Author : Billyn Abdul Category : Aysha Cool Novels
ya kai kamar zai tsone mata idon, dan haka tasa hannu da sauri ta kare. Sai ya saki dariya, itama murmushi tayi mai cike da kunya. Zuciyarta na faɗa mata abin da bakinta bai iya faɗa, cewa sabuwar rayuwa ta fara a garesu kamar yanda Inna ta faɗa mata, kuma shi mutum ne da nutsuwarsa ke girmama kwarjininsa a idanun kowa a bayyane.
“Kin tafi tunanin miye kuma Matar Abdul-rasheed?”.
Kai tsaye ta ce, “Tunanin ka”.
“Masha ALLAH akan mi?”.
Babu kwalo-kwalo ta zayyane masa kalaman Innar tata. Ya ɗan tsaya kawai yana kallonta da murmushi. Kafin ya cigaba da cin abincinsa yana jin girma da kimar Inna na ƙaruwa a ransa. Haka dai suka karya, ya taimaka mata suka gyara wajen, ta kwashi kwanikan zuwa waje danta wanke a gaban rijiya. Shi kuma sai ya ɗauki botikin ƙarfe ya fara jawo mata ruwan wanke-wanken, sannan ya fara ɗiba a botikin yana kaiwa randunan ruwansu ɗaya bayan ɗaya. A haka suka kammala aikin yace zai yi wanka. Ita da kanta ta ɗauki ruwan takai masa bayi tare da kwandon soson wanka. Ta dawo ɗakin ta saka turaren wuta ta share. A lokacin ne kuma yaro yay sallama cikin gidan ɗauke da kwanika akan ture. Bata yayi tare da mata bayanin cewa Inna ce tace ya kawo. Bata san wacece Innar ba, amma taji a ranta daga gidan su Abdul-rasheed ɗin ne. Godiya tayi da sannu, dan haka yaron bai zauna ba ya juya ya koma. Fitarsa babu jimawa Abdul-rasheed ya shigo. Ya ce, “Sallamar wa nake ji ne kamar Amadu?”.
“Wani yaro ne dai, ban sani ba ko sunansa kenan, abinci ne ya kawo yace inji Inna”.
“Oh daga gidanmu ne. To ki zauna sai ki karya”.
Idannunta a ɗan ware ta ce, “Ba yanzu muka gama karyawa ba? Naƙoshi ALLAH”.
“To Alhamdullahi, ki ajiye sai zuwa anjima. Amma kije kema kiyi wanka kada mutane su fara shigowa suna ganinki da kaya tun na jiya”.
Babu ko musu, sai ma amsa masa da tai cike da ladabi, daga haka ta ɗiba ruwan itama ta wuce bayi. Lokacin data fito harya shirya, dan haka bai zauna ba yay mata sallama ya fice dan har yara sun fara shigowa gidan. Aiko itama A'isha a gurguje ta kammala saka kaya, ta zauna tai kwalliya gwargwadon iyakarta kuma dai-dai da lokacinsa. Daga nan ta fiddo ma yaran da suka fara taruwa a gidan tabarmin karauni, sai kuma ta kwaso shantu duk ta zube dan harda ƴammata. Ai daga nan suka kafa shiriritar kiɗan shantu da ƴammata sa'anninta a tsakar gidan nan suna raira waƙoƙin gaɗa. Kafin kace mi gidan ya cika da yara. Manya dake shigowa ganin ɗakin amarya kota kansu basa bi ma, sai dai su shiga su gano su saka albarka su fice abinsu batare da sun damu ba, dan wannan ba komai bane daga amaren wannan zamanin nasu saboda ƙuruciya da ƙarancin shekaru..
