KIDA A RUWA BOOK 1 COMPLETE BY BILLYN ABDUL.txt

Author :  Billyn Abdul Category :  Aysha Cool Novels

Chapter   33 / 49

96K to 99K   out of 146.5K words

dube-duben ta ina harsasan ke fitowa, yayinda wasu sukai kansa akai ƙoƙarin riƙoshi da hanashi kaiwa ƙasa daya tafi zai zube.
     Kukan yaran nan da mata ne ya ƙara ƙarfi. Yayinda wasu a cikinsu suka miƙe da gudu zasu nufesa, amma sai sojojin suka hana hakan ta hanyar shan gabansu. Dai-dai nan wani taƙadari cikin yaran Dagger ya buɗe ƙaton dirom ɗin dake tsakar gidan ya fito yana dariya. A take sojoji suka ɗana bindugu, masu tunanin yin fata-fata da namasa har sun ɗana kunamin bindugun nasu ya turo Umman Nimrah gabansa bindiga a kanta daya ɗora mata. Sai lokacin su Zak-Shadow suka fahimci shine yayi harbin ta cikin drom ɗin kenan.
      Cikin bada umarni da kaushin harshe Major Imran ya furta, “Idan kana son tsira da sauran abinda ya rage maka na numfashi ka ajiye bindigarka”.
     Dariyar shaƙiyanci yayi, ga fuska ya shafe da baƙin abu ko gane kalar fatarsa balle kamaninsa ba'a iya yi. Da yanayin shaƙiyanci ya amsa ma Imran da, “An gaya maka goro na kasa a duniyar da har nake son ya ƙare na ƙirga riba da jari balle na damu da rayuwata. Kama bar wahalar da kanka, jinin wannan matar halattacene a wajena dan koba komai zanyi jihadi kashe mata mai tona asirin mijinta.”
     Ya faɗa yana ƙara danna kan bindigar a kan Umma dake hawaye tana kallon Zak-Shadow da zuciya ta kume ƙirjinsa, yanda kawai zai fasa kan tsinanne yake yi. Aiko tamkar wani abin siddabaru babu ma wanda ya kula da sanda ya ja kumar bindigar hannunsa ƴar mitsitsiya balle ɗagawar hannunsa sai saukar Bullet akan shegen, dan shi ɗin ƙwarraren maharbi ne kowa ya sani kuma. Kasancewar shi kuma ɗan iskan ya riga ya ɗana kunamar bindigar hannunsa a wuyan Umman Nimrah tun ɗazun harbin da akai masa ya tafi baya sai kawai yatsarsa ya motsa harsashin ya fita ya shige jikinta.
      Kusan tare Zak-Shadow da Imran suka zabura kanta. Sai dai kafin su dire ma ita ta dire a ƙasa rikica. Cikin matsanancin gigita Imran ya riƙota yana jijjigata da gwala kiran sunan Captain Musa. Murmurshi tayi mai ɗaci da ciwo hawaye na zubowa ta gefen idanunta dai-dai da malalowar jini a hannun Zak-Shadow da ya kai hannu shima zai riƙota Imran ya rigashi, sai ya kasa ƙarasawa da hannun kuma ya kasa janyewa. Da ƙyar ta iya sake yin wani murmushin tana juya idannunta da ƙyar akan Zak-Shadow...
A dai-dai nan shima munafukin nan mafi kusanci da Zak-Shadow ya katse videon daya ɗauka a wayarsa yana ɗan sakin munafukin murmurshi nasara guda biyu..........✍🏼
         
_Wato a duniyar nan ALLAH ka rabamu da maƙiyi mai fuska biyu. Kunga wanda zai nuna maka soyayya a gaban idonka a bayan idonka yafi kowa ɓataka da aibantaka ba ƙaramin azzaluminka bane. Wannan shegen na tsaneshi tun kan aje ko ina. Duk wanda yake tare damu a zahirin rayuwa da baɗini da wata manufa ya rabbi ka rusashi kafin shi ya ruguza mu😭😭🙏._



_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 47_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt
Link na grp


