SANADIN KENAN 2 HAUSA NOVELS BY TAKORI KABARA.doc

Author :  Sumayya Abdulkadir Takori Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 11

6K to 9K   out of 31.5K words

tuna kalamai na karshe na uwar Ameena.
"Ka kara kula da Ameena, ba don na raina kulawarka gare ta ba. She will need extra more....!".
"Yes! She need extra more A isha, kuma in har ina raye, sannan kudi suna da amfani za ta samu kulawa Aisha. Da gaske kula da 'ya mace sai mace. Na lura matar nan son kashe min Amina ta yi ko abinci ba ta bata ba har karfe daya na rana. Kuma ta sa maza su tozarta ta, ba don Allah ya dawo da ni ba!".
Ya san muddin ya gaya wa Hajiyan Ji-Kas wannan abin, cewa za ta yi za ta dawo ta kula da jikarta, ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bayan yanzun ta fara samun nutsuwa a gidan mijinta. Hankalinta ya tsaya wuri guda, shi shaida ne akan hakan don ko jiya ta kira shi tace ya shirya musu tafiya umrah itada Baba Liman. Zai yi (finding solution) da kansa.

Babu wanda ya fado masa a rai a wannan lokacin sai abokinsa Dr. Usman Turaki. Classmate dinsa ne, tare suka yi sakandire a Science College Dawakin Tofa. Sun shaku sosai, yanayin karatu ya raba su. Kowa da jami'ar da ya wuce da fannin da ya zaba.
A take ya zakulo lambar Dr. Turaki ya danna masa kira. Ta jima tana kara kafin matarsa ta daga. Abin da ta ce shi ne, "Doctor is on call. A gida ya bar wayarsa".
"O.k please da ya dawo ki ce ya kira ni da wannan number din, Ma'arouf Ji-kas ne".
"Insha Allahu". Ta kara da cewa, "Sai Ji-kas, insha Allahu sai Ji-kas!".
Murmushi ya yi, wanda bai shirya yinsa ba, wato matan aure ma ba a barsu a baya ba.
"Na gode Madame. A gaida yara".
"Za su ji. Allah Ya tashi kafadun Amina!!!".
Ji ya yi kamar ta yi masa addu'ar Allah ya sanya shi a aljannah. Wato komai na dan siyasa ba ya buya, kamar kasawa ake a faranti Anna tallata wa, kowa ya san matarsa ta lalle ta rasu, kuma yana da 'ya mara lafiya.
****
Dr. Turaki na komawa gida, abinci kawai matarsa Zainab ta bari ya ci, ta kasa bari ya yi wanka kafin ta isar da sakon Ji-kas. Amma ta boye azarbabi da murnarta na ta yi magana da Ji-kas, tauraron taurarin matasa na birnin Bauchin Yakubu.
"Zan kira shi gobe da na shiga office".
"Haba-Haba kai kuwa Baban Aadil, ka kira shi yanzu mana, mu ji mene ne, ka sani ko kujerar Makkah ce?"
Ya tuntsire da dariya.
"Zainab mai idon cin naira. Ki bari Allah ya ba shi kujerar, makkah kin je kin dawo insha Allahu".
Ita dai Zainab ba haka ta so ba, ta so ya kira shi tana zaune ta ji kwaf! Ko samu ne. Tunda wasu mazan al adarsu ne boye samu wa matan su.
Kamar yadda ya ce da matarsa, washegari yana shiga ofis ya bude tagogin ofishinsa, iska ta wadata, kan kujerarsa ya koma ya zauna. Ji-kas din ya fara kira.
A lokacin yana bai wa Amina (golden morn) a kofi da cokali, ya dakata ya daga kiran Turakin.
"Sai yanzu ka ga damar kira na? Na san tun jiya an gaya maka sakona. Har yanzu kana nan da halinka da na sani Usman?"
Dariya ya yi, "tuba nake Yaa Maulaya!".
Shi ma murmushin ya yi. Usman ya san ba ya son  Yaa Maulaya din nan da mates dinsu ke gaya masa sabida ustazancinsa, ba ta kan wannan yake ba yanzu, don haka kai tsaye ya zarce da gaya masa makasudin kiran.
