Chapter 143 Reading Mafari Hargitsin Rayuwa Book Complete by Ummu Muaz.txt Arewa Novels

Mafari Hargitsin Rayuwa Book Complete by Ummu Muaz.txt

Author :  Ummu Muaz Category :  True Books

Chapter   143 / 148

426K to 429K   out of 441.5K words

abinci ai wannan ya zama tarihi sofiya .

Hannun Yakaka ya kama "Wafaa mu je ki min rakiya ni zan tafi .

Sofi tana son miƙewa amma daɗin abinci ya danne ta dole tana ji tana gani Yakaka ta tafi raka Doctor Hamza ita tana kai lomar girkin Yakaka.

Bayan ta dawo daga rakiyar sa ta tarar Sofi ta gama cin abincin ta bar kome a wajen ta koma kan kujera ta hakimce .

Bata gaji ba ta tattara kwanukan ta kai kitchen ta wanke .

A ɗarare ta dawo falon ta zauna akwai wani series ne da take son kallo da bata samu damar gani ba jiya ta san suna maimaitawa da safe .

Tana zama ta ji Sofi ta jaa wani ƙaton tsaki.

A hankali ta miƙa ɗaga idanun tana kallon ta irin mummunan kallon jiya shi ta hango a idanun Sofi .

Har ga Allah tsoron yanayin kallon take domin kallo ne irin na hatsabiban mutane mugaye , kallo ne da yake ɗauke da saƙonni  masu zafi tare da ƙaƙƙarfan gargaɗi .

Ciɗak¡ ta miƙe bata tsaya ba sai ta wuce ɗaki tana jin lokacin da Sofi tayi wata ƙwafa mai ƙarfi .

Tana shiga wayar ta ta ɗauka ta ƙira Amnee suka gaisa wacce ta dunga mata nasiha tana kwantar mata da hankali kan dawowar Sofi a ƙarshe ta miƙawa Mamar su wayar .

Suka gaisa kafin su yi 'yar hira da rabin ta labarin diramar Bulama ne wanda aka kai shi makarantar kwana ta firamari amma ya gudo da kukan sa da kome a cewar sa ba zai iya barin Mamar Bulama ba .

Yakaka ta yi ta dariya tana jin ƙauna tare da tausayin ƙanin ta wanda ba su wani shaƙu da juna ba.

A ƙarshe suka yi Sallama tana sauƙe wayar ta ƙira Falmata nan ma hirar suka sha sai dai a cikin muryar Falmatan ta iya jin tana da damuwa da nan take hankalin ta ya tashi dan haka ta matsa mata kan sai faɗa mata me yake damun ta ? Ko haihuwar ce ta zo ?

Falmata bata ɓoyewa Yakaka kome nan ta faɗa mata irin matsananciyar damuwar da take ciki kan barin ta da Youssouf yayi ya tafi wajen aiki ta ɗora da cewa "kuma fa Yakaka sau uku kawai muke waya a rana kuma sau biyu kawai muke Appel vidéo a rana kafin ya tafi kuma ba haka ya min alƙawari ba cewa yayi kawai koyaushe yana tare da ni .

Shiru Yakaka tayi tana jinjina rikicin Falmata a zuciyar ta kafin ta ce "Falmata waya har sau uku a rana ? Ga kuma vidieo call ? Sau biyar fa kenan kike jin sa bai yi yawa ba Falmata ?

Kin san fa tare da matar sa yake a can , sannan ita ma tana da hakki a kan sa bakya ganin za ki shiga hakkin ta dayawa idan ya zama koyaushe kuna tare a waya ? Ni dai fatana Allah yasa bakwa doguwar wayar dare Falmata abunda duk ba za ka so ayi ma ba kar fa ka yiwa wanin ka '

Tsit Falmata tayi daga can tana ɗan turo baki kamar Yakaka na ganin ta sai cewa tayi "to ai nima ina da hakkin ni ba barina yayi ba ma gaba ɗaya ya tafi da ita ba ? ina cewa kullum tare suke kwana ? Meye dan kawai mun yi waya ?