07077532253
https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm


https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture.
https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........Kai Zak-Shadow ya shiga girgizama Umman Nimrah idanunsa na wani irin jirkicewa. Ya motsa lips zaiyi magana ta girgiza masa kai itama..
“Karka damu, a yanzu nafi buƙatar mutuwa akan rayuwar da zata cigaba da tunamin wanene mijin aurena. Rayuwar da zata cigaba da tunamin rasa ƴan uwa biyar da mahaifana a dalilin mijin aurena. Na godema ALLAH da ban koma gareshi ba sai da nasan wanene mijin aurena. Ba zan aibanta shi ba, amma ni da shi da ƴarmu tilo zamu haɗu gaban mai rarrabe ayyuka da gaskiya. Ban samu cikar burin haihuwar ɗa namiji da nai alƙawarin baka ba, amma zan damƙa maka AMANAR ƴata ɗaya tilo da kaf duniya dakai kaɗai na yarda. Dan ALLAH ka raineta tamkar yanda nake fata rainonta, ka bata ilimin addini dana zamani. Ka raini zuciyarta da jarumta irin taka da tausayi da hidima ga al'umma. Ko da wasa kada ka sanar mata ainahin halayyar mahaifinta, dan Alhamdullah Babana ya bata rubutun mantawa da shi a zuciyarta na har abada, ina kuma roƙon yay mata tasirin da bazata taɓa tunashi ɗin ba, amma ko ya cigaba da rayuwa har lokacin girmanta, ina son ta tashi da sanin shi mataccene tun tana da ƙuruciya, ma'ana ka sanar da ita ita ɗin marainiya ce gaba ɗaya ta rasa uwa da uba tun tana ƙarama. Sannan bana son tai amfani da sunansa a matsayin uba. Dan ALLAH ka riƙe min AMANAR NAJA'ATU NIMRAH, na yarda da kai bazakaci amanar dukkan alfarmata ba. Roƙo na ƙarshe har abada kada ka bar waɗanan mutanen suyi sukuni da walwala a wannan duniyar. Ka addabesu, ka zame musu KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DO...... D......”
     Ta kasa ƙarasawa saboda yanda numfashinta ke fisga. Da ƙyar ta sake jawo shi da furta, “N...Nimr... Na ɗakin Inn...nta a cikin kwalla Inn...a ta ɓoyeta. Dan ita suka fara ne... Nema su ka..she. ƙin... Nu nata da mukai yasa suka kashe Innata da ƴan uwan....a. Sunyi alƙawarin kuma sai sun kashe ta, ina tsoron kada su cigaba da bibiyar rayuwarta dan ALLAH ka kula da it.....a AMANA”.
     Harshenta ya riƙe ta kasa cigaba da maganar. Ga Captain Musa ya ƙaraso da yaran soji zasu ɗauketa a saka cikin jirgi likita ya bata taimakon gaggawa. Amma ina wannan tafiyar mai girma ce, kuma ta har abada ce ga Umman Nimrah. Hannu Imran ya ɗaga musu da ƙyar, yayinda Zak-Shadow ya motsa lips ɗinsa da ƙyar ya shiga ambato mata kalmar shahada. Idanun kan sunyi wani irin masifar juyewa jajur. Cikin aminci UBANGIJI akan lips itama ta dinga maimaita duk abinda ya ambata ganinta na juyewa zuwa ga UBANGIJI, amma kuma har lokacin Zak-Shadow ɗin kawai take kallo. A haka idanun suka kafe alamar rai dai yayi halinsa.
       A mamakin kowa gefe Zak-Shadow ya maida kansa kawai. Kaudawar da kowa yafi zargin hawaye ne suka cika masa ido. Duk da kuwa kowa yasan kuka ba ɗabi'arsa bace. Musamman idan sukai dubi da kalolin tashin hankalin da suka gani a rayuwar aikin soja da tafi wannan har a ƙasashen ƙetare. Komai baice ba ya miƙe kawai, yayinda Imran yaja ɗankwalin kanta ta rufe mata fuska tare da shimfiɗeta a wajen.
       Koke-koken mata da yaran ya ƙaru sosai, matan sun kai su goma sha bakwai, dukansu kuma matan yayyen Umma ne da ƙanne, sai yaransu. Inda Zak-Shadow ya nufa Imran yabi da kallo, a ɗakin da suka sami nasarar fiddo tsohon nan ne, nan ne kuma Umma tai nuni da Nimrah na'a ciki. Captain Musa ne biye da shi. Basu fi mintuna uku da shiga ba kuwa suka fito Captain Musa ɗauke da ƙatuwar ƙwalla irin ta mutanen da mai hoton murtala. Da alama ɗakin da suka shigan da duhu dan harda fitila a hannunsa da suka haska. Murfin kwallar ya buɗe, sai ga Nimrah a ciki da alama ma a sune take. Riga ce doguwa a jikinta ƴar kanti, tayi face-face da jinin Inna dan sanda suka harbi Inna ɗin jinin ya fallatsawa Nimrah. Karon farko Zak-Shadow daya zubama cikin kwallar juyayyun idanunsa ya kauda kansa saboda isowar Imran wajen. Cikin girmamawa ya nuna matan da yaran dake wani irin kuka mai ban tausayi. “Sir! Suma za'a wuce da su ne?”.