"A kan 'yarka Amina ne. Mun bar gadon asibiti don dukkaninmu ba za mu iya ba, ni da Hajiya ta. Saboda wasu muhimman uzurirrika musamman ni da yanayin rayuwa ta ba na tsuguno ba ne a wuri guda. Don haka ina son hiring professional physiotherapist da za ta ci gaba da baiwa Amina (treatment) a gida, da kula da ita da komai nata bilhaqqi.
Za ta baro asibiti ta zauna da Amina a gida, ta ci gaba da kula da ita tsawon shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Zan ninka mata albashin da ta ke karba a asibiti sau hudu a kowanne wata.
Sai dai Turaki ba kowacce ba, shi ya sa ma na biyo ta kanka, ban bi ta kan likitocin Amina ba, ina son wadda akwai sanayya ta sosai a tsakaninku, ka yarda da ita, ka yarda da amanarta da ikhlasi. Mai tausayi da jin kai. Mata tsoro suke ba ni Turaki, in kana da kudin da za ka ba su babu mai zama da kai tsakani da Allah. Yau na firgita, na tsorata da al'amarin mata yadda ba ka zato Usman. Sun kuma karya min zuciya, sun kara sa ni kewar Asha. Mata irinta tsiraru ne a cikin al'umma".
Dr. Turaki ya ja numfashi, zai so ya tambayi abokin nasa abinda ya firgita shi da matan, har suka yi breaking sai dinsa haka, sai ya ga hakan ba huruminsa bane. Babu wadda ta zo masa a rai sai likitar da ya raina da hannunsa, ya kwashe shekaru tare da ita, ya lakanci dukkan halayenta; Dr. Amina Mas'ud Shira.
Dukkan suffofin da Ma'arouf ke so 'proffessional' din ta kasance da su Amina ce ta mallake su, a dai likitocin mataccen kashi da ya sani a duniya.
Amma kafin nan, sai ya ce da abokin nasa,
"To me zai hana ka kara aure Ma arouf? In ta gidan ta na da matsala?"
Cikin girgiza kai kamar Turakin na kallonsa,
"Ka sani ba ni da ra'ayin aure-aure tun ina karami na. Ita wannan din, tunda yanzu na san halinta sai mu gangara a haka, a ba ni gishiri in ba ka manda. In ta yin taka tsan-tsan da ita. Beside, ban aureta don tazo ta yi min jinya ba.
Kamar yadda bana son aure-aure, haka bana son saki, ko don ingancin rayuwar yaron da za a haifa da tarbiyyarsa, don ya faru a kaina ban ji da dadi ba. Haka na yi ta watangaririya sai dana girma na san 'yancin kaina. Duk da da babu haihuwa tsakaninmu auren bai jima ba, ban sani ba ko gaba kadan Allah zai kawo.
Ga tsoron kada in tara su (mata) ya zamo cewa duk haka suke, in hakan ta faru Turaki ina zan sa raina? In yi ta saki kuma a ce min auri-saki, ko wanda ya kasa rike mace, to wanda ya kasa rike mace a cikin gidansa, yaya za ayi ya iya rike dubun dubatar al umma?
Ka ga gara mu gangara da wannan din tunda yanzu nasan true colour dinta ta bayyana halayenta na fahimceta sosai, ita kuwa har gobe ba ta san waye Ma'arouf Habibu Ji-kas ba. Wallahi! Ko kwata na ba ta sani ba, suna na kawai take ji, ita kuwa tass! Na santa yanzu".
Dr. Turaki ya nisa, dama Allah ba ya hada maka komai a rayuwa, idan ya baka wannan sai ya hana maka wancan, shi kuma Engnr. Ji-kas ga ta inda Allah ya jarrabe shi (mata), ban da ita, a ganinsa ba shi da sauran matsala a rayuwarsa.
Multi-millonnaire ne da ko ya fadi zabensa (wanda da kyar in zai fadin) kuma ba fata yake ba, ba abinda zai girgiza shi. Juma'ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta. Duk da ance siyasa bata a inda ake tsammanin ta.