Amarya A'isha bata sake tunawa da batun Abdul-rasheed ba har yamma ta samu abokan shargalle, abincin rana da aka sake kawowa ma daga gidansu, dana safen duk sun cinye ita da ƙawayen nata. Sai gab da magriba an kawo mata tuwon dare mai kawowar data kasance ƙanwar Abdul-rasheed ce Khadijah da bata koma Maiduguri ba ta kora yaran duka, sannan ta saka A'isha yin wankan dole ita kuma ta rufo gidan ta hau gyara tsakar gidan da sukama kaca-kaca. Ɗakin dai da yake ba zama sukai ba a ciki da haskensa, sai ƴan ganin ɗaki da ke shiga. Amma duk da haka shima sai da Khadijah ta sake sharo mata shi ta kunna turaren wuta, zata kunna fitila taga babu kalanzir. Dole ta ɗauki kalbar da aka aje dan sayen kalanzir ɗin ta fita samun yaro ya bada a suyo sukaci karo da Abdul-rasheed ya dawo. Koda ya tambayeta ina zata haka ta sanar masa sai shi ya amshi kwalbar yace ta koma shi bari ya sayo. Haka kuwa akayi, dan haka a gurguje Khadijah ta taya A'isha shiryawa. Sai gata ta fito tsaff kamar ba itace tai buɗu-buɗu ba. Ta bajeta da turare. Sai ga ango ya dawo. A tare suka masa sannu suka gaisheshi, Khadijah ta amshi kalanzir ɗin tana zubawa a fitila shiko yana satar kallon A'isha datai masa ƙyau a cikin jojin da Khadijah ta sakata sakawa. Yasan wannan kwalliya haka sai da taimakon Khadijan, dan ta fita wayo kuma ta girmeta. Khadijah na gama kunna musu fitilar tai musu sallama zata wuce. Amma ya tsaidata kan ta zauna har ya dawo massalaci dan kar A'isha taji tsoro. Haka dole ta zauna sukai salla tare, shi ko yay alwala da ruwan da A'ishan ta kawo masa a butar karfe ya fice massalacin...........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 14_
__________________
https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6
*_Kowace mace na matuƙar son taga ta gyara kitchen ɗinta kodan ta kalla itama taji daɗi 💃_*
*_Dunƙule kuɗin ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_*
*_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_*
*_To kwantar min da hankalinka ƙawata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sauƙi da rahusa._*
_Ta buɗe adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da daɗi, akan farashi mai sauƙi, kaya ƴan zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._💃💃
*_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 💃_*
20k monthly kayan 100k
10k monthly kayan 50k
*_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. 💃 Ga sauƙi abaka tamkar ƙyauta 💃💃😀_*
__________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________
.........Abdul-rasheed bai dawo ba sai bayan sallar isha'i. Yana shigowa Khadijah tai musu sallama ta wuce. Shi kuma ya zauna yana zolayar A'isha akan yau dami-dami tayi da baya nan?. Sai da ta ajiye masa abincin da aka kawo daga gidansu gabanshi sannan ta zauna tana bashi labari cike da farin cikin tabbacin yau ɗin ya mata daɗi. Shima sai yaji nashi farin cikin ya sake girma, da jin damuwar yanda zai tafi ya barta nan da kwanaki kaɗan dan zai koma Kano makaranta. Dole dai ya ture tunanin a ƙarshe ya lallaɓata sukaci abincin tare, daga nan suna hira yaga ta fara hamma yace taje ta kwanta. Shi kuma ya ɗakko kayan karatunsa ya fara nazari. Daga baya shima ya kwanta a nashi gado batare da yau ma yama A'isha komai ba.
Kwanakin da suka biyo baya sun cigaba da gudana ne cike da shaƙuwa a tsakanin Abdul-rasheed da A'isha. Domin kuwa cikin hikima irin ta masu ilimi yanata jan ra'ayinta da janta a jiki kamar aboki tana sake sakin jiki da shi. Gayyar yaranta kuwa na anguwa kullum tare da su take yini, a haka suka cika kwanaki goma Abdul-rasheed ya shirya komawa Kano dan kwanakin hutunsa sun ƙare. Gashi yana ƙarshen zango baya buƙatar wasa da karatunsa. A'isha taci kuka sosai har ya dinga jin kamar shima ya tayata, daga ƙarshe dai da ƙyar ya lallasheta ya tafi ya barta zukatansu cike da ɗaci.
A'isha ta koma sukuku da ita, kuma yanzu tana yini ne kawai a gidanta, amma da daddare can gidan su Abdul-rasheed take zuwa ta kwana. Da safe sai ta dawo gidanta sai kuma dare taje can. Tun tana tsangwamar kanta harta saki jiki saboda ƙannensa biyu da suke kusan sa'anni ƴammata. Ga Inna ba ruwanta, faɗanta kawai dai idan anyi ba daidai ba. Sosai A'isha take saka hannu suyi aikin gida tare da su Alawiyya, idan zasu fita ne dai Inna ke hanata binsu, ko in zasu tafi makarantar allo. Tun abin na sakata kuka harta fahimci hakan fa shine ƙa'ida da doka, tunda sauran matan yayunsa bataga suna fita ko'ina ba sai da dalili, dan haka sai ta saki jiki.
