Chapter 11 Reading YANKAN KAUNA HAUSA NOVELS By AUTAR MANYA.txt Arewa Novels

YANKAN KAUNA HAUSA NOVELS By AUTAR MANYA.txt

Author :  Autar Manya Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 13

30K to 33K   out of 36.3K words

ya ɗebe ta wajan rana Aunty Murja ta koma gida ta Yo Musu Girki bayan ta dawo Ummi ta tafi sabida ta ɗauko kayan su ta kuma gyara Hajiya don har Lokacin Saadatu bata farka ba.
Sabida allurar baccin da aka zuba mata acikin ruwan.
Ummi ta kammala Komai ta gyara Hajiya sai da akai la'asar sannan ta fito daga Gida.
Wanda tana fitowa Anwar yaɗan zuba mata ido ganin yanayin su da saadah yasa ya ƙarasa Wajanta Ummi da Anwar ya cika mata ido da sauri ta Rissuna tana gaishe dashi ya amsa yana tambayarta Ina Saadatu Dan Allah kozata Kira masa Ita.

"Tun jiya muna asibiti yanzu ma kayanta nazo ɗauka"
Ummi ta faɗa masa cikin damuwa.
Yanayin yadda yaɗan Ruɗe abin ya bata mamaki.
Cikin sauri yace mata.
"Dan Allah in babu damuwa Muje naga Jikin nata"
Sai da tayi Jim kamar ba zata Bishi ba sai kuma ta bi bayan shi ta shiga Motar suka tafi.
Wanda duk abin da ya faru akan idanun Zubaida Ne babbar ƴar Umma wadda Ta dawo daga Unguwa tun tsaiwar Anwar ta kasa ƙarasowa wajan ta zuba mai ido tana kallon shi bata Firgita ba sai da ta ganshi tare da Ummi Ai suna barin wajan tai Gida aguje tana Kiran Ummah duk hankalinta a matiƙar tashe.............


Tafiya irin ta Kurame sukai Ummi tana ta mamakin wannan Haɗaɗɗan Mutumin ne yake neman saadah to a ina suka haɗu Ko shine ya kawota Jiya Sanin babu mai amsa mata yasa ta sunkuyar da kanta ƙasa domin gaba ɗaya kwarjinin sa ya hanata sukuni ita tsoro ma yanayin ɗaure Fuskarshi yake bata.

Tana nuna masa inda zai yi da yatsanta har suka ƙarasa bakin asibitin yayi parking Ɗin Motar tashi Ita ta soma fita sannan yabi bayanta a reciption suka haɗu da Aunty murja wadda take zaune Ummi ta tsaya a wajan Aunty Murja shi kuma ya wuce Cikin ɗakin data nuna masa wanda saadah ke kwance acikinsa.

Jikinsa a matiƙar sanyaye ya buɗe Ƙofar ɗakin ya shiga ɗan ƙaramin ɗakine mai ɗauke da gado guda ɗaya sai toilet.
Cikin Nutsuwa ya ƙarasa bakin gadon data ke kwance ruwan ma ya ƙare an cire mata bacci take sosai sai dai Ganin yadda Fuskarta ta kumbura ne yaɗan sosa ranshi a hankali ya tsaya akanta ya Jingina da bango wanda hakan yayi daidai da sanda ta Motsa tana Buɗe idanunta a hankali ta sauke su acikin nashi wata irin firgita tayi da sauri ta tashi ba shiri take Ƙoƙarin dira daga saman Gadon.........
*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*




*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*19*


Ya zuba mata ido yana kallonta na wani Lokaci, kafin ya kawar da idanun nashi daga kanta, Lokacin har ta sami damar sauka daga saman gadon tana Ƙoƙarin Fita daga cikin ɗakin ma.

"Zo nan ki zauna"

Ya faɗa mata cikin ƙaramin sauti kamar mai yi mata raɗa.

Maƙe ƙafaɗa tayi kamar wata ƙaramar yarinya idanunta na kawo ruwan hawaye! shaaaa.

"Subuhanallahi, To kukan na menene?"

Ya faɗa mata cikin ƙureta da mayen kallon shi.

