Chapter 3 Reading TAWA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN SHAKUR.txt Arewa Novels

TAWA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMAN SHAKUR.txt

Author :  M.Shakur Category :  My Hausa Novels

Chapter   3 / 12

6K to 9K   out of 35.6K words

CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
1⃣5⃣
Ta dinga waige waige harta hango wata yar kofa wajen tayi tana budewa taganshi taredasu abba zaune da sauri taje kusa dashi ta zauna kallo daya yamata ya dauke kai,

Dago kanshi yayi yaga dad na kallon shukra, wanda kanta na kasa gashinta sai zubar da ruwa yake, abun ma haushi yasoma bashi lpy dad ke kallon shukra haka?? Kawai jiyayi hankalinshi bai kwanta da irin kallon da dad kema shukra ba. ya mike yace mum ina abinci mu?? Tace yana dining yayi hanyar dining itama shukra tabishi da sauri, ta zauna kujeran kusa dashi, ya kalleta yace ina hijabin ki?? Banace inzaki fito kidingasa hijab ba?? Tace hijabin yay datti ne kayakuri, yace dan kwalin kayanfa?? Tace ai banganka bane shine naji tsoro, shine nafito namanta badaura ba, yay shiru yazuba nashi abinci yafara ci gani yayi tadau spoon tanacin nashi, zaimata magana saikuma yafasa yasan tare takeci da baba saisa, kadan taci tacire hannu.

Da akazo wajen kwanciyama da kyar yashawo kanta dan kuka takeyi wai bazata iya kwana ita kadaiba, saida yay mata tsawa yace wuce ki kwanta sanan ta kwanta ya lullubeta da bargo yafito daga dakin, yana fita tatashi zaune tana kuka tana kiran babanta ahaka har bacci yay awon gaba da ita.

Da sassafe aka kira dad din thariq yay bako a office yawuce yatafi, itakuma mum tashirya shukra wai zata kaita saloon a gyara gashinta saida thariq yasa baki shukra ta yarda dan kuka tadingayi sanan suka tafi.

Wuraren 12 na rana dad yadawo gani yay ma gadi na neman fada dawani kakkyawan matashi, dad yay parking yafito, yace baba mai gadi menene haka?? kafin yay magana NAZIR ya rigashi ta hanyar dukawa har kasa yana gaida dad, dad ya amsa da fara’anshi,
Nazir yace dad dama nazo neman auren yarka ne, dad yace nibani da yarinya mace, Nazir yace wacce jiya itada wanta da daddare suka dawo, sai alokacin dad yagane shukra yake nufi, aiko dad ya daure fuska,annurin dake fuskarshi ta bace bat yace kai yaro karna kara ganinka a kofar gidana, karka kara zuwa gidanan dasunan neman shukra, shukra TAWA CE nikadai aurenta zanyi,matata ce…..

Maman shakur 😘


mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← NISFUL HAYAT 156 to d ENDTAWA CE!!! 21 to 25 →
TAWA CE!!!16 to 20
Posted on November 4, 2015 by mamanshakur
[04/11 9:14 PM] Aishat muh’d: [04/11 9:09 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

1⃣6⃣
Nazir mekewa yayi daga tsugunen dayake ya kalli dad, yace wot are u saying men?? As old as u are men?? Yarinyar dakamayi jika da itane zaka aura?? Dad ya gyara malunmalun din jikinshi yace u heard me, shukra TAWA CE, she mine, babu abunda zaka iyayi ka chanza hakan, kabar kofar gidana kafin ranka yabaci.

Nazir da idonshi yay jaa tsabagen kishi, ya kalli dad yace tsoho bari kaji, Inhar money speaks, inhar money solves problems, inhar money buy happiness wlh write it down, mark my words sai na mallaki shukra, shukra TAWA CE, shukra tafi karfin tsoho, shukra tafi karfin kowa a duniyan nan balle ma kai dazaka kai shekara 70 ko fi ma, dad ya kalleshi yace muzuba nidakai, ya kwall ma mai gadi kira budemin gate, yakoma motanshi ya kunna saura kadan ya bige Nazir, Allah yasa yay saurin matsawa ya shiga cikin gida yay parking.

