Chapter 4 Reading Yar Talakawa Complete Hausa Novels by Afrah.txt Arewa Novels

Yar Talakawa Complete Hausa Novels by Afrah.txt

Author :  Afrah Category :  Home Of Novels

Chapter   4 / 15

9K to 12K   out of 44.9K words

tana tunani a zuciyarta, lallai wannan matar batayi halin mum ba ko da kwayar zarra, shi kuma kato dashi amma sai wani shagwaba yake mtsww
[8/8, 3:56 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳🌳



By~ afrah


+2347010902548
Episode 1⃣3⃣





Taje ta kira lucy, aka kawo wa moha drink, sai kallonta yake, kallon rashin sani, ameer na haduwa da fu'ad sukayi dan wasa sai, yazo ya same ta a waje wurin balcony tana kallon flowers, dan zaman cikin ya ishe ta, ko nace tsayuwar cikin. Aunt neena muje gida, smiling tayi tace toh ta mika masa hannu.


Yau watan ta daya da fara aiki, kullum weekend tana zuwar wa umma, yaya habu an gama masa komai na tafiyar sa shima next week zai tafi, umma a kullum tana godewa Allah daya kawo masu taimakon su.

Yau da yamma ci, suna falo ita da ameer da zarah da zuby, game sukeyi , irin wanda ake kullewa mutum daya ido sai ya nemo sauran, mum na wurin mami, suna firan su, dan duk yamma sai sun hadu sun gaisa, gwanin sha'awa kamar wasu sisters suke..

An kolle wa neena ido sai faman neman su takeyi, sai dariya suke mata dan sai karo take ci da kujerun falon.
Bude kofar falon akayi, zarah dake kusa da kofar, ta kallo kofar zatayi masifa mai yasa ba'ayi knocking ba, aikuwa sukayi 4 eyes da ya Prince, har sai data sarke da miyau dan batayi tsammanin ganin saba, duk da yake ma idan zai zo baya wani sanar wa kowa. zuby ma ta kallo kofar itama taga ya prince, da sauri ta sauka daga bisan kujerar da take tana yiwa neena dariya, ameer ma sai da hanjin cikin sa sukayi kara , dan yasan halin papa dinsa.

Ita kuwa neena da ido ke kulle, sai faman neman su takeyi, har taje wurin kofa tana laluben ta, jin ta taba mutum sai ta hau murna, ta rirrike kam tana cewa, ya zarah na kama ki, now turn dinki ne, sai tattaba shi takeyi tana tsalle, wani kallo yabi ta dashi, daga kasa har sama, zani ne a jikin ta na atamfa, yadan koke, sai top data dan sha jiki itama ta fara fading, tabe baki yayi, ya wani yamutsa fuska , fuskar nan ta tamke, yasa hannun sa ya turar da ita , neena na faduwa tayi yar kara, ta bude idon ta, bayan shi ta gani yana hawa sama, hes a tall n giant man, yana sanye da wandon soja da body hug fara, saboda yadda yayi building din jikinsa top din ta zauna masa sosai a jiki. yana tafiya cikin kasaita, WANNAN WAYE? shi kuma, neena ta furta, a tunanin ta a zuciyarta tayi maganar amma ashe a fili tayi, sai dai taji muryar ameer kusa da ita yace, he's my Papa......

Mikewa tayi tana wash, zuby tayi saurin mikewa tsaye tana wiki wiki da ido, zarah ta rike kugu, yau mun shiga uku, zuby tace tara ma muka shiga ba uku ba, kinsan yadda ya tsani ganin babba yana wasan yara!!! Neena ta mike itama tana kallon su tace, wancan shine papa din little master???, suka hada baki wurin cewa Yes shine, a zuciyarta tace lallai ashe akwai rigima, dan da ganin sa dan rainin wayo ne.

