MISKILI NE COMPLET BOOK BY MOM FAREESA.doc

Author :  mommyn fareesa Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   29 / 31

84K to 87K   out of 90.4K words

biyota tana mirginewa"karfa kije ki fad'o"juyawa tayi da nufin taga ta kawo k'arshe yayi saurin rik'eta suka kama kokoyi suna dariya"gaba d'aya sun hargitse saman bed d'in"can Amaan ta sauke numfashi tana fad'in wlh nagaji hamma"ta fad'a tana kwanciya Ajikinsa tana shafa gashin kansa dana fuskarsa"ya sauke numfashi murya a kasale yace"salfad kin shirya?"uhmm"Amma hamma pls nidai....nidai karkamun me zafi"shine zaki fad'a ko?"yak'are maganar cikin kwaikwayon muryarta" duk sukayi dariya Atare"kayan jikinta yafara ragewa kafin yakaima nashanunta wata iriyar cafka "ta rintse Ido kawai sbd harma ta saba da irin wannan matsar datake sha hannunsa....tun wajen k'arfe 8:30pm Ake Abu guda 11 pm shariff be sararawa Amaan ba sbd yaji tace ko kwana zaiyi bazata gajiba" saidai yanayin yadda yaga jikinta yasaki yasaka ya fahimci dauriya kawai takeyi saiya k'yaleta"da k'yar yasamu ta gasa jikinta sukayi wanka"ko zaman kirki bata iya"tunda ta Aureshi be tab'a jumawa irin haka ba sai yau"ita kanta tausayin kanta takeyi"koda safiyar yau saida yayi da ranama haka da sukazo masauki"yanzun ma haka yakomayi"ta tabbatar da safe shima saiya komayi"sosai sharrif ya tausayawa Amaan"saida yafita yasiyo mata magunguna"sai rarrashin ta yakeyi,bayan tasha babu jumawa wani wahalallab bacci yayi Awon gaba da ita......washe gari da safe sharrif beyiwa Amaan komai ba" sbd tausayinta daya keji ba kuma sbd be soba yadai hak'ura ne kawai"wajen k'arfe 10 na safe jirginsu yatashi yanufi k'asar London......

************
Anutse suke sakkowa daga matattakalar jirgin"Amaan tayi shigar bakak'en kaya irin na larabawa"sharrif kuma yana sanye da suit bak'ak'e"yana rungume da Amaan fuskokinsu shimfid'e da wani tsadaddan murmushi sbd iskar k'asarsu ta haihuwa da suka shak'a"sunyi kyau da haske had'e da shek'i"ga Amaan da zama y'ar lukuta Ajiyar sharif harta turo gaba"sbd sadda sukabar k'asar tanada juna biyu wata guda yanzun kuma cikin watansa4 yama shiga na biyar.... mus'ab, sadeeq, Abdallah da sukazo tarbarsu ,mamakin ganin cikin Amaan sukeyi"sbd basu san tanada juna biyu ba koda ta waya ne....wayyo hamma nayi missing Nigeria wlh"inama mu wuce Adamawa....sai bayan kin haihu salfad"turo baki tayi "kinga nidai kiyi Ahankali bake d'aya bace kin kuma sani"wai dan Allah dani da ita koshi waye kafiso??"murmushi yasaki yak'i bata Amsa"Adaidai lokacin da Abdallah ya iso Aguje ya rungume sharrif "mus'ab da sadeeq na gefe suna gaisawa da Amaan"maman twins sannu da zuwa"cewar Abdallah yana cika sharrif"Amaan ta tab'e baki tana fad'in sai yanzun ka ganni?"Aita yayanka kakeyi ko?"rabu da ita Abdallah yanzun ta koma masifaffa koni tsoronta nakeyi yanzun"cewar sharrif "Ammaan ta maka masa harara tana sakin kukan shagwab'a"ya matso yakama kunnansa guda yana fad'in nine daiko? to nadena"nidai saika mari kanka zan hak'ura....wai Abokinah duk soyayyar dakukayi acan be isaba, Anan gabanmu ma sai kun k'ara yi?"sannan harda rashin kunya