Tun A'isha na ƙirga kwanakin tafiyar Abdul-rasheed harta bari, kwanci tashi sai gashi da watanni har huɗu. A lokacin ne Baba ya aika masa wasiƙar tunatarwar yazo gida ko kwana biyu yayi, koya manta yana da iyali ne yanzu. Ya kamata ya dinga sara yana duban bakin gatari. Wasiƙa ta isa ga Abdul-rasheed. Kuma ya gamsu da tunatarwar Baba, sai dai baya son zuwa gida ne saboda kaucewa abinda zuciyarsa da gangar jikinsa ke raya masa akan A'isha. Yana son ya bata damar ƙara fahimtar kanta har gaɓar kammala karatunsa daya rage watanni biyu rak. Dan haka ya maida saƙon wasiƙar baba da amsar ban haƙuri data neman uzirin bashi damar kaiwa zuwa watannin da suka rage masa. Acewarsa karatunsu ya ɗauki zafi a yanzu kuma suna gab da fara jarabawa. Bayan an kawo wa baba amsar Abdul-rasheed dole ya haƙura ya bishi da addu'a, dan ya fahimci manufarshi kai tsaye. Haka kuwa aka ci gaba da rarrafawa har watanni biyun Abdul-rasheed na karatu suka cika. A lokacin ya shirya baro Kanon dabo zuwa Bauchin Yakubu gida. Sun sha kuka sun sha ruɗani shi da amini kuma ɗan uwa Nasiru da ogansa Yaya Zubairu. Daga ƙarshe dai dole suka sallamawa tunda mai rabawa ta raba, sai dai ance sabo turken wawa ne, a wannan gaɓar wannan turke ne kafe da zukatan su Abdul-rasheed. Yaje yayma Innar A'isha sallama, dan dama yana zuwa duk kwanakin mako da yake yi a anguwar kullum safiya gaisheta, hakan yasa abincinsa daga gidansu A'isha kullum kwano ukun nan babu fashi a kwanakin ƙarshen makon. Shiko baya gajiya da godiya da yin kuma cefane ya kai ma Inna. Ya kuma yi ƙoƙari ya lallaɓata ta yarda ya saka Bashir da Tasi'u a makarantar primary da ƴaƴan gidan su Nasiru ne kawai ke zuwa a layin. Inna ta haɗa tsaraba mai yawa sai ƴar sana'ar da amarya kanyi irinta ƙulle-ƙullen kayan lwaɗayi. Haka Nasiru yay masa rakkiya har tasha tare da su Bashir, basu dawo gida ba sai da motar su Abdul-rasheed ɗin ta ɗaga zuwa Bauchi....
_________________
BAUCHI
A bisa al'adar wannan zamanin zaman mace babu ƙunshi a ƙafa da hannu kamar wani zunubi ne. Kahama kitso ƙa'idane wani na tsufa kina sake wani akai-akai. Wannan wajibi ne ga mace mai aure a kowane yare na arewacin ƙasar. Dan haka koda Abdul-rasheed baya nan a duk sanda ya dace A'isha tayi ƙunshi da kitso Inna na sakata tsefe kai cikin matan yayun Abdul-rasheed wata tai mata kitso. Hakama tana yin ƙunshi tare da su dan sukan shirya yinsa ne a tare. Dan haka da wahala ka samu A'isha babu irin wannan tsaftar. Kamar dai yau a jiya Inna ta sakata yin sabon kitso, inda Magajiya ta zuba mata ƙanana masu ƙyau harda na gaba sak dai irin na barebari. Yau kuma suka shirya yin lalle a ƙafafunsu tun safe. Haka kuwa suka sakashi har yamma yana jikinsu. Sai la'asar suka kunce, A'isha batai niyyar zuwa gidanta ba yau sam dan haka ta ɓararraje suna hira da sauran facalolinta dan a gidan ɗaya daga cikinsu akai ƙunshin. A dai-dai kuma wannan lokaci Abdul-rasheed ya iso. A gidansu ya sauka kamar yanda ya saba, dan haka Inna ta tareshi tarba mai girma. Cike da hikima irin ta manya yana zaman gaisawa da Baba ta aika akai mata kiran babbar surukarta, a soro suka tsaya, bayan ta gaisheta ta shaida mata Abdul-rasheed ne ya dawo, maza su saka A'isha ta koma gida ta gyara jikinta. Sannan su taimaka mata sauri-sauri su tayata gyara gidan shima kafin ya iso. Ta amsa da ladabi ta fice. Tana zuwa ta gwargwaɗama sauran ƴan uwanta dan haka suka tasa A'isha a gaba. Tana son jin ba'asi babu wanda ya bayyana mata, sai dai sunce umarnin Inna ne hakan. Girman suruka koda matsayin kishiyar uwar miji take girma gareshi a wannan lokacin, dan haka A'isha bata sake tari ba ta bisu, dan yanda Innarta zatai mata magana ko bata umarni ta bi haka Inna itama zatayi tabi dole dan matsayin uwar miji take a garesu.
