Author : Aisha Abdull Category : New Hausa Novels 2026
yamma insha Allah.
🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_
page 26-27.
ABBU yace kinga wancen kogin?
Muhijjinatu ta gyaɗa kai tace
''Ehy''
yace to kullum chan nake zuwa ina kamo mana kifi tamkar dai yadda nake yi dake.
Wata rana kuwa nakan kutsa dawa na kamo mana naman daji.
haka dai muka ci gaba da rayuwa a baibai.Kwananmmu arbai'n Mal.Abdurrahman ya kawo mana ziyara.
A lokacin ina ɗan tuna yara na na tambayeshi ina Haidar da Mukasshifiyya da Azkafiyyah?
yaya labarin sarauta ta anan yake labarta min komai.
Mal.Abdurrahman yace ''Abdullahi bayan ɓacewarka Safwan ya haye akan karagarka.Sannan sun kwashi dukiyarka shida Bashir wacce har ɗiyan ɗiyansu bazaiyi talauci ba.
Abbdullahi nasan jin daɗin duniya baya gabanka.
Labari mafi muni shine ƴarka Azkafiyya tana wajen me gadi.Mal.Kabir,ita kuwa Mukasshifiyyah ta na gidan Safwan a matsayin ƙasƙantacciyar Baiwa.Haidar kuwa ni da kaina na kurumtar dashi baya magana a gabansu.Yanzu halin da ake ciki babban burin Safwan shine Haidar ya sami lafiya yazo ya buɗe wannan kogon saboda sun san dokar cewa duk duniya babu mai iya buɗe kogon face ƴaƴanka sun haɗu su duka nasan security ɗin shine ............MUKSSHIFIYYA AZKAFIYYAH HAIDAR.to sunan farkon ne babu wanda ya sani daga Allah sai kai sai kuma Haidar da ka faɗa mawa.Na dubi Mal.Abdurrahman nace wannan zance haka yake,babu wanda yasan sunan kuma sunan farko sunan ƴar da Binta zata haifa ne,sannan koda Haidar yana magana a dole sai yara na sun haɗu waje ɗaya kana kogon ya buɗe dukiya ce tunda daga zinari lu'lu'lu yakutu daimon goal da sauransu kuma kuma halak malak ɗina ce ba dukiyar talakawa bace kuma ba gado bace kasuwanci na ne ya tara min...sunan farko shine MUHIJJINATU.
Kaga kenan security ɗin shine Muhijjinatul,Mukasshifiyyah,Azkafiyyah,Haidar da sun haɗu suka faɗi kalmar zai buɗe nine kaɗai zanje in buɗe ya buɗu kuma sihirrin su Safwan bazai iya buɗe wajen ba.
Company ne me zaman kansa nasaka ya haɗa min ƙofa me wannan sirrin me kama da sihiri kuma ba sihiri bane ni Sarki Abdullahi ban taɓa tsafi ba.
Mal.Abdurrahm ya miƙa mishi wani abu cikin leda yace''wannan tsari ne dakai da iyalinka Insha Allah babu abinda zai sameka.
Kuma daga yau bazaka kuma ganina ba domin mahaifiyata tana gab da dawowa.Daga tafiyar da tayi,har na samin sararin ganawa dakai amma na tura yaro na Bilal saudiyyah neman ilimin addini a domin yazo ya taimakeka a ksrya sihirin dake tare dakai.
Abbu ya ce ''nagode sosai Mal.Saidai dakayi haƙuri domin ni nafiso na qarasa rayuwata anan dani da Safwan da Bashir kowa zai mutu babu wanda zai dawwama a wannan duniyar kowa zai mutu mu koma zuwa ga Allah...
Akwai ranar tsayuwa Mal.Abdurraham yace haka ne amma rabuwa da sihirin shima abu ne mai kyau...Sannan ka sani
DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI:
1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.
2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.
3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka.
4. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa.
5. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.
6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin).
7. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka...
wannan bayani da Mal.Abdurrahn yai min yasa jikina yai sanyi na fashe da kuka ganin bazai iya jure kuka na ba ya sa ya bavce shima kukan yake kashirɓan.
A kuma lokacin Binta ta soma yunƙurin naƙuda zata haifoki......
Cikin sauri na isa gareta. cikin hukuncin
ubangiji Binta bata sha wahala ba ta sulliɓo ƴarta kyakkyawa wato ke ɗinnan.
Kina zowa duniya nayi miki huɗuba da Suna Muhijjinatu.
Aljanin dake tsare yana jiran a haihu yaji sunan domin buɗe kogo a take yabar wajen domin jinkinsa duk ya sale saboda bazai iya tsayawa a wajen ba saboda tsarin da Mal.Abdurrahmn ya saka a wajen.
Dalilin da yasa bana zuwa wajen kabarin mahaifiyarki to achan madaddalar sheɗanun yake daga chan tsarin ya kare.
Ranar da na fara kai ziyara to aranar suka ɓatar min da tunanina suka mantar dani ƴaƴana da baro Mukashifiyya Azkafiyyah Haidar.
Ke hatta sallah da ibaduna azmi duk daga lokacin na manta komai hatta waye ni daga ke sai mamanki nake tunawa a rayuwata.
Daga lokacin na gaza gane shin ni mutum ne koko dabbar daji?
daga haka Abbu ya tsaya ya fashe da kuka me ɗaci.
A wannan karon tausayin mahaifinta ya kasheta,rungumshi tayi ta fashe da matsanancin kuka,su duka an rasa me rarrashin wani......
Abbu yaci gaba da ba Muhijjinatu labari.
Safwan shine ya sadaukar da jinin mahaifiyarki ga DODON TSAFI.
A domin cikar sa shekara daya akan karagar mulki.
Tin daga lokacin ta kwanta jiyyar ciwo baci basha jinyar da baci basha sai aman jini hanci da baki.
Kwatsamḷ wata rana na shiga daji nemo magani na dawo na tarar da ita ta fita hayyacinta sai amai take hanci da baki ga ƴar jinjira gefe sai aman jini take.
Da sauri na isa garena nace''Gimbiya Bintaḷ
magaganunta su suka daskarar dani na rasa yaya zanyi,alokacin na shiga wani mugun ruɗani.
Daƙyar maganar ke fita.
''Abdullahiḷ
Karon farko a rayuwarmu da naji ta ambaci sunana.
Duk yadda zan fasalta miki mummunan tashin hankalin da na shiga a wannan yanayin abin zai baki mamaki.
Maganar ta ta sa na sandare shin suma nayi,Ina a raye?
Allah ya barwa kansa sani.
''Ina so ka rike min Muhijjinatu amana kuma bana fatan Muhijjinatu ta ƙare rayuwarta a DOKAR DAJI,ina so komin daren daɗewa a sadata da yan'uwanta.
Na kuma rokarka banaso Muhijjinatu ta qare rayuwarta A MUGUN DAJIN NAN.
La'ilahaillahu muhammdurrasulli............Banji ƙarashen maganar ba na faɗi somamme a wajen.
ban farkaba saida garen Allah ya waye sannan na buɗe idona alokacin harta sandare ita kuwa ƴar taci kuka har tayi barcin dole.
Koda buɗe idona madarar jarirai na tarar a jiye gefe anba yar harda fita irin madarar nan me suna NAN basai na tambayaba aikin Mal.Abdurrahman ne.
Na sake fashewa da kukan rashin Binta wai nida Matata Gimbiya Binta sai ranar lahira(Allah sarki Abbu ka tuna min da Humairata shikenan sai ranar lahira😭😭😭😭)
Mal.Abdurrahmn shi ya aiko min da likkafani nayi mata wanka irin na musulunci na ɗauketa na ɗanyi nesa da wajen.