Da daddare a dinning, dad da mum da zuby, suna cin abinci, prince ya sauko shima, dukawa yayi ya gaisar da iyayen sa, mum ce ta amsa masa a sake, dad kuwa daure fuskar shi yayi kawai, prince ya mike shima ya zauna.
Gabadaya zuby hankalin ta a tashe yake, bata son ma su hada ido dashi, kee! Baki iya gaisuwa bane? Zuby har sai data kware da juice din da take sipping, na'am ehh uhm ina wuni? Mtsw prince yayi tsaki, sannan ya kalli kujerar ameer yaga wayaam.
Zuby ya kalla yace ina ameeer din shi?, mum tasa baki tace, yana daki da nanny dinsa, kasan yanzu baya cin abinci a dinning, girki take masa suci a daki.
Prince ya mike, nanny? ?? Wace irin nanny ce da za'a bari tana bawa yaro abinci a daki
[8/8, 3:56 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳🌳



By~ afrah


+2347010902548
Episode 1⃣4⃣-2⃣0⃣






Dad a fusace yace, idan baka son nanny ta kular maka da yaro, mai ya hana kayi aure duk shekarun nan!!!
Mum da zuby sukayi saurin kallon dad, prince ya wani wuce fuuuu, ya haura sama, direct dakin ameer ya nufa a kule, wacece wannan da zata sa dad yayi masa maganar nan daya tsana a rayuwar sa"ace yayi aure".

Neena da ameer a daki, ta gama basa abincin sa, ta zo zata dauke plates din, ameer yayi tsalle ya haye bayan ta yana dariya, neena tayi dariya itama ta dauke shi, ta fara masa doki a bayanta. Sai dariya yake kyalkyatawa, suna cikin wasan dokin su, prince ya banko kofar ya shigo.

Tamkar wani zaki ya shigo musu, da sauri neena ta juyo dan ganin waye, ya shigo haka ba sallama balle knocking, ganin wannan kyakkyawan mutumin nan tayi wanda kullum take yaba kyawun shi, idan ta kalli pic din nan dake ajiye a bisan side drawer din ameer, amma mai domin taga murmuahin nan nasa na pic, sai taga fuskar nan a hade gam.

Wani banzan kallo yabi da shi, ameer kuwa yayi saurin saukowa daga bayan ta, yayi wurin papa dinsa, papa papa,! Prince ya riko hannun sa, zai fita da yaron, neena tayi saurin cewa, lokacin barcin sa yayi...prince ya tsaya cak, lallai wannan yar kauyen nan yar talakawan, shi take fadawa lokacin barcin dansa yayi, ita din ma bata wuce a raine ta.

Neena ganin ya tsaya sai ta matso, hannu ta mikawa ameer tace, little master, its time to sleep, muje ka kwanta, ameer kuwa ya mika mata hannu.
Prince ya juyo ya kalle ta, ta kuwa kura masa nata sexy idanun, prince yace, kee wacece da zaki fada min lokacin barcin dana yayi? Neena tayi masa murmushin ta tace, saboda nice mai rainon sa, prince ya kara kulewa see dis small rat woo, hararta yayi yace, na kori nannies sunfi goma, dan bana son raini, da shishshigi, dan haka ya nuna ta da yatsa idan baki kiyaye ba, zakiyi..... ya nuna mata kofa.
Neena tayi kasa da kanta kawai ta koma wurin ameer dake jiran ta ta kwantar dashi, prince yayi waje ya banko kofar, neena ta kalli kofar tace, an dai yi kyaun dan maciji.