Yakaka tana danne dariyar ta ta ce "a ah wallahi da kome muddin aka ce za ki dunga ratsa tsakanin lokutan da ya kamata ace yana tare da ita to ba shakka kina shiga hakkin ta haba mana Falmata ban fa san ki da zalunci ba , dan Miji yafi son ki kar ki yadda ki biye masa ya dunga ƙuntatawa matar sa .

Ni yanzu da Yaya dakta yafi son Sofi akaina za ki so ya dunga min abunda babu daɗi akan ta ?

Girgiza kai Falmata tayi tana jin duk jikinta yayi sanyi ta ce "ki daina cewa haka Yakaka Yaya dakta yana son ki ba zai taɓa walakanta ki akan Sofi ba.

"Kuma nima ba wai so nake ya dunga walakanta matar sa akaina ba kawai dai.

Ɗan shiru tayi tana numfasawa kafin ta ce "Yakaka ina son shi ne dayawa zuciyata tana min ciwo idan har na tuno yana can tare da ita ni kuma ga ni nan da ciki himm ina fama.

"Ki rage kishi Falmata kowacce mace tana son Mijinta amma domin a zauna lafiya babu cutarwa sai a dunga sassautawa ana tausar zuciya kin jin ko Gimbiya Falmata., ke ce fa Uwargidan Sarki watarana uwayen gida da kawaici aka san su domin suke jagorar Gida .

Sassauƙar dariya Falmata tayi tana jin ranta na yin sanyi ƙaunar 'yar uwar ta na kawo mata

****

Kafin cikar sati ƙarfi da yaji Yakaka ta koma zaman ɗaki saboda yadda Sofi ta kasa ta tsare alhalin ta san Yakaka tana matuƙar shakkun ta .

Muddin ta fito falo to aiki za tayi ta bar wajen ko kuma idan Doctor Hamza yana nan wanda shi bai san yadda yinin su yake kasancewa ba idan baya gidan .

Babu abinda yafi daɗa tayarwa da Yakaka hankali irin ji da tayi Doctor Hamza a jiya da dare yace cikin kwanaki biyu masu zuwa zai yi tafiya zuwa jahar Kano za shi asibitin koyarwa na Kano yin wani aiki na kwanaki uku "kenan zai bar su daga ita sai Sofi a gidan 'yar sakewar ma da take samu tayi a cikin awowi ishirin da huɗun idan yana nan zasu zama babu .

Hakan ya daɗa sanyayar mata da jiki har wani ɗan zazaaɓi take ji yana kama ta bayan bugun zuciyar ta da take ji yana sauyawa a bayan kowacce sa'a ɗaya ga kasala da ta dirar mata .

Bayan fitar sa aiki da ƙyar ta iya lallaɓawa ta fito yin girkin rana da ta san Sofi za ta iya buƙata ba wai dan cikin ta ba saboda ita gaba ɗaya ma yau tunda ta tashi bata sha'awar kome dan ko da suka zauna karin kumallo bata iya cin kome ba sai ruwan shai da ta zubawa cikin ta.

Ba irin rarrashin da Doctor Hamza bai mata ba kan ta ci abinci amma ta gagara dan kan shi yayi shiru ya bar ta bayan ya gama nazarin ta.

Fitowar ta daga ɗakin ya zo lokaci guda da ƙwanƙwasa ƙofar gidan da aka yi dan haka ta ɗan saurara jin ana sake ƙwanƙwasawa yasa ta taho ta buɗe ƙofar .

Musayar kallo suka yi ita da wacce take  tsaye a dokin ƙofar tana jifan ta da siririn murmushi mai tarin ma'anoni .

An-anty Samy .

Ta ambata a harɗe ,

"Yaks Amarya a gidan Doctor , matsa min hanya mana na wuce ko kuwa na koma ne ba'a maraba da ni ?

Da sauri ta matsa tana girgiza kai da 'yar fara'a tace "a ah ina maraba da ke mana Anty Samy sannu da zuwa .

Tayi gaba Samy baby ta bi bayan ta tana ƙare mata kallo .

Suna ƙarasawa tsakiyar Falon Sofi na sauƙowa daga sama wata 'yar shewa suka yi ita da Samy Baby kafin su taho su rungume juna suna 'yan ƙananun maganganun su na shaiɗana .

