Author : Aisha Abdull Category : New Hausa Novels 2026
: WATA RANA DA DADDARE.🖤
🖤 (horror story)☠️
Writing
by
Aishat Abdul-falalu.
(Rimin k'aura).
(Mmn Humaira.)
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una
Kullu napsin za'ikatul,maut
(Ya Allah ka jik'an Humaira da rahama,'Ya Allah kasa Chan tafiye mata Nan,'yata Humaira ina sanki Amma Wanda ya bani ya amsa,Ina sanki Wanda ya k'ago ki ya k'arb'a. Ubangiji ka k'ara danganar min da zuciya ya Allah Kai ka bani Kai ka k'arba. Ina barar addu'a ga duk Wanda ya karanta wannan Page d'in.)
WATA RANA DADDARE LABARINE DA AKA ƘAGOSHI CIKIN SIRRIN DARE, AKWAI ABUBUWAN AL-AJABI DA MAMAKI WANI IRIN BAHAGON SIRRI NE ME CIKE DA CHAKWALKWALI DA CHAKWAKIYA SAI AN KARANTA. DOGON LABARINE AKWA 1, 2, 3,4 NA FARKO ZAI ZAMA FREE NE SAURAN PAID.
Daga marubuciyar
ISHARA.
SO KO HAUKA.
SHAGALTATTUN DUNIYA.
WATA RANA DA DADDARE.
Page 1-2
A kullum tambayar da Muhijjinatu kewa mahaifinta, wanda take kira Abbu itace .
''Abbu me yasa muke rayuwa a daji, Ina mahaifiyata, Abbu ina danginmu, kai ma ina naka iyayen?
A duk lokacin da ta jefo mishi wa'innan tambayoyin zai gigice zai fita hayyacinsa
numfashin sa zai dinga fat, fat.
baƙin ciki zai tsaye ya tokare mishi ƙahon zuciya.
idonsa zai kaɗa yai jawur, wani lokacin har suma yake.
Ita kuma bata damuwa zata zauna ta tsare shi da ido bata ko ƙyaftawa amsa kurum take jira ya bata.
Yau da hantsi suna zaune ita dashi, kifi ne yake gasa musu irin manyan nan mai
ƙashi da tsoka.
Kammala gasa kifin keda wuya ya miƙo mata cikin wani ɗan ƙoƙo. karɓa tayi ta ajiye gefe tana jira ya ɗauko gishirin da yake ḅarbaɗawa.
Ba jima wa ya dawo da gishirin shima cikin ƙoƙon
zama yai ya ɗauki kifin da ke ajiye a gaban muhijjina cire ƙayar ya soma yi yana bata a baki tana ci cikin nishaɗi.
harta ƙoshi, saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya soma ci.
Bayan kowa ya ƙoshi kana Muhijjinatu ta zuba mishi ido bata ko ƙyaftawa.
''Abbu'' ta kirasa.
''Na'am ''ƴar lele.
dubansa tayi ta ƙura mishi ƙyawawan idanununta tace ''Abbu me yasa muke rayuwa daga ni sai kai, sannan me yasa bama cin hatsi, alhali kace mutane suna cin hatsi, shin mu mutane ne koko, sannan yaya kasan akwai labarin mutane a cikin gari?
Muhijjinatu ta fashe da matsanancin kuka bayan ta gama jerowa Abbunta wa'innan tambayoyi.
Miƙewa tayi tsaye tsam tare da zuwa gab dashi ta durƙusa ta riƙe hannayensa tsam, har a wannan lokacin idonta bai daina tsiyayar da ruwan hawaye ba.
''Abbu kullum sai na tambayeka amman baka bani amsa ka ƙi ka sanar min da ko muɗin su waye.. . . . . . ka bani amsata Abbu ta faɗa da ƙarfi.
Shiru ba amsa ''Abbu! "Abbu!! ta faɗa da ƙarfi tare da girgizashi.
Sam Abbu ya suma baya koda motsi, kuka ta kuma fashewa dashi da ƙarfi, da gudu ta ruga kogi da yake a tsakaninsu da kogin ba nisa ta ruga ta ɗibo ruwa ta soma shafa mishi.
Dogowar ajiyar zuciya yaja ya kirata ''Muhijjinatu!
shiru tayi bata amsa ba, wai a dole tayi fushi da Abbun nata Allah sarki ƙuruciya na aiki a nan.
Abbu dai ya washe tangarangan yana ƙoƙari ya kawar ma Muhijjinatu tunani ita kuma a ɓangarenta ɓacin rai ya linku sosai.
