Author : Mrs A.M Category : Top Hausa Novels 2025
Umma gaskia kar ki balla ta"
Dagowa nai nace "ke har kinzo"
Dariya tai tana Zama tace "gani kuwa kin gani, tun 9 nazo ko Umma".
Murmushi Umma tai tana binmu da kallo tace "haka ne sammako ta bugo kin ganta"
Hararar ta nai nace "banji dadi ba amma naso na rigaki zuwa".
Nan muka shiga Hira Mimi kuwa tuni ta tafi gidan su Hidaya, mu mukai wa Umma girkin rana kuma tare muka ci sai tsiya nake wa Aisha kasancewar tana da ciki wata 4.
Bayan la'asar muka tafi babban gida muka gaida su uwani da Yakumbo daga nn muka biya gidan Aunty Xainab maman Hidaya.
A tsakar gida muka zauna muna hira dasu Abba ji nake kamar kar na koma, Amma duk da haka wani bangare na zuciyata yana min kaikayi tun da nazo bai kirani ba hakan ya bata min rai sosai kawai na share ne tunda yace zaizo dauka ta da kansa.
Gurin 9 Yusuf yazo ya dauki Aisha, mu muna zaune Abba ne yace kema ki Kira azo a dauke ki dare yana yi
Turo baki nai nace "Abba ynxu korata kake yi"
Dariya yai yace "A'a ba korar ki nake na kawai dai naga darr tayi ne"
Sai 10 sannan ya kirani daki na shiga ina kokarin fara masa shagwaba yace "sorry ban samu zuwa ba Bashir yana waje yana jiran ki, Zeey ce take zazzabi kuma bana son na bar ta ita kadai"
Wani yawu na hadiya nace "ohk" kawai na kashe wayar, sai da na saita kaina sannan na fito sallama nai wa su Umma har waje suka rako ni na shiga mota sannan suka koma.
Muna zuwa gida kwantar da Mimi nai dama da kayan barcin ta na tafar Mata da kuma na chanja Mata su, wanka nai na tsaya ina jiran ya shigo amma shiru har 12 kwafa nai nace gobe dai a kwana nane zanga yadda za'a yi.
Washe gari ma ban gansa ba har magriba tai, Tun Mimi na tambaya ta ina yake har tayi shiru don ko kulata bana yi.
Wanka nai na shirya cikin doguwar riga mai siririn hannu, daukar basket din dana zuba masa abinci nai na bude kofar na shiga bakina dauke da sallama kusan mutuwar tsaye nai ganin ta zaune akan kujera tayi pillow da cinyar sa.
Dagowa sukai a tare suka kalle ni, murmushi na saki nace "ina wuni ashe kana nn"
Shima murmushin yake yai yace "lafia qalau, ina nn Zeey ce da rigima wai kamshin jikina take so in na matsa amai take ji, tun dazu ma taso komawa part dinta amma ta kasa Zama a ciki bata son kamshin part din nawa take so"
Dage gira nai ina murmushi nace "Allah sarki", kallon ta nai naga ta zuba min ido tana kallona, murmushi nai nace "sannu Allah ya raba lafia"
Basket din zan kai dinning yace "kawo min nan plz yunwa nake ji dama"
Banyi magana ba na dawo dashi nan zuba masa tuwon semo din nai na Mika masa, kallon Zeey yai yace "zaki ci"
Girgiza kai tai tana yatsina fuska tace "A'a" badon ranta yaso ba tana son ci amma haka baya cikin plan dinsu.
Zama nai a Kan kujera ina danna wayata kamar bansan da zaman su a Palourn ba nan kuwa hankalina yana kansu, daurewa nake kawai amma ji nake kamar na mike na fallawa Zeey Mari.
Cikin shagwaba tace "Yaya cikina ciwo yake min Ka matsa min plz"
Kallon su nai naga ta wani bude ciki shi kuma sai dan mammatsa mata yake, da sauri na dauke kaina gabana yana faduwa.
Sai da akayi Isha'i sannan na mike na koma part dina, ba dawo ba sai 10 lokacin ban same sa a part dinba, nasan yana part din Zeey.
