Author : Autar Manya Category : Romantic Hausa Novels
zata ji labarin shi koda kaɗan ne domin daga gani akwai abubuwan dake tare dashi.
Raɓewa tayi ajikin ƙofar falon shi sabida jin sautin maganganun dake fita daga cikin falon nashi Allah ya gani ba laɓe tayi ba dalilin tsayawar tata gudu take in ta Koma da kayan shayin Wani zai iya ganinta acikin ahalin gidan shiyasa ta zaɓi ta dakata har baƙin nashi su Fito sai ta shiga takai masa.
"Anwar karfa kai wa rayuwarka Illah shekaran Jiya Likita ya gama faɗa akan ciwon ka yau gashi ka Kuma kwanciya Ni bana son wannan yawan damuwar taka tunda ba cikakkiyar lafiya gare kaba"
Muryar mace ke tashi acikin falon.
Shi kam ba'a jin abin da yake faɗa sabida ƙaramin sauti da yake amfani dashi maganganu suke waɗanda suka danganci ban haƙuri da Nasiha da matar ke masa kafin ta gama ta fito Ɗauke Numfashi Saadatu tayi Lokacin da matar ta gama maganar ta fito daga falon, Wuff saadatu ta faɗa cikin falon tana raba ido yana kwance a saman Sopa jikinsa sanye da Singlet da Dogon wando yana ganinta yaɗan sauya fuska yay kamar bai ji daɗi a yadda ta same shiba.
Ƙasa tayi da kanta bayan tai sallama ya amsa mata a taƙaice.
"Yaya jikin naka dan Allah kayi haƙuri"
Ta faɗa kanta ƙasa tana ajiye Tray ɗin hannunta.
"Ke ni wannan ban haƙurin naki ya isa tashi kije"
Jitai gwiwarta ta saki a ranta take ayyana Saadatu kin zaƙe da yawa tunda bai neme kiba meye zaki kawo kanki Gurin wanda yafi ƙarfin ki.
Tashi tayi zata tafi.
"Zoki ɗauke wannan abun"
Ya nuna tray ɗin da hannun shi mai lafiyar.
Hawaye ne ya wanke mata fuska ta sunkuya zata ɗauka yabi fuskarta da kallo.
"Kukan na menene Tell me?"
Bata yi magana ba domin in da amsar da zata biyo bakinta kuka ne mai ƙarfi ta yaya ta Ƙona shi ya kwanta Ciwo ta kawo masa shayi dan ta duba shi ya gwaleta Ji take kamar ita ce silar Komai na ciwon shi shiyasa taji hankalinta ya gaza kwanciya.
"Mami Come here"
Ya faɗa yana kallonta.
Ta fahimci me yake nufi sabida haka zuwa tayi gabanshi ta zauna.
A hankali ya kalleta.
"Ke sunan mahaifiyata gareki, Aikin me kika zo gidannan sannan ke a ina kike?"
Da nutsuwa ta ɗago taɗan kalle shi.
"Ina layin ɗorawa nazo ne ina wa Wadda ta haihu anan gidan aiki ne..........
Taɗan bashi labarin dalilin zuwanta gidan nasu.
"Ina baki kuɗin maganin mama zaki koma gida ina nufin ki koma ku cigaba da Jinyar mahaifiyarku sabida duk wata ƴa mace Mutuncin ta gidan su ko gidan Mijinta yanzu haka kowa da irin kallon da zai Miki"
Tunda ya soma mata maganar taji girman shi yana ƙara ƙaruwa cikin idanunta shine Mutum Na farko a duniya daya soma taimakon ta a maza batare daya nemi komai daga wajanta ba.
Hawaye ya wanke mata fuska.
"Nagode Allah ya jiƙan mahaifa in sun mutu in suna raye Allah yaja kwana, amman na riga na amshi Kudin wannan watan"
Ya tsareta da girman idanunshi.
"Miye kikai da kuɗin?"
Ya faɗa cikin hausarshi wadda take Nuna Ainihin harshen shi wato na katsinanci.
"Dama zan kai wa Ummi ne sabida kula da Hajiya"
Shuru yayi Kamar baze yi mata magana ba can yace mata.
"I understand you, zaki iya tafiya Ki shirya kayan ki"
Daga haka ya Mayar da kanshi ya kwantar.
