Author : Sameena Aliyu Category : Romantic Hausa Novels
tambayeshi sunan shi saidai hakan bata samu domin kuwa ana ida sallah ya nemi saurayin cikin masallacin ya rasa nan ma jikin Abbah a mace ya komo gida....
***
Ta yanda Mamy ke shiga bata nan take fita ba, haka taiwa Nabila tas akan daren da tayo a unguwa, Nabilah sai ture turen baki take tana fad’in “Amma dai Mamy kiga fah yanda na dawo gidan nan jagab da tab’o koma tausayina bakiji ba kuma baki tunanin ko lafiya nake ba... Mamy fah motar k’iris ya rage bata bigeni ba shine mai motar ya wankeni da ruwan tab’o...”
“Rufe min baki sakarcin banza, rashin hankalin da kika tsaya yaja hakan ya sameki ai, banda sakarci tun yaushe ya kamata ki dawo gida sai yanzu, itama Bara’atun ai hankali bai isheta ba dama... C’mon ni wuce ki cire wannan kaya kafin ki b’ata min waje.... Sa’arki d’aya Abbanku bai tambayi ina kike ba...”
Fuuu Nabilah ta shige d’aki yanda ta tadda Marliya na aikin gyaran wardrobe d’insu wanda sanda zata fita tai d’ai d’ai dashi wajen neman hijab....
Marliya na mata welcome Sisi ko takanta batabi ba ta fad’a toilet, Nabila ta fita zakka cikin yaran Mamy gata batajin magana gata batason aikin gida idan kaga ana aiki toh Marliya ce wai donma Mamy na tak’ura mata, ita dai barta da masifarta....
Babu yanda Sameer da Shamsu basuyi ba Khalid ya tsaya yaci dinner koma ya bar motar tasa gobe da safe bakanike yazo ya duba amma fir yak’i ya tak’ura tafiya zaiyi yanda ya sanardasu da safen zai mik’a motar wajen gyara...
Gidan da yaga ta shige nan ya nufa yanda ya tadda wasu Almajirai zaune daga can gefen gate d’in gidan alamun wajen tamkar wajen zamansu ne.....
Daga can gefe yayi parking kafin ya fito yana zira hannaye cikin aljihun wando sai wani faman yatsina fuska yake...
Yaro guda ya kira cikin almajiran kana ya tambayesa ko yaga shigan wata yarinya cikin gidan d’azu bada jimawa ba...
Yaron ya d’an tsaya tamkar mai nazari.... Tuni sauran almajiran sun k’araso wajen sabida sun zata sadaka mutumin zai bayar kar a bawa guda cikinsu su rasa...
Daga yanda suke tsaitsaye rungume da kwanukan baransu d’aya yace “Ba Nabilah bace uwar masifa ta shige har muna k’ok’arin mata dariya tayi wanka da tab’o...”
Sauran sukace “Tab wa ka tab’a gani yazo wajen wannan masifaffiyar inaga dai cikin sauran yaran gidan ne..”
D’ayan ya kuma cewa “A’a Garzali itace kawai ta shige da mangariban nan...”
Zasuci gaba da musu Khalid yace “Ku dakata, sunanta Nabila...?”
A tare suka jinjina kai had’ida furta “Eh sunanta kenan uwar masifa...”
Khalid ya jinjina kai kana yace “D’ayanku ya shiga ya min sallama da ita..”
A tare yaran suka kalli juna fuskokinsu cikeda tsoro...
Khalid ya kuma dubansu cikeda mamaki kana yace “Tsoro kukeji..?”
D’aya wanda yafisu k’ank’anta yayi saurin jinjina kai had’ida furta “Zata iya hanamu zaman wajen nan idan muka shiga hark’arta, babu mai iya koda gaisheta ne cikinmu sabida masifarta...”
Khalid ya Kuma jinjina kai kana yace “Karku damu bazata maku komai ba tasan da zuwana....” Ya k’arashe yana mai saka hannu cikin aljihu...