Shuru tayi masa shima bai ƙara yi mata magana ba, haka suka kasance yana tsaye ajikin bango ita kuma tana tsaye a bakin Ƙofa ita bata fita ba ita bata shigo ɗakin ba, Ƙirjinta sai faman harbawa yake fat! fat! sabida tsananin Tsoro tambayar kanta take yaushe yazo waye ya kawo shi inda take.

Numfashinta ne ya tsaya na wucin gadi sanda taji ƙamshin turarenshi acikin hancinta a hankali take ɗago ƙwayar idanunta tana ƙare masa kallo yana tsaye akanta gab da ita sosai kamar zai Rungumeta.

Baya ta dinga ja harta kai Jikin Ƙofa ta maƙure tana Sauke Numfashi.

A hankali ya kuma ƙarasowa gabanta dab da ita kamar zasu haɗe, Maƙure kanta ta kuma yi ajikin Ƙofa tana ƙoƙawa da Numfashinta.

"Muje ki zauna"

Taji muryarshi acikin kunnenta, Turo baki tayi gaba kafin tace.
"Ni dai ka tafi"
Ya ɗan zaro ido kaɗan wanda hakan ya ƙarawa idanunshi Girma wani sahihin kyau ya bayyana a tare dashi.

"To zan tafi amman Muje kiji"
Ya wani ja kijin da ɗan tsayi.
Raɓe shi tayi ta Nufi bakin gadon ta zauna sai dai yadda tai zaman ne in ka kalleta sai kai dariya sabida kamar kace mata Ket! ne ta zura aguje.

Da sassarfa ya ƙarasa wajanta ya tsugunna a gabanta tare da kama Gefen gadon ya zuba mata ido Jin kaifin idanunshi na yawo a dukkan sassan Jikinta yasa ta ƙara shiga wani Irin yanayi na kasala da Mutuwar Jiki.

"Sai kallo kamar ƙuda"
Ta faɗa a hankali tana Ƙunƙuni.

"Ni ay nafi Ƙuda ma komai da Komai"
Ya faɗa ashe yaji, Toshe bakinta tayi da hannunta tana zare ido.

"Me yake damunki? Jiya naga lafiya lau Muka rabu"

Kamar Jira take yayi magana sai ta rushe da kuka! bai hanata Yin Kukan ba kuma bai daina kallonta ba, Kai jama'a Anwar ƙarshe ne wajan Miskilanci sai da tai Kukan mai isarta sannan ta tsagaita dan kanta.

Ya ciro Hanky ya miƙa mata Ƙin amsa tayi tare da juya masa baya ta turo mai Ƙeyarta.

Murmushi yayi mai sauti yana hango tarin Ƙuruciyarta.
"Please accept and wipe away your tears" ya faɗa yana kuma miƙa mata.

Ƙin amsa tayi ta cigaba da yin ƙaramin Kuka wanda sautin shi ke tashi a hankali.
"Mami so kike nima nayi kukan?"
Taji sautin Muryarshi cikin wani irin yanayi.
Mamaki furucin nashi ya bata.
"Wannan kukan naki yana damuna Dan Allah ki bari"
Ta kuma jin furucin sa.
Ajiyar zuciya ta sauke jin tayi shurun yasan shi tashi ya dawo Kusa da ita ya zauna ƙafaɗun su na jeruwa dana Juna.
Da sauri ta matsa a hankali sautin Muryarshi ke tashi.
"Bana jin zan tsaya yi Miki Ɓoye Ɓoye sabida iya ƙwayar idanuna kaɗai Kika kalla kinsan yadda nake ji game dake, Bazan takura miki akan sai naji dalilin kwanciyar ki anan ba amman ina roƙon ki da Ki daina Kuka wannan Kukan naki yana ƙara Kiɗimani Please zaki Aure Ni?"

Gabanta ne yayi wata Mummunar faɗuwa wani irin kuka mai ƙarfi ya tawo mata Furucinsa na ƙarshe ya tsorata ta ya Kiɗimata.

A wahalce ta ɗago tana Binshi da kallo still hawaye na kwarara acikin Idanunta Shima idanunshi yana kanta sai dai bai Kuma ce mata komai ba.