Dan danan suka taimaka mata da dukkan abinda ya dace, ruwan wankanta kanshi yasha turare kala-kala a cikinsa. Hakama ɗakin suna kammala gyara mata suka baɗesa da turaren wuta. Basu taɓa mata gadon miji ba suka barta ta gyara da kanta suka fice zuwa nasu gidajen lokacin anata kiraye-kirayen sallar magriba. Hakan yasa cike da mamaki A'isha ta fara kici-kicin gyaran baban gado dake matsayin na mijinta Abdul-rasheed, zuciyarta kuwa cike da wasi-wasi akan mike faruwa ne wai? Gashi kafin su tafi sai da sukai mata kashedi akan ta zauna a gida karta ce zata biyosu ta jira. Bata fahimci mi suke nufi ba sai da Abdul-rasheed yay sallama yara biye da shi da kaya niƙi-niƙi. Ita jitai ma kamar ta firgita, dan haka ta fito wuff da fitilar ƙwai a hannu domin haskawa, hakan ya bama Abdul-rasheed damar ganinta fes a cikin sirritaccen hasken mai cike da ƙayatar da mai kallo. Tayi ƙyau cikin atamfa mai tabarma sabon ɗinki ne daga cikin kayan lefenta da sai yau ta saka. Turus ta tsaya tana kallonsa itama kamar yanda yake kallonta, sai dai shi nashi kallon na shauƙi ne da kewa matsananciya. Itako na mamaki ne da ruɗanin bazatar tasa. Sun zubama juna ido harna fin minti ɗaya har yaran nan suka ajiye kayan suka fice abinsu suka barsu dan saurin komawa suci tsarabar daya bayar a basu a can wajen Inna. Sai da aka kabbara salla ne hankalin Abdul-rasheed ya dawo jikinsa. Numfashi ya furzar a hankali yana janye idanunsa daga cikin na A'isha da suka tara ƙwalla, cike da sanyin murya ya furta, “Bani buta kada na rasa salla gaba ɗaya”.
Sukuku ta koma ciki kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta ɗakko masa butarsa ta ƙarfe, tazo gabansa ta durƙusa ta miƙa masa. Amsa yay yana kallonta shi dai, dan harga ALLAH sai ya ga ta ƙara masa cika a ido da girma, shi yana can tunaninta na hanashi sukuni da isasshen barci, itako da alama ko'a jikinta daɗinta take ci, ƙaramin murmushi yayi kawai, kafin ya maida hankali yayi alwalar ya fice gudu-gudu sauri-sauri dan har anyi raka'ar farko ma. Sauƙin ma massalacin kusa ne da su gab.
Koda aka idar da magriba bai dawo ba, A'isha ma data idar da tata sallar tana zaune shiru, tama rasa miya kamata tayi ita kam, a haka yaro yayi sallama, ta amsa tana miƙewa hannunta riƙe da fitila. Tire ne da kwanika akan yaron, dan haka ta ajiye fitilar tana faɗin, “A'a Salihu kayan nan basu maka nauyi ba?”.
“A'a basuyi ba. Inna ce tace na kawo miki. Tace tana gaisheki sai da safe”.
“To na gode Salihu, amma kace mata ai yanzu ma zan taho gidan nima”.
Shi dai Salihu ya amsa da to ya fice abinsa. Itama dai ta ɗauki turen ta shige da shi ciki. Tuwo ne da miya sai fura damammiya a kwanon sha, ta tabbatar furan Baba ne aka ɗibo, dan Abdul-rasheed akwai son fura kamar Baban. Baki ta kuskure tai sallar isha'i dan an fara. Bayan ta idar ta miƙe, tabarma dake matsayin ta miji dake can saman babban gadon a maƙale ta taka ƙaramin gado zata zaro. Sai dai hannunta yaƙi ya kai, dan dole sai ta hau gadon zaifi mata daɗi amma bata son hawa ta saɓa a ganinta laifi ne. A yanda take ta amsa masa sallamar da yayi, ta cigaba da ɗiɗɗishenta na son ɗakko tabarmar. Inda take ya ƙaraso, ya tsaya a bayanta gab sosai, cike da kulawa da tausasawa ya ce, “Mizaki ɗauka haka Matar Abdul-rasheed?”.
Da yanayin shagwaɓa na wahalar da take sha ta ce, “Tabarman can mana, amma kamar ance ta gudu min na kasa na jawo”.
Hannayensa ya harɗe a ƙirji yana kallonta, ya ce, “To banda abin A'ishatu ai ta miki nisa ne, ga hanya mai sauƙi ki taka gado ki hau ki ɗakko kawai, tanan inda kike baƙya tsoron ma ki faɗo”.
“A'a zan iya a haka, kuma fa na faɗa maka tun ranar hawan gadon nan babu ƙyau”.
“Okay na manta haka ne fa, amma ai nima nace ki hau na yafe miki tun a waccan ranar ko. Kinga nidai sakko na tayaki ni”. Yay maganar yana kamata cak ya sauke ƙasa. Kafin ta ankara ya sakata a jikinsa ya rungume...........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 15_
__________________
_A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da