Author : Jamila Umar Tanko Category : Romantic Hausa Novels
darasi.
Wayarsa ce a kusa da ni lamba ce marar suna take ta kiransa, bai amsa ba bance komai ba. Daga qarshe sai lambar her excellency ta shigo nan ma ya kalle ni na kalle shi, sannan ya dauka. Na kasa kunne ban ji me take fada ba amma amsar da yake bata godiya yake ta yi cikin ladabi.
Ya na ajiye waya na daka tsalle na miqe, yau dai ina da abin fada. Na yi ta tijara, na yi zage-zage na zagi Jalilah da yayarta her excellency, nayi habaici. Da bai yi niyyar fita ba na ga ya dauki mukulli a fusace zai fita sai na tare qofa na ce babu inda zai je yau.
Ya fusge jikinsa na sake damqe shi, ganin hankali yara ya tashi sun zo sun jeru su na kallonmu sai ya fasa fita ya dawo ya zauna. Ya bata fuska yana huci daga gani ya fusata hakan ya sa nima na sassauta dan zaa iya yin batacciya.
Bugun qofar falonmu ake yi na je a fusace na bude sai ga Safiyya da Stephanie da alama a gigice suke. Tabbas na tabbatar yau zaa yi hayani ba zan so Usman ya ji wannan badaqala ba dan haka sai na tare qofa na ce mu su mu je waje, muka fita na ja qofa na rufo falon. Na ce aje gidan Safiya mijina na nan.
Sai kallon-kallo muke yi da su, mu na shiga falon sai stephanie ta fara magana cikin fushi wai me na je na cewa boka? Na ce duk abinda kika gani haka aka yi? Mu ka fara hayaniya, sai Safiya ta shiga tsakani ta ce mu zauna a yi magana a hankali.
Dakyar na yarda na zauna, Safya ta fara magana a nutse cikin lallashi, gaba daya a kidime take.
Tambayata ta yi da gaske na je garin su Boka? Na tabbatar mata na je. Ta ce an karya min asirin ne nawa ni kadai ko har da na su? Na tabbatar ma ta ba nawa kadai ba har da na su a cikin gadara da kuma rashin tsoro.
Safiya ta dauki salati ta dora hannu akai, yayin da Stephanie ma ta dora hannu akai tana ambaton abin bautarta. Na tambaye su kun gama in tafi?
Stephanie ta rusa kuka ta ce "daman ba kowa nake kaiwa wajen mutumin nan ba, Safiya saboda ke ne na kai ku gashi kin jawo mana wannan marar mutuncin muguwa ta je ta karya min sirrina, shiyasa tun jiya mijina ya tsane ni komai na yi sai ya dinga yi min tsawa har yana maganar shi zai kwashe kayansa ya koma wajen mahaifiyarsa. Tun daga nan na san akwai dalili.
Na tabe baki na ce "ko zamu je gaban mijin na ki a baje magana? Daman in ba mugunta ba ta yaya za ki raba shi da uwarsa da danginsa?"
Safiyayya ta ce " Fatiti me na yi miki da har za ki yi min haka? Ki karya na ki mana ke kadai."
Na harare ta na ce " kin fi kowa sanin abinda kika yi min ai. Lokacin da na shiga talauci ku dukkanku, wanne irin wulaqanci ne ba ku yi min ba? Wallahi in baki rabu da ni ba sai na bude maganar nan mijin kowa ya ji labari har mijina in ya so a sake mu gaba daya."
Daga nan suka tabbatar na kai qololuwar rashin mutunci suka yi saranda, na fice na bar su anan.
Ina fitowa motar Mufida na gani ban ganta ba amma naga wasu gardawa biyu da wasu manya akwatuna da alama ta dawo.
Sai na ji gabana ya yanke ya fadi ragagas abin mamaki motar Usman kuma bata nan.
KISHIN BALBAL
PAGE \* MERGEFORMAT 1
# $ % < = W? X? Y? [? \? ^? _? a? b? d? ????????y?e?X?H@<@<@<@<