Tashi tayi Jikinta duk yayi sanyi harta kai Ƙofar fita ta kuma dawowa.
"Me zan ce wa Hajiya?"
Shuru yayi mata sai da ta kuma nanatawa.
Sannan yace mata.
"Kice mata Anwar yace zai mayar dake Gidan ku, Ki basu kuɗin da suka baki"
Jimm tayi tare da sakin Ajiyar zuciya kafin ta fita daga Falon nashi.
Daran ranar Saadatu bata rintsa ba, Ta rasa ina maganganun sa suka dosa amman ta bawa zuciyar ta amsa da Taimakonta yake so yayi.
Washe gari Sabgarta ta shiga ganin bai mata magana ba.
Shima a nasa ɓarin Ayyuka ne suka taru akan shi a office, Ga Binciken daya tsaurara akan Fitar da kuɗin da akai bawai Biyan Kuɗin ne yayi Mishi ciwo ba A,a zafin Zargin da Abba ke masa shine ya ƙara tunzura shi akan dole ma sai ya Gano yaya akai Kuɗin suka fita wannan dalilin yasa a wannan rana ya dakatar da Alhaji Jamilu ya kuma dakatar da Chief Information Officer lamarin daya Girgiza zuƙatan mutane Biyun wato Alhaji jamilu yayan Mama matar Mahaifin Anwar da Amininshi wanda suke haɗa ka wajan cuta da handama acikin Kamfanin.
Anwar bai shigo gidan ba sai yamma Lis part Ɗin Innah ya wuce yaci abinci sannan ya fito zuwa nashi part Ɗin Lokacin daya shiga ana kiran sallar magariba alwala yayi ya fita masallaci sai da yayi sallah sannan ya Watsa ruwa Cikin shiga Black Jeans da white shirt ya fito yana ta baza ƙamshin turaren shi na Tom ford Oud wood, Babban falon su ya Nufa Baba kande tana ta hidimar haɗa Girki da sauri ta russuna tana gaishe dashi ya dakatar da ita.
Dan baya so babba kamarta tana rissuna mai.
"Baba kiramin wannan yarinyar mana"
Bata fahimta ba.
Yanayin yadda take yine ya nuna masa hakan.
"Wadda aka kawo sabuwar nan"
Da sauri baba kande ta juya ta shiga ɓarin su ta kirawo saadatu data ke zaune ta idar da sallah dan Lokacin ta sami tsarki sabida dama bata wani Jimawa.
Gaban sa'adah ya faɗi sanda Baba kande ke sanar da ita Alhaji ƙarami na kiranta.
Tashi tayi ta biyo bayan Baba kande zuwa falon.
Baba kande ta wuce Kitchen ita kuma ta Nufi inda yake tsaye ya harɗe hannayen shi a saman Ƙirjin shi.......
*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*
*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*
*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*
_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*
*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*
*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO
*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*18*
Tunda ta doso wajen shi yake binta da kallo ta ƙasan idanunshi wanda ba lallai itan ta gane irin kallon ƙurullar da yake yi mata ba.
A hankali ta ƙaraso gabanshi ta tsaya daga nesa dashi ta sunkuyar da kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
"Wuce muje"
Ya faɗa mata a taƙaice.
Ɗago idanunta tayi tare da yin raurau da su kamar zatai kuka! kafin tai magana cikin sakarci kaɗan tace masa.
"Nifa ban gama shirya wa ba"
Tsira mata kaifin idanunshi yayi wanda yasa ta yi saurin Kauda kanta tana jin wata irin faɗuwar gaba.
Cikin ƙaramin sauti ya furta.
"Muje ko"
Ya faɗa lokacin daya juya domin fita daga falon bata da wani zaɓi face na bin bayan shi ko Kuɗin bata mayar wa da Husna ba haka zalika bata ɗauki kayanta ba, Bare tai wa Baba kande sallama.
Sai da ta ƙara da Gudu sannan ta cimmasa sabida saurine dashi ba ɗan kaɗan ba a bakin wata farar Mota ta tarar dashi sai da ta ƙaraso sannan ya shiga ɓangaren driver ya sa hannu ya buɗe mata kusa dashi sannu a hankali ta shiga cikin Motar ta zauna.