Cire kayana nai na kwanta akan gado sai wajen 12 ya shigo wanka ya fara yi Sannan ya hawo gadon yace "baby nayi missing dinki"
Banxa nai masa ina jinsa sai shafa ni yake daure wa nai naki kulasa har ya gaji ya kyale ni, shafa wuya na yai yace "sorry baby naso zuwa na ganki amma Zeey bata Jin dadi tana ciwon ciki shiyasa ban kyale ta ita kadai ba ynxu ma sai da na lallabata tai bacci don sai kuka take min bata son kamshin dakin ta"
Ban yi magana ba sai dan matsawa danai daga jikinsa kawai ina lumshe ido, kallon bayan ta yake da mamakin mai take nufi badai fushi tai ba knn.
Da asuba ma ina tashi part dina na nufa duk raina a jagule, breakfast na hada na kai part dinsa na gyara masa sai lokacin da nake sa turaren wuta ya shigo daga part din Zeey.
Kallon sa kawai nai na dauke kaina na koma part dina, badai ni yake ma haka ba sbd Zeey mu zuba nida Shi.
Da mamaki yake kallon ta yana mamakin wai fushin mai take, ganin bai sami answer ba yasa ya koma part dinsa kawai daga kafada.
**********
Cikin sati biyu har Wata rama nai sbd abubuwa sun chanja sosai, ynxu ban cika samun lokacin Saba ko ranar girkina ne balle ma ranar da bani da girki, kullum da sabuwar tsirfar da Zeey zata bullo da ita.
Ni Kam da haushi ya kamani akwai lokacin dana ce masa ya koma part dinta kawai na bar mata kwana na, ko yaushe tana part dinsa anan take wuni sai dare take tafiya ranar girkina daren ma sai ya tafi rakata ya dade kafin ya dawo.
Yauma girki nane shigowa ta knn da abincin sa, ajiye masa nai akan dinning ina shirya masa abincin Zeey ta shigo tana yamutsa fuska.
Kallona tai tace "plz zaki hada min zobo shi nake sha'awa".
Banza nai mata kamar banji mai tace ba.
Kallon Azlan tai ta shagwabe fuska tace "Yaya kasa ta hada min zobo plz shi nake bukata, nasa masu aikina sun hada min bai min dadi ba."
Mikewa yai ya karaso inda nake kallona yai yace "kina ji fa tana fadin ki hada mata zobo, ki taimaka kinsan halin da take ciki kinji".
Dagowa nai na zuba masa ido hawaye suna taruwa aciki gyada kai kawai nai na juya na fita daga part din.
Wani murmushi Zeey tai a ranta tace an kusa zuwa gurin
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[24/09, 20:04] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 39
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃
*Mrs Dnah perfumes nd more*
*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*
*Muna Saida*
*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.
*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*
*Phone number*
+234 702 577 7778
Location kano
Na dade a kitchen ina kuka kafin na bude fridge dama ina da zobo da nayi jiya, a jug na zuba mata nasa a tray da cup.
Lokacin dana shigo palourn tana kwance akan cinyar sa yana matsa mata hannu wai ciwo yake mata, kallo daya nayi musu na dauke kaina.
Ajiye wa nai akan center table nace "gashi koh"
Kallona yai so yake su hada ido ya rarrashe ta da ido amma taki basa wannan damar, tabbas yasan yana shiga hakkin ta amma wani zubin Zeey ke rike sa, ko yayi kokarin yakice ta daga jikin sa sai ta fara kakarin amai ita a dole kamshin jikin sa take so.
Mikewa Zeey tai tana yatsina fuska tace "ngd sosai fah, kinsan shi ciki ba abinda baya saka so kawai ji nai ina san shan zobon ki"
Gajeran murmushi nai nace "Allah sarki haka ne kuma kinsan laulayin ma in ya hadu da kwadayayye abin muni yake"
Da sauri na dago daga zuba zobon datai tace nice "kwadayayyiyar?"1
Gira daya na daga nace "wani abun kika ce"
Da mamaki ta kalli Azlan tace "Yaya kaji wai nice kwadayayyiyar kawai sbd nace ta sammim zobon ta, kuma fa ba laifi na bane kawai dai cikin ne yasa ni jin hakan."
