Author : Sameena Aliyu Category : Romantic Hausa Novels
kai ne Mamani sabida tsabagen kwad’ayi da son abin duniyarta ta shige abinta, girgiza kai Basmah tai had’ida yin k’wafa ta shige ta rik’e Mamani kafin tai masa wani b’aranb’araman a motar, lokaci guda take tunanin yanda Nabilah zata d’au abin...
Khalid na tafe Dattijuwar na jansa da hira wanda akasarin hiran nata marassa kangado ne ko ba’ace maka ba kasan tsufa ke d’awainiya da ita..
Bai ida shan mamaki ba saida Basmah ta nuna masa gidan nasu... Ya dubesu yana mamaki zuciyarsa na masa fari k’al don idan har wannan Kakar Nabilah ce tabbas yasan zai samu wajen zama sosai ta wajenta...
Mamani sai yaba hankalinsa take yayinda Khalid yaji dad’in ci gaba da janta da fira... K’arahe dai har Basmah ta shige gida takaiwa iyayenta rahoton abindake faruwa, sukakaw yo gangami don ganema idanunsu dama tun kwanakin baya suke kad’a gurmi tsakaninsu cewa wani had’edd’en saurayi ke zuwa wajen Nabilah saidai babu wanda ya isa ya fito fili ya fasa gurmin sanin cewa wacece Nabilah...
Nan suka hangesu tafe sun nufi sahen Mamanin da Khalid d’in...
Nabilah kaw da dawowarta kenan daga makaranta ta sauk’a a adaidaita ta hangi motar Khalid k’ofar gidansu, mamaki ya isheta musamman data iso wajen taga alamun babu kowa cikin motar.. Gabanta na dukan tara tara ta nufi cikin gida....
SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_
*35*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Tinda ta shigo gida ta kasa zaune ta kasa tsaye, yanda take tunanin zataga Khalid bata ganshi ba, toh kodai ba motarsa bace... No she can’t be mistaken tabbas motarsa ce, toh ina yake...? Kodai aje motar kawai yai k’ofar gidansu...? Amma mai zai kawo motar tasa k’ofar gidan nasu...?
Ita kad’ai sai sak’e sak’e take, ta sak’a wannan ta warware wancan, Marliya dake zaune gaban socket tana gugan kaya hankalce take da ‘yar uwar tata, a ‘yan kwanakin sosai ta fahimci canzawa da Nabilah tai, wasu lokutan ko magana kake mata bata amsawa sai ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, balle daren jiya yanda taji tana waya ta tabbata da wani take wayar...
Nabilah ta kuma mik’ewa zata fice a karo na kusan hud’u... Marliya ta katseta da fad’in “Wai ina kike zuwa ne... Lafiya kuwa...?”
D’an dubanta Nabilah tai a yatsine kana tace “Toh uwar sa ido kitchen zani wajen Mamy, koda magana ne... Uwata...?”
K’unshe dariyarta Marliya tai kana tace “A’a Allah baki hak’uri...”
Nabilah tai gajeren tsuka kana ta fice... Saida ta kuma sad’ad’awa ta lek’a sashen Abbah kaman wata munafuka kafin ta dawo kitchen ta tadda Mamy tuni ta ida abincin dare ta zuzzuba...
Gaisar da Mamy ta somayi tana tayata jere abincin....
Mamy da tun ganin Sameer take fama da tinane tinane sama sama ta amsa Nabilar kana ta umarceta ta d’au abincin Mamani takai, Nabilah a duniyarta ta tsani a aiketa sashen Mamani, gaisuwa ma don dole ke kaita tasan saura sarai idan ta tsallake kwana guda bataje ta gaidata ba d’aid’aya Mamy zata mata...
Babu halin ta doje taje ga Marliya a parlor na zaune bataga fuskan hakan ba balle ma ko a mafarki bata isa ta fad’iwa mahaifiyar tata haka ba...
D’aukan abincin tai ta fice yanda taci karo da Marliya a hanya ta ida gugan zata nufo kitchen wajen Mamy kafin Mamy tai mata tatas daga ita har gugan nata tace wasanta ta zaunayi tana ganinta a kitchen donma itace ba Nabilah ba datasaba shan mitan Mamy wanda gwara ai maka duka a cewar Nabilah...
Tareta Nabilah tai da fad’in “Ke Leeya wai bakiga bak’o ya shigo gidan nan ba....?”
Marliya ta dubeta da mamaki kana ta girgiza kai tace bak’o kuma...?”
Nabilah ta jinjina kai tace “Eh mana Abbah baiyi bak’o ba...?”