"Bayan abin da kayi Min Jiya yau ma Biyoni kayi ka Ƙara tarwatsa Min sauran Farin cikina? yaudarar taka ta Koma aure na domin ka cimma Burinka Mummuna akaina?"
Tsira mata ido yayi tunda ya ganta bata taɓa yin doguwar magana dashi kamar haka ba zaƙin Muryarta ne ya ƙara Jefa shi Cikin wani yanayi bai san me zece mata ba sai ya zuba mata ido ya wani rafka tagumi yana cigaba da kallonta.

"Nidai zan aure ki sabida Allah After this I don't know what to say"
Ya faɗi har Lokacin idanunshi yana Kanta wayar shi ta shiga Ringing! a hankali ya ɗauka yana magana wadda ba zata ce ga abin da yake faɗa ba.

Lokacin Nurse ta shigo ɗakin ya tashi ya fita yana cigaba da wayar Bayan ya gama wayar ya shiga wajan Likita suka ɗanyi abun da zasu yi ya Biya Kuɗin komai aka basu sallama da tarkacen magunguna ɗakin ya koma Lokacin su Ummi sun shiga wajanta yaɗan Dubi Aunty Murja wadda take gaishe dashi ya amsa a taƙaice yana ce wa zasu iya tashi ya aje su agida sabida an basu sallama yana faɗin haka ya fita wajan Mota.

Sai da Aunty murja tai wa saadah jan ido sannan ta saka hijabi dan da cewa tayi babu inda zata Bishi.

"Meye haka saadah ni banga wani aibu a tare da bawan Allah'n nan ba yana da Nutsuwa kuma ba yaro bane daga gani"
Cewar Aunty Murja.
Ummi tai dariya kaɗan tana cewa.
"Ko shine ya kawo ki Jiya ne? ni a ƙofar Gida na ganshi yace Ina mami na kasa ganewa sai da ya kwatanta Min ke sannan na gano ki"

Hararar Ummi saadatu tayi tana cewa.
"To in ba shi ba waye ne ni ya wani takura ni tunda naje Gidansu ya hanani sukuni kinji wata yaudara wai aure na zeyi Kuma bai ce yana sona ba dama ana aure haka?"
Aunty Murja da Ummi dariya sukai kafin Aunty Murja tace mata.
"Taso kar yaga Mun zaunar dashi mayi maganar a gida ai ba zamu bar wannan damar ba"
Tashi sukai tare da tattare abubuwan su A motar ma sai da saadatu tai masa taurin kai don yace ta shigo gaba tace ita a baya zata zauna sai da taga ranshi yaɗan ɓaci sannan ta shiga aikuwa har suka je Gida bai yi mata magana ba Ko kallonta bai yiba yana dire su yabar wajan faɗa Aunty Murja ta rufe ta dashi tana cewa.
"Ke bada ban soyayya ba uban me wannan Mutumin zai dake ba ajin ki bane shine zaki watsi da damar Ki, Wannan fa wani Luɗifi ne Allah yayi Miki Karki wasa da damarki saadah Ki gwada bashi dama baki san abin da Allah ya Ɓoye ba"

A bakin Ƙofar Gida suka rabu da Aunty Murja suka shiga gida ita kuma ta shiga nata Gidan.

Gidan nasu kamar babu kowa ɗaki suka buɗe suka shiga Hajiya duk ta ɓata Jikinta sabida haka basu zauna ba saida suka gyara Hajiya tas sannan Suka Shiga sabgar gabansu.

Saadah ta kasa gayawa Ummi abin da Anwar yayi mata ta dai ce mata shine ya kawo ta Jiya ya nemi ta daina aiki agidan su yau kuma yace mata auren ta zeyi yadda Ummi ta shiga Murna ne ya bawa saadatu mamaki.

Har dare saadah tana zuba ido ko Anwar zai dawo ya dubata amman shuru babu shi babu Ɗuriyar sa wasa wasa har tsayin kwanaki Uku babu Anwar Babu labarin sa suna samun abinci wajan Aunty Murja sannan Kamalu yana basu ɗari biyar Kullum Tunda ta dawo Gida Kamalun daya zo Taga yanayin sa kamar yaɗan sauko Har faɗa yay ma Abbati na dukan daya mata to wannan Rufin asirin ne yake riƙe dasu saboda har zuwa wannan kwanaki Anwar bai kuma zuwa wajanta ba Tun tana shiga ɗaki tai kuka har ma abin ya zame mata Jiki Dan wani Bin ko zama tai sai taita tunanin shi A yanzu ta yarda da soyayyar shi ta shiga zuciyarta tun ranar data ganshi taji Tana yi masa wata irin soyayya mai wuyar a fassarata.

