Chapter 83 Reading Mafari Hargitsin Rayuwa Book Complete by Ummu Muaz.txt Arewa Novels

Mafari Hargitsin Rayuwa Book Complete by Ummu Muaz.txt

Author :  Ummu Muaz Category :  True Books

Chapter   83 / 148

246K to 249K   out of 441.5K words

zaman jiran dai-daituwar jirgi da ya ɗauke su tsawon awanni uku da rabi ,

Biyamuradi Youssouf tare da Falmata da Mama suka bi sawun takwarorin su masu tafiya zuwa United States of America , a sawu na farko suka taka matakala ,  kafaɗar sa ta dama ɗauke da Mama wacce ta sarƙafo hannayen ta a jikin wuyan sa , ɗaya hannun nasa  ya zare daga cikin na Falmata da tunda suka shigo airport ɗin yake kaffa-kaffa da ita yana riƙe da hannun ta , duk kuwa da yadda take yawan mutsu-mutsu da hannun tana son zamewa amma ya ƙi kulawa bare ya bata dama , ya maida hannun sa bisa ƙugunta tare da matso da ita jikin sa , a hankali yace da ita ,

Fatima ki kulla da kyau ki saurari takun ƙafa ta bissa matakala muke ,

ba tare da ta amsa ba ta gyaɗa kanta , tana jin yadda tsikar jikin ta ke miƙewa .

Cikin jerun kujerun first class suka yi mazauni akan kujerun su masu ɗauke da numbobin su da suke fuskantar juna , sai ɗan teburi a tsakanin su , bayan zaman su ya yunƙura tare da ɗaurawa Falmata seatbelt ɗin ta ya koma ya zauna tare da ɗaurawa Mama nata , bai tsimaya ba ya ɗaura nasa .

A hankali ya kai hannun sa ya kamo hannun Falmata da yake kan teburin gaban su , ya damƙe hannunta guda cikin nasa dai-dai lokacin da zazzaƙar muryar shugabar masu dauke da alhakin kula da walwalar mutanen cikin jirgin "Chief flight Attendant ," ta karaɗe cikin jirgin ɗauke da sanarwa da take cewa :

  “Ladies and gentlemen, this is Rose jackson and I’m your chief flight attendant. On behalf of Captain Mike Abraham and the entire crew, welcome Turkish Airlines flight  non-stop service from Niamey Niger Republic to Washington DC United States of America.

Our flight time will be of  9hours and 11minutes. We will be flying at an altitude of  feet/meters 5612 miles .

At this time, make sure your seat backs and tray tables are in their full upright position and that your seat belt is correctly fastened. Also, your portable electronic devices must be set to ‘airplane’ mode until an announcement is made upon arrival. Thank you.”

Ta sake maimaitawa cikin yaren faransanci .

( Mesdames et messieurs, voici Rose Jackson et moi, votre agent de bord. Au nom du capitaine Mike Abraham et de l'ensemble de l'équipage, accueillez le vol sans escale de Turkish Airlines entre Niamey Niger Republic et Washington DC, États-Unis d'Amérique.

Notre temps de vol sera de 9 heures et 11 minutes. Nous volerons à une altitude de 5612 milles.

À ce stade, assurez-vous que vos dossiers de siège et vos plateaux sont dans leur position verticale maximale et que votre ceinture de sécurité est correctement bouclée. De plus, vos appareils électroniques portables doivent être en mode "avion" jusqu'à ce qu'une annonce soit faite à l'arrivée. Je vous remercie.")

Girgizan da jirgin ya ɗauka shi yasa ba shiri Falmata ta sake ɗora ɗayan hannun ta akan na Youssouf tana ƙanƙame sa  hannayen su suka cure guri guda , kamar yadda zuciyoyin kowannen su ke ƙoƙarin jawo kusanci a tsakani .

Idanun sa a kafe kan fuskar ta dake bayyana tsoro ɓaro-ɓaro .

Cikin ikon Allah jirgin ya samu dai-daituwa a sararin subahana ya shilla da gudun gaske cikin tafiyar gaibu bisa iska a tsakanin sama da ƙasa .

Nigeria

Tafiyar kwana ɗaya da yini biyu ta sada Hajja da birnin Maiduguri , da la'asar sakaliya motar da ta kawota ta dakata a ƙofar gidan Prof .

