suwaye samarina kuwa manyan kawuna ne wallahi?"
Meena tace "wai dan Allah baki ji haushi ba da yake bin budurwar Sadik?"
"Haushin me zanji Meena? Dama halinsa ne kamar ɗan Akuya haka yake, kuma naga ai ba mijina bane da zanji haushi"
Nas yace "Amma kin san da haka kike biye masa?"
"Yes saboda nima akwai abunda nake samu a gurinsa"
"To gaya mana menene?" Nas ya faɗa cike da fitsara yana wani kashe ido.
Taslim tace "kai dai Nas Allah ya shirye ka da gulma, budurwar Sadik da yake bi, dalili biyu ne yasa yake binta"
Meena tace "wane dalili kenan?"
Taslim tace "akwai tsama da ke tsakanin su, da ba kowa ya san meya haɗa su ba, dan haka yake son yin amfani da budurwar Sadik gurin rama abunda ke tsakanin sa da Sadik ɗin"
Amin yace "Ni kaina ina mamakin yadda lokuta da dama na kanga ƙiyayyar juna a tsakaninsu, duk da suna pretending, amma meya haɗa su ne?"
Taslim tace "ba za'a ji mutuwar sarki a bakina ba"
"Kar Allah yasa aji ɗin, in tai tsami maji, nayi mamaki da duk zamnmu da Sadik be taɓa gayamana abunda ya haɗasu da Mubarak ba"
Meena tace "ba abun mamaki bane, saboda yanayin halinsa, duk son nishaɗinsa, he has a private life, bakomai ze haɗaku yaje yana faɗa ba"
Amin yace "gaskiya ne, Sadik yana da halaye na ban mamaki, masu kyau kuma abun koyi, a zaman mu na tabattar wallahi son da yake wa yarinyar nan da gaske yake sonta, ita ma kuma tana matuƙar son sa, sedai abune mawuyaci gidansu su bari ya aure ta, saboda 'yar talakawa ce sosai"
Taslim tace "ni zan gaya maka 'yar talakawa ce, wallahi se an sa gidansu uku zuwa huɗu a gidan mu, ai ni naje na taho da ita ranar birthday ɗin ta"
Nas yace "dama ai batun wani aure tsakanin sa da Yarinyar nan ba abune me yuwuwa ba, shiyasa ake bashi shawara kawai ya huta da ita a wuce gurin, amma ya tsaya yana shirme wai shi Aurenta zeyi kamar ba namiji ba, kalli da yadda aka sa yai kissing ɗin ta, daga baya kuma wai yazo abun ya dame shi, wasu lokutan yai ta abu kamar ba wayayye ba"
Amin yace "ba haka bane, daga Yarinyar ne, da ya samu tantiriya, da zata gogar da shi sosai, da irin su Taslim ya samu, amma ita she's so innocent, shi yasa na koma jin tausayin ta dan da farko haushi take bani, amma daga baya naga idan Sadik ya lalata rayuwarta abun ze mata yawa, ga Talauci ga kuma lalacewa"
Nas yace "kai tafi can, ka bibiya ba abunda ba ta sani ba, yaran nan na yanzu, kai yanzu in aka cewa iyayen mu muna zagawa square mu huta, zasu yadda ne? Kai dai kawai ai sha'ni duk rufa rufa ce abun"
Taslim tace "kuma wallahi Yarinyar nan da zata shigo layi, zata ɗau haske zata gara manyan mutane, dan tana da kyau ga uban diri kamar babbar mace"
Meena tace "ai abunda yake sake ruɗar Sadik kenan, wannan dirin nata"
Nan suka cigba da gulmace gulmacen su.
Seda aka idar da sallar azahar, sannan aka tashi daga fadar nan, Sadik yaga shirme a gurin 'yan ƙauye kala kala.
Yadda suke kawo ƙara, wasu akan filaye wasu dabbobi, ba wanda yafi bashi takaici irin cases ɗin Aure.
Wata mijinta na satar mata awaki ya siyar, wata yana cin mutuncin ta, hadda me kawo ƙara akan tana ciyar da dabbobin mijinta dusa yace ze biyata amma baya bayarwa.
Shari'a kala kala, wasu abun haushi da takaici haka Sadik ya dinga jin su.
Ƙarewa gidan kallo Sadik yake, yana tunanin ta ina ze fara haurawa ya gudu daga gidan? Sedai katangar gidan doguwa ce sosai.
Sadik yana sha'awar kallon dawakan da suke burga, dan haka ya tsaya a gurin yana kallon yadda suke cin abinci suna huci.
Kamar an mintsine shi, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko ƙaramar wayarsa ya kira layin Farhan, by luck yaji ta fara ringing.