Marliya ta d’anyi shiru tamkar mai tunani kana ta girgiza kai tace “Gaskiya ni banga wani bak’o ba hasalima Abbah bai dawo ba ko kinga motarsa a gareji ne...?”
Nabilah ta d’an tab’e baki tace “Yo ina na lura, kinga zo kishige kafin Mamy ta lek’o...”
Aiko bata kai aya ba Mamyn ta lek’o tana fad’in “Wai ba aikanki akai ba Nabilah... Ke kuma kin tsaya biyeta naki aikan na jiranki.... Tsayuwar mai kuke ne..?”
Ko wacce tai hanyarta suna baiwa Mamy hak’uri, Marliya ta rab’a ta gefenta ta shige tana tunanin yau d’ain kaman wani abin na damun Mamy...
Tana tafe tana tunanin mai ya kawo motarsa k’ofar gidansu, kaman daga sama ta hangesa da Mamani biyedashi da alama ya fito tafiya ne...
K’iris ya rage Nabilah bata kifar da abincin ba, wannan wane irin mutum ne... Yau Abbanta gobe Kakarta... Shin miye tsakanin Khalid da mutanen gidan....
K’irjinta yaci gaba da wani irin bugu.... Tai saurin sa kai zata juya saidai tuni Khalid ya hangota...
Bud’e murya yai kafin ta fice a k’ofar Mamanin yace “Aah k’araso mana aima tafiya zanyi....”
Maganar da yayi ya sanya Mamani dake faman masa zuba kai dubanta ga k’ofar...
Nabilah ta tsaya cak ta kasa ci gaba da tafiya, tamkar ta zunduma a guje haka taji gashi ta kasa juyowa...
Mamani kaw ganin yarinyar da ake magana da ita tak’i juyowa ya sanyata yab’e baki tace “Ke wacece tsaye wajen nan ko bakijin magana ne...?” Nan ma Nabilah bata juyo ba sai rintse idanunta da tai da k’arfin gaske...
Mamani ta nufeta cikin dogara sandarta tana fad’in “Ai wato ina fad’a maka Haladu sam yaran gidan nan basajin magana, gado sukai wajen iyayensu mata...”
Jin zata saki layi ya sanya Nabilah saurin juyowa tana aika mata mugun kallo baki a cune, fuska babu alamun walwala tace “Aini aika na kawo kuma bansan kinada bak’o ba...” Tasa kai abinta zata shige d’akin dukda cewa Khalid tsaye yake wajen, da k’yar ta wuce gabansa musamman data tuna ko mayafi babu jikinta...
Mamani ta dawo da baya tana fad’in “Kaga rashin kunyar tasu koh... Toh wannan ina fad’i maka itace babbarsu a rashin ta ido, batada kunya ina fad’a maka babban abin takaicinma wai sunana gareta...”
Khalid kaw banda murmushi yana satan kallon Nabilah data had’e gabas da yamma baya komai, Mamani tace dashi shigo ai kaci abinci, baka bar gidan nan ba sai kaci abinci Yaron arziki Haladu....”
Wato har cikin ransa yakejin banbarak’wai d’in nan idan ta kirasa Haladu shi bai tab’a sanin mai suna Khalid ake fad’iwa hakan ba sai a baki Mamani...
Ya d’an shafi kansa kad’an yace “Baaba ba Haladu ba Khalid sunan...”
Mamani ta dubesa tsegege kana tace “Kajimin dai, wayace maka ba sunan kenan ba, ai asalin sunan kenan Haladu mu haka muka sani, kuma ka kirani Mamani don haka kowa ke kirana kaji koh shige muje...” Ta k’arashe tana turo shi ciki ta dawo dashi parlorn, sosai sukaso baiwa Nabilah dariya ganin draman Khalid kesha shida Mamani...
Batabi takansu ba ta mik’e zata fice Khalid ya bita da kallo yanda tai tamkar bata tab’a saninsa ba ko gaisuwar fatar baki bata masa ba...
Mamani ta tsareta da fad’in “Ke ke dakata shige ki kawo masa faranti da cokali yaci abinci... Kuma ki kawo na ‘yan gayu don kin gansa sarai d’an gaye ne...”
Nabilah ta dubeta a kufule kana takai dubanta ga Khalid wanda fuskarsa kega wayar salulansa, tana jira taji yace bazaici ba ta sami excuse d’in tafiya amma da yake d’an duniya ne shiru yai alamun zaicin kenan...
Mamani ta katseta da fad’in “Zaki wuce ne kokuwa....?”
K’wafa tai a hankali kana tasa kai ta shige kitchen d’in Mamanin da ba girki ake ciki ba kawai dai kayan amfani ne ciki...