Miƙewa tayi tsam dagudu ta ruga ta nufi
tafkeken kogon, sai da taje gaf dashi ta dubi Abbu dake nesa da ita ya zuba mata ido, azatonsa ruwa zata sha.
bai ankara ba yaji kalaman Muhijjinatu wai'nda koda cikin barci bai taɓa zaton ƴar lelensa Muhijjinatu zata faɗa mishi wa'innan maganganu ba.
''Abbu'' nayi nayi dakai ka faɗa mini koni waccece ''Shin mu wanne halitta ne , me yasa muke rayuwa a DOKAR DAJI kaƙi ka sanar dani, kullum innayi tambaya sai ka faɗi ka suma, to zan faɗa kogon nan ruwa ya jani, in yaso sai ka huta da gani na. . . . . . . . . .
kafin ta ƙarasa jikinsa ya katse da ƙyarma bakinsa ya soma ƙyaf, ƙyaf.
''Karki aikata haka Muhijjinatu'' ki ceci rayuwata kece farinciki na dawo gareni koda zan mutu to zan sanar dake komi dawo gare ni Muhijjinata. . . . .
''Da gaske kake zaka bani sirrin komai?
gwaɗa kai yai alamar farin ciki.
da gudu ta dawo kusa dashi ta rungumoshi ta baya tace ''Ina jinka Abbuna''
juyo da hannayenta duka biyun yai ta gabanshi ya zaunar da ita ƙaunarta da soyayyar ɗa da mahaifi na daɗa lunkuwa a kowanne saƙo na jikinsa.
''Abbu bani amsar tambayata''
ta faɗa tana goge ƙwallah.
''Muhijjinatu share hawayenki.
Zan amsa miki tambayarki a yanzu.
Cikin mamaki ta ɗago ta dubeshi tace''Abbu da gaske?
karon farko a rayuwarsu da yai mata magana mai daɗi a duk lokacin da ta tsare shi da tambayoyinshi.
Yace nutsu Muhijjinatu ''Zan amsa miki kaɗan daga tambayoyin da kikai min.
Waro ido tayi farin ciki ya gaza ɓoyuwa.
''Da gaske kake Abbu?"
gwaɗa kai yai alamar ''Ehy. kafin ya ɗora da faɗar.
Idonsa ya kaɗa yai jawur sosai yace wa'inda zan amsa miki su nake da amsar su wa'inda ban amsa miki kuwa bani da amsarsu. . . . . . . . . .
Abbu ina jinka. . . . .
To be nex page.
Da sannu zaku ci chakwakiyar da ke ciki.
Ku ci gaba da kasancewa da Mmn Humaira a domin jin ci gaban labarin.
07049138863.
Call 07012329134.
[12/25, 11:21 AM] Rip my dauther: WATA RANA DADDARE.🖤
🖤 (horror story)☠️
Writing
by
Aishat Abdul-falalu.
(Rimin k'aura).
(Mmn Humaira)
from the writer of
Ishara.
So ko hauka.
Shagaltattun duniya.
Page 3-4.
Abbu yace ''Muhijjinatu tambayar farko da zan amsa miki ita ce.
"Labarin mutane da nake baki a mafarki nake gani. . . . .
''Abbu ta katseshi.
Dakatar da ita yai ta hanyar cewa''Ba sai kin kuma jefo ni da wata tambayar ba tsaya. Banaso na fara ƙarya iya abinda na sani shi zan sanar miki. .
Tambaya ta biyu dalilin da yasa muke rayuwa a dokar daji shine, tabbas mutane suna rayuwa a cikin gari, to amma mu me yasa muke zaune muna rayuwa a daji?
Kinga kenan amsar a bayyane take mu ba mutane bane, ina ji a jikina muɗin wani jinsi ne cikin halittu. . . .
Shiru Muhijjina tayi ta zubawa Abbu ido, da alama dai bata gamsu da amsar da ya bata ba, sai wani maƙoƙon baƙin ciki ya kuma tokare mata ƙahon zuciya ''Me ma yasa ta tsaya ɓata lokacin ta najin wa'innan bahagon amsar daga bakin mahaifinta?
shi kuma ta ɓangarensa yana cikin zullumin ƙar ta kuma jefo masa wata tambayar da ta shallake tunaninsa.
''Abbu idan ya kasance muɗin wasu nau'in halittun ne to ina 'yan uwanmmu?
kowacce halitta da take rayuwa a DOKAR DAJIN NAN tana da ƴan uwa to mu ina namu?