        Kansa ya jinjina masa da bin jejin da kallo. Sai kuma ya duƙa tare da saka hannu cikin kwallar ya ɗakko Nimrah gaba ɗayanta, kafin ya furta, “Alamu sun nuna basu kaɗai bane. Dan yara mata ne sukafi yawa anan, mazan basu wuce shekaru uku-uku ba. Dole ne akwai wata tawagar yara mazan gidan ɓoye a cikin jejin nan mutanen nan sun ɗiba”.
      “Tabbas nima ina hasashen hakan Sir. Musamman idan mukai la'akari da furucin tsohon da yace adadin jikokinsa maza sunfi matan yawa”.
      Shiru yay yana nazarin maganar Imran ɗin. Yayinda idanunsa ke bin mata da yaran da kallo a tsanake. Sosai kukan da suke ke taɓa masa ƙasan zuciya. Amma da yake ƴan mazan mazane na gaske babu alamar hakan a saman fuskarsa. Sai ma ɗauke idanunsa yay cikin bada umarni yace a sakasu a mota. Sosai ihunsu da karuruwa ta ƙara ƙarfi. Ɗauke kansa yay tare da yima Imran magana ƙasa-ƙasa.
    Kai Imran ya jinjina masa, shi kuma ya wuce jikin motar da yazo a kai ya saka Nimrah a baya ya kwantar. Imran dake bin matan da kallo nuni yay da yara kusan goma ya ce a fito da su. Bayan ya raɗama Captain Musa magana a kunne shima. Cikin gamsuwa Captain Musa ya matsa yayma sauran nasu magana shima. Aifa take suka ɗaura bindigu akan yaran.
      Ihun iyayen ne ya sake ƙarfi, yayinda suke roƙon kar a kashe musu yara dan ALLAH. A kausashe Imran ya furta “Idan har bakwa buƙatar rasasu suma ku sanar mana ina sauran ƴaƴanku suke? Barazanar mi sukai muku suka kwashe su?!!”.
         Shiru sukai alamar matuƙar jin tsoron yin magana. Dan kuwa takunkumi akai musu ta ƙarƙashin ƙasa akan idan suka faɗa a bakin ransu su duka. Takaici da ɗacin daya mamaye maƙoshin Zak-Shadow ya daka musu tsawa. Yanda amon muryarsa mai matuƙar saka razani ta ratsa jejin ya saka su sake shiga razani. Tuni wata tsohuwa ta fara bayani jikinta na rawa. “Iya muke nan muka rage a gidan. Dan da yawan yaranmu maza suna birni neman kuɗi. Wasu kuma sun gudu bamu san inda suke ba”.
      Shi ɗin jami'in tsaro ne na soji mai matuƙar fiƙrah da kaifin basira. Yayi matuƙar sanin aikinsa ta yanda ko'a furucin baki yakan iya tantance na gaskiya da akasinsa. Dan haka kai tsaye ga gane ya kuma fahimci tsohuwar a tsorace take. Batare da ta sake cewa komai ba yay nuni da a saki yaran. Ai a guje suka shiga komawa wajen iyayensu wasu har suna tintsirawa a ƙasa suna tashi.
     Fitowa su Zak-Shadow sukai ƙofar gida, aka bar yaran sojoji kusan goma sha a ciki tare da su. Mizai faru, mintuna goma su Imran basu ƙulla da fitowa a gidan ba dan suna tattaunawa ne kawai sukaji tarwatsawar abu mai ƙarfi ta yanda su kansu sai da suka zabura gefe dukansu.
     Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ashe duk wannan abun dake faruwa bomb ne ɗaure a jikin ɗaya daga matan gidan, shiyyasa suka kasa faɗar inda sauran yaransu dasu Dagger suka ɗiba a jiyan suke. Gaba ɗaya kuma ya tarwatsa gidan da matan, da yaran, da sojojin da aka barsu da su su wajen ashirin. Wannan da shine tashin hankali ba'a sanya maka rana. Dan ba gidan ba hatta gidajen makwaftansu dake lafe a gida hankula a tashe tako wace kusurwa sun tarwatse. Sai dai kaga mutum yay sama an dawo da shi ƙasa a tarwatse, wasu ma sasan jikin duk a rarrabe.
      Wannan abu ya zafafi Zak-Shadow da fusatashi, dan kuwa tunda ya damƙa Nimrah a hannun Imran sai kawai yay sabuwar ɗammarar aiki da kansa ba umarni ba. Yaƙi da karan kansa ba jiran yara ba. Hankalin su Captain Musa ya tashi ganin yay wani hatsabibin tsalle ya shige motar yaƙi mai zazzage maƙiya da gurneti suka san ran ƴan maza ya ɓaci. Aiko da gasken ya ɓacin, kuma ranar yaran Dagger sun tabbatar ya ɓacin. Dan da karfin ikon ALLAH a maimakon Captains shi da kansa ya jagoranci runduna guda a cikin jejin suka dinga zaƙulo yaran daga. Wani mahaukacin kisa yake musu mai cike da fushi da baƙin ciki. Gaba ɗaya wannan yinin Zak-Shadow baiyi tsayuwar awa ɗaya ba da sunan hutu. Ga sojoji an sake ƙaro masa. Lungu da saƙo ya dinga zaƙulosu, dan kuwa bai gushe ba zai da ya gano sabon wajen haƙar ma'adanan daya sashi fahimtar dan su aka haddasa wannan sabon tashin hankalin na kwanakin nan. A take ya saka sojojinsa suka rufe wajen haba ɗaya...
Zakusha mamaki idan nace muku duk wannan abun da ake munafukin nan bai gaji da ɗaukar video a wayarsa ba, dan cikin aljihun riga ta gaba ta sakata cike da dabara, duk kuma inda Zak-Shadow ya sanya ƙafa yana biye, hasalima shine ɗauke da wayar sadarwa a baya da jakar harsasai yana ɗurama Zak-Shadow a bindiga...

