Chapter 7 Reading MIJIN BABATA NE Book Complete by Ummu Jafar.txt Arewa Novels

MIJIN BABATA NE Book Complete by Ummu Jafar.txt

Author :  Ummu Jafar Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   7 / 8

18K to 21K   out of 21.7K words

masa alamar eh, hawaye ne suka riƙa zuba a idonta saboda ƙaryar da tayi musu.

Dady ne ya kalle Mumy yace ko zata iya raƙata har agane inda dangin ta suke?.

Mumy daman ita tunda taga yarinyar tashiga ranta, ai Dady ko baki bai rufe ba Mumy tace,

" Ai ɗa na kowa ne, Allah ya tayamu riƙo".

Da Ameen suka amsa, sannan Mumy tariƙa hannun Hasa'u suka fito dan su koma gida.

******
Koda gari ya waye mijin Mumy yacewa Mumy ta bashi kuɗin saboda baya son ya makara, ko beark batayi ba jiki na karkarwa ta tashi tace yayi mata izini zata je gidan ƙawarta ta dawo, izini yayi mata tare dayi mata kashedi karta jima, tace yanzu bazata jima ba zata dawo.

Mayafi ta ɗauka bata tsaya ko ina ba sai gidan wata ƙawarta wato Hajiya Suwaiba mai adashe.

Sosai Hajiya Suwaiba tayi mamakin ganin Mumy dan ita kan rabonta da Mumy tunda ta aure tsinanin yaro nan, kallon Mumy tayi sama da ƙasa tace,

" Amarya kece yau agidan? ina ango yake yabarki kika fito yanzu da sassafin nan, ko har kungama cin amarci ne?".

Mumy tace,

" Ke ni banso haka daman ko yana nan ai zan fito".

Wani kallo Hajiya Suwaiba tayi mata kana tace,

" Kedai Allah ya kyauta, ina ƴata Hansa'u?".

Gaban Mumy ne ya faɗi dan wallahi ita har ta manta da wata Hansa'u, kawar da tunanin Mumy tayi tace,

" Keni ba isakanci nazo kimin ba, daman kuɗi ne nazo ki aramin har zuwa ƙarshin wata, saboda mashin zan saya na basuwa haya, kuma jiya koda aka je ya ƙara kuɗi, shine nace bari nazo wajanki nasan zan samu".

Da yake da Hajiya Suwaiba da Mumy akwai amana, ba musu Hajiya Suwaiba ta tambaye Mumy nawa take so, gaya mata tayi ta ɗauko mata, haɗi dayi mata fatan alhairi.

Mumy ana bata kuɗi jiki na karkarwa tayi ma Hajiya Suwaiba sallama ta kama hanyar komawa gida.


Koda tashiga gida yana waya da budurwarsa yana gaya mata yau yake son su haɗu da ƙawayenta shi ya salamesu yasan ya gama da komai amaryarshi kawai yake jira, jin Mumy tayi sallama ne yasa yayi mata sallama akan sai yazo .

Amsawa Mumy sallama yayi yana faɗin,

" Oyoyo Baby kin dawo, sannu da hanya kinji ƴar aljannah, dan indai nine to na janye miki ƙafa kishiga aljannan mosoyiya".

Sosai Mumy taji Daɗi, dan haka cikin shagwaɓa ta faɗa jikinshi tana faɗin,

" Baby andace ka gansu nan".

Bakinshi ya haɗe da nata ya fara tsotsa, har yayi nasarar rabata da kayan jikinta, wasa yashigayi da ita son ranshi yana nuna mata zallah soyayya, amma tabbas idan yana tare da Mumy tunanin Hansa'u ce yake tare da ita shiyasa yake zaucewa wani lokaci.

Sai da yashayar da ita ruwan soyayayya, sannan daga baya yayi wanka yayi beark kana ya karɓi kuɗi yafita.

Kai tsaye gidan iyayenshi ya nufa, koda yaje yasamu Yayarshi da ƴan uwanshi ana taganin kayan lefe akwati biyar akayi mata, sosai yaji daɗi shida ƴan uwanshi, shaida musu yayi ko gini yau za'a kammala koma na gidanshi amarya kawai suke jira, daɗi suka ji kamar su zuba ruwa a ƙasa susha.

Kuɗi ya bawa Auntyn shi yace a sayo ma Babarshi kayan da zata sa ita da Babanshi ranar aurenshi, aikuwa sun jidaɗi ba abinda suke samasa inba albarka ba, daga bisani yayi musu sallama ya fita.