Amaan ta koyo"sbd nasan ita d'in me kunya ce"Amma gashi ta canza"dariya tayi ta b'oye fuskarta Ajikin shariff"kaga bana son sharri zaka sakamun mata Agaba"mus'ab yayi murmushi duk suka gaisa"driver ya kwashe kayansu da tsarabar da suka jibgo yaloda a boot"sharrif yabmatso ya bud'ema Amaan mota ta shiga"mus'ab ya matso dab dashi yana fad'in Abokinah harda tsaraban d'an saudiyya ko London muka samu?"shine ko Amana Albishir ta waya?"wlh mus'ab ko Ammi bata saniba"salfad tasaka rigima kar Asanarwa kowa kunya takeji" shiyasa nayi shiru kawai"yanzun gashi yafito kowa yagani ko? To Ai dama d'an dumane yad'o yakeyi mijin tace"nan gaba kad'an k'ilan ko bacci zakayi sai Amaan ta yarda"banza d'an saka Ido"yafad'a yana tab'e baki" mus'ab yakama dariya dariya"Amaan kuwa harta gaji da jiransa tafara jero masa flashing "babu shiri ya shigo motar"su kuma su sadeeq suka shiga motar mus'ab "kai tsaye gidan Ammi suka nufa"suna isowa Amaan tayi k'ok'arin bud'e marfin motar da sauri" shariff ya rik'e hannunta yana fad'in saurin me kikeyi ne mmn twins?"twins kakemun fata salfad?"Eh mana bakiji me Abdallah yace ba?"yafad'a yana binta da wani irin kallon dake saurin kashe mata jiki"Ahankali tace"nifa babu ruwana dashi"shida Akace sudan zai tafi kuma shine yadawo?"tafiyar bata yuyu bane"nidai Allah ka cikani baka san yadda nayi kewar Ammi bane"to idan ta tuhumi meyasa Aka b'oye mata kina d'auke da jikantafa?"yafad'a yana d'age gira"kukan shagwab'a tasaka tana k'ok'arin gartsa masa cizo yacika hannun nata yana murmushi batare daya furta komai ba"ita kuma ta bud'e k'ofar suka fito Atare"wanda k'asan zuciyarta itama kunyar Ammin ta ganta da cikin ne"haka dai ta daure sharrif na rik'e da hannunta suka wuce interest d'in shiga cikin gidan"tunda Ammi taji horn d'in motoci ranta yabata sune tana duba window ta hangosu sunyi kyau gwanin burgewa" Alamar hankalinsu A kwance yake"saidai idonta na hango mata cikin Amaan ta kama baki"sai kuma tayi murmushi tana zaton k'ilan kunya sukeji daga ita har sharif d'in shiyasa basu sanar mata ba... tana fitowa daga cikin d'akin su kuma suna shigowa cikin parlourn da sallama "oyoyo ga Amaan ga Amaan"ta fad'a tana murmushi "shikenan bara nina koma"cewar sharrif yana had'e rai "sadeeq da Abdallah dake bayansu suka tun tsure da dariya Amaan na tayasu,kafin taje ta rungume Ammi suna murnan ganin juna"sharrif kuwa y'an miskilancin suka motsa"tunda suka gaisa yatambayi ya gidan be koma mgn ba"Amaan kuwa tama nuna bata damu dashiba sai surutunta takeyi itada Ammi da sadeeq dake saka musu baki jefi jefi" koda zasuci Abinci cewa yayi beci"Amaan ta kallesa suka had'a Ido ya wurgo mata harara "Aransa yace"yanzun zamu koma gidan yarinya badan sbd kin gansuba kika shareni....hamma pls kataso muje"nidai kasan yunwa nakeji wlh idan baka ciba ni bazan ciba "ta kare maganar tana jan hannunsa "Ammi ta d'auke kanta daga barin kallonsu"dan tana son ma ta keb'e da sharrif d'in sbd zasuyi wata mgn me mahinmanci dashi....
'?
wannan book d'in na kudine ! idan kina buk'atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

d'
=?%? *MISKILI NE*d'
=?%?