<<<<<>>>>>>

       Kwanaki huɗu cir su Zak-Shadow na yaƙi a wannan yanki. Sun ci nasarar zubar da yaran su Dagger zubarwa mai muni, a ƙarshe kuma Zak-Shadow ya kama Dagger da hannunsa kamar yanda yay alƙawarin cikin awanni ɗari da yardar ALLAH. Sai ko UBANGIJIN ya yarje masa ya kuma tallafa masa kafin cikar a wannan ya cafke Dagger ɗin..
Ta ko ina ƙasa ta ɗauki labari akan kama Dagger da Zak-Shadow yayi da hannunsa. Da yanda ya jagoranci wannan yaƙi na tsawon kwanaki shida da kansa ba zaman bada umarni ba shi da Major Imran. Ta ko'ina gidajen tv dana rediyo zance su kawai kake ji. Dan kuwa sun nuna matuƙar jarumta da mazantaka na murƙushe ƙungiyar duhu da ƴan barandan data tara irinsu Dagger. Sai dai abinda Zak-Shadow da al'ummar ƙasa basu sani ba. Murƙushe su Dagger kashe maciji ne kawai batare da dare kansa ba. Saboda su Dagger sunan karnukan farauta kawai suke amsawa, manyan mafarutan na gefe suna kallon komai dake faruwa suma.