Samy baby za ta zauna Sofi tayi maza ta hana ta "friend me za ki zauna yi anan ? Ta shi mu tafi sama akwai muhimman maganganun da kin san nan ba muhallin yin su bane ba .

"Ok friend

Samy baby ta furta haka tana miƙewa tsaye ta ɗau jakar ta kafin ta mayar da ganin ta kan Yakaka wacce take rakuɓe a gefe wata 'yar iskar dariya tayi mai kama da shewa

"Hehehe Yaks kenan ka ga manyan amare masu harin miƙamin uwargida an gaishe ki  Yaks da tsaurin ido .

Shiru Yakaka tayi bata ce ƙala ba gaisuwar da ta yi niyyar yi ma ta fasa jin yadda Samy Baby take mata ba'a sarai ta fahimta .

Kitchen ta koma su kuma su ka hau sama suna shiga ɗaki Samy Baby ta lailayo wata ashariya ta kwatsawa Sofi .

"Kina me Sofi ? Nace kina me har kika bari yarinyar nan ta samu sakewar da zata fara haramar ajiye ƙwai a gidan nan ? Na shiga uku Sofi ina mai tabbatar miki taki ta kusan ƙarewa a gidan nan .....

Sofi da lokaci ɗaya ta diririce idanun ta suka sake shigewa ciki da in'ina a muryar ta tace "me..me ..kika ce ban..ban fahimta ba wanne irin ƙwai kuma kamar wata kaza'

"Yo ai ga ki nan babbar kaza Sofi tunda har kika kasa gane Yarinyar nan Yaks tana da shigar ciki kike zaune baki sake baki ɗau kowanne irin mataki ba...

Bata ankara ba ta ji Sofi ta sakar mata Mari da yasa shiru ya gifta wajen .

Kafin ta tsinkayo muryar Sofi tana cewa "kar ki sake min wannan mummunan Fatan mummunan zancen ,

"kin yi hauka ne Sofi za ki mare ni ?

"A turu nake Samira ya za ki zo kina barazanar fasa min zuciya da mugun fata ki sa na faɗi na mutu tun kwanana bai ƙare ba .

Gyara fuska Samy Baby tana ƙoƙarin shanye fushin ta saboda tarkon da take son ɗanawa kar ya lalace ta sassauta muryar tace

"Wallahi tallahi I swear Sofi Yarinyar nan ciki ne da ita ki nutsu ki dawo hankalin ki tun wuri mu yiwa tufka hanci kafi....

Wani razanannan ihu da Sofi tayi da ya amsa gidan gaba ɗaya sai da yasa Yakaka wacce take kitchen ta zabura tana dafe ƙirji a take taji zuciyar ta ta hautsina da daman tunda tafara girkin warin Albasa ke ɗaga mata hankali.

Ba shiri ta bar baro kitchen ta wuce ɗaki tana mayar da numfashi "anya Sofi kan ta ɗaya ?

"Samira da gaske kike ? da gaske kike da gaske ?

Kamar an safure ta ta miƙe tayi hanyar fita daga ɗakin da gudu Samy baby ta bita ta riƙo ta .

Kufcewa tayi tana watsa mata wani mugun kallo kafin cikin muryar da ta buɗu kamar ba ta ta ba tace "ki bar ni naje na kashe ta na farka mata ciki na zo miki da ɗan tayin cikin na ta wallahi sai na kashe ta.

Kallon baki da hankali Samy baby ta jefa mata kafin ta ce .

"Dallah Sofi ki nutsu ya kike abu kamar wacce ba tayi karatu ba ? Kina abu kamar wata jahila kina tunanin yanzu idan kika je kika kashe 'yar mutane ke ma za ki rayu da Hamzan ne ba tare da an miki ɗaurin rai da rai ba ko kuwa ke ma a kashe ki.

"Na yarda a kashe ni idan na kashe ta akan dai mu rayu ni da ita alhalin ta raba ni da farin-ciki na ina ji ina gani bakin-ciki zai kashe ni na mutu na bar mata duniyar su rayu ita da Mijina .