Plate da spoon ta d’auko ta d’auraye had’ida serving spoon ta ijiye saman tray ta dawo fuska a d’aure ta dangwala kusada k’afafunsa....
“Kaga rashin hankalin nata koh, toh k’one masa k’afafu su zama bak’ak’e tinda naki bak’i ne....”
Nabilah datazo wuya hak’urinta ya gaza tace “Aidai wajenki na samo bak’in k’afar tinda na Mamy na fari ne tass....” Tai maganar tana murgud’a baki....
“Kaji koh.. Kaji rashin kunyar tata, ai Manu ya rasa d’ah tinda ya Ma’aruf sauran kam duk gayyan yuyuyu ne... Zuba mashi abincin...” Ta k’arashe tana gwagwiyan goro lokaci guda ta mik’e ta nufi d’aki kaman mai neman wani abin...
Nabilah tai k’wafa kana ta bud’e flask d’in, tuwon shinkafa ce fara sol d’auri d’auri a leda, leda guda ta d’auka ta kwance ta saka cikin plate d’in zata kuma d’auko wata ledar yace da ita “Ya isa haka idan kuma ba tayani ci zakiyi ba...”
Takai masa mugun kallo had’ida d’auke idanu tana mai gyara zaman rigarta duk gaba d’aya a tsarge take ga Mamani ta gama yarfata...
Gaba d’aya a tak’ure take, ta soma k’ok’arin mik’a hannu zata janyo d’aya flask d’in yai saurin mik’a hannunsa ya tura mata kusanta, ba tareda dubeshi ba ta shiga kiciniyar bud’ewa...
Khalid ya mik’o hannu zai bud’e tai saurin janye hannunta...
K’uri ya mata yanda tai tsananin b’ata fuska, ya tab’e baki alamun ko inkula kana yace da ita “Na fasa taimakon ki bud’e da kanki kafin na kira Mamani nace mata rowa kike min...”
Ta kalle shi a kufule kana ta janye idanunta tana tab’a marfin taji ya bud’u alamun ya bud’e kenan....
Lafiyayyar miyar taushe ne wanda yaji bushesshen kifi da naman Sa... K’amshin ya daki hancin Khalid sanda taci gaba da serving d’insa bawai don ranta naso ba...
Tana gama serving d’insa ta soma k’ok’arin mik’ewa amma saiji tai ta kasa tashi sabida kallon da yake binta dashi, tai k’wafa cikin zuciyarta don ko magana ta kasa masa...
Khalid ya janyo plate d’in kaman zai soma cin abincin, itakoh sai satan kallonsa take ganin kaman hankalinsa ya koma kan plate ya sanyata mik’ewa a hankali, daidai sanda Mamani ta fito hannunta rik’eda takardan foster Clark...
“Ungo jeki had’o masa abin sha, kya bashi abinci haka babu ruwan zak’i ce maki akai shi ya saba cin abinci haka ne babu ruwan zak’i...?”
“Mamani fah baice maki zaisha ba don Allah ki k’yaleni na tafi aiki fah nake...” Tai maganar kaman zata runtuma kuka...
Shiko Khalid yana cin tuwon yana satan kallonsu ko tofawa baiyi ba...
“Aiki a’a kecema agogo, nace kece ma agogo... Shige ki had’o masa aikin naki ya jiraki...”
Nabilah ta gallawa Khalid da ya maida hankalinsa kan abincin da yakeci harara tai k’wafa a hankali... “Mamani da gaske baisha ki tambayeshi kiji....”
“Ke banson rashin kunyar banza a ina yace miki bayasha... Kai Haladu wai bakasha abin zak’in d’akin tsohuwa ba...?”
Khalid da bawai yama fahimci meye abinda ake shirin bashin ba amma duk dai salon kada Nabilah ta tafi yace “Idan an bani zansha Mamani....”
“Toh kaji d’an gari.... Maza shige ki had’a masa d’auki k’ank’ara a firiji (Fridge)...” Mamani ta fad’i tana zama kujeran data tashi...
Kaman zatai kuka haka ta shige kitchen, Hajiya Mamani taci gaba dajan Khalid da hira, idan tace Haladu shiko sai ya gyara mata yace Khalid ne, k’arashe ya fahimci Mamani ba daina ce masa Haladu zatai ba, sosai yaci abinci saida yaji mamakin kansa shida ba gwanin son tuwo ba amma tass ya cinye wanda Nabilah ta zuba masa...
Nabilah ta shigo d’aukeda k’aramar tray da jug had’ida cup bisa, wannan karon ta warware d’ankwalin kanta ta d’an rufe jikinta dashike yanada d’an girma...