''Kai waccece ta haifeka?
"Sannan Nima Ina mahaifiyata?
tirƙash!
chakwakiya.
dafe kai yai wani irin tashin hankali marar misaltuwa ya ziyarci dukkanin wata gaɓa da sashe dake jikinsa.
''Me yasa a duk lokacin da Muhijjinatu ta tuskeshi da tambayar dangi yake shiga ruɗani?
wani mugun bala'i da musifa da tashin hankali ke riskarsa a lokacin.
Abu na farko zaiji tamkar an ɗauki dutse an guma mishi aka, abu na biyu bakinsa zai mutu murus!
"ABBU ta kirasa.
Firgigit ya juyo ya zuba mata ido kafin tace wani abu yai saurin katseta ta hanyar faɗar ''Muhijjinatu muddin kina a raye Akwai WATA RANA DADDARE da zan bayyana miki komai ina jin lamarin ya kasance sirri ne domin DADDAREN komai ya faru sau ɗaya tak WATA RANA DADDARE nakan tuna waye ni.
kema waccece ke ki jira lokacin yazo da zarar yazo to zan tashe ki komin NISAN DARE na fayyace miki SIRRIN.
Gaba ɗaya kan Muhijjina ya toshe kwalwar ta ta shiga chakwakiya, lissafinta duka ya kwance sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba wanda ya kuma cewa uffan, Muhijjina dai Abbu ya ida jefa ta cikin wata rikita rikitar ya ida chaƙuɗata ya ida damalmala mata lissafi.
Miƙewar Abbu ya katse shiru, dubanta yai yace''Muhijjinatu zan tafi daji na ƙutsa na nemo mana naman dabba domin na gaji da cin kifi hakanan.
Kema nasan ya gundure ki ko Muhijjinata?
Ya faɗa fuskarshi cike da annuri.
ba yabo ba fallasa ta dube shi tace''Abbu
banasa so kana yin nesa dani, wata rana
idan ka daɗe sai naga tamkar ba zaka dawo ba Abbu bana son rabuwa dakai ko kaɗan rashinka a tare dani yana rikita ni da jefani cikin matsananciyar damuwa.
Sannan bana san wani abu ta cutar min dakai daka bari mun ci gaba da cin kifin mu tinda shima abunci ne.
dafa ta yai ya soma bubbuga kafaɗarta yace''Muhijjinatu kece bugun numfashina idan na rasaki rayuwata bata da amfani kamar yadda kike jin niɗin rayuwarki ne nima haka nake ji a jikina.
Don haka kar ki damu zan dawo kinji.
Cimak ya ɗagata ya tafi da ita a saman gadon da suke kwana wanda shi ya sassaƙa shi da itace. Kwantar da ita yai
kana ya ɗauki baka da wuƙaƙensa ya rataya ya luluƙa cikin daji
''Sai na dawo Muhijjinatu.
To Abbu karka daɗe.
Murmushi yai ya juya ya tafi yana kallonta.
Ita kuma ta sarda kai ƙasa hawaye na tsiyaya.
Share don girman Allah.
07049138863.
Call 07012329134
ƙahon zuciya ''Me ma yasa ta tsaya ɓata lokacin ta najin wa'innan bahagon amsar daga bakin mahaifinta?
shi kuma ta ɓangarensa yana cikin zullumin ƙar ta kuma jefo masa wata tambayar da ta shallake tunaninsa.
''Abbu idan ya kasance muɗin wasu nau'in halittun ne to ina 'yan uwanmmu?
kowacce halitta da take rayuwa a DOKAR DAJIN NAN tana da ƴan uwa to mu ina namu?
''Kai waccece ta haifeka?
"Sannan Nima Ina mahaifiyata?
tirƙash!
chakwakiya.
dafe kai yai wani irin tashin hankali marar misaltuwa ya ziyarci dukkanin wata gaɓa da sashe dake jikinsa.
''Me yasa a duk lokacin da Muhijjinatu ta tuskeshi da tambayar dangi yake shiga ruɗani?
wani mugun bala'i da musifa da tashin hankali ke riskarsa a lokacin.
Abu na farko zaiji tamkar an ɗauki dutse an guma mishi aka, abu na biyu bakinsa zai mutu murus!
"ABBU ta kirasa.