Nazir komawa motanshi yayi ya dafe kanshi dan sarawa yake, ya tabbatar inhar baiga shukra yauba hala sai ciwo yakamashi dan jiya kasa bacci yayima, ciro taba yayi ya kunna yana zuka daga bisani kuma yaja motanshi yabar unguwar.

Dad na shiga gidan dakin hj yawuce yaga basu dawoba, yakirata awaya ta dauka, hj wai haryanzu ba’a gama gyaran bane?? Tace alh yanzunan aka gama, gamunan zuwa, yace to yakashe wayan, zama yayi yay shiru yana tunanin, maisa yakejin son shukra?? Yarinyar da jiya yafara ganinta, nifa ba yaro bane shekara 75 ina zankai yarinyar dako 17 batakaiba, jiyakeyi wani wutan sonta na ruruwa a ranshi, dukya kosa sudawo rabonshi da ganinta tun jiya da daddare.

Thariq ne ya shigo dakin da sallamanshi dad ya Amsa, yazo ya zauna kusa da dad ya daura kanshi a cinyan dad, dad yay murmushi yasa hannu yana shafa kanshi yace thariq baka girma ko, gaka da kani amma haryau saika dinga shagwaba, yace dad ai ni har yanzu nima autane, dad yace imran dinfa shida yake 4 years kaiko kakusa kai 31, yace son tashi muyi magana.

Maman shakur 😘
[04/11 9:10 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

1⃣7⃣
Thariq ya tattaro hankalinshi yaba baban, yace son yaka mata ka ajiye iyalifa wai mesa bakason yin aurene?? Thariq ya sosa keya yace dad wlh inaso nazama kaman kai ne, nafison saina kai 40 years zanyi aure.

Dad yaji kaji wauta ko, ni danakai 40 bakasan phd dana tsaya nayi bane. kai kariga kagama karatu kazama likita, is tym ka ajiye iyali nima naga jikoki na, ya shafa kanshi son will u do dat 4 u dad?? Yay murmushi yace dad tunda kanason hakan naji zanyi, amma kadan ban lokaci na gama program dinan danakeyi a ABU sheka na zaria, dad yace shikenan son Allah maka albarka.

Dad yace zancen karatun shukra fa?? Thariq yace dama inaso nasata a school kafin nakoma zaria, a ss3 ta tsaya bata cigaba ba saboda lack of money, yanzu inason nasata a makaranta da imran yake tunda sunada secondary sai sudinga zuwa tare, sanan nasata a islamiyya da kuma haddan asabar da lahadi, dad yace hakan nada kyau my son, am proud of you, Allah yabaka ikon cika alkawarin daka dauka na rainon shukra yace Ameen, daganan suka cigaba da fira.

Wuraren 1 suka shigo gidan, mum taimata shopping sosai ta siyo mata kayayyaki dadai sauransu, tunda suka shiga falo dad ke kallon shukra, itako tana hango thariq da sauri taje kusa dashi ta zauna akasa ta kama kafanshi ta rike gam, shidai thariq tunani yake anya shukra zata chanza kuwa?? ta shigo bata gaida kowaba, kuma tazo tawani rikemai kafa.

Mum ce tai magana tace sannu shukra wato ke thariq kadai kike yarda dashiba, mu dodanni ne, tunda muka fita takewani dar dar dani kaman na satota, amma daga ganin thariq har kinje kusa dashi kin zauna, alh ne yay magana haba hj kidena takurama yarinyar nan, yarinya ce ahankali zaki bita, bata saba damuba, lallabata zamuyi tayi harta sake, hj sake baki tayi tana kallon Alh.

Alh ya kalli shukra yace shukra baby, ahankali ta dago ta kalleshi, oya zokusa dani ki zauna kinji baby na…

Maman shakur 😘
[04/11 9:10 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

1⃣8⃣
Make kafada tayi alamun bazata zoba, dad yace shukra baby bazaki zo kusa dani ki zaunaba?? Niko maman shakur na gyara zama ina kallon drama ga dukkan alamu dad baisan shukra ba,

Kara make kafada tayi, dad ya kura mata ido yana Kallonta, bude baki tayi a shagwabe tace ni ba shukra baby bace, ni yar baba ce, yar baba sunana, haka babana ke kirana ai, habawa mai mum zatayi inba dariya ba hhhhh, tace alh ai kaji hakanan zaka wani batama yarinya suna, bari imran auta yadawo daga school yaji kanacema wata baby akwai rigima kasanshi da kishi. Thariq na jinsu amma ko tak baiceba, damashi ba mutum mai yawan magana bane.