Haka naje bakin kabarin na zauna bayan na tona na zauna tun safe har rana ta take kuka nake ba mai rarrashina,danaga babu sarki sai Allah haka zalika Binta tatafi tafiyar da bazata dawo ba yasa na tashi na saka ta gidanta na gaskiya nayi kuka me cin rai mussammn sa'adda ɗibar ƙasa ina zubawa wayyo Allah na!!!😭😭😭
kukan Muhijjnatu ya farkar dani na miƙe na ɗauketa na juya da nufin barin wajen wannann baqar guguwar tataso.
Dakan ƙwarangwal.
Sarki Abdullah!
naji ankirani da wata baƙar murya me amo.
Arazane na juyo da matuqar mamaki zatona Mal.Abdurrahmn kaɗai yasan inda nake.
Hhhhhhhhhhh!!!!!!
wannan mugunyar dariyar ta katseni.
Sarki Abdullahi Safwan ya cuceka ya ƙwace maka sarauta Bashir ya kwashe dukiyar dake gidanka,sun ƙasƙantar da rayuwar ƴaƴanka.
Tun sa'arda Safwan ya haye karagar mulkinka har yau babu wanda ya tambayi kana ina,koda mutuwa kayi ai ɗanka zai gajeka to ɗannaka magajinka yana chan qasqaskance.
Hatta matarka su suka kasheta suka ƙasƙastar da rayuwarka A DOKAR DAJI.
Idan harka amince da dokokina zan tsaya maka zan ɗaukar maka fansa zaka dawo rayuwarka kamar da da iyalinka ƴaƴanka zasu dawo sarautarka zata dawo Gimbiya Binta ma zamu dawo maka da ita,kana da damar ɗaukar fansa badon komai ba sai don ƴar jinjinrannan da bata cutar da kowa ba.
Koko kafiso ta qare rayuwa A DAJI cikin DABBOBIN DAJI?
na ɗago na dubi shi meye sharaɗin?
hhhhhhhhhhhhhhh
ba wani abu me wahalarwa bane illah kayiwa DODON TSAFI SUJADA......
MATARKA Gimbiya Binta zata dawo sarautarka zata dawo.....
zaka fita daga ƙangin musifar nan ƴaƴanka da ka baro zaka ruske su........
''Ni bazan iya yiwa wata halitta sujada ba,haka zalika tun wanzuwar duniya ake mutuwa har yau babu wanda ya taɓa dawowa.....
Tin daga lokacin duk sa'arda naje wajen kabarin mamanki haka nake karo da sheɗanu nnan suna bijiro min da wannan buqatar,daga lokacin ban kuma zuwa ba haka naita rainonki har kawowa iyanzu da nake baki labarin nnan ƴaƴana sarauta duk ɗan uwana Safwan ya kwace da ƙarfin bokayen da yai imani dasu wannan shine ƙarshen labarin.........
(wayyo da dama makaranta na sun tausayawa abbu da dama sun tausaya wa rashin sallar da Abbu ya kwqshe bayayi ku tuna cewa duk zunubin y a rataya akan sarki safwan kuma kar ku manta ƙiƙiƙrarren labari ne me kuke ci na baka na zuba kunsan rayuwar Abbu bazata qare a haka ba akwai fa Allah.
Sannan labarin Mallah Abdurrahn da gaske akwaishi kuma labarinsa gaskiya ne .karku gaji ku jirabkaɗan.)
)
🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_
page 28-29.
**ANDAWO LABARI**
Muhijjinatu ta ɗago ido ta dubi mahaifinta,wanda ya dage iya san ransa yanata kuka haiƙan.
Muhijjinatu tace''Abbu ni idan ina kuka kaine me rarrashina,kai kuma kukan ka yana sakani kuka,shin kai kayi kuka ni kuka waye zai rarrashi wani?