Yau duk wani abu wanda ya rage sai da ya kammalashi na aurenshi har kayan da zai sakawa sai da ya saye ya kai ɗinki, sauran kuɗi ya kai ajiya saboda idan Amarya tazo yasamu abinda zasu kashe.

Bayan ya kammala sannan yaje wajan abokinshi yace dan Allah sutafi wajan mai gidanshi mashin yake so abashi yana acaɓa.

Haka kuwa akayi suka je mai gidan abokinshi yace yaje gobe za'a bashi mashin amma fah shekara ɗaya ne zai gama, sosai yaji daɗi yayi masa godiya sannan ya koma gida wajan Mumy ya shaida mata gobe za'a bashi mashi.


===================

Babu ɓata lokaci Hauwa ta isa wajan da aka shaida mata Ahmad na can, koda taji ta sameshi, yana ganinta yayi murmushi yace,

" Rai kanga rai, tun ranar bansake ganinki ba?".

Murmushi Hauwa tayi tace,

" Koni bansake ganinka ba , ko yanzu hanya ce ta haɗa mu, saboda har zan wuce na ganka zaune shine nace bari na zo mu gaisa".


Murmushin jin daɗi yayi yace,

" Gaskiya kin kyauta kuma nagode".

" Bawani ka gode zo karakani wallahi daman ina ta tunanin yadda zanyi tafiya ni kaɗan, hala ina Hajiyar ka ta barka kai kaɗai?".

Hauwa tafaɗi haka haɗi da ruƙo hannusa suka fara tafiya.

" Wallahi yau biki garesu, ai jina nake duk ba daɗi".

" Ayya ai tunda kasaba kullum kana jikinta dole kaji ba daɗi".

Ta faɗi haka dai-dai lokacin da suka tsayar da mai napep.

Shiga sukayi basu tsaya ko ina ba sai unguwar da ta kama hayar ɗaki, kai tsaye ɗakin ta buɗe suka shiga sai wani rangwaɗa take mishi, shiko sai kallonta yake yana murmushi birgewa.

Lemo ta kawo masa mai sanyi ta aje gabansa, zama tayi kusa dashi kamar ta mayar dashi ciki sosai Hauwa ta birgeshi dan yanzu shima yasan sirrin gari, gwara ya tsaya ya kwashi gara, suna ciki haka Hauwa sai daɗi takeji tarkonta yayi, wayarshi ta fara rura, kin ɗauka yayi saboda ya shagala sai wasa suke shida Hauwa.

Sai da aka saki kira sannan yayi ƙarfin halin ɗauka, koshi dayaga sunan Mamarshi ya bayyana.

Tun baiyi magana ba Mamarshi tace,

" Duk inda kake kazo wallahi ance ga mahaifinka can rai hannun Allah, dan Allah Ahmad kaje ko dan albarkar haihuwar dana maka".

Ta kai ƙarshin zanci da fashewa da kuka.

Bai ce da ita komai ba ya tsinki wayar kana ya dube Hauwa yace,

" Bari naje na dawo?".

" Ina zaka tafi?".
Tafaɗi haka tare da zare ido.

"Wallahi mahaifina ne ba lafiya shine zanje".

" Ayya to in ba damuwa ko zamu iya zuwa tare".


Yace muje bawata damuwa........




*COMMEN AND SHARE*



*SUMMY M NA'IGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*




*SHAFI NA 19*


Har Hauwa zata ɓuda baki ta yi magana sai Inna tace

" karki kuskura ki gayawa mijina magana ai ko ba komai ubanki ne".

Abinda ke damunta ne yasa ta kyalesu ta fara ɗaukar kaya tana kaiwa ɗakin da yace, sai da ta kammala sannan lnna tashi ɗakin haɗi da zama gyafin katifa, kallonta Hauwa tayi idonta taf da hawaye tace,

" Kaicona lnna! lnna bakimin zaɓin uba ba wanda zan nunawa duniya nace shine ubana, kisana yau ina cikin ƙunci da ta kaicin kasancewa ta ƴa ga Babana, ashe lnna Baba na da ɗa Ahamd shine baki taɓa gaya min ba?".

Kallonta lnna tayi ciki da mamakin ta tace,

" Wani Ahamd kuma? ni dai nasan tunda mahaifinki ya sakeni bansanshi da wani ɗa ko ƴa ba wadda akace yau ya aure ya haifa, sai dai idan na matan da yake tare da sune, to wani abu ne ya faru?".

" Barshi kawai lnna bazaki gane ba, danshi ake so mutum yasan wanda zai aura".
Ta faɗi haka lokacin da take tashi ta bar ɗakin.