Ya kunna ya tashi Motar suka bar wajan a bakin gate ya danna Horn masu gadi suka Buɗe masa suna ɗaga mai hannu ya fita daga harabar Gidan gaba ɗaya saman kwalta ya cilla hancin Motar tashi.
Tafiya ce suke kamar ta Kurame yana sane daya zo layin yaɗan wuce da sauri tace.
"Ga layin namu fa"
Yaɗan kalleta yana cewa.
"Nina ɗauka Kurma ce ay"
Dariya ta saki kaɗan tana sa hannunta tana rufe fuskarta.
Cikin layin nasu ya shiga yana tafiya a hankali har yakai daidai inda ta Nuna masa ya kashe Motar ya ɗan kalleta.
"Ki shiga gida to sai da safe"
Magana take son yi masa amman kwarjinin shi ya hana ta furta abin da take son gaya masan.
"Ko na rakaki?"
Ya faɗa yana ɗage girar shi guda ɗaya.
Sunkuyar da kanta tayi tare da kama Murfin Motar zata buɗe ta fita.
Da sauri ya kamo hannunta.
Itama da sauri ta ɓamɓare hannun nata daga Cikin nashi.
"Ashhh kin fama min Ƙunata"
Ya faɗa mata a hankali.
Da ɗan ɓacin rai ta juyo gareshi zata yi masa magana, Yay saurin hanata furta maganar ta hanyar Rungumeta ta baya yana zuba mata dukkan Nauyin shi Kokawa suka shiga yi acikin Motar hankalin Saadatu yayi Mugun tashi.
Sai da tayi da gaske sannan ta iya Rabashi da Jikinta sai faman Nishin azaba take Ranta a tsananin ɓace ta kalle shi da Manyan idanunta waɗanda suka Sauya launin su zuwa jajir.
"Dama haka halin ka yake? mai yasa kayi min haka daman dan ka lalata min rayuwata ka rabo ni da Gidan dana ke sa ran samun halak ɗina?"
Sai hawaye! shaaa suka soma ambaliya a saman fuskarta.
Dafe kanshi yayi yana Ƙoƙarin saita Nutsuwar shi a hankali ya zira Hannu Cikin Aljihunshi ya ciro kuɗi masu yawa wanda bai ma san adadin suba ya kama hannunta ya damƙa mata gaba ɗaya ya kasa magana.
Watso mai da Kuɗin tayi Jikinsa.
"Allah ya kiyaye na amshi Kuɗin ka ko zan rasa komai bazan iya amsar Kuɗin kaba Kuma sai Allah ya saka Min abin da kayi Mini"
Daga haka ta fita daga cikin Motar tana wani irin Kuka mai tsuma rai da zuciya.
A guje ta faɗa Gidan ko sallama bata iya yiba
Da kuka ta shiga ɗakin su Ummi na sallah Ummi tana idar da sallar ko addu'a bata tsaya yiba ta Juyo tana tambayar sa'adatu.
"Lafiya kika shigo da kuka! menene mai ya faru?"
Ummi ta faɗi maganar a firgice ganin yadda saadatu take Gursheƙen Kuka!
Baffa yana bakin dakalin Ƙofar Gida yana kallon sanda motar ta sauke saadatu har zuwa sanda saadatu ta fito daga cikin Motar Murje idanunshi yayi yana kuma Buɗesu tabbas saadatu ce ta fito daga Motar Jikin Baffa har tsuma yake wajan takewa saadatu baya zuwa Cikin Gidan daga tsakar Gida ya soma ƙwala mata kira.
"Saadatu! saadatu!! fito nan Munafukar Allah, yau Allah ya tona miki asiri dama na jima ina zargin ki yau dai Abin Ɓoye ya fito Fili"
Saadatu daga cikin ɗaki ta Matse Ummi jikinta sai rawa yake tana tsiyayar hawaye!
Ummi ta ɗago tana kallon Yadda saadatu take kuka! adaidai nan Baffa ya ƙaraso gaban Ƙofar ɗakin yana Bugawa da ƙarfi yana kuma nanata Kiran sunan saadatu.
"Idan baki Fito waje ba zan tona Miki asiri a cikin unguwa kowa yaji"
Da sauri Ummi ta kama hannun saadatu suka fito tsakar Gidan.