Ta dire tray d’in gabansa, zata tashi Mamani ta kuma umartanta cewa ta zuba masa...
Badon taso ba ta d’au cup d’in ta shiga tsiyaya lemun, citta ta samu a kitchen d’in ta d’an markad’a ta tace ta had’e da lemon tsami kad’an sai d’an fosterclarck d’in data zuba kad’an sai sugar nan koh ya bada flavor mai dad’i tamkar lemonade...
Salon kar Mamani ta barta ta tafi yace ya gama cin abincin da an tattare wajen...
Nanma Mamani ta umarci Nabilah data tattare wajen....
Nabilah data cika fam k’iris ya rage bata fashe ba ta d’ago tana watsa masa mugun kallo kaman zatai kuka...
Murmushi ya sakar mata a hankali had’ida kashe mata idanu guda yana mai ci gaba da sipping drink d’insa...
Fuuu ta wuce da kwanukan kaman zata tashi sama...
Mamani tace “Maza ki fasa kwanukan na uwarkice babu asarana ciki ehe...”
Ko amsata Nabilah batai ba ta shige abinta, ai komawa sashen Mamani da bata iyayiba kenan, ko kitchen wajen Mamy bata biya ba ta fad’a d’aki tana maida numfashi...
Kaman wacce aka zabura tai saurin k’arasawa drawer d’in data aje teddy bear d’in da bata ta ciro tana duba...
“Who are you... Maiyasa kake bibiyan kowa a family na... Mai kake nema....?” Tamkar mai magana da mutum haka take maganar... Ta jima tana duban Teddy d’in tamkar mai jiran amsa daga gareshi saiji tai wayarta na faman ruri... Ta d’an firgita kana ta aje teddy d’in zata nufi wayar nan teddy d’in wanda idan yai babban motsi ke fad’in wasu kalmomi ya kuma fad’i mata kalaman _I love you_
Kallo tabi teddy d’in dashi kana ta nufi wayarta dake k’aran alamun shigowar sak’o...
Ta rausayar da idanu had’ida fuzar da iska kana ta d’aga wayar tana k’ok’arin karance sak’on...
_I’m waiting for you outside.._
Saida ta karance kusan sau uku kafin ta zauna saman gado tana tunanin martanin da zata maida masa bayan haushin da suka k’unsa mata shida Mamani...
_Mantuwa kai ko abincin ne bai isheka ba_ Ta rubuta ta tura masa..
Murmushi Khalid yai kana ya shiga tura mata reply kaman haka _Idan baki fito ba zan shigo har yanda kike na sameki kinsan zan iya... So you’ve 2minutes to decide, is either ki fito ko na shigo na sameki... Just 2 minutes.._
Rausayar da idanu tai kana takaima teddy d’in harara tace “Bazan fita ba saidai kai duk abinda kaga dama...”
Marliya dake tsaye bakin k’ofa tsoro da mamaki suka kamata ganin Nabilah ta saka teddy gaba tana tsigalesa...
“Addah Naby lafia..?”
Marliya ta tambaya tana dubanta...
Nabila ta d’an shafi goshinta tace “Lafiya mana mai kika gani...”
Marliya ta k’arashe shigowa d’akin kana tace “Yo niko naga komai, kin saka gunki gaba kina masa masifa, waima ba cewa kikai ma Kausar zaki kai ba.. Addah Naby anya lafiya kike...? Marliya ta k’arashe tsoro kwance saman fuskarta..
Janyo hannunta Nabilah tai sanda wayarta ta d’auki ruri kana tace “I’ll explain to you later, bani hijab d’inki kiga na fita yanzu zan dawo, karma Mamy ta sani dan Allah...” Ta k’arashe tana kwab’e hijab d’in daka kan Marliya ta zira ta fice cikin sauri...
Marliya ta bita da kallon mamaki tafito parlor a sanyaye....
A b’angaren Mamani kuwa sai k’irga kud’ad’en da Khalid ya bata take tana zirawa k’ark’ashin kwalla tana shimai albarka yanda kasan bata tab’a ganin tsaban kud’i ba ko sallama taji anayi zata tura k’ofa da sandarta sannan ta zaune akai kafin ta amsa sallamar...
***
Jingine jikin motarsa ta taddashi ya bada baya waya manne kunnensa na hagu abinka da lefty.....
Tai tsaye tana k’arema kwantattun sumarsa da a kullum cikin shek’i suke kallo, yanda ya bada bayan nan tamkar ta suri dutse ta runtuma ma k’eyarsa haka taji, tayi tsaye tana tunanin Khalid ya juyo yana dubanta, kaman wanda akacemasa juyo...