Sadakan kud’i ya basu wanda tsaban mamakin yawan kud’in basusan sanda suka soma had’e baki wajen cewa bari suyi masa iso da ita ba... Sai zuba masa godiya suke tsananin tausayin yaran na d’awainiya dashi, yaran da basu wuce ace suna makaranta ba, wasu ba takalma wasu kayan duk a b’arke... Sosai suka baiwa Khalid tausayi sanda yaji suna fad’in abubuwan da zasuyi da kud’in da yanda zasu b’oye kada matar Malam ta gani ta k’wace.. Wasu na fad’in zasu sai takalmi wasu na fad’in sun samu kud’in karin kumallo na sati guda koma fiyeda haka...
Kasancewar jikinta ya b’aci yasa tai wankan darenta mai iyanin ta sauya shiga cikin kayan bacci, suna zube parlorn Mamy suna kallon tashan wasan kwaikwayo lokaci guda suna cin tuwo itada Marliya Mamy na gefe tana ci gabada yiwa Nbilah fad’an rashin natsuwarta...
Cin tuwon kawai Nabila take tasan yau sai gari ya waye Mamy ta daina d’ago maganar gashi ba itace a d’akin Abbah ba, babban abinda yafi bak’anta mata rai shine yanda ake cewa tai koyi da k’anwarta Marliya...
Sallaman yaro almajirine ya katse Mamy yanda ya sanar dasu ana sallama da Nabilah a waje...
Tuwon da Nabilah kenan bata had’iyeba ya tsaya mata a mak’oshi....
SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_..............DA RABO_
*19*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Mamaki bai saki Khalid ba ganin gidansu Nabieela suka nufa, har k’asan ransa yake jin dad’i don dama nan yayi niyyan zuwa ya danna mata wani wulak’ancin kafin ya tafi tinda itace silan kwanansa har biyu a garin.....
Marliya ce ta masu iso har parlorn Abbah, Khalid sai dubanta yake yana hango tsananin kamanninsu da Nabila gashi dai ita wannan ga dukkan alamu saliha ce kuma mai hankali ba kaman wancan uwar bala’in ba....
Haka kurum Sameer yaji yarinyar ta kwanta masa sai murmushi yake yana dubanta yanda take kaikomo da kayan ciye ciye da shaye shaye gabansu....
Tambayarta sunanta yayi ta d’ago a hankali tana dubansa kana tace “Marliya...”
Sameer yace “Sannu koh Marliya mun gode.....”
Kanta a k’asa tana murmushi ta fice....
Jim kad’an Abbah ya shigo ya taddasu, nan suka soma gaidashi gaba d’ayansu, Khalid sai yafi kowa zak’ewa da son suyi sabo sosai da Abbah saidai ya lura shi Abban wani irin mutum ne wanda yakeda tsananin tsarewa, harta uban gayyan wato Sameer ba wani hira suke ba da alama kawai Allah ne ya had’a jininsu...
Tray mai d’aukeda ruwan sanyi Mamy ta hanga gefen fridge da alama Marliya ta mance bata kai masu ba, Nabilah ce gefenta tana had’a tray d’in abincin Mamani nan Mamy ta umarceta ta bar abinda take takaiwasu Abbah da bak’insa ruwa...
Sam Nabila batason shiga kan mutane don tasan wani cikin bak’in ya fad’i mata ba daidai ba tana iya danna masa mummunar kallo wanda har sai sun had’a idanu bak’on ya fahimci haka idan kuwa babu Abbah wajen ta jifa masa magana tai gaba abinta....
Badon taso ba ta d’auki tray d’in ta nufi sashen Abbah, sam bata kawo zatai artabo da mutum mai irin kamanninsa ba cikin gidansu, wani wawan birki ta danna tana mai kuma k’yafta idanu alamun badai gizo yake mata ba, tabbas shi d’in ne, Innalillahi toh mai yakeyi a gidansu, mai ya kawosa gidansu harma parlorn Abbanta, wannan wane irin mutum ne tai gamo dashi, kardai yasan Abbanta ne...?