Abbu ka daure kayi jarumta kayi haƙuri Abbu.
Share hawayen fuskarsa yai da gefen hannunsa yace.''Dole nayi kuka Muhijjinatu kuka ya zamar min dole,duk DAREN DA na tuna wannan labarin kwana nake kuka sosai kamar zan haɗiye raina da zarar gari ya waye zan manta kowa da komai da ya shafeni.̇..
Abbu ya kamo hannun Muhijjinatu ya haɗa da nashi yace''Muhijjinatu ina neman alfarma a wajenki.
''Tame fa Abbu? ta faɗa fuskarta ɗauke da mamaki.
''Duk abinda kake so Abbu koda raina ne zan mallaka maka.
Cikin tsananin tausayi yace.
''Gobe idan rana ta fito ina so zan ɗoraki a hanya ki shiga gari.
Da izinin ubangijin musulunci zaki haɗu da mutanen kirki,da zasu riƙeki tamkar ƴarda suka haifa,Muhijjnitu kina buƙatar abubuwa da dama a rayuwarki kina buƙatar ilimi kina buƙatar kisan kanki matsayin ki na ƴa mace.Daɗin daɗawa kina buƙatar abokin rayuwar da zaku rayu ku tara zuri'a ke idan da raboma zaki iya haɗuwa da ƴan'uwanki Mukasshifiyya Azkafiyya Haidar.
Muhijjinatu kina buƙatar farinciki kina buƙatar kiji daɗin duniya ni rayuwata ta kusa ƙarewa rayuwata dake ba dawwamammiya bace.dole wata rana za'a wayi gari babu ni a duniyarnan.
saboda kullum rana girma yana ɗaɗa ruskata ranarda aka wayi gari babu ni yaya zakiyi,Waye zai ci gaba da nemo miki abinda Zaki ci?
duk ranar da babu ni to daga ranar zski zama bebiya alhali da kunnenki zaki zama makauniya me duniya,duniya zata juye miki,sannan daga ranar kin gaman jin daɗin duniya,amma idan kika shiga gari kinga zaki haɗu da 'yan'uwanki mutane zaki ga abun mamaki iri-iri zaki ga jarafta wacce ma tafi taki amma yanzu ma ke kanki baki san ƙadddara me kyua ba ko akasinta.
Idan na barki a haka na cuceki ranar lahirabAllah zai tuhume ni.̧kuma kinga idan na ƙyaleki ban cika ma mahaifiyarki wasiyyarta ba.
ni ina ji a jikina keɗinnan zaki zama wani haske a rayuwa.
Amma idan rayuwarki ta ƙare a dokar daji na cutar dake muguwar cutarwa ma ranar lahira Allah (S.W.A.) zai tuhume ni bazan so hakan ya kasance ba......
Yanzu me kika zaɓa?
ya ƙarasa dogayen zantukansa da kafe ta da ido baya ko ƙyaftawa.
Duk dogayen zantukannan idanuwanta a ƙasa suke sarde bata ɗago ta dubeshi ba.
''Ke nake saurare Muhijjinatu!
firgigit ta ɗago ta zuba mishi ido.
Hawaye share,share a fuskarta abin gwanin tausayi.
Bakinta na kyarma tace.
''Bazan iya ba!
"Bazan iya ba!!!
A lissafinka kace shekaruna sha takwas a duniya,tin tashi na ban san kowa ba sai kai ban rayu da Uwa ba haka zalika dangina duk ka maye min gurbin su kawai rana ɗaya sai ace in tashi in barka in tafi ina?
Duniya????
Duniya meye jin dad'in duniyar Nan?
Nifa sam bansan jin daɗin duniya ba balle ya birgeni kuma koda zanji daɗi a duniyar nan to muddin ya kasance batare da kai ba nikam na yafe bana buƙatarsa Abbu na roke ka ka daina yimin maganar rabuwa dakai bana buƙatar hakan.Abbu ina tare dakai duk tsanani duk wuya baza mu rabu ba.