Firgigit ya juyo ya zuba mata ido kafin tace wani abu yai saurin katseta ta hanyar faɗar ''Muhijjinatu muddin kina a raye Akwai WATA RANA DADDARE da zan bayyana miki komai ina jin lamarin ya kasance sirri ne domin DADDAREN komai ya faru sau ɗaya tak WATA RANA DADDARE nakan tuna waye ni.
kema waccece ke ki jira lokacin yazo da zarar yazo to zan tashe ki komin NISAN DARE na fayyace miki SIRRIN.
Gaba ɗaya kan Muhijjina ya toshe kwalwar ta ta shiga chakwakiya, lissafinta duka ya kwance sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba wanda ya kuma cewa uffan, Muhijjina dai Abbu ya ida jefa ta cikin wata rikita rikitar ya ida chaƙuɗata ya ida damalmala mata lissafi.
Miƙewar Abbu ya katse shiru, dubanta yai yace''Muhijjinatu zan tafi daji na ƙutsa na nemo mana naman dabba domin na gaji da cin kifi hakanan.
Kema nasan ya gundure ki ko Muhijjinata?
Ya faɗa fuskarshi cike da annuri.
ba yabo ba fallasa ta dube shi tace''Abbu
banasa so kana yin nesa dani, wata rana
idan ka daɗe sai naga tamkar ba zaka dawo ba Abbu bana son rabuwa dakai ko kaɗan rashinka a tare dani yana rikita ni da jefani cikin matsananciyar damuwa.
Sannan bana san wani abu ta cutar min dakai daka bari mun ci gaba da cin kifin mu tinda shima abunci ne.
dafa ta yai ya soma bubbuga kafaɗarta yace''Muhijjinatu kece bugun numfashina idan na rasaki rayuwata bata da amfani kamar yadda kike jin niɗin rayuwarki ne nima haka nake ji a jikina.
Don haka kar ki damu zan dawo kinji.
Cimak ya ɗagata ya tafi da ita a saman gadon da suke kwana wanda shi ya sassaƙa shi da itace. Kwantar da ita yai
kana ya ɗauki baka da wuƙaƙensa ya rataya ya luluƙa cikin daji
''Sai na dawo Muhijjinatu.
To Abbu karka daɗe.
Murmushi yai ya juya ya tafi yana kallonta.
Ita kuma ta sarda kai ƙasa hawaye na tsiyaya.
Share don girman Allah.
0704913886
page 5-6
Kwance take tana ta safa da marwa har rana ta take Abbu bai dawo ba.
Zuciyartavta cunkushi da tarin tambayoyi ta rasa me bata amsa cikin shekara uku da suka shuɗe ta fara sanin abubuwa na tambayar tushen asalinsu da jinsinsu.
Amma wanda ya kasance shine jigo kan lamarin ya kasa bata amsa akan komi
to ita yanzu yaya zatayi da rayuwarta?
Sud'in wa'inne kalar jinsun halittane?
"Me yasa suke rayuwa a DOKAR DAJI.?
dukkanin dabbobin dake rayuwa a dajin nan su da yawa ne, amma me yasa suke rayuwa su su kaɗai?
wannan bahaggon al-amari ya gaza misaltuwa tabbas abune me cike da chakwakiya waye zai warware mata shi
*** b***
Rana ta ƙwalle ƙwal, farkawar Muhijjinatu kenan daga barcin ranar da
ta daɗe tanayi wanda bata san sa'adda ya saceta ba.
Jikinta ya soma karkarwa
''Shin ina mahaifinta?
Tin safe Abbu har yanzu shiru''
gabanta ya dinga dukan tara tara zuciyarta ta dinga safa da marwa.
Duk wannan matsananciyar yunwar dake addabarta sam bata ji tunaninta kawai ina Abbunta yake.
Lallai ba abinci kaɗai ke magance yunwa ba tashin hankali ma yakan gusar da ita.
fargaba zullumi duka sun taru sun cukurkuɗewa baiwar Allah ita kaɗai.
Chan da taga ba sarki sai Allah ta dawo wajen bukkarsu ta zauna dirshan ta dinga dirzar kuka yi take ba ƙaƙƙauta wa zuciyarta tana tafarfasa. . .
Kuka take sosai bilhaƙƙi da gaskiya.
***
Tana tsaka da yin kukan ne taji an dafa mata kafaɗa ''Muhijjinatu ''Meke damunki?. . . Kafin ya rufe baki ta tashi cikin farin ciki ta maƙalƙaleshi sai kuma ta fashe da kuka tana share hawaye.