"DR. AMINA MAS'UOD SHIRAH!".
Ya furta masa a hankali da sauti mai dan kauri da ake kira (husky). Mai nuna muhimmancin wanda ya ambata a gareshi.
Ma'arouf ya amsa, "Wace ce haka?"
"Sunan likitar da ta siffantu da komai da ka ambata ne Ma arouf. Daliba ta ce, mu muka koyar dasu muka yaye su, Physiotherapist ce".
"Ka yarda ta hada duk abubuwan da na lissafa a sama Turaki?"
"Har ma ta zarta. Proffessional ce da ta san kan aikinta. Ta karbi (award) na Best Physiotherapist of Africa, sannan 'yar babban gida ce. Ba ina nufin 'yar masu kudi ba, a'ah ko kusa, gidan tarbiyya da mutunci. Ina fatan ka gane?"
"Na gane, ka yi mata magana toh, cewa zan dauketa haya na tsawon shekara daya in ba ta da aure. Ta kula min da mai sunanta paralysed diya ta. Zan ninka mata albashinta sau hudu in iyayenta za su amince. Duk 'weekend' sai ta tafi gida, ta kwana biyu, ni kuma zan maida 'weekend' lokutan zamana a gida da Amina in ci gaba da kula da ita in ba ta nan har sai ta dawo, ina son mahaifiyata ta huta".
Dr. Usman wata irin zuciya ta ciyo shi, "Me ye amfanin zama da matarka to idan har ba za ta iya jin kan abin da ka haifa ba, ko da na kwana biyu a sati?"
Ma'arouf ya yi murmushi, zuciyarsa ta hango masa yadda karti biyu suka tube Amina a gaban Laila dake toshe hanci cike da kyankyami, idanunsa suka rine sukayi jajawur.
"Idan har bayanin da na yi maka a sama bai gamsar da kai ba, ban san kuma wane bayani zan yi maka ba. Ban aureta don tazo tayi jinya ba".
"Kana da sanyi da yawa Ma'arouf (she deserve punishment). Ba kuma na komai ba sai na karin aure".
"Ba ni da ra'ayi Usman, wannan kadai na neman kashe ni da bakin cikinta ina ga na karo wasu su hadu su taru su haukata ni? Beside, ni fa ba ni da idon kallon mata har in ji sun yi min. Wannan din ma su Hajiya suka kallo min ita, ba su san kara da kiyashi ba ce daukar marar sani. Mu je a haka ni da Laila Turaki, na yankewa zuciyata irin zaman da zanyi da ita, aurena da ita bai da alaqa da diyata!".
Cikin tausayi Dr. Turaki ya ce,
"Ni ka ba ni kwangila in kallo maka. Na rantse ba duka suka taru suka zama daya ba".
Dariya ya yi kasa-kasa.
"Turaki, ka ki ka gane da gangan, mu bar zancen nan, so boring".
"Na bari". In ji Dr. Turaki,
"God bless you". Inji Ma arouf .
"Amin".
Duk suka yi shiru.
Zuciyar Turaki na tafarfasa, in shi ne da wannan matar wallahi sakinta zai yi, ko da a ce da gold aka kera ta. 'Yar guda daya? Marainiya? Mai lalura? Alhalin ubanta ya mallaka miki duk wani jin dadi na duniya? Shi ne alfaharinki, gadararki?
Sai ya tuna kuma fa Ma'arouf dan siyasa ne ba komai zai yi ba ko don ya tsira da mutuncinsa. Ya nisa. Amma ya kasa magana.
Ma'arouf ya katse shirun nasu da cewa, "Yaushe za ka yi magana da likitar?"
"Insha Allahu gobe. Yau tana off, kuma sai ta rubuta (leave without pay) in har ta amince. Zan yi kokari a ba ta (leave) din, don ba kowa a ke baiwa ba, kuma yana dan daukar lokaci. Ga shi zabe saura sati biyu, don haka in ta amince cikin sati biyun za mu gama komai. Allah ya ba ka nasara, kuri'unmu na tare da kai Ma'arouf.
