Allon Sihiri Book 3 By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

Author :  Abdulaziz Sani Madakin Gini Category :  Arewa Pen

Chapter   3 / 3

6K to 7.2K   out of 7.2K words

daki guda ba,shi kadai zai
kwanta a
cikin wannan turaka tare da ALLON SIHIRI,don
haka
ya zama wajibi kowannenku ma yaje ya nemi
inda
zai sa hakarkarinsa.Kuma yace lallai ku kwantar
da
hankalinku tamkar tsumma a randa,yayi muku
alkawarin cewar babu abinda zai taba lafiyar
jikinku
koda kuwa kwarzane guda da izinin
ubangijinsa.Koda gama fadin hakan sai Bakon
Jarumi ya shige cikin turakar ya janyo kofar ya
rufeta ruf ya bar Dazyan tsaye sororo a kofar
dakin
tare dasu Sarauniya Akisatul Sauwara,suma sunyi
cirko cirko suna mamakin bakon jarumin.Abinda
ya
fara fado musu arai shine."Menene dalilin dayasa
bakon Jarumin bazai iya kwana tare dasu ba a
cikin
daki guda?Kuma menene dalilin dayasa duk a
tsawon wannan lokaci bai yarda anga fuskarsa
ba?
To waishin ma shi Namije ne ko Mace?Lallai
akwai
bukatar su tantance hakan domin su san hanyar
dazasu bi su rabashi da ALLON SIHIRI.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta dubi dan wada Dazyan tace
ashe maigidan naka ma bai yarda da kai ba
tunda ya
kasa kwana tare dakai a cikin daki guda?Koda jin
wannnan batu sai Dazyan ya takarkare ya bushe
da
dariya lokaci guda kuma yace yake wannan
sarauniya kiyi sani cewa ni kaina bansan ko waye
maigidana ba,ban san matsayinsa ba ko
asalinsa,hasalima haduwata dashi bata wuce ta
shekara uku ba,kuma a tsawon wannan lokaci
ban
taba ganin fuskarsa ba,kuma ban taba jin
muryarsa
ba bare kuda kuka hadu dashi a yau din
nan.Shawarar da zan baku kawai itace,ku yarda
da
duk abinda kukaji ya fada,kuyi imani dashi,in ba
haka ba kuwa karshenku shine NADAMA gami da
yin MUMMUNAN KARSHE!Nidai yanzu zanje na
nemi
inda zan kwanta saboda na gaji likis kuma nima
barci nakeji.Amma maigidana yace na shaidawa
miki
ke Sarauniya Akisatul Sauwara cewa lallai kema
ki
ware dakinki ke kadai domin a ka'idar addininmu
haramun ne kiyi cudanya da mutanen da basu
kasance muharramanki ba.Koda gama fadin haka
sai
dan wada Dazyan ya hango wani karamin daki
dake
can gefe daya wanda kofarsa ke bude
wanwar,kawai
sai ya tafi izuwa cikin dakin ya kunna kai
ciki.Koda
ganin haka sai Sarki Darmanu ya bishi da
sauri.Ita
kuwa Sarauniya Akisatul Sauwara sai ta tsaya ta
kama duru duru ta rasa dakin dazata shiga.Daga
can
kuma sai ta nufi wani babban daki wanda
kofarsa ke
rufe.Da isarta sai tasa hannunta ta murda
kofar,bisa
mamaki sai taga kofar ta bude da
kanta.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta kunna kai izuwa cikin
daki.Tana
shiga sai kanta ya daure tamau ta kamu da
tsananin
mamaki,ba don komai ba sai saboda ganin irin
kayan kawar dake cikin dakin.A tsakiyar dakin an
ajiye wani lumtsumen gado mai girman gaske
wanda
aka cikashi da kayan taushi na alfarma.Sannan
kuma akwai kofar kewaye a cikin dakin.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta leka cikin kewayen shima
taga