Shima dariyar yai yana ƙoƙarin ajiye ƙatuwar dabbar da ya kaso musu ko meye ?oho!
gefe ya ajiye kafaƙin dabbar kana ya kamo Muhijjinatu yai yace ''Ƴar lelen Abbu meke damunki, me yasa min ke kuka?
murmushi tayi kana tace''Abbu ba kaine ba ka daɗe sai, naga kamar ba zaka kuma dawowa ba.
Murmushi shima yai ya ɗora da faɗar ''Shikenan don na daɗe sai aka ce miki bazan dawo ba.
Sinne fuskarta tayi ƙasa alamar kunya.
Chan kuma tace''Abbu bana san kana nesa dani, bana san rasaka, bansan kowa ba, banda komai sai kai, kai kaɗai nake gani inji daɗi a rayuwata duk ranar da ya kasance na rasaka bansan yadda zanyi da rayuwata ba. . . . . . .
Katseta yai yace''Ƙwarai Muhijjinatu akullum abinda kemin yawo a rayuwata kenan idan kika rigani tafiya yaya zanyi? lokacin da muke rayuwa nida mahaifiyarki haka mutuwa tazo ta ɗauke min ita tabarni ƙwallin ƙwal, to sauƙin tabarmin sanyin idaniya ƙeɗinnnan ya nunata, to yanzu zullumina ranar da za'a wayi gari niko ke babu ɗaya wayyo Allah!
Wannan ita ce kaɗai damuwata bani da damuwa face wannan.. . . . . . Ya faɗa tare da goge hawaye masu zafi. . . . Muhijjinatu ta miƙe ta goge mishi ƙwallar da suka tarar masa a kwarin ido tace''Abbu nasan mutuwa tana da tausayi babu yadda za'ayi ta ɗauke ɗaya tsakanin ni ko kai tabar ɗaya duk tare zata ɗauke mu Abbu. . .
Kawar mata da damuwar yai ta hanyar cewa''Maza tashi ɗauko wuƙa a gyara naman kinji?
a zuciyarsa kuwa yana sane da damuwarsa yasan dole ranar zata zo ranar da mutuwa zata ɗauke shi koshi ko Muhijjinatu. . . . . Tunaninsa ya tsaya lokacinda ta miƙa masa wuƙar mai kaifin tsiya.
Kamo kafaƙin yai ta riƙe yana yankawa suna labari.
har yai dubarar da yai ta haɗa dutse da dutse wuta ta kama ya ɗora naman saman wutar.
07049138863.
Call 07012329134
🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_
page 7-8
Cikin ƙanƙanin lokaci naman ya gasu.
Muhijjinatu ta ɗauki tsoka ta cusa baki kana tace''Abbu cikin naman dawa meye ka kaso mana?
Murmushi yai batare da ya bata amsa ba yace ''Kedai ci ƴar lelena.
''Abbu da alama ba ƙaramin fafatawa kayi da dabbar nan ba ko?
a wannan karon ma bai bata amsa ba murmushi ya kuma yi sosai da alama dai murmushi al-adar Abbu ce.
bata damu da rashin bata amsar da bai ba, sai tace''Gaskiya Abbu kai jarumine wannan katotuwar abu haka.
A wannan karon fashewa yai da dariya yai tayi ba ƙaƙƙautawa.
''Muhijjinatu tambayarki tayi yawa.
***
**ABUJA STATE**
''Haba Daddy yanzu naji gari ba matse ba takura. Amma a kano talakawa sunyi yawa kullun gida baya rabo da ƴan maula, musamman dangin Mommy na ƙauyen nan ga ɗauɗa ga talauci, kokai yanzu ai ka huta Daddy.
Farida ce me wannan magana tanayi tana kallon mahaifinta Alh. Bashir wanda ya kwashe da dariya, dama halayensa sak sune Farida ta biyo.
Haj. Zainab dake jinsu ta zuba ma Farida ido jira kurun take su haɗa ido ta harareta amma Farida ta kasa haɗa ido da ita.
Alh. Bashir yace ''Ai Farida komi kike so a duniyar nan nima shi nake so babban burina shine inga kin zama babbar ƴar boko ki zama professioir.
Farida ta kwashe da dariya tace, Daddy dole nayi karatu kodon kai a duniya kai kaɗai ke sona Daddy.
suna cikin taɗin friend ɗin Farida suka shigo ba ko sallama,
kallo ɗaya zakayi musu ka tabbatar da su duka sun ƙoshi da rashin tarbiya.
Alh. Bashir ya zauna ya bararraje cikinsu yana dariya harda ƙyaƙyatawa.
Da zai tafi taransfer 1 miloin yai musu a account, bayan fitarsu wata daga ciki ke cewa.
''Amma Farry