Shafa kanta yai yace "sorry kinji, ba doctor tace kar ki dinga stressing kan ki ba."
Dagowa yai ya kalle ni, nima zuba masa ido na nai a cikin nasa ma masa wani kallo kafin na juya na fice daga part din takaici kamar zai sa na dora hannu aka.
Zeey kuwa hankali kwace ta shanye zobon duka bata bari Azlan ya sha ba, wani bangare na zuciyarta kuma yana mata gargadi akan abinda take shirin aikatawa.
Ko minti 10 batai da shaba cikin ta ya soma Mata ciwo, tun tana daurewa har ta kasa ta saki kuka.
A rude Azlan ya fito daga dakinsa don wanka yayi dama, karasowa gurin ta yai da sauri yace "lafia me ya faru".... Bai samu damar karasawa ba sbd jinin daya ga yana gudu a jikinta.
A rude ya tallafo ta yana girgiza ta ganin ta daina motsi, ajiye ta yai ya mike a guje ya nufi part din Batul.
A zaune ya same ta tana kallo Mimi kuma tana kwance akan carpet, da gudu ya karaso inda nake ya mikar dani, wani irin bugawa kirjina yai ganin sa a haka ban taba ganin sa cikin tashin hankali irin wannan ba, riko sa nai ganin jikin sa kamar yana rawa.
A nutse nace lafia Daddy mene ne
Ajiyar zuciya ya sauke yana nemo nutsuwar sa yace Zainab ce
Dan hade rai nai nace me tayi
Girgiza kansa yai yace sako hijab kizo muje jini take zubarwa
Zaro ido nai a tsorace jin abinda yace ban tsaya Jin karin bayani ba na tafi daki da sauri, hijab na sako na fito ban same sa a Palourn nawa ba hakan yasa na bi sa part din.
Ba karamin tsoro naji ba ganin yadda jini yake gudu a parloun, da gudu na karasa inda yake na taimaka masa muka fito da ita, bayan mota ya kwantar da ita na shiga bayan na dora kanta akan cinya ta, sosai tsoro ya rufe ni dan yadda take ma kamar ba rai a tare da ita.
Gudu yake sosai har Allah ya sa muka karasa asibitin, muna zuwa aka dauke ta sai emergency.
Tsayawa mukai don mun kasa ma Zama, duk da nasan bawai son Zeey nake ba har raina amma hakan bai sa ni Jin tsoron kar ta mutu ba ko ba komai ban tsane ta ba kawai dai kishi nake da ita.
Muna tsaye Mummy da Mami suka shigo kusan a tare kasancewar ya kirasu ya fada musu, a rikice Mummy ta taho gurin sa tace "mai ya same ta"
Shiru yai kansa a kasa duk yadda yake mayar da magana sai yaji yau baxai iya magana ba, ganin yaki Mata magana sai ta juyo guna tace "mai ya same ta"
A tsorace nace "Nima ban sani ba kawai yace nazo mu kaita asibiti sbd bleeding din da take".
Zaro ido tai tace "bari tai"
Da sauri Azlan yace "mummy ki daina cewa haka mana ba bari bane insha Allah cikina yana nn".
Sai after 2 hours sannan likitan daya shiga dubata ya fito, da sauri muka nufi gun sa dukan mu.
Kallon Azlan yai yace muje office nayi ma bayani
Kafin yace wani abu Mummy tayi caraf tace "fada mana kaganni nan mahaifiyar tace, shi kuma mijin tane, wannan kuma sirikar tace kuma matar Wana ce duk ba bare sai dai waccan da yake Kishiyar tace."
Daga kai yai yace "ta samu miscarriage ne a sanadiyar maganin zubar da ciki da ta sha mai karfi a lemo."
A rikice Azlan yace "kamar ya maganin zubar da ciki ynxu cikin ya fita knn."
Daga masa kai yai yace "da kyar muka samu muka tsayar da zubar jinin ku gode ma Allah ma da alama bata dade da Shan maganin ba don yana da karfi sosai, a drink tasha kuma da alama shine abinda tasha na karshe."