Tana fita dai-dai lokacin da ake shigo da kayan amaryar Alhaji Abu mata sai kuɗa suke, tsaki Hauwa tayi kana ta dube matanshi da ƴaƴanshi dake tsakar gida kowa na sabgar gabanta tace,

" An daiyi asara, ni banyi dacin uba ba wasu basuyi dacin uba da miji ba".

Tana faɗin haka tasa ƙafa ta bar gidan saboda taje ta samu mafita.


Sosai hankalinshi ya tashi ganin Hauwa ta tafi kodan halin da taga mahaifin shine, wata ƙila haka ne, amma har ga Allah Hauwa tashiga ranshi dan shi yanzu burinshi bai wuce yaganshi tari da ita sona shan soyayya ba, amma gaskiya Mamarshi bata kyauta ba, da yanzu yana can yana hutawa da Hauwarshi mai kayan ni'ima, yajima tsaye yana tunanin yadda zaiga Hauwa sannan ya samu wasu almajirai manya ya gaya musu aikin da za suyi musu sannan ya dawo wajan mahaifinshi, gyaran jiki da ɗaki akayi haɗi da sanya turare aka sauya mishi ɗaki sannan ya biya su suka tafi.

Bayan ya bashi fura yasha ne yasamu ya buɗe baki da ƙar yace,

" Amadu ina Hauwa'u, ba yanzu nagan ku tare ba, amma gaskiya naji daɗi da kuka san juna".

Kallon Baban Ahamd yayi tsaf sannan yace,

" Baba daman kasanta ne?".

Murmushi yayi irin na ƴan duniya yace,

" Kamar ya nasanta Ahamad, na haifita sannan kace na san ta"......." mikace Baba!".

" Nace nasan wannan aikin iyayenku ne suka haɗa ku, ko dai kun je gidan lya gaishta ta haɗaku, dan haka kasani baka da ƴar uwa kamar Hauwa, duk nine na haifeku , amma kuyi haƙuri da yadda rayuwa tazo".

Jikin Ahamd ne ya ɗau karkarwa kana yace,

" Kana nufin Hauwa Yaya tace?".

" Eh wallahi hala kai ka ɗauka kaine yaya, saboda ka ganta da ƙaramin jiki ko, kai ko ka biyoni da Babban jiki".

" Nashiga uku, amma Baba kacutar damu dan wallah a halin yanzu Hauwa budurwa tace!!.

Da ƙafi uban ya tashi zaune abinda yajima baiyi ba, kullum yana kwance saboda ya kasa koda tankwashi ƙafar bare asa ran zai iya mutsi yau shine ya tashi zaune saboda razana.


A hankali yake taka ƙafarshi har ya isa parlour da yake tunanin zai sami mahaifiyar tashi, zaune take tama kallon labarai tayi kyau abinta da ka ganinta ba abinda ke damunta.

Da sallama yashigo, karɓa masa tayi batare da ta ɗago ta kalleshi ba, wanja ƙafarta yazo ya zauna sannan ya gaisheta haɗi da jingina kansa a ƙafarta.

Yajima ahaka amma bai ji tayi masa abinda take masa ba, wato tasanya hannuta akansa tana ya mutsar masa suman kanshi, haka take masa tun yana yaro shiyasa yake son tayi mishi haka.

Dubanta ya yi har ya buɗa baki yayi magana sai yaji muryar Dady na faɗin,

Ɗan Hajiya saukar yaushe?".

" Duk da yanzu ka girma shiyasa naga ko tafiya zakayi babu dole kasanar damu".

Murmushi yayi haɗi da basu haƙuri yace tafiyarce ta zo a bazata, sai Dady yace to muma yau zamuyi maka baza ta, dan tabbas ƙarshin watannan zamu ɗaura maka aure da wadda duk wadda muka ga dama, amma idan kaga mu bamu isa da kai ba kaje kagayawa Hajiyar da ke goya maka baya.

Har ya buɗe baki yayi magana sai Dady yace bana son jin komai daga gareka nariga na gama magana sai ka farashirin karɓar amarya kai da abokanka da ƴan matan ka.

Dady na gama faɗar haka suka barmishi parlour kanshi sai juya masa yake.

