Author : Jamila Umar Tanko Category : Romantic Hausa Novels
masa. Kin ce aikinki ne ko? Kin karanci nursing ne? Toh ai shikenan ba kwa buqatar ku je asibiti ki kular min da shi sosai please. Ina so ya sami sauqi da wuri don akwai aikin da zamu yi ranar Monday, daga safe har dare."
"Aiki kuma?" na zabura na maimaita yayin da zuciyata ta hango min wani aiki na daban ba na qirga kudi ba. Ina jin zuciyar Usman na dukan uku-uku saboda tabbas ya san Murjanatu tana qoqarin jawo masa jaraba.
Ta yi miqa ta yi hamma ta tsugunno daf da fuskar Usman ta dafa kafadarsa ta fada cikin wata sanyayyaiyar murya " calm down my manager soon za ka sami lafiya ka ji? Ina da account number ka zan turo maka kudin magani."
Ban san sanda na saka hannun na tunkude hannunta daga jikinsa ba.
Matar nan sai cewa ta yi "oh sorry na taba wajen ciwon ko?"
Sai ta sa hannu ta dafa kaina ta jinjina ta ce "sannu madam ki na qoqari sosai,ki samu ki sasanta shi da Mufidah su daina fushi, talaka ne yake fada da saurin fushi su kuwa dukkansu su na da rufin asiri."
Haushi ya kama ni na kawai da kaina gefe, da kyar na samu ta fice dan da ta qara wasu mintuna ina niyyar in tashi in tura ta waje in rufe qofar.
"Wannan masifa da me ta yi kama?" Na fada a bayyane yayin da na tashi na je na buga qofa da qarfi na rufe na saka mukulli na datse na zare mukullin na kai kicin na boye. Yau zan ga yadda wata shegiya zata zo dubiya ko sasanci kuma. A fusace nake na yi tsaki ya fi kala dari na dauko ruwan roba marar sanyi na zo na dungurawa Usman a gabansa na cillo masa ledar maganin, na ce ka sha ka wuce daki ka kwanta gara kwanta nima in huta. Haba wannan wanne bala'i ne haka? Ai gara matan kano gara ma mu koma kano da zama duk iskancin matansu babu masu yin tsirara da cakumar mazan mutane a gaban matansu.
Ya harare ni ya fusata ya ce " kada ki sake yin wata magana, anan ina baccina kika tashe ni kika uszura dole sai na tashi na fita wajen su Mufidah gata can tana yi mana sharri. Da matar nan yau ta mutu da haqqin ranta sai ya rataya akanki. Murjanatu kuwa sai dai ki mutu har abada ba zata iya canja halinta ba haka ta saba mu'amalarta da maza. Babu komai a ranta shiyasa bata gane wani baqin kishi da baqar maganar da kike gwaba mata ba. Babu abinda zata yi da mijinki na yi imanin ko daura mata ni aka yi a qafa zata kwance ta wurgar, ba irinmu take kulawa ba. Ita da take soyayya da 'yan kwallo na duniya fitattu ba 'yan super eagles ba ma. Toh zuciyarki zata buga a banza akan su, dan su ba ajinmu ba ne.
Haka mufidah da kin san ko ita wacece da kudin da ake biyanta akan case daya da take tsayawa masu sharia da baki bata lokacinki ki na kishi akan talaka irina ba ma.
Mata sun fita sun yi ilimi su na neman abinda zasu rufawa kansu asiri, ke kina nan ko kwalin difuloma ba ki da shi kina bata lokacinki akan talaka namiji mai kwadago."
Ban taba jin baqar maganar da tafi mari zafi ba daga bakin Usman sai a a yau.
Ya tashi yayi cilli da ledar maganin ya shige daki ya bar bi anan a tsaye. Na san fushi yayi ba zai sha maganin ba sai dai ciwon ya kashe shi. Na san yadda zan masa bari ya huce idan ya ga hawaye a idanuwana zai sauko ya shiga lallashina.
Na dubi kaina a mufubi na ga duk na jejjeme na rame na fita hayyacinta saboda matan nan 'yan duniya da suka yiwa mijina rufdugu. Me yasa sai Usman bayan ga Dr. Isa da Musa can, su ma ai kyawawa ne likitoci masu aji?
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun." na fada yayin da na dora hannu aka na sulale na zauna.