"Na yarda za ta mutu amma ba ta irin wannan hanyar da kike son bi ba ko da kashe ta kike son yi ki bari sai an kauda-bara ta yadda za ki kashe ba tare da an samu mai iya ɗaga ido ya dube ki ba ko kuwa ma kawai a mata abunda zai kashe ta ba tare da an zarge ki ba .

"Ta yaya faɗa min hanyar ?

Sofi ta furta hakan jikin ta har wani mazari yake , a kaikaice Samy baby ta dube ta cikin ran ta kuwa dariya take kwasa "Yau Sofi uwar bin Bokaye har wata nahiyar ita ke tambayar ta yaya za'a yi ? Lalle notikan cikin kan Sofi sun kwance baki ɗaya .

Gyara zama tayi tana jin Allah ne ya kawo mata hanyar warwarewar tata matsalar da kome ya kwaɓe mata bariki tana ƙoƙarin kwashe kayan ta daga kanta ta juya mata baya ta bar ta a cikin rana dan kuwa ko Alhaji Gali a halin yanzu fiye da watanni uku kenan ta daina ganin ƙeyar sa alhalin lokacin biyan kuɗin gidan haya yayi haka tana ji tana gani bayan ƙara mata sati biyu da masu gidan suka yi suka zo a ƙarshe suka kore ta sai gidan ɗaya daga cikin abokan shaiɗanan ta ta koma da ko kaɗan ba jin daɗin zaman gidan take ba saboda ba shi da wani hali sosai irin mazan nan ne da Zina ta aure su wanda ko basu da sisi sai sun yi ta.

Fahimtar hakan da tayi yasa ta fara ƙulla wacce za ta fissheta idan zaman Abujan ya gagara ne tana iya komawa ko Damaturi ne ta karkaɗe kwalin ta ta shiga neman aikin da za tayi ta riƙe kan ta dan kuwa ko a mafarki ta san bata doshi Maiduguri gidan Ubanta ba bata ma da matsugunni a gidan sannan ita a karan kanta bata jin za ta iya rayuwa ƙarƙashin iyayen ta.

Sai dai me ? Kuɗaɗen da suke account  ɗin ta ba zasu ishe ta yin irin rayuwar jin daɗin da take tsarawa kan ta ba ko da ta koma Damaturu domin so take ta shiga gari sosai ta wataya a ƙarshe ta samu wani ɗan Matashin kyakkyawan Saurayi haka ta chaka masa su yi aure .

Dan haka ido rufe take neman kuɗi tunda kuwa yanzu dama ta samu da zata iya samun su daga Sofi to me za ta jira ?

Muryar Sofi ta katse mata tunani ta da take cewa " Ni kin hana ni naje na aiwatar da manufata ke kuma kin yi zaune shiru baki kawo wata hanyar ba ki faɗa min ya zan yi ?.

"Sofi ki buɗe bakin Aljihu kiyi ɓarin kuɗin na san dai kin Fahimceni ni kuma na miki alƙawarin ko nan da birnin Sin ne zan je miki wurin Boka ba sai kin ma tafi da kan ki ba bare har a iya zargin ki .

Da wata irin Murya Sofi ta ce " ki koma min karnataka Samira gurin Bokan da ya min aiki akan zuciyar Doctor zan baki adireshin sa da kome sannan zan bayar da kuɗin da zai ishe ki har kije ki dawo da kuma kuɗin aikin sa , bana so na motsa ma daga tsakanin su domin ko kallo bana so ya sake shiga tsakanin su ....

Samy Baby wacce tafi zaƙuwa da zancen kuɗin jin tarkon ta yayi kamuwa tace "amma fa kin san kuɗaɗen dayawa Friend..

"Ko miliyan ishirin ne zan sayar da gwalagwalai na na baki kuɗin bana so a ɗau lokaci nasan kin san manyan mutane a ƙasan nan dan haka samun visa ba zai miki wahala ba idan son samu ne cikin satin nan ki tafi kai ni idan zai yiwu ma cikin kwanaki biyu masu zuwa saboda bana so bana kuma fatan yarinyar nan da ita da abunda ke cikin ta su sake yin sati ɗaya a duniya .