Yau saura kwana biyar a ɗaura aure Kabir da amaryarshi Nana, kuma a yau ne Kabir yake so ya gayawa Mumy zaiyi aure, danshi koda gari ya waye ba inda yaje, duk abinda take son shi yake yimata, sai kwasar soyayyya suke ta mutunci, ita ko Mumy sai kafa-kafa take kar tayi abinda zai ɓata mishi rai, ranar gida ya wuni har dare, bayan sunci abinci sunyi wanka, dan yau ko wanka tare sukayi , har man shafawa shi ya shafa mata haɗi da sanya mata kayan bacci waɗanda ranshi ke so, kallonta yayi ciki da nuna mata tsantsar so yace,

" Baby wallahi sonki ko da yaushe ƙara ruruwa yake a zuciya na, dan Allah ki taimaka min kici gaba da zama dani kada ki barni, duk da a halin yanzu ni mai laifine a gareki".

Bata ce dashi koma ba ta haɗa bakinshi da nata waje ɗaya suna kissing ɗin juna, sai da sukayi son ransu sannan tace,

" Baby duk yadda kake sona ni nasan nafika sau dubu wallahi soyayayarka zata illatani dan Allah kar ka barni, burina a koda yaushe naganin tare da kai".


" Muna tare masoyiya ta, ba wanda ya isa ya rabamu ko anƙi ko ansu dole abarmu, amma ina so ki fahince ni, wallahi nima badan son raina haka zata faru ba, kiyi haƙuri kinji, saboda Mumy ce ta haɗa ni da ɗiyar abokiyar ta, wai ita yarinyar ce ta ganni wai ba wanda take so sai ni, duk wanda yafito tace sai ni, shine su Baba suka ce tunda yarinya tace ni take so nayi haƙuri ayi aure, tun kafin na buɗa baki sai Mamarta tace komai ta ɗauke min har sadaki itace zatayi komai, burinta kawai na aure yarinyar, shine Baba yace to tunda haka ne ranar alhamis za'a ɗaura aure".......wata ƙarace Mumy ta sanya wadda gidan gabaki ɗaya sai da ya amsa.....





*SUMMY M NA'IGGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*Tsarawa da rubutawa*
*💞UMMU JA'AFAR💞*





*SHAFI NA 18*

Tashi sukayi kai suka fita, ɗaki ta rufe kana suka kama hanya zuwa dubin Baban Ahamad, mai napep suka tsayar Ahamad ya gaya mishi sunan unguwar da zai kai su, tana jin sunan unguwar tace itama idan sun gama dubiyar Babanshi itama su zo aduba Babanta, yace da ita ai ba damuwa Allah ya basu lafiya.

Dai-dai ƙofar gidan mahaifinta yace mai napep ya tsaya, kallonshi tayi sosai amma ta kasa buɗa baki tayi magana.

Bayan sun sallami mai napep suka kama hanyar shiga gidan, gabanta ne yayi mummunar faɗuwa lokaci ɗaya wani jiri ya fara ɗi barta.

Faɗuwa ta tafi tayi Ahmad da sauri ya rungumota haɗi dayi mata sannu, kallonshi ta farayi amma ta kasa magana har suka shiga ɗakin da yake kwance sai wari yake saboda yayi kashi kuma anrasa mai kula dashi.

A wannan lokaci Ahmad ne ya rufe hancinsa, ita ko saboda shiga ruɗani ko warin ɗakin bata jiba, a hankali ta buɗa baki tace,

" Ahmad shine ma haifinka?".

Bai ce da ita komai ba ya riƙo hannuta yafito waje kana yace,

" Kiyi haƙuri Baby nazo dake wannan wajan ko?".. ...tsawa ta daka masa tace,

" Tambayarka nayi kabani amsa?".

" Eh shine Hauwa, nasan bai dace yazama ubana ba ko, kiyi haƙuri nima bana jinshi a matsayen uba".

Hannu Hauwa ta ɗaura saman kai kana tace,

" Shikenan tawa ta ƙare!.

Ta faɗi haka hawaye na zuba a idonta.

Da sauri ta bar wajan cikin tafiyar gudu-gudu sauri-sauri.

Ahamd na ganin haka shima ya fara sauri yana kiran sunanta amma ko wagowa batayi ba bare yasa ran zata karɓa.

Yana ciki sauri dumin ya kamota sai ga mai napep ta tsayar shiga tayi haɗi da faɗa masa inda zai kaita tace yayi sauri.

Dai-dai ƙofar gidansu aka sauke ta, kuɗi ta bashi batare da ta karɓi canji ba tashiga gida hankali tashe.

Tun a soron gida ta fara jin hayaniya natashi haɗi da jin sautin kukan Babarta, cikin azama ta faɗa gidan kamar walkiya, abinda idonta yaganine yasa tayi tsayuwar daba tashirya ba.