''Na yafe jin daɗin duniya,yanzun dai ka
tashi mu kwanta ina jin gari ya kusa haske ko.
Batare da yace uffan ba ita ta jawo bargon fatar dabbar da suke rufa ta lulluɓa musu.
Kafin kace me barci me daɗi yai awon gaba dasu.
Asuba ta gari Abbun Muhijjinatu.
***
Farida cikin tsananin ƙuna da ɗacin rai take duban Alh.Bashir ranta ya dugunguza tace.
''Daddy yanzu duk wata social media an tura hotunan matsiyatan nan amma shiru ba labari.
Alh.Bashir ya ƙuta yace.
''Ni kaina abun ya ɗaure min kai duk wata state dake nigeria na aika jami'an tsaro amma shiru kaman an aika bawa garinsu.
''To Daddy meye abin yi yanzu?....
🖤WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]_
Page 30-31-
ALH.Bashir yace tun tashina a duniya babu wanda ya taɓa wulaƙantani,shiyasa ma ban zauna waje ɗaya da ɗan'uwana Safwan ba saboda wulaƙancinsa babu wanda ya ragawa.
Farida ta cije leɓen ƙasa. zuciyarta na turiri tace''Kema abin baƙin ciki ƴar matsiyata ma.......Alh.Bashir yace''Waye ya faɗa miki ƴar matsiyata ce? Sai Kuma yai shiru....To Daddy ubanwa ya haifeta bnda tsohon me gadin nan.....Inji wa Azkafiyya ba ƴar matsiyaci bace,ubanta yafi ubanki komai banda zalunci ke da baki isa ki nuna Azkafiya da yatsa ba........Ya ishiki Haj.Alh.Bashier ya katse matarsa dake saukowa saman Upstar
juyawa tayi fuskarta ɗauke da murmushi mayalwaci.
Fareeda ta zubawa mahaifin nata ido tana jiran ƙarin bayani akan maganar Mommynta.
''Daddy da gaske ne maganar Mommy?
''Ke ƙyaleta kin dai santa da tausayin talaka.
Karki sake ki biyewa maganarta bare ta dà̀me ki.
Farida ta gyaɗa kai alamar gamsuwa.
***
Mariya Mal.Kabir Azkafiyya,tsintar kansu sukayi cikin wani ƙyauye na fulani.
Mariya tace ''Nashiga uku Mal.Tsafi ka koma..Taya ka iya yin layar ɓata Mallam kardai tsubbu kake?
Saboda Azkafiyya zaka kauce hanya?
karfa ka manta Alh.Bashir babu abinda zai iya yi mana saboda Azkafiyya tunda yasan bamu muka haifeta ba,to don me za'a hukunta mu da laifin da bamu muka yi ba haka zalika ba ƴarmu tayi ba?
Wani irin tari ya sarƙi Azkafiyya ta zaro ido warwaje tace''Mama dama baku kuka haife ni ba na shiga uku!
''Karki kuma kira na da Mama ni ba uwarki bace,Mal.Ba ubanki bane mu bamu taɓa haihu.........
Toshe mata baki Mal.Kabir yai..
''Haba Mariya duk aikin alkharin da kikai rana ɗaya ki toshe ladarki.....Kuma ni ban taɓa tsafi ba kuma bana shirka,nima tsintar kaina nayi nanɗin tamkar yadda kika tsinci kanki a nan.
Mariya tace A gaskiya Mal.Sai dai ka zaɓa ko ni ko Azkafiyya domin bazan iya tafiya da yarinyar da ban san asalinta ba da tushenta kaima ma fa cewa kayi tsintar ta kayi,ƙir,ƙiri muna gidan kuɗi cima me daɗi makwanci me daɗi amma ƙiri,ƙiri dalilin ta mun dawo ƙauyen da bamu san makomarmu ba.