Murmushi yai ya gyara tsaiwar sa, yana jiran ta ɗaga.
Sedai bata samu ta ɗaga ɗin ba, a ƙalla ya kirata kusan sau uku amma bata ɗaga ba, haka ya haƙura ya koma neman layin Mother, sedai shi kuma yaƙi shiga.
Gajeren tsaki yai, ya waiga bayansa yaga wannan dogaran tsaye da bulalai kamar masu gadin bawa, haka ya juya ya shiga cikin gidan yana kumbura baki.
Yana shiga ya cire wannan uban kayan da aka sa shi ya saka, ya zauna daga shi se vest da dogon wando.
Ya zauna akan katifar nan yai shiru, gaba ɗaya jin sa hake kama a prison, ba wani abun ɗebe kewa, ba abokai ba kallo, ba yawo, ga wayarsa Babbar caji ya kusa ƙarewa, ga kewar Mother da yake yi, gaba ɗaya abun duniya ya dame shi.
Farhan se da taje gida, Sannan taga missed call ɗin Sadik, gashi ta riga ta dawo gida, dama wayar kullum a silent take, shiyasa ba ta ji ringing ba.
A gaggauce take komai, dan ta samu ta fita Islamiyya da wuri, ta kira Sadik, dan ba halin ta kira shi yanzu a gida, za'a iya jinta.
Sadik ya zauna ba daɗewa yana jiran ya samu yai bacci, aka zo aka kirashi seda yai tsaki sannan ya fito.
A turakar Hakimi aka sashi a gaba, da bulala aka kuma narka masa irin tuwon da yaci da safe.
Sadik yana ci yana goge gumi, haka ya dinga cin tuwon nan, ji yake dama ya mutu ya huta da wannan jarabar.
Seda yaci sannan ya koma ɗaki ya kwanta, zuciyarsa a cunkushe.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya tashi zaune da sauri ya duba yaga Farhan ce.
Cikin hanzari ya katse kiran, ya kirata sedai ba ya jinta sosai, a haka yace "Baby ina kika je ne na kira baki ɗaga ba?"
"Ina school ne, ka san wayar tana silent tun jiya nake trying lambarka taƙi shiga, se da na dawo gida naga missed call ɗinka, na bari seda na fito Islamiyya sannan na kira ka"
Cikin damuwa Sadik yace "Baby ina cikin damuwa da tashin hankali wallahi"
"Subhanallah, meyafaru ne?"
"Kin ganni haryanzu ina ƙauye, ba kiji ba kya jina sosai ba?"
"Eh naji abun ya bani mamaki"
"Daga zuwa dubiyar nan aka hanani komawa gida, an barni a nan ina ta shan wahala"
Cikin damuwa Farhan tace "meyasa to aka barka a ƙauyen?"
"Kakana ne yace se an barni, baki ga yadda na koma ba, ba zan iya zaman garin nan ba, ina nan ina tunanin yadda zan gudu"
Farhan tace "ya salam, ka dena batun guduwa karka ɗaga musu hankali, kayi haƙuri ka zauna zuwa lokacin da zasu bari ka tafi"
"Farhan ba zasu bari in koma gida ta daɗin rai ba, se gana min wahala suke, ba ruwa ba wuta, ba irin Abincin da nake so tuwo fa ake bani, ga ina missing ɗin Mother, ga kema ba kya kusa dani, cajin wayata ma ya kusa ƙarewa, tunda na zo banga an kawo wuta ba, ba wanda na kira ba wanda ya kirani wace irin rayuwa ce wannan kamat wani bawa dan Allah"
Tausayin Sadik ya mamayeta gaba ɗaya, cikin damuwa tace "ka kwantar da hankalin ka Dear, dan Allah kar kayi wani abun da ze ja maka ɓacin rai kayi haƙuri, kasan su iyaye ba'a jayayya da su"
"Kakan ni na ne fa ba iyaye na ba, shima Abba ya tafi ya barni a nan, ban zaci Mother zata bari in kwana a garin nan ba ma"
"Kakanni suma iyaye ne, kayi haƙuri zuwa lokacin da zasu bari ka dawo kaji my"
"Hmm ba Zaki gane halin da nake ciki ba, duk yadda zan misalta miki ba zaki gane ba"
"Zan gane mana, na sani zaman ƙauye babu daɗi amma kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka kaji my love"
"Lovely ya zanyi, but definitely se na bar garin nan ba zan iya zama ba, and am missing you sosai wallahi"
"Am missing You too sweetheart"
"Are you sure?" Yai maganar yana shafa sumar kansa.
"Au ƙarya nake kenan?" Tai maganar a shagwaɓe.