Nisawa tayi tana gatsa gefen bakin ta da haƙori tace " Sannan so nake na kashe ta da hannun na Samira da hannu na nake son kashe ta shine kaɗai abunda zan iya mata da zai sa zuciyata ta wanku daga baƙin-cikin da ta samu a ta sanadin ta dan haka daga kin isa can an yi aikin kawai ki ƙirani ki sanar min ina mai tabbatar miki da sai dai ki dawo ki tarar ana zaman makokin mutuwar ta .

Shiru Samy Baby tayi tana kallon Sofi cikin ran ta tana girmama rashin Imani irin na Sofi yau ta zama rana ta farko da ta fara jin shakkun samuwar cikakken hankali ga Sofi to kodai tana da rauhanai ne ????? Ko kuwa Mai rabon shan duka ne da baya jin Bari




Assalam Alaikum masu karatu.

Albishirin ku ?

Na san kun ce goro goriya goro .

Yau Maman 'yan biyu tagwayen shafuka ta muku.

Ina nufin kar ku motsa shafin nan tare yake da ɗan uwan sa da yakasance kuma murfi na baki ɗayan littafin Mafari insha Allah .

A sha karatu lafiya .
[4/15, 8:17 PM] +234 706 503 6187: MAFARI

           ( HARGITSIN RAYUWA)


UMM'MUAZ



KARSHE



(A)







A daren ranar Doctor Hamza bai dawo daga aiki ya tarar da Sofi a gida ba saboda tunda rana suka fice ita da Samy ko Yakaka bata san fitar su ba .

Hakan ba ƙaramin ɓatawa Doctor Hamza rai ya yi ba saboda ai tsagoron raini ne matar auren ka ta fita unguwa ta kai har dare ba tare da ta nemi iznin ka ba .

Sai dai halin rashin lafiyan da ya zo ya tarar da Yakaka a ciki ya ɗauke masa hankali daga kula haukar Sofi .

Nan take ya shiga bata duk wata kulawar da ta dace domin samun tabbacin abinda yake zato .

Maƙurar farin-cikin da zai iya cewa bai taɓa jin yanayin sa ba ya tabbata a zuciya da kewayen jinin jikin sa baki ɗaya lokacin da gwajin fitsarin da ya yiwa Yakaka ya bayyana masa da tabbatuwar zaton sa

Yakaka tana ɗauke da gudan jinin sa a Mahaifar ta nan da wasu watanni zai zama uba bayan shekaru bakwai da ya kwashe da yin auren sa na farko wanda hakan ya sadar da shi cikar shekarun sa arba'in cif ba tare da ya samu ɗan kan sa ba .

Sai fa yanzu da Allah yayi tsiron halittar gudan jinin sa a tare da Yakaka shi kuwa da wacce irin kalma zai miƙawa Ubangiji godiyar sa ?

Ganin sa ya mayar kan Yakaka wacce take bacci hankalin ta kwance da ba domin larurar saurin bacci na mata masu ƙaramin ciki ba a ɗan zaman su da yanzu-yanzu tayi fitsari ta ba shi yayi awu bai ci ace kafin ya gama gwajin har tayi bacci ba .

Fuskar ta ya tsirawa idanu yana jin wani ƙaunar ta mai ƙarfi tana sake fisgar sa har yana jin kamar babu wani sarari da yayi saura a zuciyar sa da ƙaunar ta bata riga ta cika ba .

A hankali ya ɗaga hannu yana shafar kumatun ta da suka sake yin suɓulɓul suna ƙyalli na musamman .

Zazzaɓin da ya dawo ya tarar da shi ya rufe ta sosai a yanzu ya sauƙa saboda ya bata maganin sauƙe zafin jiki ta sha .

"Wafaa .

Ya ƙira sunan ta a hankali yana ɗan hura mata iska a fuskar ta '

Buɗe idanun ta da suka yi nawi tayi tana kallon sa a raunace .

"Wafaa yaya kike jin jikin yanzu ? Za ki iya tashi muyi sallah ?

"Habibi nayi sallar isha ina jin bacci sosai ni.

"Na san kin

143 / 148

Chapters