Don haka muddin kana san ci gaba da zama dani sai dai ka zaɓa koni ko Azkafiyyah.
Kuma karka manta mahaifinka yace muddin ka rabu dani bai yafe maka ba,kuma ya rigada yabar duniya bare kaje ka nemi Affuwarsa.
Kuka me ƙarfi Azkafiyya ta fashe dashi tace.Mama Dama duk kallon da nike muku,Baba daman ba kaine ka haife ni ba?
wani mugun tausayinta ya kama Mallam Kabir yace,Aa Azkafiiya karki ce haka nine Babanki........
Yaushe ka haife tan sai dai idan ciki kayiwa wata ta haifo maka ita,ka dubi wannan tsaleliyar budurwar kamar balarabiya kana baƙi kace ƴarka ce.....
''Kai Mallam lokaci yayi da zaka faɗawa yarinya gaskiya.
''Ke ta kira sunan Azzkafiiyah.
Tsintarki mukayi,kuma tunda kin zame mana bala'i gara mu jefar da ƙwallon mangwaro....
Kuka sosai Azkfiyyah keyi gwanin tausayi idonta ya kaɗa yai jajir.
Mal.Kabir ya saukar da Ajiyyar zuciya yace.
''Ina neman Alfarma wajenki Mariya duk naji uzirinki.
Gatsina baki tayi tace''Tame fa?
''Kin ce sai mun rabu da Azkaffiyh ko?
''Ehy ƙwarai ince ai da hausa nayi magana bada wani yare ba.
''Ajiyar zuciyar takaici yai yace''To ina so mu samu mutsugunni,kafi nnnan ina so kafin na sallami Azkafiyyh zan sanar da ita ko ita ɗin waccece.
''Am don wannan ba damuwa muje a sami matsugunniN.
Suna tafiya Mariya nata bala'i ''Banda musifa da fitina yarinya kina banza a wofi ki saka hannu ki dallarawa me gidan da muke ci ƙarƙashinsa mari.
Ni abin tambaya ta ma waye ya jefo mu nan muda ke tsakiyar ɗaki.
Mal.Kabir ya girgiza kai yace amman ni da aka maran baki ji zafi ba ko?
Tinda bakisan daraja ta ta mijinki ba.
*****
**DOKAR DAJI**
**DA SAFE**
Wannan barci da su Muhijjinatu da Abbu keyi barci kaman na mutuwa har kusan ƙarfen biyun rana.
to ai ba'a bun mamaki bane in ku kayi duba da a DAREN jiya sun raba DARE suna hira.
Sai da rana ta iskosu dai dai wajen taga sannan Abbu ya farka yana tashin Muhijjinatu.
Tangaram ta miƙe daga barcin da shike idon nata ya ƙoshi da barci bai sha wahalar washewa ba.
Ki tashi ki wanke baki da fuska ki ɗauko sauran naman jiya ki cinye ni kuma zan shiga daji na samo mana wani naman.
Farin ciki ya washe a fuskarta babban burinta shine Abbunta yabar wajen taje wajen baƙin Al-jani ya ɗorata hanyar da zata yaƙi Sarki Safwan da Alh.Bashir.
WATA RANA DA DADDARE🖤*
_(horror story)☠️_
Written by
Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira)
The writer of:
*Ishara.*
*So ko hauka.*
*Shagaltattun duniya*
*And now WATA RANA DA DADDARE*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amala tagari]
page 32-33.
**DOKAR DAJI**
Haka ta zauna cikin tsantar farin cikin Don son ganin Abbu ya bar wajen domin ta tafi ta aiwatar da buƙatarta a wajen Baƙin al-jani.
''Washi! Abbu ya faɗa.
Cikin sauri tace.
''Abbu Lfy?
dafe kai yai.
''Muhijjinatu,ina jin matsanancin ciwon kai bazan iya gwagwarmaya da dabba,babba ba Amman bara