Kai tsaye ta sauƙa ta shiga gidan , tarɓa ta musamman ita da direban suka samu daga sabbin ƴan aikin gidan guda biyu tare da Rahima da daman duk ansan da zuwan su .

Bayan magarib ta nemi iznin zuwa gaishe da prof da  zuwan su a ɗazu suka tadda shi tare da baƙi , hakan ya sa basu samu ganin sa ba sai yanzu .

Bayan doguwar gaisuwa tare da godiyar da akayi musayar su tsakanin  Prof da Hajja , taƙaitatciyar hira suka yi wanda duk rabin ta akan Al'amuran da suka shafi taɓarɓarewar tsaro ne tsakanin Niger ɗin da Nigeria da har kawo yau Ƴan tawayen Boko Haram basu saduda sun bar yin kisan mimmiƙe tare da ɓarnannaki tsakanin ƙanana da ma manyan garuruwan Niger da Nigeria ba .

Sannan kuma har kawo yau gwamanatin ƙasar Nigeria ta gagara kawo ƙarshen hare-haren ƴan kungiyar duk kuwa da cewa cikin ƙasar tushe da MAFARIN kafuwar ƙungiyar da ta jefa Dubunnan rayukan Al'umma cikin HARGITSIN RAYUWA yake .

Shin yaushe ne kome zai kawo ƙarshe ? Yaushe ne abubuwa zasu koma dai-dai ? Yaushe ne za'a ƙira ƙungiyar Boko Haram da shuɗaɗɗan lamari da ya zama tarihi ?  Allah Shine Mafi sani .

Hajja ta miƙe ta ƙarasa gaban Prof tana miƙa masa envelop ɗin dake ɗauke da hoton Mama ,

Alhaji ga hoton Amaryar taka ta Niger ka ga yadda ta girma duk da ƙarancin lafiyar ta amma ta miƙe .

Miƙa hannu yayi ya karɓa yana dariya , dai-dai da shigowar Doctor Hamza wanda ya dawo daga Masallaci .

To toh Masha Allah , Babu kome ai kowacce cuta Allah yayi maganinta , sai dai idan har sanin ɗan Adam bai kai ga gano maganin ba .

Ƙwarai maganar ka dutse Alhaji .
    Cewar Hajja .

ya zaro hoton yana gyara zaman gilashin idanun sa , bayan sun haɗa baki wajen amsa sallamar Doctor Hamza ,

ka ga Babban Likita , Likita bokan turai , ƙarshen ƙwaƙƙwafi da bincike sai likita , lalle tafiyata bana me sa'a ce tunda naci karo da kai , shekaru fiye da biyar rabona da na ganka .

Murmushi yayi yana zama daga gefen ƙafafun Prof .

Hajja sannun ki da zuwa , da fatan kin  samu isowa lafiya ?

Lafiya ƙalau Likita ,yaya bayan rabuwa ? Ya iyalin naka ?

Duk kowa lafiya hajja .

To Alhamdulillah .

Masha Allah wannan Amarya tawa ai tafi kama da ƴaƴan nasara , ga dukkanin Alamu tana da wayo .

Prof ya furta haka yana mayar da hotunan cikin envelop ɗin .

Wayo kuwa na sosai Alhaji ai Mama sai godiyar Allah ba shakka tana da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin ɗaukar abu

Allah shi rayata , ya bata lafiya , yayi Albarka cikin rayuwarta ita da sauran yaran musulmai baki ɗaya !

Ameen Ameen Alhaji

Hajja ta amsa tana sanya hannuwanta biyu ta karɓi envelop ɗin da yake maida mata , ta miƙe tana yi musu bankwana tare da barin falon ta koma cikin gida .

Baba , wacce yarinya ce hajja ta kawo maka hoton ta ?

Doctor Hamza ya tambayi Prof .

Ya buɗe baki da zummar bashi amsa shigowar ɗaya daga cikin dattijan unguwar da suke cin abincin dare tare da Prof ya katse musu hirar .

Abuja

Yakaka ce a zaune kan hannun kujerar falon Malama Maryam gabanta kuwa babbar jakar kaya ce da take shaƙare taf da kaya , daga gefen ƙafafunta ma wata ƴar matsakaiciyar jakar ce .

tana shirye tsaf cikin dogon hijabinta da yake har kusa da idon sawun ta , fuskar ta fayau babu ko kwalli , ramar da tayi ta fito sosai akan fuskar ta da idanunta da suka ɗan zurma ciki .

daga gefe a cikin falon Lubna ce a zaune tayi jugum tana kallon Yakaka wacce idanun ta ke kallon ƙasa , tayi shiru tamkar ba sune masu yin dararraki ba muddin suna waje guda .