Haka tayita jerowa kanta tambayoyi babu mai amsa mata su, Khalid kuwa tamkar ance ya juya sukayi idanu hud’u da Nabilah dake tsaye wajen tamkar an dasata, murmushi ya sakar mata had’ida kashe idanu guda irin taji mamakin nan koh....
Lokaci guda tai saurin saita kanta kana ta nufi parlorn kanta a k’asa, gaisuwan jam’u ta masu don bata fatan dogon gaisuwa ya shiga tsakaninta da d’aya daga cikinsu....
Sauri sauri ta fice daga parlorn k’irjinta naci gaba da bugu....
Saida ta sami bango ta tokare take iya sauk’e numfashi mai nauyin gaske, murmushinsa kurum take hangowa wanda ya kasa b’acewa daga k’wayan idanunta, da ace bata ganshi sau biyu kafin yau ba k’ila tace kamanni sukayi don ta tabbata babu abinda ya had’a Abbanta da wannan mutumin, toh amma shid’in ne dai, toh wai waye shi ne kam.... A hankali ta lumshe idanunta domin kuwa izuwa wannan lokaci lamuran mutumin ya soma bata tsoro...
Aunty Lami ce tazo zata shige ta kafe Nabilah da idanun ganinta cikin yanayi wanda bata tab’a ganinta cikin irinta ba...
K’arasowa tayi had’ida dafata kana tace “Nabila lafiya kike....?”
Sai sannan Nabilah ta bud’e idanu tana duban Aunty Lami....
Saurin turb’une fuska tayi kana tace “Lafiya mana Aunty... Barin shige...”
Bata jira cewan Aunty Lami d’inba tai shigewarta....
Kallo Aunty Lami ta rakata dashi tana mai nazarinta, gyara mayafinta tai kana tasa kai ta nufi parlorn Abbah....
Ganin da bak’i a parlorn ya sanyata sakin fuska sosai yawa mutuniyar k’warai tana wani aza mayafi ta k’arasa tana fad’in “Bak’i ne mukayi... Sannunku da zuwa....”
A tare Shamsu da Khalid suka soma gaidata kafin Sameer ya had’iye abincin dake bakinsa shima ya d’ora da gaisuwan a lokacin da ya d’ago fuskarsa....
Wani irin mummunar fad’uwan gaba ne ya dirarwa Aunty Lami sanda tayi tozali da idanun Sameer, ta kasa amsa gaisuwan da ya mata ta kuma kasa daina kallonsa, badon a zaune take ba tabbas da jiri ya iya kayarda ita....
Abubuwan da suka faru shekaru 30 baya suka shiga dawowa kwanyarta, har saida Abbah ya furta “Lami ana gaisheki ko bakiji bane...”
Sannan Aunty Lami ta iya kimtsa kanta....
Murya a d’an sark’afe ta amsa murmushin yak’e bai bar saman fuskarta ba....
Sauri sauri ta fice daga parlorn ta nufi nata sashen ta d’auki wayarta babu shiri....
Hajiya na faman rabon fad’an Hafiz da Sahariyya kan tak’urawa d’iyarsa Kausar da Sahariyya keyi taji wayarta na faman ruri cikin d’aka...
Fad’i take “Ku kuka sani ku cinye kanku idan bazakuji maganata ba, wannan yarinya taka mai jinin tsiya a tareda ita gwarama kayi auren ka kaita can wajen matarka ta kular maka da ita...” Tana ida fad’in haka ta nufi d’aki tana lalumar wayarta yanda ta tadda wayar ta katse, ganin wacce tai mata kiran ya sanyata saurin sake dialing layin....
Hafiz dake mak’ure da wuyan Sahariyya fad’i yake “Wllhi kinji na rantse babu yanda zankai Kausar nan gidan zata girma tinda ku kuka tilastama uwarta barinta don haka dole ku kula da ita, kin sanni kinsan banida kyau kukan yarinyar nan na sakeji wllhi sai nayi ajalin idanunki k’wara... Shashashar banza...”