Washe gari da safe, neena ta gama shirya ameer dan zuwa makaranta, ta kai shi har mota ta dawo, mum na saukowa dan fita zuwa aiki, neena ta gaishe ta sannan tace, ki shirya wa Na'im breakfast pls, ladi mai aiki bazata zo aikin safe yau ba, neena tace, toh mum, ta bude baki ta tambaya waye shi, amma har mum takai kofa dan cikin sauri take.
Tana nan tsaye ta rasa mai zata girka , dan bata masan waye Na'im din ba, zuby ce ta fito tana gyara gyelen ta, da gani itama cikin saurin take, neena ta tare ta dan ta bata shawarar maia zata girka, tace anty zuby ina kwana? Zuby na saurin ta tace lafiya neena, nizan fita lecture sai da rana zamu dawo, neena tace anty zuby dan minti uku, zuby tadan tsaya tace neena zarah na waje tana jirana yi sauri, neena tayi saurin karasowa wurin ta tace, mai zan dafa na breakfast wai na Na'im? Zuby tace ki dafa masa abu mai sauki kawai tunda bawai kin kware bane, tayi saurin yin waje.

Neena ta rike kugu, abu mai sauki, miye mai sauki? Mtsww , kicin ta nufa , tayi tsaye tana tunani, can tace, bari nayi masa, koko da kosai , tayi murmushi abincin yaya habu kenan.

Ai kuwa niimatu tahau, hada kokon ta dama akwai kullun, kosai kuwa har fita tayi tabi layin su neman nika da kyal ta masu wurin da akeyi, aka mata ta dawo da sauri ta hada komai, tana gamawa ta wuce daki da sauri tayi wanka sannan ta dawo falo tana karatun wani book na uncle faruk daya manta.

Tayi awa daya amma shiru bako bai zo ba, can taji kamar tafiya daga bayan ta, saurin juyowa tayi, taga papa din ameer ne, prince bai ko kalli inda take ba, dinning ya nufa yaga wayam, ladi ya fara kwala wa kira, yaji shiru, neena tayi saurin zuwa wurinsa tace, ladi bata zo ba, ya wani yamutsa fuska, yace ina abincina? Niimatu tace nima ban sani ba, yaja tsaki ya ciro wayar sa ya kira mum, can ya kashe wayar ya kalli neena yace, ke! Tayi saurin kallon shi, yace mum tace abincina na wurin ki, niimatu ta girgiza kai, ni abincin Na'im akace nayi
[8/8, 4:01 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳🌳



By~ afrah


+2347010902548
Episode 2⃣1⃣-2⃣5⃣







A fusace prince yace, kee da Allah je ki kawo min abincina!!!, neena tayi saurin shigewa kicin dan yadda yayi mata tsawa ba karamin tsorata tayi ba.

Yana zaune a dinning, yana danna wayar sa, duk a kule yake yau dinnan, gashi suna da meeting da general yau.

Neena ta ajiye masa abincin, ta juya zata wuce, dan ta fara tsorata da shi, tsawar ya kara daka mata, ke! Zo kiyi serving dina!, neena ta dawo kamar ta fashe da kuka.
Ta fara bude flask ta zuba koko a cikin cup, da sauri prince ya matsa yana toshe hancin sa, ya mike yana nuna cup din, miye wannan haka dake da odour din nan, neena ta kalli cup din, koko ne lafiyayye tayi, tace koko ne, prince yace yuks, pls jeki zubar dashi pls, neena ta sauke lumfashi ,sannan ta dauke duk abunda ta kawo ta kai kicin, takaici ya ishe ta sosai, duk wahalar dasha ya zama a banza.

Washe gari Saturday ne, ranar zataje weekend dinta, kuma tayi sallama da yaya habu.

Sai data gama komai na hidimar ameer, sun fito falo ita dashi, uncle faruk, zarah, mum, da prince ke a zaune, da gani dai prince din yau shima baya da fita.

Suna shiga falon, neena ta gaishe su, hannunsu a sarke ita da ameer, mami tace, su ameer za'ayi kewar neena, mum tace aikuwa dai, ta bar mana rigima.
Zuby ce ta shigo falon da cup a hannunta, wannan kokon fa a flask na ganshi, kuma da zafin sa, tayi one sip tace wow da dadi, neena tace ni nayi jiya, ta kalli prince da gefen ido, ya wani basar kamar baya wajen.
Zarah ta mike ta nufa kicin din tana cewa, nima bari na zubo nawa.
uncle faruk daya gama amsa waya yace, neena kawo min book din nan pls, neena tayi saurin zuwa ta kawo masa, tana mika masa tayi musu sallama ta tafi.
[8/8, 4:01 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳🌳



By~ afrah


+2347010902548
Episode 2⃣6⃣-3⃣0⃣







A tsakar gida ta iske umma, tana zaune suna fira da wata laraba, nan makotan su.