Hayaniyar bataliyata ne suka nufo ni da gudu wato yarana kakaf guda hudu sun tashi daga bacci, guda biyu daga cikinsu manyan jikinsu jagab sun jiqe da fitsari, sai zarni suke yi amma su na yi min musu cewa ruwan sama aka yi, ya shigo ta wundo ya jiqa musu kayan jikinsu, alhali ba lokacin damuna ba ne ma.
Haushi ya sake rufe ni, nan fa ni da su muka rankaya cikin dakinsu da gudu, na bi su da duka.
Wasa-wasa Murjanatu ta qauro gidan nan da zama dan har da wata qatuwar akwati na ga an shige da ita. Biyu daga cikin ma'aikatanta ta taho da su Rabecca mace mai shara da goge-goge sai namiji chef Jimoh shine mai girki wato kuku. Babban likitanta da ake ji da shi a jahar shi yake zuwa har gida ya duba Mufidah da Usman. Ko sun buga na qi bude qofa sai ta kira Usman a waya yana bacci haka zai taso ya bude musu. Kada ku zaci idan sun shigo qafafuwanta da bakinta ba za su zauna a waje daya ba, bata yin shiru ta dinga shiga ko ina a gidana tana yi min iya yi. Ta kushe wani abu, wani abu ta ce yayi kyau, wanda ya tsufa ma a shara take jefawa ta ce zata siya mana wani. Kuma idan ta fita zata siyo din ta kawo. Bata tsaya anan kadai ba duk abinda kuku ya dafa sai ta kawowa Usman, kada ku dauka kadan ne mai yawa a cikin farantai, haka zaa dinga shigowa da su ana jerawa. Kaza guda baa daddatse ta aka huda cikinta a zuba shinkafa ko dankali a ciki. Irin abincin da ko wuqa aka saka min a wuya ban san ta inda zan fara hadawa ba. Tabbas akwai matsala babba dan ada Usman ban da abincina bai san akwai irin wadannan kayan dadin ba, amma a yanzu ya gane ashe a baya jagwalgwalo yake ci.
Dr.Isa kuwa tunda su ka shigo sau daya shi da Safiya ya dandana abincin nan kullum sai ya zo, tare suke ci da Usman duk da ma dai Usman yana tsoro kadan yake cin na ta, nawa yake ci dan dole, sai ya turawa yara da Dr.Isa su cinye wancan.
Ko ban fada ba ya san a cikin kwanakin nan qiris nake jira ayi bala'i dan haka lallaba ni yake yi kamar kwai. Ya na sake yi min bayanin cewa duk wannan abun na dan lokaci ne in yi haquri, haka halin Murjanatu yake komai da zuciya daya take yi babu maganar wata soyayya a tsakaninsu.
Har ya yi min albishir da cewa matsalar da ke tsakanisa da Mufidah ta warware, Murjanatu ta sanar da Area manager cewar Mufidah ta yafe kuma zata zo ta bude account din. Ta tilastawa Mufidah sai da ta yi magana da manaja ta tabbatar masa cewar t yafe dan haka ya janye kai qarar Usman Lagos komai ya wuce.
Duk da Usman bai je ofis ba amma ya sami labarin komai daga wajen abokansa da kuma Murjanatu. Na ji dadi sosai Murjanatu ta kyauta ta ceto rayuka, sai dai wannan yafiya ta Mufidah bana fatan kuma in ji an zo an hade da sunan zumunci.
Amma kuma daga baya aminta ta juye ta koma tsakanin Dr.Isah da Murjanatu, ba ta cika kula Usman ba idan Dr.Isa na nan da shi ake hirar, daman kuma shi idonsa idon mace sai Allah. Dan haka Safiya ma ta shiga fargaba da matsananciyar damuwa.
Na buga tagumi na takure a quryar gado abin duniya ya dame ni. Duk wata baqar magana da habaici babu wanda ban gwabawa Murjanatu ba, amma sai ta nuna bata ma gane abinda nake nufi ba. Ita a rayuwarta ta rantse babu fushi, babu fada, balle gaba. Farin ciki kawai da haba-haba da jamaa take yi kullum. Ita dai a ci dadi, a saka kaya masu kyau, a hau mota mai kyau, a yi ta labari ana dariya da barkwanci.