Malama Maryam ce ta fito itama shirye take , ta kai dubanta ga Yakaka tana jin yadda tausayin ta ke sake narkar da ranta tabbas Yakaka tana buƙatar majiɓanci cikin Rayuwar ta .

Yakaka tashi mu tafi , lubna taya ta ɗauko kayan ku kai cikin mota Abban ku yana jiran mu , kar mu rasa motar farko ko ta biyu , saboda mu samu isa da wuri tafiya daga Abuja zuwa Maiduguri da tazara gara muyi sammako . 

Jikin Lubna babu kuzari ta miƙe tana gyara zaman hijabin jikinta ta sunkuya ta ɗau ƙaramar jakar tare da kama gefen babbar ta taya Yakaka riƙewa ,

Sun zo tsakar gida Lubna ta jaa ta tsaya da hakan ya sa Yakaka waigowa .

idanunta cike taf da ƙwalla tace

Sahiba irin rabuwar da zamuyi kenan babu bankwana ? Shekaru biyar ba kwana biyar bane Sahiba ban so ba zaki tafi tare da maɗaukakiyar damuwa .

ɗan guntun murmushi Yakaka tayi ,
Sahiba kin san har abada kina cikin mutanen da bazan iya mantawa da su ba cikin rayuwata , cikin kowanne irin hali na tsinci kaina , nima zanyi kewar ki Lubna , ta ƙarasa zancen siririyar ƙwallar da bata shirya zubowar ta ba na sauƙa bisa ƙuncin ta .

Idan kika tafi a yanzu waye zata maye min gurbin ki ? Waye zata zama babbar ƙawata a bikina ? Da ke muka tsara kome Yakaka .

Idan Allah ya yarda zan dawo Lubna , zan halarci bikin ki na ɗau Alƙawari , amma dole na tafi a yau shekaru biyar Falmata tayi cikin rashina ,

Hon ɗin da aka matsa da ƙarfi shi yasa suka fara taku cikin hanzari ba tare da sun sake musayar wata kalma ba a tsakanin su .

Ƙarfe takwas da rabi na safe motar da su Yakaka tare da Malama Maryam suka shiga domin tafiya Maiduguri ta ɗau hanya ɗoɗar .

Tafiya ce me nisa ta tsawon fiye da awanni takwas tsakanin Babban birnin tarayya Abuja da Birnin Maiduguri dan haka a saboda yawan tsaye-tsaye akan hanya daga jami'an kula da hanya da suke gudanar da bincike , ya sa dare ya fara shiga har ƙarfe shida na yammaci ta gota , wanda hakan kuma ya sa dole su yada zango a garin Damaturu saboda lokacin dokar hana zirga-zirgan motoci ya shiga ( curfew)  ala tilas suka kwana a tasha ,

Washegari da hantsi ƙarfe tara suka shiga garin Maiduguri , a idanun Yakaka babu wani sauyi da garin ya samu tsawon shekaru biyar ɗin ko kuwa dan hankalinta bashi kan duban yanayin garin ne ? Baki ɗaya ta ƙagauta ta ɗora idanunta akan ƙanwarta da ƴar ta .

Tsawon lokacin rabuwar ta da garin bai sa ta manta da sunan unguwar da ta bar Falmata ba , dan haka bayan sauƙar su a tasha kai tsaye ta shaidawa direban taxi da ya ɗaukesu da kayan su unguwar da zai kai su .

tafiyar mintoci 15 kachal ta sada su da unguwar , layi bayan layi ta kwatantawa direban har zuwa gaban gidan da a koyaushe yake yawan samun gyaran da yake sake fiddo kyaun tsarin ginin dai-dai da na zamani .

Bayan sun sauƙe kayan su a gefen hanya daga jikin katangar gidan Yakaka tace ga Malama Maryam

Ummi bari na shiga na nema mana iznin shiga da kayan mu .

To Yakaka .

taku ta fara yi tana jin yadda zuciyarta ke bugu da fargabar da ta rasa takamaimai dalilin samuwarta daga ƙasan ran ta ,

ta kawo kusa da ƙofar gidan aka buɗo Babbar ƙofar ya danno hancin motar sa yana ƙoƙarin fitowa ... !!!!