Yana ida fad’in haka yayi jifa da ita kana yayi ficewarsa sai faman fito yake hula a karkace ya nufi wajen sahibarsa Sawwama.....
Tinda Aunty Lami ta d’auki wayar Hajiya ta fahimci babu lafiya.....
“Wai meke faruwa ne ni dan Allah ki sanar dani.....” Hajiya tace hankali tashe...
Aunty Lami ta samu jikin gado ta jingina kana tace “Haule anya kin tabbata Ma’aruf ya mutu...? Haule anya Ma’aruf ya zama tarihi kaman yanda muke tunani, anya Ma’aruf bazai dawo garemu ba....?”
Dukda bugu da k’irjin Hajiya keyi bai hanata dariyar yak’e ba kana tace “Haba Lami meye kuma kike neman maida mutane baya ana ci gaba a rayuwa, wane irin Ma’aruf...? Idan dai Ma’aruf d’an gidan Usman Mailafiya ne ya jima da mutuwa saidai mai kamanninsa, kinga kima daina sak’awa zuciyarki wannan mummunar zato don Allah....” Ta k’arashe tana zama bakin gado....
Girgiza kai kurum Aunty Lami take tamkar Hajiyan na dubanta kana tace “Inaga dai baki fahimci abinda nake nufi bane Haule amma idan da hali yau d’in nan mu had’u gidan Aminiyar sirri ta fad’i mana gaskiyar abinda tayida Ma’aruf Mailafiya don wllhi yau nikam nayi tozali dashi a raye....”
Jikin Hajiya ya d’anyi sanyi, gyara zamanta tai kana tace “Shikenan Lami mu had’u gobe gidan Aminiya tinda dai yaukam kinga dare yayi, ke nake jiyewa kinsan wannan baud’edd’en mijin naki ba bari zaiyi ki fice ba ni kuwa nawa mijin dama a tafin hannuna yake... Ma had’u goben....”
Aunty Lami ta amsada “Toh shikenan Alhaji na fita Kasuwa zan fito...”
Daga haka sallama sukayi ko waccensu tana sak’e sak’e cikin zuciyarta.....
***
Washe gari haka Nabila ta tasa Mamy gaba da tambaya ko tasan bak’in Abbah...
Mamy ta umarci Marliya data kwashe dankali cikin mai kana ta dubi Nabilah dake shirya wanke wanken plates cikin drawer tace “Kici gaba da tambayata abinda bai shalleki ba kar kiyi aikin dake gabanki....”
Nabilah ta turo baki gaba tace “Kai Mamy tambaya shikenan ya zama laifi ai da Marliya ce ko Addah suka tambayeki amsasu zakiyi, Mamy Dan Allah su wayesu...?”
Girgiza kai kurum Mamy tayi kana tace “Nabilah ban sansu ba hasalima ban shiga parlorn ba har dai suka tafi kina gani ai... Toh yaya za’ayi na sansu kin kuma san Abbanki kinsan wane irin mutum ne ba kasafai yakeso ana haurawa kansa ba musamman idan yana tareda bak’i, ballanata ma kinsan ba shigan zanyi ba idan ba shine ya buk’aci hakan ba... Wai me bak’in suka miki ne...?”
Ta k’arashe maganar tana mai jefo mata tambayar had’ida tsareta da idanu...
Girgiza kai Nabila tai cikin sauri don bataso Mamy ta fahimci wani abin kana tace “A’a basumin komai ba kawai dai na tambaya ne.....” Kan Mamy ta kuma jefo mata wata tambayar ya mik’e ta d’au markad’en kayan miya ta zuba cikin blender....
Girgiza kai kurum Mamy tai kana tace “Allah sa dai ba wani tsaurin idon kika masu ba don nasan halinki....”