Kallo guda ya mata ya d’auke kansa yana ci gaba da amsa wayarsa, wani takaicin ya kuma lullub’e Nabilah, tasa kai zata juya cikin gida sabida tsananin takaici saijiyo muryarsa tai yana fad’in “Ina zaki...?”
Ta tsaya cak ba tareda ta juyo ba.. Badon Teddy d’insa dake duk’unk’une cikin hijab d’inta ba da tuni ta juya cikin gida hasalima da ko fitowa bazatai ba kawai dai don tana son maida mashi kayanshi ne...
A hankali ta juyo ta taddashi yanda yake tsaye....
Khalid ya murmusa a hankali had’ida zira hannaye cikin aljihu ganin yanda Nabilah tasha mur...
“Thanks for the food... it was delicious...” Ya fad’i idnunsa akanta....
Tinda ya soma magana idanunta ke k’asa tana duban k’fafunsa da Mamani ta zage mata nata k’afafun akansu, ta kuma duban nata k’afafun sai taji kaman yanzu Mamani ke zage mata nata k’afafun tai saurin maida yatsun k’afafunta cikin takalami, hankalin Khalid ya karkata kan abinda take duba yatsun k’afafunsa...
Murmushi ya kusa kufce masa, lokaci guda yake furta “Sun maki kyau ne..?”
Tai Saurin d’agowa a d’an razane tamkar wacce aka mintsila, lokaci guda ta had’e fuska tace “Allah ya sawak’e...”
Khalid ya murmusa a hankali kana ya tab’e baki yana mai furta “You know there’re some certain things that we can’t simply hide...”
D’agowa tai had’ida d’an masa wani duba “And there’re some certain people that we can’t simply stand them...”
“Are you sure about that...?” Ya tambaya cikin kashe murya....
Bata kuma tsayuwa basa amsa ba ta mik’a masa teddy d’insa tana fad’in “Ga abinka nan banso, just stop stalking me please..”
Khalid ya shiga kad’a d’an makulin hannunsa yana dubanta murmushi kwance saman fuskarsa....
Tai tsaye tana jiran taji ya amsa abinsa dashike kauda kanta gefe tai... Bata ankara ba sai k’aran tashin motarsa ta jiyo kafin tai wani aune ya bad’eta da k’ura ya bar wajen....
Tai saurin matsawa baya don kar ya had’eda ita baki sake tabi bayan motar tasa da kallo zuciyarta na k’una, amma wannan shi a sahun rainin hankalinma ajin k’arshe yake, kaman ta fashe da kuka haka ta shak’e wuyan teddy d’in ta nufi cikin gida ga ‘yansa idon unguwar zaune benci benci bakin kantina...
Hango Aunty Lami da tai ta sauk’a a adaidaita kuma wannan karon ma Hajiyar Ya Hafiz na cikin keken ya sanyata d’an lab’ewa cikin sauri ta lalumi wayarta ta shiga neman layin Aunty B da shike ta sanar da Aunty B d’in komai gameda zarginda takewa Aunty Lami kuma Aunty B tace she should keep her updated gameda komai don tasha alwashin tayata zak’ulo gaskiyar al’amari, idan har da gaske su Lami su suka sanadiyan gushewar farin cikin ‘yar uwarta sai yanda k’arfinta ya k’are wajen d’aukan fansa ga ‘yar uwarta....
***
Sameer ya kuma dubanta da mamaki kana yace “Are you serious zaki baro aikinki a Kaduna ki dawo ki zauna dani a nan...?”
Siyama ta kuma janyo hannunsa guda ta shige ciki tana mai furta “Of course Partner, na amince zan biyo aurena na kula da kai...”
Sameer ya tura yatsun hannunshi guda cikin nata yayinda ya mata matashi da b’angaren kafad’arsa guda kana yace “Baki tunanin Uncle bazaiso hakan ba...?”
D’an dubansa tai kana tace “Kaman ka mance Daddy duk abinda nakeso shi yake so, that won’t be an issue besides nayi serving company d’inshi na tsawon shekaru ya kamata yanzu kuma nabi mijina duk yanda zaije, I can’t afford to lose you Partner...” Ta k’arashe murya cikeda shagwab’a...
Har cikin zuciyarsa yake mamakin canzawa da Siyama tai lokaci guda, wata b’angare na zuciyarshi kuwa najin dad’in canzawan da tai dukda cewa har yanzu yanaji kwance k’asar zuciyarsa kaman akwai abinda take b’oye masa, amma sam baiso tunanin nasa yaci galaba a zuciyarsa abinda ya bayyana dashi ake amfani yafi aminta da ya yardarwa kansa cewa