Assalamu Alaikum wa Rahamatullah ta'aala wa barkatuhu .

Yan uwa masu karatu Maza da Mata,  ina mika sakon gaisuwa ta tare da fatan Alkhairi a gareku.

Sannan ina mika godiya ta ga dukkanin daukacin Mutanen da suka samu damar kirana a waya da wadanda suka bar sakonni su na gaisuwa tare da addu'o'in samun waraka ga 'ya'ya na,  har ma da wadanda Allah bai basu dama ba,  kalmar nagode ai tayi kadan wajen bayyana muku jin dadina , sai dai nace Alherin Allah ya isar muku a duk inda ku ka yi bigire .

    

Ehen Uhum uhun-hun

Kai daga jin wannan guntattakin sautukan da suke tasowa daga kasan maƙoshi ka san da su nake,  o'e da o'e ko kuwa dai a takaice na ce ghost r-r-readers 😂

Ba kome , Ba kuma zance kome ba , amma ku saurari haɗuwar ku da ɗanliti , Ah to meye ? Ai shine zai rama min irin cin tuwo a ƙoƙon da kuke min 😢.

A cigaba,  eh nace a cigaba da labewa a bayan labule . 😂 😂

Nagode .

  
MAFARI

( Hargitsin Rayuwa )


Umm'muaz


35





Doctor hamza ba tare da ya dubi sashin da Yakaka take tsaye ba yayi wucewar sa yana waya da 蓷aya daga cikin abokan aikin sa na nan Asibitin Maiduguri wanda ya masa 茩iran gaugawa sakamakon neman sa da ake a asibitin jahar saboda wani aiki na gaugawa da za'a yiwa wata mata da take halin bu茩atar taimako ,

Kan ta a 茩asa tana satar kallon gefen fuskar sa , zuciyar ta cike taf da addu'o'i iri-iri , ta wuce ta 茩arasa wajen maigadi wanda ya tattara dukkanin hankalin sa akan ta ,

Sama-sama ya amsa gaisuwar ta ya 蓷ora da tambayar ta wajen wa ta zo ?

Wajen Rahima na zo .

tace da shi tana fatan kar ya hana ta shiga gidan saboda wannan maigadin ba茩on fuska ne ba wanda ta sani a da ba ne聽

Kallon tsanaki yayi mata bai hango wani alamun rashin gaskiya a tattare da ita ba ,

Ki shiga tana ciki .

Yace yana komawa kan 蓷an bencin sa na zama .

Hamdala tayi bayan ta yi masa godiya ta taka tana nufar cikin gidan da bai zamto ba茩o ba a gareta , tsarin sa bai sauya ba illa zuciyar ta da take cike da taraddadin hasashen da irin fuskar da Mutanen gidan zasu 茩arbe ta da hakan ya hana ta kuzarin isa cikin gidan cikin 茩an茩anin lokaci

Da duk takun ta guda kunnuwan ta suke sake kusanto mata tashin muryar ta suke,聽

da bata riga ta manta amonta ba ko dan ita 蓷in tana daga cikin mutanen da suka gwada mata 茩auna a duniyar ta ne ?

Hajja dan dai kince kin manta fuskar maman ta ne amma idanunta sak na mamar ta ne , sosai tana 蓷ibar yanayi da mamarta sai dai ko kamannin Baban ta yafi 茩arfi ,

ai babyn nan 茩arshe ce a kyau wallahi kamar naje Niger na kwato ta nake ji , Allah sarki baby na Allah dai ya baki lafiya , yasa a dace wajen neman maganin nan , Allah kuma ya ji茩an Mamar ki me kirkin nan .

Da murmushi hajja ta amsa da Amin Amin Rahimatu聽

聽聽 A hankali ta sau茩e idanun ta a bayan Rahima lokacin da ta 茩araso 茩ofar falon , wacce ta juya baya tana 茩o茩arin sa茩ala tangamemen hoton Mama cikin jerin hotunan da suke killace a jikin bangon inda aka tanadi sashi na musamman domin ajiyar hotuna ,

茒aya daga cikin hotunan da hajja ta zo da su ne da ta kai aka wanke mata shi zuwa Babban takardan hoto aka yi mata gidan sanya hoto na musamman tare da sanya shi a cikin gilashi .