Yau Kimanin kwanaki Biyar rabonta da Anwar Aunty Murja ce ta shigo Gidan da yamma sabida Aunty Murja bata shakkar Umma kai tsaye take Shigowa gidan.

Zama Aunty Murja tayi a kusa da Saadah taɗan kalleta kaɗan.

"Ni kam saadah kina fama da zazzaɓin dare ne?"
Saadah tai Murmushi mai ciwo tare da cewa.
"Mai kika gani wallahi lafiya ta ƙalau"
Ummi ta kalli Aunty Murja tana cewa.
"Nima na rasa me yake damun ta Kullum sai ta Ɓoye kanta taita Kuka nasha kamata tana Kuka to amman naga kamar bata son nasan damuwarta ne shiyasa nai mata shuru"

Saadah ƙasa tai da kanta bata Iya cewa komai ba saboda ita kaɗai tasan yadda take ji acikin zuciyarta game dashi.

"Saadah meke damun ki? sannan ina wanda ya ɗauko mu daga asibiti ina maganar ku ta tsaya?"
Ƙirjin saadah ne yaɗan Buga kaɗan ta ɗago ta kalli Aunty Murja sai ga hawaye na zuba daga idanunta anan Aunty Murja ta gano bakin zaren Damuwar saadah Cikin Hikima Aunty Murja tace mata.

"Kodai tun daga ranar bai Kuma zuwa ba?" saadah ta ɗaga mata kanta alamun "Ehh"

Aunty Murja tace "Shine kika rame haka lallai soyayyar taki da gaske ne Hajiya saadah an faɗa soyayya ai maganin ki yayi Ko nine haka zan Miki haba ai Nima kaina naga alamun ranshi ya ɓaci Ƙiri ƙiri Kika ƙi shiga motar shi fa Kuma Shine ya biya Miki Komai na asibiti dan da Mijina ne zai Biya zuwan shi yaje wajan likita ya biya Komai amman dan baki da Kirki agabanmu Kika dinga Nuna halin taurin kanki zuciya yayi ina ga baki da Number shi da se Ki masa waya"

Saadah ta ɗan zaro ido tana cewa.
"Ni bani da Number shi Aunty Murja ina ganin fa dama Yaudarata zeyi Ina shi ina Aure na Ɗan Gidan Alhaji Sule Kurfi ne fa naji Wadda ta kaini aiki gidan tana gaya Min To Aunty ina wannan mai Kuɗin ina ni"

Ta faɗa cikin karaya.
Murmushi Aunty Murja tayi.
"Ni kuma gaskiya banga yanayin shi yayi kama da mayaudari ba, sabida daga gani ba yaro bane Kuma yana da Nutsuwa nafi zaton Fushi yayi ko wani uzirin kin san manya fa sai an Musu uziri Ko kuma Hidimar Gida"
Murmushi Saadah tai.
"Bashi da mata gaskiya ni dai ban san mai ya hana shi zuwan ba"
Aunty murja ta zaro ido.
"Bai da mata tabb Allah yasa rabonki ne wannan ai Kika aure shi zaki Shagwaɓarki son ranki dan naga yana da shekaru kawai dai bamai Kule Kule bane amman ai yaci ace yana da ƴaƴa ma Kita addu'a kuma ki kwantar da hankalinki Kinji"
Aunty murja ta dinga kwantar mata da hankalinta.
Har ta ɗan sami Nutsuwa sallama sukai Aunty Murja ta koma Gida daran ranar Saadah labarin Anwar taita bawa Ummi wadda Ummin ta lura Anwar yayi wa ƴar uwarta Shigar sauri cikin zuciyarta.

*************

Yana tunanin anya bai shiga haƙƙin taba baya son takurawa Mutum sabida haka sai ya yanke shawarar rabuwa da ita Ko hakan zai sa ta samu Nutsuwa sabida haka koda yaje Gida ya tarar da Ɓacin ran Abba sosai na sallamar da yayiwa Alhaji jamilu haƙuri ya bawa Abba wanda ya Umarce shi akan lallai lallai ya mayar da Alhaji jamilu kan Kujerar shi.