Suka zube a gaban Baffa.
"Dama ni na jima ina zarginku to yau na ga komai da idanuna saadatu ashe ba wanke wanke da shara kika jeba ashe yawon iskanci kika je uban waye ya sauke ki a mota?"
Ya faɗa cikin ƙaraji.
Wanda faɗin maganar tashi tayi daidai da sanda Abbati ya shigo gidan Umma dasu Jamila kuma suka fito daga cikin ɗaki.
Yowa kanta baffa yayi kamar zai daketa yana kuma tambayarta.
Toshe bakinta tayi tana wani irin kuka!
"Ba magana nake Miki ba uban waye ya sauke ki a mota? wato mu zaku mai da marasa tunani Kin tafi wajan namiji ya kwana dake, Shine zaki fake da tafiya wajan aiki"
Kuka saadah take sosai a wannan karon.
"Wallahi Allah Baffa Babu wani Iskanci dana je ɗan gidan ne yace na dawo Gida na cigaba da Kula da Hajiya wallahi Iya gaskiyata kenan Kuma shine ya kawo ni har nan"
Baffa yayi wata irin dariya.
"Bayan ya gama lalata dake Ko? babu wanda zaku rainawa hankali kawai kawaliya ce tai Miki Hanya kika je kikai kwana biyu kika dawo Gida To bari Kiji ba agidana wannan abun Kunyar ba wallahi bazan ɗauka ba sabida haka tun wuri Ku haɗa ina ku ina ku Kubar Min gidana danni ba zakuja Min zagi a cikin Unguwa ba"
Da sauri saadatu ta kama ƙafafun Baffa tana wani irin kuka!
"Baffa iya gaskiyata kenan Wallahi bai min komai ba in ƙarya nake kazo Muje Gidan ka tambaye shi"
Wani irin naushi abbati yakai mata babu ji babu gani yahau dukanta Ummi ta rungume saadatu wanda ya haɗe su gaba ɗaya yana duka har wata tsuma yake.
"Mu zaku wulaƙanta? dama ni Jikina ya bani ba alkairi ne ya fitar dake daga gidannan ba ashe yawon Iskancin ki kika tafi to yau saina Illataki na lalata duk wata Kafa da namiji zai gani ajikinki har yayi sha'awa" Cewar Abbati yana dukan su Umma dariya take Ɓoyewa tana furta.
"Abbati kai mata a hankali fa kar Cikin nata ya zube bafa a dukan mai Juna biyu"
Duk da saadatu tana cikin Jin raɗaɗin Dukan da yake mata sai da ta juyo ta dubi Umma saboda raɗaɗin Maganar Umma yafi Dukan yi mata zafi!
Babu irin Cin zarafin da Baffa bai Musu ba Kuma babu wanda ya ƙwace su daga dukan abbati har seda ya gaji dan kanshi sannan ya soma Kumfar baki yana balbalin bala'i Ummi ce ta janye sa'adatu suka shiga ɗaki Lokacin saadatu Ko hannunta bata iya ɗagawa Kuka kam tayi shi harta Godewa Allah taja wa Anwar Allah ya isa tafi Cikin Carbi ta la'ance shi har babu adadi don shine Silar Jefata Cikin wannan matsala a haka sum sum dashi kamar na Allah.
"Saadatu Meye dalilin ki na baro Gidan aikin sannan na kasa Gasgata gaskiyar maganganun Baffa shin waye ya kawo ki acikin Mota?"
Cewar Ummi.
"Kema zargina kike kema ba zaki Min Uzirin ba shikenan Ni kawai gwara na mutu na huta"
Sai ta soma yin wani Irin tari wanda ya ɗagawa Ummi hankali Duk taurin zuciyar Ummi kuka take na ganin Halin da ƴar uwarta ta shiga Hajiya dake kwance itama kukan take ganin Saadatu bata yin Motsi yasa Ummi fita don neman ɗaukin mutan gidan nasu amman Duk ihun da take babu wanda ya Kulata Ganin wankin Hula na neman kaita dare yasa ta fita Gidan Aunty Murja Wadda ta biyo Ummi zuwa gidan babu yadda Saadatu take Haka suka ɗagata Mijin Aunty murja ya ɗauko Motar shi suka sakata aciki wani Ƙaramin asibiti dake kan titin Rijiyar zaki suka kaita Nurses suka amshe ta da gaggawa Suka shigar da ita ɗakin duba marasa lafiya.