Da gudu ta shigo gidan cikin murnar ta, umma tace kee, kuma bako sallama? Neena tayi dariya dokin ganinki ya mantar dani umma na, laraba tayi dariya, tace niimatu har an shigo mana kenan?, neena na shirin zama tace ehh na shigo inna laraba ina wuni?, inna laraba ta amsa da lafiya, sannan ta mike tayiwa umma sallama ta fita.


Su niimatu sunsha fira sosai da umman ta, sai tambayar yaya habu takeyi, umma tace ai ya fita siyo wasu kaya dazai tafi dasu.

Bayan sallar mangariba, yaya habu ya shigo gidan, da gudu neena taje ta rungume shi tana murna, yaya habu yayi dariya, ke bakya girma, neena ta shagwabe fuska tace, baka missing dina, kullum nazo weekend ban cika fa haduwa dakai ba, yaya habu ya shafa kanta, ina missing dinki mana, ya mika mata wata leda, ta amsa tana murna, laaah fruits ne umma, umma tayi murmshi ai sai ki ta sha, sarkin kwadayi.

Washe gari da sassafe, yaya habu yayi sallama dasu, neena tayi tayi umma tabar ta ta raka sa amma umman tace a'a; har kuka tayi dazai wuce dan Allah ya hada jinin su sosai da yaya habu.


Ranar da neena ta tafi weekend, da daddare family na falo, abba daya dawo daga tafiya yace, su neena har an tafi weekend dinne? Mum tace ta tafi dazu da safe, dad yace ai yarinyar tana kokari sosai, faruk yace gaskiya kam, kullum tana nan tare da ameer tana kula dashi, ameer dake kwance kusa da zarah ya mike, yayi wurin mum yace, grany ina jin barci, mum ta kalli zuby, zubaida kai shi dakin shi, zuby na mikewa ameer ya make kafada, ni wurin papa zan kwana, dad yace toh kaishi wurin mahaifi nasa, ai gara yadan taba rainon dan nashi, abba yace, na'im kam sai addu'a, dad yaja tsaki, ai ba biye masa zamuyi ba, shekaru har shidda, amma mutum ya kasa ci gaba a rayuwarsa, mami tace a kara masa hakuri yaya, mum tace, abun nasa ne ya wuce wuri dayawa, dad yace , ni na gama yanke hukuncin yi masa aure da koma wacece, mum tayi saurin kallon dad,"ita kam bata son ayiwa danta dole"
Dad ya gyara zaman sa yace, idan faruk ya kammala bautar kasar sa, hadasu zamuyi ayi musu aure kowa ma ya huta, abba ya kada kai hakan ma yayi.

Zuby na kai ameer, ta iske prince a zaune yana amsa waya, da gani da ogan sa yake magana, dan yadda ya nustu.
Tana kaishi tayi saurin barin wajen.
Ameer ya samu wuri ya zauna, yana kallon papa dinsa dake waya, prince na gama amsa wayar ya kallo ameer, come n sleep dear, ameer ya mike ya karaso kusa dashi, yace papa sai an canza min zuwa kayana barcina, an wanke min baki, prince ya mike a gajiye yace , kaje kayi sai kazo mu kwanta cos am sleepy already, ameer yaa make kafada papa, ni ban iya ba, prince ya tsaya daga cire rigarsa da yake yace, ohh god toh muje na maka.