an kawatashi da bahon wanka na zinare.Kawai
sai ta
koma falon tayi tsalle ta fada kan wannan
luntsumemen gado cikin jin dadin huce
gajiya.Amma
kuma har a sannan raunikan jikinta basu daina yi
mata dan zogi da radadi ba.Nan take Sarauniya
Akisatul Sauwara ta fada kogin tunani.
¤P¤H¤Y¤S¤I¤C¤I¤S¤T¤
AL'AMARIN Yarima Lubainu kuwa,bayan yaga
kowa
ya shige cikin daki an tafi an barshi shi kadai a
tsaye sai ya kama yawo a cikin gidan yana
neman
dakin dazai shiga ya kwanta shi kadai.Ba don
komai
yake son ya sami inda zai kwanta ba shi kadai
sai
saboda ya sami damar dazai zauna yayi tunani
da
nazari ya yankewa kansa shawarar da zata
fissheshi.Da yake wannan fada ta Boka Darbusa
tana
da tsananin girma tamkar gari guda,kuma gashi
anyi
gine gine da yawa a cikinta na kawa,sai Yarima
Lubainu ya rude ya rasa ma bangaren dazai
shiga
domin da yayi yunkurin shiga wani dakin saiya
hango wani wurin wanda ya fishi kyau da
kawa.Yana
cikin wannan kai kawo ne ya shigo wani bangare
dabam na musamman wanda aka killaceshi a
wuri
mai ban al'ajabi.Shi dai wannan wuri ya kasance
tamkar lambu kuma an kewayeshi da katangar
zinare,sannan an zuba shuke shuke na 'ya'yan
itatuwa na marmari kala kala ga kuma tsuntsaye
masu kyau ababan sha'awa kuma kofar wannna
lamby a bude take.Har Yarima Lubainu ya gifta
kofar
zai wuce gaba sai ya jiyo shesshekar kuka cikin
muryar MACE!Al'amarin dayai matukar bashi
mamaki kenan,domin a zatonsa bandashi dasu
bakon jarumi babu sauran wani mahaluki a cikin
wannan gida.Yarima Lubainu ya dawo da baya ya
tura babbar kofar kambun ya kunna kai ciki.Yana
shia sai ya kame,idanunsa suka zazzaro
sakamakon
abinda yayi arba dashi.Ba komai ne abinda yayi
arba
dashi din ba face wata zabgegiyar kyakkyawar
Budurwar ALJANA a daddaure cikin wata
murtukekiyar sarkar tsafi waccce ta kanannade
hannayenta,kafafuwanta da sauran sassan
jikinta,kuma sarkar an zagayata ne a jikin wata
dirkar tsafi mai tsananin kaurin gaske wacce fiye
da
rabinta ya nutse a cikin karkashin kasa.Abin daya
daurewa Yarima Lubainu kai dangane da wannan
Aljana shine ko a bakin masana labarai bai taba
jin
cewar akwai halitta mai siffarta ba.Rabin jikinta
na
bil'adama ne,daga kasan cibiyarta zuwa
kanta.Daga
gwiwar kafafunta zuwa tafin
kafafunta kuwa na Aljanu ne.Kash!in badon
wannan
ratsin siffa ta Aljana ba dake jikinta da Yarima
Lubainu zai iya cewa duk duniya babu wata 'YA
MACCE mai kyan wannan budurwa ba.Koda
Yarima
Lubainu ya hada idanu da wannan budurwa yaga
idanunta sunyi sharkaf da hawayemkuma gata a
daure cikin sarka,sai nan take yaji ya kamu da
tsananin tausayinta.Amma da ya tuna cewa nan
fa
gidan Boka Darbusa ne babu mamaki ma wani
tuggun ne aka shirya musu aka ajiye wannan
Aljana
domin su fada tarkon wahala,sai kawai ya juya
da
nufin ya fice daga cikin lambun,kawai sai yaji
aljanar
ta budi baki cikin murya mai zaki da bai taba jin
irinta ba kuma mai tsananin taushin gaske
tace,haba
yakai Yarima Lubainu,ya ya kai daka kasance
mai
tausayi da jin kai zaka tafi ka barni a cikin
wannan
hali?Ka sani cewa shekara uku kenan wannan