*75&76*





.......duk yadda amaan taso mutumin nata yatashi yabita suje suci abinci k'iyawa yayi"saima yakoma mata sak sharrif d'insa nada"sudai sadeeq da abdallah kallonsu kawai sukeyi suna dariya"sosai amaan ta k'ule saidai bata tanka kowaba ta koma kan kujerah ta zauna tana danna waya, sharrif kuma yana satar kallonta sbd dama so yakeyi ya ganta cikin irin wannan yanayin tafi masa kyau"wai yaya baraka tashiba sbd anty amaan?"cewar sadeeq"kaga mlm ba'a shiga tsakaninmu inama ruwanka?"murmushi yasub'uce mata ta kalli sadeeq ta masa gwalo tana tashi tsaye sharrif yabiyota suka wuce dining area"salfad! uhmm ba gida zamu koma ba?"toni me zaka mun idan mun koma?"kinfi kowa sani yarinya" ya k'are maganar yana ja mata kujerah ta zauna shima ya zauna gefenta"abinciccika masu rai da lafiya na gargajiya dana zamani gasu nan"amaan ta zuba musu sunataci suna santi "sai tsokanarta yakeyi, sadeeq da abdallah da ammi nata kallonsu daga nesa"bayan sun gama yatafi masjeed shida abdallah sbd ankira sallar azahar"ita kuma amaan tabi ammi d'aki sukayi tasu"bayan sun gama ammi nata kallonta sbd ba k'aramin kyau da canzawa taga tayiba"hak'orin makkan data sa yamata kyau sosai"ita kuwa kunya dukta kamata sai taga kamar cikin ammin ke kallo"na d'auka kota can adamawa zaku wuce kafin daga can kuyo tanan....itada zuwa adamawa sai bayan ta haihu insha allah "cewar shariff ko ajikinsa daya shigo ya tsintsi maganar"to allah ya sauketa lafiya"cewar ammi daga haka tayi shiru"yayinda amaan batace komai ba saima mik'ewa tsaye tayi tace"ammi bara nakoma parlourn "wanda tayi hakanne sbd ta basu waje su gana"kuma hakan yak'ara mata mutunci wajen ammin "bayan ta fita shariff ya zauna kan sofa yana shafa kansa"dama inason muyi wata mgn dakai"to ammi ina jinki" kaga yanzun dai idan madeenah ta k'are karatunta za'a sa musu rana da sadeeq "inaso kafin ayi auren nasu nima nayi nawa auren.... atake fara'ar dake saman fuskar shariff ta b'ace b'at"yayi kicin kicin da fuska yana fad'in haba ammi! wane irin mgn ne haka?"bayan bani nan wani ke zuwa ko?"kin manta abinda alh yahaya yaso yamana ne?"dama nasan zakayi wannan tunanin "ba wani bane alh kabiru ne abokin mahaifinku....wannan ai cin amanane ammi"yana abokin mahaifinmu zaice zai aure ki? ya katseta fuska bbu walwala"raya sunar manzon allah s a w d'in shine cin amana sharrif?"wuce nayi auren nayi ne kome?"to bari kaji! na riga na gama mgn sbd na shawarci y'an uwana "ban sanarwa sadeeq da abdallah ba na bari saina fara yimaka mgn"sbd nasan zab'inka shine nasu"idan sbd gidan mahaifinku d'aya zama naku ayanzun"har nike zaune ciki kuke tak'ama saina bar muku gidanku naje gidansa wata tsiyar ce"sbd ina lallab'aku shiyasa kukeyin abinda kukaga dama bama kamar kai....sosai gaban sharrif yafad'i yana tunanin kodai alh kabiru bebar ammi hakaba"sbd k'aramar mgn sai fad'a take masa haka...idan baza kayi mgn ba tashi kabani waje" kaje kaja matarka kubar min gida....yanzun ammi sbd y'ar wannan maganar har ranki zai b'aci?"babu komai aure daine ko?"allah yasa alkhairi bana fatan abinda zai saka kibar gidan nan har abada"idan na miki laifi sbd maganar auren kiyi hak'uri "yana fad'in hakan