Kayan ɗakin Babarta ne aki fitar wa waje ga Alhaji Abu na tsaye yana faɗin wallahi in har bazaki zauna wancan ɗaki ba wallahi sai dai ki bar gidannan da tabbas ba wanda ya isa ya hanani aure......tun bai kai ƙarshin zanci ba Hauwa tayi dirar mikiya kansa tace,

" Aure ? da wace abu zakayi aure? wace kaddararrace zata aureka?".

" Uwaeki ce kaddarra ita da ta aure tsohon ɗan tashi irin ubanki".

Ido da hanci Hauwa ta saki tana kallon Alhaji Abu, a hankali ta furta mike shirin faruwa dani ne!.

Bayan su Mumy sun sauka gida ɗaki ɗaya aka warewa Hansa'u akace shine ɗakin ta, kuma idan bai mata ba za'a sauya mata ɗaki, godiya tayi harda kukanta saboda wannan kularce bata samu ba a wajan Babarta.

Kwanan shi biyar garin abuja sannan ya dawo gida, kai tsaye part ɗinshi yashiga, wanka yayi sannan ya nemi waje ya kwanta dan ko iyayenshi basu san ya dawo ba bare abokanshi, sam ya manta da wata yarinya gaba kiɗaya ya manta da ita bare yace yaje gidan hutawarshi.

Baccinshi yayi mai isarshi sannan ya tashi yayi wanka kana yayi sallah sannan ya fito dan ya gsishe da Mumyn shi.


Abdulrazak kenan yaro kyakyawa ga kuɗi ga aji.

Koda gari ya waye ya je karɓar mashin akace ba'a kawo ba sai sati mai zuwa, dan haka yazo ya shaidawa Mumy halin da ake ciki da ta tambayeshi ba kasuwa yaje saya ba, sai yace akwai wanda yayarda dashi kuma shi mutmin yasan mashin mai kyau shiyasa ya bashi yaje legos ya sayo masa.

Sai Mumy tace ai tunda ga kuɗi isasu da kasaye abunka anan yafi tsayawa jiran aje logos, yanzu da hanya ba kyau.....har ta buɗa baki tayi magana ya daka mata tsawa yace,

" Badan kin bani kuɗi bane zaki tsareni da faɗa, idan kuɗin ki kike so sai a mayar miki ai ba dole, kuma ba roƙonki nayi ba ke kikayi ra'ayi ki bani, sannan zaki zo ki tsareni da maganar banza".

Jiki a sanyaye Mumy tazo ta faɗa jikinshi tana faɗin,

" Dan Allah Baby kayi haƙuri wallahi ni ba haka nake nufi ba dan Allah Baby".

Ta faɗi haka kamar tayi kuka.

Tsaki ya jamata haɗi da tunkuɗeta daga jikinshi ya tashi ya shirya yafice gida.

To tundaga lokacin ya sauya ma Mumy, idan ya fita gida baya dawowa sai ƙarfe ɗaya na dare idan kuma gari ya waye tun ƙarfe bakwai na safe yafice kuma sai ƙarfe ɗayan dare, Mumy tayi kuka har ta zuba masa ido, shiko duk ba komai ke riƙeshi ba sai hidimar bikinshi......


Commen and share.


*SUMMY M NAIGE✍️*
*🤦‍♀️🤦‍♀️ MIJIN BABATA NE🤦‍♀️🤦‍♀️*




*ZAFAFA WRITTERS FORUM....📚✍🏻*

*Z.W.F.🏝️*



*MARUBUCIYA*
*UMMU JA'AFAR✍️*




*SHAFI NA 20*


Haɗe yayi a jikinshi haɗi da buga bayanta, sosai ya kijin yadda take sauke zuciyar, haƙuri ya fara bata kana yace,

" Kinsan Allah duk son da nake miki da kinyi min haukar nan da mata keyi wallahi zaki sha mamaki dan wallah zan baki horo wanda bakiyi tunani ba, shawara nake baki gara ki natso ayi komai cikin kwanciyar hankali".

Yana faɗar haka ya sauke ta daga jikinshi cikin nuna ɓacin rai

Tana ganin haka ta tashi jikina na karkarwa tace,

" Baby karka damu wallahi na ɗau alƙawri bazanyi tashin hankali ba, amma kasan dai dole nayi kishi akanka ko?".

" Naji".
Haka yace da ita a taƙaice.

Fuska haɗe ya tashi ya shirya ya bar gidan ko beark bai tsaya yayi ba, ba yadda batayi ba yace a'a akwai inda zai je.

Badan taso ba haka yashirya ya bar gida.

Tunani ta fara tayaya za ta karɓo mijinta dan itakam tabbas bata son

7 / 8