Ganin ta ta mika kan hoton , fuskar da ta gani jikin hoton ya sauya bugun zuciyar ta nan take , a hankali take wara idanun ta tamkar wacce ta warke daga makanta , kamar yadda take jin zuciyar ta tana bu蓷ewa da wani irin yanayi 茩a茩茩arfa , 茩ofofin gashin jikinta baki 蓷aya suka bu蓷e suna tsattsafo da gumi聽 ,

Taku ta fara yi tana 茩ara kusantar hoton da zuciya da tunaninta baki 蓷aya suka tafi ga fuskar dake jikin sa.

Ha茩i茩a bata ta蓳a ganin ta ba amma kusancin dake聽 tsakanin uwa , mahaifiya da abunda ta haifa daga cikin jikinta ya wuce wasa ya kuma wuce聽 hankalin duk wani me tunani 茩auna ce me rassa da take ya蓷o a dun茩ule da babu me iya ganin zurfn ta bare a iya hasaso iyakar ta聽 ,

Bayan Rahima ta zo daf ta tsaya tana sake nutsar da idanun ta akan fuskar mama wacce tayi 拼ar kyakkyawar dariya a hoton.

Hajja wacce ta mi茩e tsaye daga gefe tayi sororo tana bin Yakaka da ido kafin tace

Ke , Ke , Ke baiwar Allah lafiya kike kuwa ? Zaki shigo mana gida haka sangam-sangam babu sallama bare neman izni ? Kin kuma zo kin yi tsaye 茩ere-re uwa wacce ta ha蓷iyi ta蓳arya ince ko baki da lafiya ne ?

Rahima wacce bata ji tsayuwar Yakaka kusa da ita ba , saboda raggon taku marar sauti da Yakaka tayi a yayin isowa wajen , ta 蓷an waiga sashin hajja lokacin da take gama sar茩afe hoton a inda ya dace tare da janye hannun ta daga jikin hoton ta waigo tana cewa

Hajja da wa kike magana ne ?

Fuskar ta ce ta kusan ha蓷uwa da ta Yakaka da ya sa ta 蓷an jaa baya

Bismillahi waye ha...

Kalmomin ta ta ha蓷iye mu茩ut , ma茩wallon ma茩ogoron ta ya motsa kamar yadda idanun ta suka firfito da mabayyanin firgici baro-baro a cikin su ,

聽 Shekarun da suka raba ha蓷uwar fuskokin su basu yi yawan da zasu sa su mance da kamannin juna ba .

Ya-Ya-Yakaka ke-ke kece ??

Rahima ta furta muryar ta tana makyarkyata kamar yadda kwakwalwarta take hautsinewa da kokonto ,

Yakaka wacce zuciyar ta ta za茩u da son samun tabbaci akan gudan jinin ta , ba tare da ta janye idanun ta daga kan hoton ba ta lalubo hannuwan聽 Rahima ta dam茩o su da 茩arfi ,

Rahima, Rahima ni ce聽 ,
聽 Ta zarce da tambayar ta
wannan ,?聽 wannan Mama ce ? 瞥a ta Mama ?

聽聽 Rahima wacce tunanin ta ya gama dun茩uluwa waje guda , ta fisge hannuwan ta da matu茩ar 茩arfi bata tsaya ba ta taka da gudun gaske tana nufar 茩ofa , kafin ta 茩arasa ficewa ta 蓷aga murya tana sanar da Hajja .

Hajja ki gudu wallahi Fatalwar Maman Mama ce wannan .

Turus hajja tayi tana bin bayan Rahima da kallo , kafin ta sake waigo Yakaka wacce bata bi ta kan kalaman Rahima ba tamkar ma dai bata kai ga fahimtar me kalaman Rahima ke nufi ba .

Ta saka hannu ta 蓷ago Hoton ta ciro shi daga mazaunin sa , tare da ri茩e shi da hannuwan ta duk biyu , tamkar ta ri茩e yar jaririyar ta .

Kai tsaye ta nufo Hajja da hoton , fuskar ta da wani irin yanayi na chaku蓷uwar tsantsar farinciki da kuma fargaba tace

Wannan 拼ata ce ko ? Mama ce ko ?

Kafin ta 茩araso hajja ta juya da 拼ar sassarfa tana 蓷ingisa kafafun ta da basu cika lafiya ba ,

Un-un-un 拼ar nan , ni kuwa ina zan sani ?

83 / 148

Chapters