yamik'e tsaye yabar d'akin kamar zai tashi sama"gaba d'aya kuma ammin sai taga kamar bata kyautaba"sharrif na fitowa amaan ta kallesa"atake ta fahimci ransa ab'ace yake"ko mgn be mataba saidai hannunta yakama ya d'auki hand bag nata da wayarta dake gefe yayi hanyar k'ofa da ita"sadeeq da abdallah suka bisu da kallon mamaki"sanin halinsa na zafin zuciya yasaka tabishi da yadda yakeso batare data tankaba "koda suka iso parking lot da hannu yayima driver mgn"kafin ya bud'e motar yasaka amaan sannan ya zauna kusa da ita"ta kwanto ajikinsa batare data ce komai ba ...har suka iso gida babu wanda yace uffan"ko wane da irin kalar tunanin dayakeyi"sharrif yayi dana sanin dawowa k'asar inda yasan b'acin ran dazai samu kenan daba yanzun zasu dawo ba"duk ma'aikatan gidan sunata k'ok'arin gaishesu amaan ta sanar musu suyi hak'uri agajiye suke"shidai uban gayyar be tankaba yana dai rik'e da hannunta suka wuce babban parlourn gidan mutum ukku na biye dasu d'auke da tsarabar da sukayi"ko ina share goge k'al dashi"bayan sun ajiye suka fita"amaan dake zaune gefensa ta kama hannunsa guda ta fashe masa da kuka"yabita da kallo da idanuwansa da sukayi jajir"ya zare hannunsa guda datake rik'e dashi yakai saman bakin ta data b'are ya rufe mata bakin yana girgiza kansa had'e da yimata nunal d'in menene?"bakai bane kaketa fushi daga dawowarmu"pls nidai hamma kayi mgn mana konaji sanyi cikin zuciyata"yaka mata kasanar mun meke damun ka ?"amaan fad'in bashida amfani"tunda aikin gama yagama"nasan kinsan alh yahaya da y'ar sa iftihal wanda ammi ta aura?"eh nasan komai"to yanzun wani abokin abban mune yakeso ya aureta na nuna bana so shine ranta ya b'aci"banaso na zama sanadin b'acin ran mahaifiyata amaan "yah salam! to hamma cewa kayi baka amince ba har tayi fushi?"uhmm"kayi hak'uri ka koma yanzun kasami sadeeq da abdallah kununa mata kun amince"sannan nasan kasan beda matsala wanda zata aura d'in ko?"k'in mgn yayi"amaan ta girgiza kanta ahankali tace "hamma ammi fa bata wuce aure ba"ka barta tayi abinta ta sami ladar"kuma zai k'ara mata mutunci wajen idanuwan jama'a "pls salfad kaje ku bata hak'uri kaji ko? ta fad'a cikin rarrashi had'e da kwantar da murya"ya d'auki kusan second 5 kafin yace" to idan nadawo meye zaki bani?"kaina gaba d'aya zan baka nawan"kyan alk'awari?"tana murmushi tace cikawa"ta k'are maganar tana jan hannunsa saiya fisgota ta fad'o saman jikinsa ya rungumeta itada cikin"murya can k'asa yace"pls inaso na gaisa da baby nah salfad"tunda ajiyarsa ta fara bayyanah ajikin ki kike wahalar masa da daddynsa ko?"nidai kaje kadawo pls"shikenan tunda korata akeyi" dama mun had'u da wata y'ar budurwa a face book kinga sai naje wajenta.....be rufe bakiba ta juyo ta ballo masa harara tana turashi"yasaki guntun murmushi yana fad'in wasa nake salfad"amarya kuma uwar gida agidan fahad shariff keda kishiyasa har abada insha allah"kin isarmun da komai habibaty"k'ank'amesa amaan tayi cikin jin dad'in kalamanta "daga k'arshe suka fara kissing d'in juna"da k'yar ta samu ta lallab'a shi yatafi"ita kuma ta wuce saman su inda bataba masu aiki damar zuwa ba"da kanta ta gyara sashensa dana ta"sannan ta shiga wanka "tana