Sunje dakin, komai a kimtse an gyara, prince ya dauko masa wasu green nighties, ameer yayi saurin cewa , no papa green din na monday n friday ne, prince ya saki baki, kayan barci ake raba wa kwanaki, jawo amir din yayi yace, oya sa ni bana da time, amir ya turje yaki saka kayan shi na friday ne da monday, ai blue din ne na Saturday, prince yajaa tsakk ya dauko masa blue din ya saka masa.

Oya muje toilet ayi brush din, zasu shiga amir yayi saurin tsaida prince, stop papa, ya dauko masa takalmin da neena ke sakawa idan zata shiga toilet din, sa wannan, sanna shima ya saka nashi, yana murmshi, prince yayi dan mamaki, amma ya share kawai, yayi masa brush suka fito.

Da safe kuwa, amir yaki saukowa daga kujera, shi sai an bashi hot milk da anty neena ke basa , prince yayi tsakin, yayi fadan amma amir yaki saukowan, can ya fita yana bala'i, a falo ya iske mum da zuby a zaune suna hada wasu takardu, mum wai ina wannan nanny din taje ne? Mum tace taje weekend, prince ya rike kugu mum ta dawo gsky, mum tayi saurin kallon shi, ban gane ta dawo ba,? Prince yace yaron nan ya cika rigima wlh , ya kalli zuby, ke kai masa hot milk nina gaji, ya zauna gwajab a kujera, mum ta kalle shi tace, na'im ! Ta kira sunan shi, yes mum ya fada yana gyara zaman shi, mum ta gyara muryar ta, ya kamata ace by now ka manta da dik abunda ya faru baya, u should go on wit ur life my child, kaga fa dad dinku ya gama shawarar yi maka aure tare da faruk, da sauri prince ya kalle ta "aure" mum ta tace aure mana, kullun mune hiring nannies, ya kamata kodan amir kayi auren nan na'im, prince yayi shiru, mum ta matso kusa dashi tace, mai zai hana ka fara zuwa wurin ikram ,
Prince ya sake kallon mum😳 ya maimaita suna "ikram!!!!!! Mum tace ai gara ikram din tunda baka san dawa dad din naku zai hada ka ba
[8/8, 4:04 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳🌳



By~ afrah


+2347010902548
Episode 3⃣1⃣-3⃣5⃣






Prince ya kura wa mum ido, mum ta sake muskutawa tace, u know bazan baka shawarar banza ba, ikram wayayyace, she is educated n social too, kawai dai kula da ameer dinne I knw bazatayi ba, prince ya tabe baki, yace den mum ba amfanin auren ta, cos ni kozan aure, zan auri wadda zata kula min da ameer ne kawai, bana da ra'ayin sake soyayya da ko wacce irin mace, yana maganar ransa a bace.
Mum ta sauke ajiyar zuciya, kada ka damu, ni da mummy (mummy din su ikram kenan), mun yanke shawarar yadda komai zai kasance, ranar na aiki neena, nanny din amir, mummy ta ganta, kuma tayi mata , so mun yanke shawarar koda ka auri ikram, neena sai taci gaba da kula da amir din, kawai makaranta zaka nema mata taci gaba.
Prince yashafi gefen fuskar sa, ya hura iskar bakin sa, sannnan ya kalli mum, toh shikenan ba matsala, amma gara dai ta san manufar auren mu, dan mum kin sani.....mum ta tsaida shi yayi na sani na gane, zan fadawa mummy komai.

Niimatu tayi kwanakin ta biyu tare da umma, cikin gata dajin dadi , kamar kada su rabu.

Da sassafe ta shirya ta hau hanyar komawa aikin ta.

Ta shigo gidan ba kowa a falon, taji motsin ladi a cikin , lekawa tayi tace ina kwana inna ladi?, ladi ta washe baki, antyn amir kin shigo? Neena tace na shigo inna ladi, bari nayi sauri naje na tashe shi,kada ya makara, bakwai har tayi ma, inna ladi tace toh maza jeki, neena tayi saurin haurawa sama.

Tana shiga dakin amir taga wayam, ta rike

4 / 15