"Wane ni in ƙaryata Baby na, sonake in ƙara tabattar da abunda kike faɗa ne"
"Hmm to ai shikenan, bari in ƙarasa Islamiyya"
A ɗan shagwaɓe yace "ban gaji da jin muryarki ba Farhan"
"Nima haka, amma kasan komai a ɓoye nake yi"
"Hakane, kiyi fatan zamana a garin nan yai silar warwarewar matsalata"
"Insha Allah, zanyi mana Addu'a sosai, Allah yasa su barka ka dawo"
"Ameen, in ma basu barni ba zasu wayi gari suga na gudu, nace ya batun yaron nan ya kuma miki wani abu ne?"
"A'a tun ranar nan ba ƙara ganinsa ba"
"To shikenan, ki kula sosai duk abunda kika gani wanda baki yadda da shi ba ki sanar min, bana son ɓoyemin abubuwa da kike"
"Shikenan insha Allah, amma baka gayamin meya haɗaku da shi ba"
"Karki damu, idan na dawo zan baki labari, duk da ban taɓa gayawa wani ba, ni dai ki kulamin da kanki Farhan, kinji my wife".
"Karka damu, Farhan taka ce kai kaɗai, as Sadik is for only me"
Murmushi yai yace "hakane, naji daɗin wayar nan in kin rage min damuwa sosai, sekin dawo Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen ya Allah, have a nice day"
Ta katse kiran.
A hankali bacci yai awon gaba da shi, duk da ba wani jin daɗin baccin yake ba.
Nazir ya kasa zaune ya kasa tsaye, tuna sakamako ya nuna Lilly na ɗauke da juna biyu, yanzu tsoron sa Allah tsoronsa Asirinsa ya tonu, ya san ya shiga uku idan Asirinsa ya tonu, dan kuwa ya kaɗe har ganyensa, gata 'yar gidan soja ga cin mutunci da zubewar mutunci da ze fuskanta.
Ganin zaman tunani ba ze fishshe shi ba, yasa ya tashi yai wanka ya shirya, ya fita neman mafita.
Abu kamar wasa, ko Abinci ya gagari Mother ci, saboda tunanin ɗan Autan ta, abun ya dameta ƙwarai amma Abba yaƙi bata fuskar da za tai masa ƙorafi.
Duk da shima dannewa yake kawai, dan ya san Sadik ba ze taɓa jin daɗin zaman ƙauyen nan ba, amma ba ya son ya nuna dan kar Mother ta samu damar yin ƙorafi.
Yauma Sunusi ya zo gurin Farhan taɗi, sedai ba ta sauya zani ba, taƙi kula shi balle ta tofa komai, shikaɗai yake ta zubarsa kamar an kunna tanki.
Can ya nisa yace "Farhanatu, dan Allah wai meyasa idan nazo ba kya son sakin jiki dani ne? Da har gaisheni kina yi amma banda yanzu na rasa me nai miki"
Haɗe rai tayi ta sake ɗauke kanta, daga barin kallon in da yake ma saboda baƙin ciki da take ji ba duk lokacin da ta kalleshi.
"Ki kalleni mana ki min magana ko naji daɗi"
"Aikuwa ka daɗe ba ka ji ba, ni dan Allah in baka da abun cewa ka bari in shiga gida bacci nake ji"
"Haba Farhan yanzu maganar da nake miki bata da mahimmanci a gurinki? Ina son mu tattauna akan yadda zata kasance da bikinmu"
Farhan ta ɗan murguɗa baki tace "Allah ya kiyaye"
"Me kika ce?"
"Ni bance komai ba, dan Allah kaga seda safe"
"Saboda Sadik ne yasa kike min wulaƙanci?"
Waiwayowa tai da sauri ta kalle shi, amma ta basar tace "waye kuma Hakan?"
"Kin fi ni sanin waye hakan, sedai abunda nake son ki sani shine, ke tawa ce an riga an bani ke, ni iyayen ki suka sani dan haka ki fita sabgar wannan ɗan Yaron"
"Kai ka san shi ni ban san shi ba"
Sunusi yace "kin fi ni saninsa, tunda yake kawoki a mota, wato ni talaka ne shine kika ɗaura ɗambar wulaƙanta ni, to na dena lallaɓa ki in kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba"
Galala Farhan tabi Sunusi da kallo, ya akai ya san Sadik, kuma ya san shi ke kawota gida a mota.
Guntun tsaki ta ja ta shige cikin gidan su, tana cigaba da tunani.
Yauma Sadik cike da zullumin yadda ze bacci a wannan ƙungurmin ƙauyen ya kwanta, yana duba hotunan wayarsa, sosai ya dinga kuka lokacin da yaci karo da hoton Mother, yana missing ɗin babarsa sosai da sosai, ya rungume wayar yana kuka.