Safiya ta shigo dakina a gigice hijabinta a baibai. Ina ganinta sai da gabana ya fadi. Na tambaye ta "lafiya ?"
Ta zauna a gefen gadona muryarta na karkarwa ta ce " Maman Ahmad! Haka za mu zuba ido a gidan nan mu zama 'yan kallo? Mijina kullum yana gidan nan da sunan dubiya tun zuwan Murjanatu ya kasa nutsuwa kullum nan yake zuwa ya ci abincinta, ya dawo min gida yana ta yi min santi har da cewa kada in dafa komai in zo mu hau sama mu ci. Ya na cewa ko kukun nan zai dauka ya koya min girki. Idan na lura wato yanzu ya raina nawa abincin kenan."
Zafafan hawaye ne suka yi ta zubawa daga idanuwanta, nima kwalla ta cika min ido raina ya sake baci yayin da na fara jin wannan yanayin na ko a mutu ko ayi rai, a yau dai zaa yi ta ta qare.
Na zabura na diro daga kan gado na kama qugu na ce "Safiya taso mu fita falon nan yau a yi ta ta qare kawai. Su zaba ko mu ko su Murjanatu.
Safiya ta jawo hannuna ta ce "zauna ki ji. Idan muka fita muka yi hayaniya da mazanmu daga su mazan har su Murjanatu zasu gasgata cewa rashin wayewa ne ke damun mu, zasu manna mana hauka ne kawai.
Kuma kina gani dai matar nan Murjanatu tana gane komai amma sai ta basar, babu irin harara da baqar maganar da ba ma gwaba mata amma ko a jikinta. Ta fi mu wayo da wayewa da ilimin zamantakewa. Kada ki ce bata ganewa, ko kuma baqar maganarmu bata yi mata ciwo wallahi ta sani tsabagen duniyanci ne. Bata fushi shiyasa take cin ribar komai. Amma duk mai saurin fushi baya cin riba a komai.
Gara ma mijinki Usman yana yi yana jin nauyi da tsoron ki. Ni fa? Doctor ba ya kawowa ma cewa laifi yake yi min sannan kuma ban isa in yi qorafi ba, sai ya rufe ni da fada.Ya nuna min da na iya dafa abinda yake ci anan me zai kai shi kwadayi. Kullum su na yi mana gorin ilimi, mun qi karatu, mun qi mu koma makaranta."
Na gyara zama cikin tashin hankali, tabbas Safiya ta fadi gaskiya, dukka na san da wannan.Na tambayi Safiya "menene abin yi? Dan ni kaina ya kulle gaba daya.
Safiya ta ce " In Murjanatu ta san wata bata san wata ba, na san yadda zamu yi mata mu ma. Mu biyo ta qarqashin qasa mu yi mata illar da ba zaa taba ganewa mu muka yi mata ba."
Abinda ya fara kawo min a rai shine ko 'yan daba take so mu yi haya su sassafe ta? In haka ne kuwa mun taro masifa saboda tana da conection a qasar nan sosai haka da security da suke gadinta, wata rana tare da su take yawo, wataran kuma a kyamara suke ganin shige da ficen ta dan na ji tana fadawa Usman haka, a motarta akwai CCT CAMERA haka a cikin jakarta duk sanda take so a kula da ita tana kunnawa.
Na bude baki ina kallon Safiya cike da zumudin son jin abinda za ta ce.
Safiya ta kawar da kai gefe cikin jimami ta ce " na yanke shawara kawai mu je mu sami batangaliyar nan qawata stephanie ta raka mu wajen abokan nan na qauyensu wanda ta ce in kisa kake so kafin ka dawo gida za ka tarar an mutu, idan farraqu ne a take zaa yi tawarwatsiya a watse , idan hauka ne a take wanda ake so zai shiga bola. Mu hada kudi kawai mu je ta kai mu, amma ta ce da tsada dai."
Sai a lokacin na tuno da wannan bayanin, tabbas an yi haka tare ta bamu labarin nan. Stephanie qawar Safiya ce tare su ka yi sakandire ta na yawan zuwa wajen Safiya don gidanta a bayan layinmu yake babu nisa.
Nan da nan na ji ina gumi ya rufe ni kuma na ji a jikina mun gama samun mafita. Na dafa kafadar safiya na ce amma fa tace da sharadi ya ce in har mutum yana da addua kada ma a kawo masa shi a jawo masa bala'i, kin san fa wannan dalilin ne yasa ba mu je ba, dan mazanmu masu yawan yin addu'oi ne.