Suna zaune suna fira jefi jefi, shidai alh hankalinshi nakan shukra wanda har yanzu tana rike da kafan thariq gyangyadi ma takeyi, wani kakkyawan yaro fari mai kama da thariq saidai shi karami ne bazai wuce 4 years ba ya shigo da gudu yaje ya rungume thariq, thariq yace little champion jiya daddare nadawo amma wai harkai bacci, imran yace bro ai mum tafadanmin shine baka tashen ba kuma dazani school kana bacci. Yajuyo yagaida mum da dad sai alokacin ya lura da shukra da tunda ya shigo ta boye fuskanta akafan thariq.

Sakin baki yayi yace bro wacece wanan cirema kafa zatayi?? Kowa na dakin yay dariya, thariq yace shukra ta dago fuska ta kalleshi yace meet my brother imran, yace imran wanan anty kace sunanta shukra.

Imran yace wow bro wlh tanada kyau kaman balarabiya, yazo zai taba fuskanta abunku da yaro shukra takara maida fuskanta taboye, yace laaaaa bro anty tawa yar kauye ce, tsoron mutane take ma, shukra ta dago fuskanta tace ni bana tsoron mutane, kuma niba yar kauye bace, imran ya gyara tsayuwa yace is dat soo, ok inhar baki tsoron mutane biyoni da gudu to, ta kalli thariq ya gyada mata kai aiko tabi imran da gudu, shima imran ya kwasa a dari

Mum da dad sunta dariya, thariq yadanyi murmushi, mum tace inhar imran ne zata gaji da gudu yaronan dayake kaman barewa ga shegen surutu….

Maman shakur 😘
[04/11 9:14 PM] Aishat muh’d: [04/11 9:11 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

1⃣9⃣
Nazir na komawa gida yafada jikin mum dinshi sai huci yake tace lpy bomboy?? Bakagan ta bane?? Yace mummy am just angry am not in d mood to answer any of ur questions. Tace haba bomboy ka amsawa hala in samo ma maganin matsalan ka.
Yace mummy naje gidan wani tsoho nagani yacemin wai aurenta zanyi, mum wlh inhar ya aureta mutuwa zanyi, inason yarinyar kakkyawa ce mum wlh.
Mummy tace to inane gidansu? Yace mum ni bansan takamamman gidansuba, inda naga sun shiga naan naje kuma tsoho yacemin wai aurenta zaiyi, tace ka kwantar da hankalinka kacigaba da zuwa anguwar duk randa kaga yarinyar kafadamin, namaka alkawari ko wacece ita TAKA CE bomboy ya rungume mum din yana murna.

Thariq yajisu shiru yasa yabisu yana zuwa dakinta yaga bata wurin yana zuwa dakin imran yagansu kan gado tana koyama imran home, murmushi yayi har cikin zuciyanshi yaji dadi yanda tadan sake.

Washe gari Wuraren 10 yafito yasameta tareda mum suna gyara abinci a dining, abincin dake hanunta ta ajiye tana murna taje wurinshi dagudu kaman zata rungume yaja baya da sauri ke me haka?? Murya kaman tamai shirin kuka tace ina kwana, kafin ya amsa sukaji muryan dad yana thariq ka kiyayenifa, kaga yanzu ka bata mata raiko? Kai bakaji dadiba yarinya tasoma sakewa damu yau tareda mamanka sukai girki kawai dan tazo gaisheka zakaimata tsawa yay kwafa ya kalli shukra yace shukra baby jeki cigaba da aikin ki make kai tayi tace sunana yar baba.
Tawuce tatafi wajen mum tana tafiya tana waigen thariq daya saki baki yana kallon dad, harga Allah yasomajin wani iri game da dad amma ya basar yaje ya zauna a dining.

Abinci suka zauna ci, shukra ta zauna kusa da mum tana tsoron taje wurin thariq yamata tsawa abincin ma takasaci kadan taci, dad yace shukra baby cimana dan Allah kidanci kadan kinji, ta make kafada thariq yace jeki shirya nakaiki school registration ta tashi ta tafi daki.