Bata jira cewan Nabilar ba tai ficewarta...
Nabilah da Marliya suka kalli juna suna k’unshe dariya,Marliya tace “Mamyna case... Addah Naby kema dai Dan Allah ki daina tinzira Mamy sai kuyi zaman lafiya...”
Harara Nabila ta galla mata kana tace “Ke idan aka biyeta Mamy toh fah a gidan nan ma sai aci kashi akanmu, k’yaleta kawai haka zanci gaba da lallab’a kayana wataran zatai missing masifar nawa da taro mata magana...”
Da mamaki Marliya ke dubanta kana tace “Addah did I hear you right...? Kikace wataran Mamy zatai kewar fad’anki, uhm kodai kodai Mamy ta kusa yin sirki ne....”
Ludayin gefenta ta janyo zata kwad’awa Marliya, Marliya ta sukunya tana dariya kana tace “Kinga gaban mangyad’a nike kiyi hak’uri don Allah, nifah kawai tambaya nai.....”
K’wafa Nabilah tai kana tace “Dama baki sunkuya ba, wllhi Allah sawak’e na tsaya kula wani namiji bayan duk halinsu guda ne, ga Addah can tayi auren wahala bataji dad’i ba ga Mamy ma ba wani dad’in auren takeji ba Aunty Bara’atu mijinta kullum baya nan wayasan uwar mai yake tsinanawa a can barikin, zamana a gida gaban iyayena yafin zaman gidan wani gardi da idan yamin badaidai ba garin nan sai ya mana kad’an don wllhi da ace ni ce Ya Hafiz ke aure da tuni ya gama shiga taitayinsa...”
Sallaman Aunty Lami ne ya katsesu... Marliya ta amsa da sakin fuska yayinda Nabila ta tab’e baki taci gaba da abinda take...
Lek’owa kitchen d’in Aunty Lami tayi tana fad’in “A’a ‘yanmatan gidan ne a kitchen, iyye kaga yaran Mamy....”
Idan kayan miyan da take juyewa cikin tukunya sunyi magana itama zatai magana, Marliya ce dai gaisheta fuska fal fari’a kana tace mata Mamy na ciki...
Har saida Aunty Lami ta ambaci sunan Nabila kafin Nabilar ta juyo a tak’aice tace da ita ina kwana... Shikenan gaisuwar bata kuma cewa komai ba...
Jin muryar Aunty Lami yasa Mamy fitowa suka soma gaisawa, nan Aunty Lami d’in ke sanar da Mamy zata gidan Yayarta Rabi bataji dad’i ba....
Mamy tace “Ayya Allah ya bata lafiya, kinsan shigowar daminan nan sai a hankali yanayi ya canza sai ayiya cututtuka...”
Aunty Lami tace “Wllhi fah Mamy abin saidai addu’a...”
Mamy tace “Haka ne ki gaidata da jiki....”
Aunty Lami ta amsa da “zataji sai na dawo...”
Mamy ta amsa mata da “A dawo lafiya...”
Nabilah na kitchen tana kwaikwayon maganan Aunty Lami kana tai k’wafa tace “Salon munafunci...” Juyowa tai ta dubi Marliya dake dubanta da mamaki kana tace “Ke kuma idan ina waje kika kuma biyewa wannan munafukar matar tana wani jan mutane da wasa wllhi kema sai na daina miki magana tam...”
Dariya kawai Marliya tai kana tace “Um naga dai matar babanki ne don haka itada Mamy matsayinsu d’aya, besides Aunty Lami battada matsala tun tasowarmu haka muka gansu zaune lafiya da Mamy....”
Tsuka Nabila tai kana tace “Aikin banza wannan da gani ruwan munafukai ne da ita shiyasa sam tamu batazo d’aya ba... Nidai na fad’a miki idan ina waje kema kiyi banza da ita kafin na tunb’uke miki hak’orin gaba....”
Girgiza kai kurum Marliya tai tana dariya kana ta fice a kitchen d’in ta bar Nabilah da masifarta...