azzalumin Boka Darbusa na tsare dani anan,ina
jiran
ranar da zakuzo ku koreshi daga cikin wannan
fada
ku ceceni.Koda jin wannan batu sai mamaki ya
sake turnuke Yarima Lubainu ya dubi Aljanar
cikin
alamun rashin yarda yace,wace ce ke kuma ya
akayi
kika sanni har kika san cewa zamu zo wannan
fada
mu kori Boka Darbusa?Sa'adda aljanar taji
wadannan
tambayoyi guda biyu ko uku sai hawaye ya zubo
mata,tace ni sunana BADI'ATUL SARIRA,Kuma
nice
'ya guda daya jal a wajen mahaifina Sarkin
Bokayen
Aljanu na duniya kaf,wato ZARHASU IBINI
SAMBILA.A cikin wannan duniya kaf in banda
Boka
Darbusa babu wani mahaluki daya kai mahaifina
karfin sihirin tsafi da kuma tarin sirrikansa.Loka
cin
da mahaifina da Boka Darbusa suka gano cewa
karfinsu yazo daya a sirrin tsafi sai suka zamo
manyan ABOKAN GABA ya zamana cewa
kowannensu na kokarin ya hallaka dayan ya
rabashi
da dukkan sirrikan tsafinsa.Asalin wannan ALLON
SIHIRI da kuka daukoshi a dakin tsafin Boka
Darbusa
a hannun mahaifina yake,daga baya ne bayan
Boka
Darbusa ya samu nasarar kashe shi ya
daukeshi.Ba
komai ne yasa Boka Darbusa yaki kasheni ba ya
daureni anan face cewa koya hada ragowar bari
biyun na ALLON SIHIRI dana Mahaifina bazai iya
cika
burinsa ba face nidin nan na karanta masa
wadansu
dalasiman tsafi dake jikinsa na fassara masa su
yadda zai fahimta,saboda yaren a akayi rubutun
dashi a jikin Allon Sihirin mahaifina ni kadai ce na
iya shi a duk fadin duniya,saboda mahaifina ne
ya
kirkireshi kuma tun ina yarinya karama ya koya
minshi.Ina mai rokonka daka taimakeni ka
kwanceni
daga cikin wannan sarka yanzu in dai kayi min
haka
ni kuma nayi maka alkawarin cewa zan iya raba
bakon jarumi da wannan ALLON SIHIRI,a cikin
dakika
daya jal,sannan na daukeka na kaika KOGIN
BAHAR
IMFAL a cikin abinda baikai rabin sa'a ba mu
shiga
cikin karkashin kogin na tsinko maka dan itaciyar
dazaka sha ka warke daga cutar da YARIMA
MANGUL ya sanya maka ka dawo cikakken da
namiji
ka koma ga matarka,babbar masoyiyarka
YAZARINA
ku fara sabuwar rayuwar aure cikin farin
ciki.Ladan
wannan aiki nawa kawai shine ka bar min
wannan
ALLON SIHIRI.Koda Aljanar tazo nan a jawabinta
sai
hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ainun ya
rasa irin amsar da zai bata.Abinda ya fado masa
a
rai shine,shin zai iya yarda da wannan Aljanr
kuwa?
To ai idan ma ya yarda da ita kamar yaci amanar
su
Sarauniya Akisatul Sauwara ne!
WACE IRIN SHAWARA YARIMA LUBAINU ZAI
YANKE
AKAN WANNAN DAMA DA YA SAMU?
MAI ZAI FARU TSAKANIN SU SARAUNIYA
AKISATUL
SAUWARA DA BAKON JARUMI IDAN GARI YA
WAYE?
WANE HALI BOKA DARBUSA YAKE CIKI BAYAN
YA
FALFALA DA GUDU IZUWA CIKIN DAJI BAYAN
SUN
FAFATA AZABABBEN YAKI SHI DA BAKON
JARUMI
DON YA TSIRA DA RAYUWARSA?
WANENE BAKON JARUMIN DAYA BAYYANA?
YAUSHE YARIMA YAKE CIKA BURINSA NA
SAMUN
LAFIYA DAGA LALURAR DA YAKE CIKI?
WAISHIN INA LABARIN YARIMA MANGUL?
WAYE ZAI MALLAKI ALLON SIHIRI.
Mu hadu a littafi na hudu(ALLON SIHIRI-4)don jin
cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari.

3 / 3