Doguwan riga tasa ta daura hijab tafito, mum tace muje na shiryaki bahaka ake shiryawaba tabi bayan mum, mum ta dauko wani atampa riga da sket black da dot din yellow a jikinsu tasa takawo wasu takalmi masu dan tudu yellow tasa mata, tai mata make up tasa mata pink janbaki abun yahade da pink lips dinta ta daura dankwalin nan daurin nan da ake kira August meeting😜, tafesa mata turare ta dauko gyalee siriri yellow tabata. ita kanta mum tsayawa tayi tana kallon shukra kayan sun mata kyau gashi rigan yadan matseta kirjinnan acike, tai kyau kaman yar larabawa.

Shukra ko bata saba sa irin kayanba duk sun mata wani iri a jiki, mum tace mutafi thariq na jiranki, thariq yakira mun awaya tafito sauri nake, mum ta kalli shukra tace kitafi yana jiranki a mota ahankali take tafiya da takalmin dan jitake kaman zata fadi. tana fitowa daga dakin tai tuntube da ball din imran ihu tasaki ta tafi luuuu zata fadi thariq dayake tsaye yana danna waya yay maza yakai hannu ya tarota tafada kan hannunshi

Lumshe ido tayi sanan tabudesu ahankali ta daurasu kanna thariq, tsayawa yayi yana Kallonta har yanzu tana hanunshi bai mikar da itaba, zubawa juna ido sukayi…..

Maman shakur 😘
[04/11 9:12 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

2⃣0⃣
Kokarin kwace kanta daga hanunshi tafarayi dan tamike, firgigit yadawo daga duniyar daya lula ya kalleta are u all right?? Baki bugebako?? Tace eh, yasaketa yay gaba tana binshi a baya makaranta sukaje anmata interview duk thariq na wurin mamaki yake dama haka shukra keda kokarin ss3 suka bata ran Monday zata fara zuwa yabiya mata kudin komi suka baro school din.

Yana tuki yana satan Kallonta, murya mai zaki yaji tace Nagode Allah kara bude,murmushi yay mata kawai batareda ya amsaba,
Agaban wani super market mai suna EVERYDAY SUPERMARKET yay parking yace mata fito muje tafito siyayya yay mata sosai suna kaiwa wurin chocolate tasa hannu ta dauka zata bude taji thariq ya daka mata tsawa wanda saida yajawo hankalin mutanen wajen, Nazir dake tsaye yana biyan kudin abunda yasiya yajuyo wazai gani shukra shi, jiyayi thariq na mata masifa wot are u doing shukra?? Baki da hankaline?? Naki ne dazaki dauka?? Cikin muryan kuka tace inaso nefa, Nazir da ranshi yagama baci, wanchan guy din yanama shukra tsawa gaban jama’a.

Yakara daka mata tsawa ajiyeshi jiki narawa ta ajiye, ya gungura keken tana biyedashi yaje yabiya kudin abun suka fita, shikuma Nazir chocolate din yasiya dayawa yabiya yabiyo bayansu, da sauri yakarasa lokacin zasu shiga mota shukra sai kuka takemai,

Zuwa yayi kusa da shukra ya share mata hawaye a tsorace ta matsa baya, da gudu ta zaga inda thariq yake ta labe abayanshi, Nazir yakara biyota wurin baby na ga chocolate dinki kishaa, takara rirrike thariq, thariq yajuyo ya kalleshi malam bata bukatan chocolate dinka kawuce kabamu wuri.
Nazir ya kwantar da murya shukra inkina ma Allah ki karba kinji, ciro kanta daga jikin thariq tayi tajuyo har tamika hannu zata karba thariq yace wlh inkika karba zan bata miki rai wuce ki shiga mota da sauri ta shiga hartana tuntube.

Shikuma yajuyo ya kalli Nazir stay away 4rm my sister, ba kalar ka bace, kanwata matar natasastsen namiji ce, kamili, karabu da ita ka kuma dena binmun last warning.
Yawuce yashiga motan yaja, suna kaiwa gida yaba mai gadi kayanta yakai mata daki, shikuma yawuce ya shirya dan yanason yakoma yau saboda ana kiranshi a asibiti, yana gama shiri ya shigo yaganta zaune falo bai cemata komiba yawuce dakin mum yay mata sallama taimai addu’a, yafito ya ganta jugum.