***
Wajajen biyar na yamma Khalid ya sauk’a a Kaduna dashikema bai fito da wuri ba saida ya tsaya ya kammala wasu abubuwan....
A parlor ya tadda Siyama da Yesmin first cousin d’insa d’iyar Yayan Ammi dake karatu a Cyprus, rabonsa da ita zaikai shekara biyu ko fiyeda haka idan bai mance ba...
Siyama na hangosa murmusinta ya k’aru kana tace “Speaking of the devil... Kinga gashi nan sauk’arsa kenan....”
Baice mata komai ba sai uwar harara da ya danna mata
Cikeda zumud’i Yesmin ta ajiye glass of lemonade dake hannunta ta juyo tana dubansa fuska fal fari’a.....
SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_
*20*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
“Ya Khalid sannu da zuwa, ya hanya...?” Yesmin ta fad’i cikin kashe murya....
Kallon kirki bata ishi Khalid ba yace da ita “Kina lafia...?” A tak’aice...
Nanma saida ta kuma murmusawa had’ida juya idanu kana tace “Lafia lou, it’s been a while...” Bai bari takai ayaba yace “As you can see I just got home, I’m pretty tired... would you please keep your greetings maybe for later....” Ya k’arashe yana d’aga mata giransa sama alamun Yes a gajjiye yake...
Nan fah jikin Yesmin yayi sanyi ta juyo suka had’a idanu da Siyama, sosai Siyama taji kunyar abinda Khalid yayiwa yarinyar nan Yesmin tasan za’a rina hakan kallon su Ammi kurum take idan taji suna mafarkin had’a Yesmin da Khalid, basusan Khalid wane irin baud’edd’en mutum bane shiyasa...
Har ya isa staircase Siyama ta d’an bud’e murya tace “Eyya shalelen Daddy sannu da hanya ko nazo na baka massage ne...?”
Rolling idanunsa yayi yana mai dubanta a kaikaice kana yace “Spare me your false sympathy Siyaam...” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai sa kai da yai yayi haurawansa sama...
Duban Yesmin Siyama tai fuska d’aukeda murushin yak’e kana tace “Ehen mai ma nake ce miki....?”
Girgiza kai Yesmin tai kana tace “Cousin anya Khalid zai soni kuwa...? Kiga fah abinda yayi...”
Murmushin Siyama ta kumayi kana tace “Kar ki damu cousin idan dai Khalid ne ya wuce haka, but I believe you can change him....”
Sauk’e deep breath Yesmin tai kana tace “But are you sure he doesn’t have a girlfriend...?”
Murmusawa Siyama ta kumayi kana tace “Wa... Wannan...?” Ta kuma d’an murmusawa kana tace “Dukda fad’a da muke yawan yi Khalid bai tab’a b’oyemin komai ba na rayuwarsa... Idan da ace yanada I’ll be the first person to know.. My brother is single... Shifah wannan baida lokacin ‘yanmatan ma pride d’insa bazai bari ya nemi budurwa ba shiyasa nace miki idan kinyi hak’uri you can win him over...”
Kurb’an lemonade Yesmin tai tana jinjina kalaman Siyama...
A b’angaren Khalid kuwa Haurawa sama da yayi yaji dama bai shigo sashen Ammi ba gaba da’aya, Aunty Hidaya ya hango mahaifiyar Yesmin Yaya ga mahaifiyarsa....
Cikin sauri yasa kai zai juya saidai tuni Aunty Hidaya ta hangoshi, bud’e murya tai cikeda far’a kana tace “A’a Son suk’ar yaushe....?”
K’ak’aro murmushi yayi yace “I just arrived Aunt.... Mun sameku lafia....?”
Aunty Hidaya ta kuma murmusawa kana tace “Lafiya lau Saifullahi... Ya aiki...?”
Murmushi Khalid yayi don ita kad’ai ke ce masa Saifullahi kana yace “Lafiya Aunt... Aunt