Safiya ta harare ni ta ce "ke ina kika ga alamar addua a jikin Murjanatu da Mufidah? Da qarin gashin ko da shigar banza? Kin taba ganinsu da hijabi ko da qur'ani? Kawai dai dan sun kira kansu da musulmai ne amma ban ma yarda musulman ba ne."
Dadi ya kamani na yi tsalle na rungume Safiya na ce "ai ni na manta da wannan bokan ma kwata-kwata, da tuntuni da an raba Mufidah da gidan nan, har na tsaya zuciyata zata fashe mijina zai halaka a banza, dan ya kusa rasa rayuwarsa a dalilinta. Zo mu je gidan stephanie kawai yanzu, a saka ranar tafiya kome take yi gobe ta bari ta zo ta raka mu kawai."
Safiya ta ce "gobe asabar Dakta yana gida ba zai bar ni in fita ba, mu san dai qaryar da zamu shirya musu daga nan zuwa litinin.
Na ce "ni gani nake litinin ta yi min nisa gara ayi da wurwuri."
Safiya ta jawo wayarta ta kira stephanie an kuwa yi katari stephanie tana bakin get dinmu zata shigo. Ai sai farin ciki ya kama mu muka dungumo muka fito.
Usman da Isa ne a zaune a falo su na hira bayan an ci abincin Murjanatu an yi qet. Kan dining table dina yayi kaca-kaca da shawarma da kaji da pizza. Baa yi mana tayi ba, dan sun san ma ba zamu ci ba. Su ka daga ido su na kallonmu galala sun tabbatar sun yi laifi, kowaccenmu ta hada girar sama da qasa ta wuce. Ina jin Usman yana cewa Haidar ga mama can zata sauka qasa ka bi ta, ka ishe mu da barna. Da gangan na bugo qofar falon da qarfi na rufo su dan kada ma ya ce zai hada ni da daukar yaro.
Qofar gidan Mufidah a bude, kusan sati guda da faruwar abin nan, ban ganta ba sai a yau dan kullum tana can ciki. A falo mu ka ganta a zaune sanye take da wandon Jeans iya guiwarta da riga marar hannu, gashin kanta ya tuje ya baje babu ko tajewa. Na hango bandeji a qaurinta, da alama ta fi Usman daddaujewa, alama ta nuna tana jin jiki, dan sai cije baki take fuska ta yi mata luhu-luhu.
Babu abinda muka hasko a zuciyarmu sai yadda idan mazanmu suka fito suka ga narkekiyar mace a haka, ta fi mu komai, gaskiya akwai matsala.
Ta hararemu muka harare ta sai ta cewa Rabecce mai aiki ta rufo mata qofa. Daman Rabecca ta hado mata shayi tana miqa mata. Rabecca ta zo ta datse qofar.
Mu na saukowa mu na tattauna wannan abin takaicin. Amma cikin zuciyarmu cike da farin ciki dan mun ji a jikinmu mun gama samun mafita.
A kan matattakala muka ci karo da Murjanatu tana hawowa. Wani tsadaddan leshi ne a jikinta amma duk an yanke an zubar da rabi, an yi dinkin 'yan duniya matsatsiyar doguwar riga (gown) wacce aka yi ta kamar 'yar kanti. Maganar gaskiya in ka na so ka ga sabon abu toh ka nemi Murjanatu, dan qanqararriyar 'yar gayu ce. Ta na ta amsa waya, ban da dallar miliyan babu abinda muke ganewa a cikin turancin. Duk da tana waya amma sai da ta yi mana murmushi ta daga mana hannu. Babu wanda ya mayar mata a cikinmu, ta zo ta wuce ta tsakiyarmu. Qamshin turarenta ne ya daki hancinmu, ita ma na ta qamshin turaren daban ne ba irin na Mufidah ba. Irin qamshin da ko ka bar wajen sai wajen ya wuni yana yi . Balle ace sun zauna ko sun rungumi abu. Sai mu ka ji mun raina kanmu, mu ka kira kanmu da muna mata ba mata ba, tabbas wadannan su ne mata. Amma kuma zasu raina kansu nan gaba kadan, za su gane su ne basu da wayo.
Stephanie mu ka