fitowa ta sami shariff kwance kan bed dagashi sai d'an guntun boxer"suna had'a ido ya d'age mata gira "harka dawo?"eh salfad"kinsan meya bani mamaki?"uhmm uhmm"bayan mun gama rarrashinta sai cewa tayi nasan sharrif amaan ce ta turoka ko? nace eh cikin mamaki"sai cewa tayi allah yayi mata albarka hak'ik'a kayi dace"kaima sadeeq allah yasa madeenah ta kasance irin haka"kai kuma abdallah allah yabaka ta gari"amaan na murmushi tace"ameen ameen"to y'an mata sai azo a sauke alk'awari ko?"sallah fa zanyi hamma"kumafa nidai saida dare ko?"ta k'are maganar cikin shagwab'a "kinsan allah kije kiyi sallarki tun kafin nazo na karya miki alwallah"sanin halinsa k'aramin aikinsa ne yayi fin hakan yasaka tayi shiru ta nufi gaban ward rope ta d'auki doguwar riga da hijab"bayan tasaka ta kabbara sallar"tana sallamewa ta zauna zaman yin azkhar "tana cikin yin azkhar d'in saidai taji sharrif yayi sama da ita"daga ita har cikin yanufi saman bed"tanata kukan shagwab'a daga haka komai yaci gaba da wakana......
kwanci tashi asaran me rai! yau da gobe batabar komai ba"rayuwa ta lula"amaan suna rayuwa me dad'i ta hanyar zuba ingantacciyar soyayya da kulawa da juna dukda dai wata ran akan sab'a"tuni ammi tayi aurenta"alh kabiru tsakanin sa ga allah ya aureta "yanada mata guda da yara 5"gefe guda kuma ansaka ranar auren madeenah da sadeeq wata biyar masu zuwa"yayinda daddy ya yafema anty zabba'u saidai yace"babu batun maida ita d'akinta"yanzun babu laifi mommy na kulawa da yaran"zancen da akeyi ma ansaka ranar auren shamsiya itada nasir sbd yasaki waccan matar tashi"shima hamma yusuf ansaka masa rana"kuma abin farin ciki duk wata gudane za'ayi harda nasu madeenah.... amaan me juna biyu ta tabbatar abinda ke cikin cikinta d'an gata ne gaba da baya"sbd kowa zancen cikin yakeyi"ammi ta tanaji komai na haihuwa"ada sharrif yace banan zata haihu ba"ammi ta hana tace"idan ta tashi yin haihuwa ta biyu ko inama zasuje suje batada matsala"amma haihuwar fari anan gida nigeria zata yita.....ayau yakama week end babu office"tun wayewar garin safiyar yau amaan takejin jikin nata sai ahankali daurewa kawai takeyi"sbd ko yaya tace batajin dad'i zakiga sharrif yadamu ya lailayeta sun tafi asibiti"sadeeq kuwa kullum sai yazo gidan yadubata ko bata magani ko tambayarta yatakeji?abdallah kuwa idan bashida lactures zaizo yayi zaune yana bata labarin yadda zasu dinga wasa da yaron da zata haifa musu"sbd shi namiji yakeso ahaifa"sadeeq da amaan da shariff duk y'a mace suke so"kuma sharrif ya hana aduba musu meye zasu haifa"yanzun haka dai sadeeq yace"idan namiji ne zai bama abdallah million guda"shi kuma yace "idan macece zai masa wanki da guga na shekara guda"shidai shariff da amaan dariyace tasu.... abubuwan basu ida dagulewaba saida sharrif yabuk'aceta"sbd wannan cikin baya hanashi yayi budurinsa son ransa ajikinta"wajen k'arfe 12:30pm ciwofa yafara cin k'arfin amaan "sharrif dake zaune gefenta yana danna mata k'afafuwan ta yace" yaya dai salfad?pls hamma marata ke ciwofa,kuma abinda ke cikin sai motsi yaketa yawan yi... ai muje asibiti kawai salfad"kinga dama saura 3days edd naki yacika"yafad'a yana tashi tsaye yatai maka mata ta