Yace shukra zan koma zaria ana nemana a clinic,kimin addu’a kinji, yajuya yafita dagudu tabishi har zai shiga mota saiya tsaya daya ganta, rike mishi hannu tayi tana kuka sosai dan Allah karka tafi, wlh inhar dan abunda nayi dazune bazan karaba plz, kaga kaine babana na biyu, plz dont go, i dont want u leave me, kuka take sosai tana rike da hanunshi,

Dago jajayen idonshi yayi dan tabala’in bashi tausayi ahankali yace shukra bazan dadeba zan dawo kinji, ki zauna dasu mum kinji, ta make kafada tana kuka, sa hanunshi biyu yayi ya dago fuskarta shukra kallen i promise u next week Saturday zanzo nadubaki, kinsan ke AMANATA ce, i soo much care about u shukra, ki koma cikin gida tafiya take tana waigen shi yadaga mata hannu yana murmushi.
Saida tashiga gida sanan yashiga cikin mota dauran kanshi kan starry idonshi yay jajir dago kanshi yayi yashafa fuskarshi ya fuzar da iska yace shukra ke TAWA CE!!

Masu karatu kunfaji ga uba, ga da, gakuma Nazir,
Towai shin shukra TAWA CECE????.

Maman shakur 😘

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← TAWA CE!!!16 to 20TAWA CE!!! 26 to 30 →
TAWA CE!!! 21 to 25
Posted on November 5, 2015 by mamanshakur
[05/11 7:59 PM] Aishat muh’d: [05/11 7:56 PM] Aishat muh’d: TAWA CE!!!

2⃣1⃣
Tada motanshi yayi yabar gidan, shukra na komawa cikin gida dakinta taje ta kwanta, ta fashe da kuka jitayi mutuwar baba yadawo mata sabuwa fill, mum ce tashigo tadinga lallabata haba shukra baganiba, bayace zai dawo next week yadubaki ba, nasan thariq akwai cika alkawari zai dawo kinji ta girgiza kai.

Mum ta rungumeta tana lallashinta hartai bacci, mum tabar dakin, lokacin da imran yadawo yazo dakin tadan sake harta koyamai home work daganan tafito taga mum a kitchen.

Mum tace shukra hala imran ne yatashe ki?? Ahankali tace no bashivane, takarasa cikin kitchen din tareda mum sukai girkin mum takoya mata abubuwa dayawa.

Bayan magrib duk suna zaune a falo imran na jikin ta yana wasa itakuma tai shiru tunanin baba take dayanzu fa suna hanyan dawowa daga gareji, sallaman dad sukaji mum ta tashi ta rungume shi, amma gabaki daya hankalinshi yanakan shukra, ture mum yayi daga jikinshi yakarasa cikin falon da sauri ganin shukra dayayi cikin damuwa ya tsugunna gaban shukra,

Murya kasa kasa yace shukra baby?? Menene?? Meke damunki?? Hj taimiki wani abune?? Kifadamin dan wlh bazan bari wani yatakura miki a gidanan ba yana maganan yana kallon fuskan mum da alamun da ita yake.

Shukra ta girgiza mai kai, yace to Menene yayanki thariq kikeson yadawo?? Ta dagamai kai, yakara kwantar da murya yace karki damu ran sati zaizo kinsan banason ganin ki cikin damuwa, imran dayaga dad yadane jikinshi dad ya dakamai tsawa kai bakaga ina magana bane?? Imran yatashi yana kuka yaje ya rungume mum,

Dad ya fito dawani kwali acikin ledan daya shigo dashi ya mika mata adan tsorace ta karba yace kinga wanan wayan takice, nasamiki layi da komi aciki, kinga ai zai debe miki kewa, banason ina ganinki cikin kunshi kisaki jiki kiyi walwala kinji.

Tace to Nagode, yace yauwa shukra baby, oya tashi muje kici abinci yarike mata hannu da sauri ta fizge hanunta, taje wurin mum tace mum kinga wayan da dad yasiyomin, ita shukra bata lura da yanayin mum ya chanza

3 / 12