     Duk da hankulan shugabannin ƙungiyar duhu a tashe yake da kama Dagger ɗin da daƙile aikinsu na haƙar ma'adanai a karo na biyu da duk Zak-Shadow ya taka rawar gani wajen cin nasa a kansu a gefe ɗaya suna jin nasarar mallakar yaran da suka saka aka satar musu dake a hannunsu. Duk da kuwa Zak-Shadow da kansa ya ƙwaci yara kusan talatin a wata maɓoya dake cikin jejin bayan ya tarwatse yaran Dagger da suma ke a wajen. A yanzu yaran dake hannunsu basu wuce ashirin ba, sai na ƙarshe da suka ɗiba a gidan iyayen Umman Nimrah da suma ɗin dai Zak-Shadow ya kafa ya tsare akan nemansu da fatan dawo da su...........✍🏼
        

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_*
*_+227 98 94 12 81_*
*_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_*
*_+227 98 94 12 81_*


*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899*
*_Moniepoint MFB_*
*_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya: 👇_*
*_Telegram Number 09032345899_*


*_AREWABOOKS (Vvip)_*
*_Chapters & Audio_*
@BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276*
*_Access Bank_*
*_Bilkisa Ibrahim Musa_*


*_Kati MTN:- (500)_*
*_09032345899_*


*_Shaidar biya:-_*
*_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*


*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_*
*+234 805 568 7449*
*_Telegram Number👇_*
*+234 903 234 5899*





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*




*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*


*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._



_Chapter 48_

__________________

*🔥 RASH BEAUTY WORLD 🔥 duniyar kayan mata masu kyau da arha ,Ina masu son kaya na kyan gani, amma basu son tsada? To, *ki daina nema!* Rash Beauty World ta zo miki da komai:

*👗 Abaya masu kyau na zamani Egypt/dubai*
👜 *Bags masu kyau*
*👠 Takalma masu ɗaukar ido*
💍 *Jewelry masu ƙyalli kamar na sarauta*
🍽️ *Kayan Kitchen masu amfani da kyau*

*Koma da Naira kaɗan za ki yi shopping kamar sarauniya!* 👑💃

✅ Farashi mai sauƙi
✅ Kayamasu quality
✅ Fast delivery


*Shiga group dinmu yanzu kiga sabbin kaya ,Kayanmu masu kyau ne kuma farashi mai sauƙi!
Kar ki bari a baki labari don samun kayayyaki masu inganci*
👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/GzcU1TcAem21oJedkisrhj?mode=wwt

*RASH BEAUTY WORLD – Inda kyawu da araha suka haɗu!*
__________________


*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk


*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________

.........“Wai wannan tsinannen mutumin aljani ko mutum?”.
      Viper ya faɗa cikin yaren da suke amfani da shi, muryarsa na fita da ɗaci da zafin yanda yake jin tsabar tsanar Zak-Shadow.
          “Mutum ne Viper, sai dai uwarsa ta haifa mana bala'i da masifa ne kawai wlhy.....”
     “Ni ma ta gaskiyar Viper ban yarda mutum bane ba sam. Duba fa yanda yake wajiga burukanmu, a karo na biyu ya sake rushe nasarar mu. Taya zamuce mutum ne? Idan ko har mutum ne shi ɗin shugaban matsafa ne matsiyac.....” ya gagara ƙarasawa saboda hawayen da suka zubo masa sharr. Haka yake da baƙar zuciyar tsiya, shiyasa suke kiransa da suna Black Spider. Kukan nasa kuwa tamkar ya ƙara tunzurasu ne, musamman oga da har yanzu baice komai ba tun ɗazun. A karo na farko yayi gyaran murya, hakan yasa duk suka bashi hankalinsu, Black

33 / 49