Jingine kanshi yayi a jikin Sitiyarin Motar yakai Minti Goma a wajan kafin ya tayar da Motar tashi yabar Layin Cikin kasala yake Driving zuwa Gida gaba ɗaya kanshi ya Kulle Har ya ƙarasa Gida ya Fita daga Mota Ya shiga part Ɗin shi bai gama dawowa daidai ba wani Irin Yanayi ke Fisgarshi bai ɗauka zai kamu da wuri haka ba.
Tun ranar daya soma ganinta a part Ɗinshi da yamma Da alamun ɓatan kai tayi ta shigo masa, Yaji gabanshi ya faɗi bai son soba sabida bai taɓa Yiba amman yana Jin lamarin ta mai girma acikin zuciyar shi bai damu da ƙasƙancin taba shi dai yafi damuwa da tarbiya.
Babu laifi taci jarrabawar shi, sabida yana Gudun sharrin mata tunda akwai tabo acikin zuciyar shi bai ɗauka zai kamu cikin sauƙi ba sai dai Tun ranar daya ganta ya kasa sukuni ya kasa Nutsuwa ita kaɗai yake kalla acikin Idanunshi.
Yayi saurin kauda ita ne daga Cikin Gidansu sabida kar ayi amfani da ƙarfin Ta azuciyar shi a cutar da Shi sabida Yana jin baze Taɓa Jure kawaici akanta ba, ita ce mace ta biyu data ji tausayin shi bayan innah ita ce mace ta biyu data kare Lafiyar shi sanda za'a cutar dashi Tabbas Lamarinta mai girma ne a gare shi.
Lumshe ido yayi yana Neman yafiyar Allah na rungumar da yayi mata wanda ba don komai yayi mata hakan ba sai don ya ƙara gwadata akan wankin ido ko itan ta kasance acikin jeri ƴammata masu wankakken idanu sai dai kashh bai samu nasara akanta ba sai ma ƙarin Tashin hankali daya gani kwance a cikin ƙwayar Idanunta hakan ya bayyana masa tsantsar kamun kanta.
Kama lips ɗinshi yayi yana Tsotsa Jinshi yake a wata irin Duniya ta daban yana jinta a ranshi amman yana Jin nauyin furta mata kalmar da zata haɗa zuƙatansu waje ɗaya sabida yana ganin kamar har yanzu akwai sauran Lokaci.
Mirginawa yayi tare da matse ƙaramin Pillown dake gaban shi yana sakin sassanyan Numfashi da ƙyar ya tashi yayo sallar Isha'i wata irin kewa yake Ji acikin zuciyar shi da gangar Jikin shi kwanciya ya kuma yi babu Jimawa bacci mai daɗi wanda ya jima bai samu ba ya ɗauke shi.
Washe gari bai yarda sun haɗu da Abba ba sabida Tun jiya yake ganin Kiran abba amman yayi Buris sabida yasan baze wuce maganar Alhaji Jamilu bace.
Ayyukan shi ya cigaba dayi acikin Office koda ya kammala Komai da yamma ya fito daga Office yana driving yana sakin Murmushi wanda tunda ya tashi a safiyar yau Fuskarshi ke cike da Wannan Murmushi wanda ya nuna zahirin farin Cikin da yake Ciki.
Hanyar Gidansu Mami ya nufa sunan daya sa mata kenan Sanye yake Cikin farar shadda ƙal wadda Kallo ɗaya zaka yi wa shaddar ka gane zahirin tsadarta.
A ƙofar Gidan su yayi parking ya fito daga Cikin Motar ya jingina ajikinta yana neman yaron da zai aika ya kira masa ita.
Ummi da Aunty Murja a wajan saadatu suka kwana wadda zazzaɓi mai zafi ya rufeta fuskarta duk ta fashe Ba yadda Aunty Murja batai da Ummi akan ta tafi gida ba amman taƙi data takura mata ma sai ta saka mata Kuka dole mijin Aunty Murja yace to ta kwana da ummi.
Washe gari da Zazzaɓin saadatu ta kuma tashi, sai amai take ruwa aka saka mata bacci