Daga cikin Gida Duban Duniya Kande tayi wa Saadah bata ganta ba, sabida ko kaɗan bata kawo cewar Da Anwar suka Fita ba Ganin har dare yayi babu Saadah yasa ta sanar da Mama wadda mama ta kira Hadiza tace mata ba'aga Yarinyar data kawo ba Hadiza tace bata nan tana ƙauye amman In ta dawo zata Je Gidansu Yarinyar da haka Suka bar maganar sabida Hidimar Sunan Husna da suka Shiga Ita ta ɗauke hankalinsu daga Bibiyar Ina saadah tayi.
Kuɗin data bari ma Da kande ta kaiwa Husna cewa tayi ta Riƙe Kande taita Godiya Hanan kuwa data ji Saadah ta tafi har Rawar Murna tayi sabida dama bata ƙaunar yarinyar Ko kaɗan.


Anwar ya shiga sabgar gabanshi sai dai duk yadda yaso ya cire saadah a zuciyarshi abin ya faskara ko Rufe idanunshi yayi Hotonta yake gani Gaba ɗaya jiyay ya shiga damuwar rashinta.

Yau kimanin sati rabon shi da ita dafe yake da ƙirjinshi dake yi masa zafi Yana kwance a saman Doguwar Kujera a falon shi.
Khalid ya shigo cikin shirin fita.
"Lafiya na ganka a kwance ba zaka fita Office bane?"
Khalid ya faɗa masa yana zama a gefen shi.
Tashi yayi tare da yamutsa fuskar shi kaɗan.
"Bana jin daɗi yau ba zan fita ba"
Khalid yaɗan tsira masa ido.
"Innah ma tai min Complain na yadda ka sauya kwana biyu Zamu iya shearing Matsalar ka?"
Anwar ya jingine kai da Jikin Kujerar yana sakin numfashi.
Khalid ya miƙe a zuciye.
"Ka mayar dani soko Ni ko meye ina sanar dakai Anwar akwai abin da ke damunka Ko wannan yarinyar ce?"
Da sauri ya ɗago yace.
"Wa kenan?"
Khalid yayi Murmushi tare da cewa.
"Ban sani ba kafini sanin ta ay wadda na zo na tarar dakai da ita ban san dai alaƙarku ba amman nasan matsalar baze wuce daga wajan taba"
Anwar yayi Murmushi.
"Yes ita ce kasan Ni bana yaudara ban taɓa yin soyayya ba bare na yaudari ƴammata wallahi Auren ta zanyi sabuwar mai aikin gidan ce..........
A takaice ya gayawa Khalid Komai dake faruwa.
Khalid yay dariyar shaƙiyanci.
"lallai ka shiga da yawa akanta zaka fasa zuwa Office daɗi na da Gobe saurin zuwa da kana ganin kamar bani da abinyi Ko kadai Ji yadda soyayyar take Ko?"
Anwar ya harari Khalid cikin wasa tare da cewa.
"Ni dai ka bani shawara raini ne bana so gaskiya Kuma ban iya rarrashin mace ba bare na lallaɓata"
Khalid dan dariya har da ƙwarewa.
"Aifa shiyasa naga kana kwance ka dafe Ƙirji kaga tashi Muje Office daga nan sai Muje wajanta Ko?"
Tashi yayi ya shirya suka fita har suka kai Office labarin saadah yake bawa Khalid yana jaddawa Khalid yadda yake Jin tausayin ta.
Khalid ya dire Anwar a office ya wuce shima wajan la'asar suka tashi ya Kuma Biyowa suka tafi tare don Anwar bai fita da Mota ba.

A ƙofar Gidan su saadah sukai Parking Khalid ne ya fita ya sami yaro yace yaje ya kira Musu saadah acikin wancan Gidan Sanda yaron yaje saadah tana bacci Ummi ta tasheta Fuskarta duk ta Kumbura idanunta ya ƙara Girma ta sa Hijabi ta fita Ido Huɗu sukai da Khalid wanda ta ɗan shaida shi sabida haka sai ta ƙarasa wajansu ta ɗan tsaya daga Nesa batare data yi magana ba...........*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*



*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN

11 / 13