Ka dauke ta ka kai ta wurin mahaifiyarka har a gama zabe ya fi sauki, za kuma ka fi samun nutsuwa tunda ka riga ka rabota da asibiti. Da an gama zabe mun ga abin da Allah ya yi sai a dawo da ita. Amina ta zo.
Jikina yana ba ni za ta amince, saboda tana ganin girmana, kuma ba ta yi auren fari ba".
Da wannan suka rufe tattaunawar tasu, Ma'arouf ya yi ta yi masa godiya.
*****
Shi da kansa ya shiga bayan mota tare da Amina, aka sa mata seat belt. Akilu direba da securities dinsa da sauran masu mara masa baya in zai je ko'ina suka dau hanyar Jigawa daga Bauchi. Daga nan suka yanke hanya suka shiga Gwaram suka mika Ji-kas.
Hajiya ta yi mamakin ganinsu. Don ko jiya sun yi waya bai ce da ita za su zo ba. Shi kuma ba ya so ya barta ta kwana cikin (suspense) ne na menene dalilin da zai kawo su adaidai wannan lokacin. Ya shigo dauke da Amina a kafadunsa ya kwantar a kan gadon Hajiya. Sannan ya nemi kujera mai taushi cikin kujerun Hajiyar ya zauna.
Ba ta tambaye shi komai ba sai da ta fara cika shi da abinciccika kala-kala a gabansa da ababen sha masu sanyi daga firizarta. Ga shi lokacin zafi ne.
Ya sauko daga kujerar zuwa kilishi ya zauna ya tankwashe kafafunsa. Hajiya ta zuba masa ruwa ya wanke hannunsa a kwanon silver, Allah ya taimake su sun yi sallolinsu a hanya.
Ta ce, "Me ya faru ne na ganka da Amina?"
Ya yi dan shiru yana tunani, muddin Hajiya ta ji halayen Laila ba za ta dauka ba. Balle abinda ya shafi Amina, bata aje yarinyar nan kusa a zuciyar ta ba, soyayyar da take yiwa mahaifiyarta gabakidaya ta dawo kanta. Karamin hukuncin da za ta yi shi ne, Laila ta koma gidan ubanta, shi ya sa auren gaggawa ba shi da amfani. Shi kuma babu saki sai ladabtarwa a tsarin rayuwarsa.
Tuni ya rufe (account) din da ya bude wa Laila, ya kuma yi alkawarin ba zai sake zuba komai ba, ta nemi guminta daga 'boutique' din da ya ba ta jari ta bude, kuma ba karamin tashin hankali ta shiga ba da faruwar hakan, don ba wani ciniki mai yawa ta ke yi a 'boutique' din ba saboda tsadar kayan sai matan manya ke iya saye.
"Na kawo Amina wurinki ne saboda za mu tafi umrah Saudiyyah ni da Laila sai bayan zabe za mu dawo".
Hajiya ta ce, "Masha Allah, to Allah ya ba mu nasara, a je lafiya a dawo lafiya, Allah ya tsare. In ce ko kun taho mata da kayanta da pampers?"
"Eh an taho da su suna mota. Bari na yi wa Idris magana ya fito da su".
Mutane dankam sun taru a kofar gidan Hajiya Saude suna jiran fitowarsa. Yau dai duk uzurinsa ya sa a ransa zai saurare su, ya yi musu maganin matsalolinsu ya roke su su yi wa Amina addu'a ba a san tsarkin bakin mutum ba.
Falon Baba Liman na saukar bakinsa aka bude masa. Jama'arsa da securities da sakatare Idris suka shigo, sannan al'ummar Ji-kas suka shiga shigowa daya bayan daya suna fadin matsalolinsu Idris na kirgo abin da ya ce a ba su yana ba su daga (brief-case) din hannunsa. Yana fadin,
"Ku yi wa yarinya ta Amina addu'a Allah ya sa tana da rabon sake taka kafafunta a doron kasa!".
Ai kuwa Amina ta sha addu'a har 'ya'yansu kanana sun sa sun yi wa Amina addu'a a makarantun allo.
Daga Ji-kas kai tsaye Abuja suka wuce shi da mukarrabansa, gidansa na Apo, ya ma manta da wata Laila.