tashi suka wuce wani d'aki "duk abinda zasu buk'ata sharrif ya had'a cikin wani babban troley kafin su fito yakira masu aikinta yace suje zasu fita.....lokacin da suka shigo cikin mota abin yak'ara k'arfi addua kawai amaan keyi"arud'e sharrif yakira sadeeq yasanar masa yaje asibintinsa yanzun gasu nan isowa amaan ke labour" kuma yasami doctors mata babu wani namiji ko yarinya nurse da zata duba masa mata"yana gama wayar dashi yakira ammi"tasanar masa su had'u can"suna isowa sharrif beyi wata wataba ya d'auki amaan yashige labour room d'in da ita"kasancewar sadeeq be isoba amma yayi waya"sai masifa sharrif keyi cikin labour room d'in yak'i fita wai agabansa zasu dubata"saida ammi da sadeeq suka iso suka masa mgn sannan yafita"itama ammin fitowa tayi itada sadeeq tana bashi baki sbd sai safa da marwa yakeyi yayi uban gumi"bayan sadeeq yatafi office"suna tsaye sukaji sallama"ammi ta juyo ta amsa sallamar wata mace tana tsareta da ido sbd taga kamar ta santa"matsowa tayi ta duk'a gaban ammin ta fashe da kuka tana fad'in nice ibtihal ammi"nasan bazaki ganeniba sbd rama da duhun danayi"hak'ik'a duk wanda duniya tayi galaba kansa ya aureta har yayi sharholiya acikin ta"tofa yayi hasara kuma yana tare da dana sani.....kinga dallah ki dena mana wani zancen banza munata kanmu"ki tashi kibamu waje ko jikinki yaga miki"tunda dama duniyar ta juya miki baya ai dole kiyi nadama marar amfani"cewar sharrif atsawace yana binta da kallon banza"ta mik'e tsaye tana share hawayenta ammi ta tsaidata ta zaro dubu goma a jaka ta bata"hannu na kirma ta amsa tana godiya ta wuce"daga yanzun bance ka koma irin hakaba sharrif "dama kwanaki sadeeq ya gayamun ta kamu da ciwon k'anjamau"tana bin asibitoci yawon neman taimako sbd dangin uwarta dana ubanta babu wanda zai taimaketa"tunda daga uwar har uban kowa ya mutu...ita irin wannan rayuwar idan mace ta fara yinta"jinta takeyi babu ya ita"kuma babu abinda zatayi da manyan kud'ad'e zasu shigo mata sai hakan"saidai duk ranar da duniya ta dena yayinsu tayi juyin waina dasu saidai addua"fatanmu allah ya shiryi masu irin halinta "yana k'ok'arin mgn aka bud'e k'ofar labour room d'in..... atare ammi da sharrif suka nufi bakin k'ofar suna kallon doctor d'in"tayi murmushi tana fad'in ta sauka lafiya"ansami baby boy"ina dr sadeeq?"alhamdulillah nayi me gida"yau allah yanuna mun ranar danaga sharrif ya haifi d'an kansa"kai masha allah! cewar ammi cikin jin dad'i da tsantsar farin ciki"uban gayyar kuwa hannu sama ya d'aga yana godiya ga allah "doctor d'in na k'ok'arin komawa ciki sadeeq ya iso yana fad'in da alama ta sauka ko?"eh ta sami d'a namiji "cewar ammi"ok doctor kije ki shiryata itada babyn akaisu d'akin hutu"yak'are maganar yana rungume sharrif yace"congratulations yaya"kaga abdallah yaci million guda kenan?"gaskiya bazan iya bashi ba"kama isa ? yadda ka cika baki kayi alk'awari dole ka cika"barama na kirashi nasanar masa"cewar ammi tana zaro waya"sharrif kuwa cikin tsantsar farin ciki yacika sadeeq yakira mus'ab da hamma yusuf "cikin k'ank'anin lokaci kowa yaji labarin haihuwar amaan....me jego kuwa taji yau yadda akeji"bata tab'a zaton haka haihuwa takeba"bayan

29 / 31