Vibrating wayar tayi alamar saƙo ya shigo, ya ɗaga saƙon ya fara dubawa.
"Am missing You hubby, i pray you come back soon, kar wani abu ya faru"
Saƙon Farhan ne bana wani ba.
Ya kira layinta, amma wayar taƙi tafiya, ya watsa wayoyin gefen katifa, ya fashe da kuka.
Sir Nazir yana office ɗin sa, ya turawa Lilly saƙon yana son ganinta ta wayar salula.
Kusan mintuna ashirin da tura mata saƙon se gata ta shigo Office ɗin.
Yai sa'a lokacin corper George ya fita daga Office ɗin nasa.
Ta samu guri ta zauna Sannan ta kalleshi cikin rauni tace "wace mafita ka samo mana?"
Ya gyara zamansa sannan yai ƙasa da muryar sa yace "Mafita ɗaya ce Fatima, shine a zubar da cikin nan"
Ta kalleshi tace "Amma ta yaya?"
"Ga magani na taho miki da shi, ki fara jarraba magani mu gani ko ze fita"
Lilly ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ancemin fa ana mutuwa garin zubar da ciki, ni tsoro nake ji kar Maman mu ta gane na shiga uku"
"Ba zata gane ba ai, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki bi instructions ɗin da zan baki kiyi amfani da maganin"
Lilly tace "wallahi tsoro nake ji"
"Lilly idan ba ki yadda an zubar ba yaya zamuyi kenan? Ko so kike Asirin mu ya tonu?"
Ta girgiza masa kai, yace "Yawwa dan Allah kiyi haƙuri, ki amfani da maganin ba abunda ze faru insha Allah, idan ba kya so a gane ki bari se da daddare kowa ya kwanta seki sha"
Tace "to"
Ya ɗakko wata ƙaramar kwalba wadda babu sticker bakomai a jikinta ya bata yace "ga shi nan, idan kin ci Abinci kin ƙoshi, seki shanye maganin duka, in Allah ya yadda cikin ze fita"
Ta karɓa tare da zura kwalbar a aljihun rigarta.
Ya share mata hawaye, yaita rarrashin ta harta ɗan kwantar da hankalinta Sannan ta koma aji.
Kwanakin Sadik uku a ƙauye, ba komai yake iya ci ba, ta dole ya iya amfani da banɗakin su, saboda yadda wani Abincin ke ɓata masa ciki, har wata rama yayi saboda azabar damuwa, Nana kuwa yanzu yake bata sosai da sosai, ita kanta ta san an takura shi fiye da kima.
Dama kusan kullum ana kawo kilishi ko tsire gidan Hakimi saboda Nana, ga tatattaciyar madarar shanu, ko fura da Nono da fulani ke kawowa duk dan saboda ita Hakimi yasa ake kawowa, saboda suna cikin abunda take matuƙar so.
Sadik na zaune da safe, an dawo daga wannan tilawar da ake in an idar da sallar Asuba, ya duba wayarsa yaga saura kara ɗaya a ƙaramar wayarsa, babbar kam tuni ta ɗauke.
Ba tsammani yaga kiran Mother ya shigo, cikin rawar jiki ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa.
"Auta na" shine abunda Mother ta faɗa cikin sanyin jiki.
Ai take Sadik ya fashe da kuka yace "Mother, kin manta dani kun dena sona ko? Kin san ba zan iya zama ba amma ki ka bari Abba ya kawoni ya barni a nan, life is so hard for me here"
"Sadik ba yadda zanyi da mahaifinka, fafur yace kar in kuskura in shiga maganar nan, nayi nayi da shi ya ɗakko min kai amma yaƙi, yanzu ya kake?"
"Mother wallahi zan mutu in ba'a zo an ɗauke ni ba, na gaji wallahi, komai ba daɗi am missing You so much"
"Am missing you too my love, dan Allah Sadik ka dena kuka zan cigaba da lallaɓa mahaifinka wallahi ko bacci bana iyawa"
"Mother, am living for 3days without hearing from you, am missing home dan Allah Mother ki zo ki tafi da ni, wallahi bana son irin Abincin da suke bani, bana jin daɗin komai"
Kawai Mother ta fashe da kuka, ji tai an zare Wayar daga hannunta, ta juya da sauri taga Abba ne a tsaye ya kara wayar a kunnensa yace "Sadik meyasa zaka ɗagawa mamanka hankali meye haka? Kukan me kake?"
"Abba ka dena sona, ka barni a garin nan ni ba zan iya zama ba, am missing home dan Allah kazo ka tafi dani"
Abba ya danne zuciyarsa a kausashe yace "Kai nutsu, da girmanka zaka dinga