Bayan ya huta sai ya samu 'privacy' ya yi ibada yadda ya kamata shi kadai a gidansa. Ya roki Allah idan mulkin nan alheri ne a gare shi, Allah Ya ba shi nasara, in ba alheri ba ne Allah ya musanya masa da mafificin alherinsa.
Washegari ya wuce Saudiyyah umrah.
****

RANAR ZABE
Yau asabar 9/9 ita ce ranar zabe. An tafka zabe, kowa ya fidda gwaninsa daga manyan jam'iyyun guda uku, NPC, APP da PCP. Masu magudi sun yi duk iya abin da za su iya na magudi, sun yi sun more. In banda 'Sai Ji-kas, wallahi sai Ji-kas, insha Allahu sai Ji-kas' ba ka jin komai daga bakin matasa, sai fastocinsa da ake ta rabawa ana lillikawa a ko'ina. Hakan ce ke faruwa a kowanne yanki (ward) da kowacce karamar hukuma (local government) na Bauchi guda ashirin da biyu.
Can na gano Ilyan Goggo ya jefa wa Ji-kas kuri'a, Dr. Turaki da matarsa Zainabu, Amina da Goggonta da Inna Zulai duk Ilya ya tattago su sun zo zabe sun jefa wa (NPC). Amina na ta mitar Ilya ya sa ta sha rana babu gaira babu dalili. Ya dauko naira dari biyar daga aljihunsa ya bata.
"Ungo ki sha lemo mai sanyi ki jika makogaronki, ni ai kin yi min komai tunda kin kadawa masoyina kuri'a".
Ta wafce 500 din, "Wallahi ta zo kenan ba zan ba ka ba, Mirinda biyu zan sha mai sanyi. Na gaji da kunun Aya. Mu yi maza Goggo, wallahi ina da aiki yau a gida, tunda yau da gobe kadai nake (free), zan yi bitar wasu littattafai".
Goggo ta kyabe baki, "Haka dai, nan aka fi kauri".
Ba ta tanka ba, don ta san me Goggo ta ke nufi. A ganinta (at 25) tana da sauran lokaci da Goggo za ta damu kanta. Sai ga likita Umar Bolori shi ma ya je ya jefa wa Ji-kas tare da matarsa, kannensa maza da mata. Alhaji Mansur da iyalinsa kaf ba a barsu a baya ba. Matasa da jama ar gari kuwa maza da mata duk sun tafi suna ta jefa wa (NPC).
A daren wannan rana aka tabbatar da Engnr. Ma'arouf Habibou Ji-kas a matsayin wanda ya lashe kujerar gwamnatin jihar Bauchi. Sai addu'a ake da fatan alherin Allah ya taya shi riqo, ya kama hannunsa Ya fidda shi kunyar al'ummar jihar Bauchi wadanda suka tsaya karkarshin ranar nan cikin kishirwa da yunwa suka zabo shi don ya shugabance su, sabida kyakkyawar shaidar da suka yi masa.

A lokacin da aka fadi sakamakon zaben kansa na kasa, ya yi sujjadah a Maqama Ibrahima. Ji ya yi kansa ya yi wani irin nauyi, at the same time gabansa ya fadi. Irin yanayin da ya tsinci kansa a lokacin da aka tabbatar masa da ya haye kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Bauchi North. Nauyin dubun-dubbatar al'umma ba abu ne mai sauki ba.
Sai da ya koma inda ya yi masauki (hilton), ya yi shirin kwanciya bacci, sannan ya kunna wayoyinsa guda uku.
Sakonni ba adadi, har ya rasa na wanda zai bude. Sai ya ce akwai na iyaye, bari in fara da su, throughout yau ban gaisa da su ba.
Na Baba ya fara budewa, "Wallahu galibun alaa amrihi... Ka ce alhamdu lillahi har sau uku. It is done. You are the elected governor".
Yadda Baba ya fada haka ya yi, wani farin ciki ya lullube zuciyarsa. Mulki zuma!
Sai ya bude na Hajiya,

"Mun ji abin

3 / 11