Innanillaihi wa innanillaihir raji'un kawai Azlan ke fada yayinda Mummy ta fashe da kuka, Mami kuwa sunkuyar da kai kawai tai ba karamin murna suke ba kasancewar zasu sami jika amma kuma sai gashi cikin ya fita tasan Abie zai ji fitar cikin sosai kasancewar yadda ya kwallafa rai akai.
Cak tunanin sa ya koma akan abinda doctorn yace tasha maganin ne a drink kuma da alama shine abinda tasha last, a sauri ya dago ya kalli inda Batul take wacce tunda likitan yace cikin ya fita take ambaton sunan Allah.
A harzuke ya nufo inda take, da sauri na dan zabura ina Kallonsa gaba na yana faduwa.
Cikin wani irin kallo dana kasa fahimtar mene ma'anar da yace "me yasa kika sa mata maganin zubar da ciki"
Wani irin bugawa kirjina yai a tsorace da kuma inda inda nace "Ka.....m....aaa...r.. y...aaa"
Tsawa ya daka min wacce tasa na fashe da kuka ba tare dana shirya ba, girgiza kai nake a rude nace "wallahi Daddy ban sa Mata komai ba mai yasa zan so cikin ta ya zube"
A tsawace yace "karya kike dama ta dade tana fada min kamar kina mata bakin ciki nace mata ba haka bane, Ashe da gaske bakin cikin kike mata har gashi kin yi sanadiyar zubar jinina".
Girgiza kai nake a tsorace nama kasa magana don tashin hankali
Janyo sa Mami tai tace "kana da hankali kuwa Azlan kasan mai kake cewa, meye hadin ta da miscarriage din Zainab"
Girgiza kai kawai yai yace "Ita ce Maa dama Zainab tasha kafa min cewa tana mata bakin ciki ina karyatawa, itace ta bawa Zainab zobo kuma shine abinda tasha last ko 10 minutes ba'a yiba ta fara bleeding".
A tsorace nace "wallahi Mami ba abinda na samata a zobon, kuma itace tace nayi mata already dama ina da shi a fridge kawai zuba mata nai a jug na kai mata".
Wani irin kallo yake mata Wanda ya sa na kara fashewa da kuka.
Mummy da take ji zuciyar ta na tafarfasa ta fizgo ni, ina juyowa ta falle min wani marin da sai da kaina ya bugu a bangon da nake jingine, dafe gurin nai ina tsugunna wa a kasa nadamar kai mata zobon nake, da kuma tunanin tashin hankalin da yake jirana.
Mami ce ta matso da sauri ta matsar da Mummy dake kokarin kai ma Batul dundu, cikin lallashi Mami tace "haba Hajia bai kamata ki mare taba, nasan Batul baxa ta taba tunanin cutar da wani ba har ma takai ga zubawa Zainab maganin zubar da ciki, ki Jira ta farka muji ta bakinta".
A hasale Mummy tace "ban gane mai kike nufi ba Maryam nufin ki Zainab ce zata zubar da cikin ta da gangan, kema dai kawai son zuciya kike son yi anan amma ko tunanin haka nasan Xainab baxa tayi ba"
Shiru kawai Mami tai don bata son ta Kara wani maganar da zai zo yasa su fara ja'in sa tsakanin ta da Mummyn, daga ni Mami tai tace "tashi kije driver ya maida ki gida kinji, insha Allah komai zaizo da sauki".
Kallon ta nai ina hawaye nace "Mami kin yadda baxan aikata hakan ba"
Murmushi Mami tai tana shafa kaina tace "duk da ban dade da sanin kiba amma nasan baxa ki iya tunanin cutar da wani ba"
Ajiyar zuciya na sauke koba komai na samu relief tunda da akwai Wanda bai yadda cewa zan iya aikata wannan sharrin da aka lakaba min ba.
Drivern Mami ne ya mai dani gida gaba daya hankali na a tashe yake, babban abinda yafi data min hankali shine yadda naga Daddyn Mimi ya dau zafi sosai....
*********
A asibitin kuwa sai karfe 6 Zeey ta farka, duk da ta mugun galabaita amma hakan bai Hana ta tuno da plan dinsu ba, kallon Azlan da yake zaune a gefenta tai cikin muryar data Kara lankwashewa tace "Yaya mai ya same ni ba abinda ya sami babynmu koh"
Rike mata hannu yai kawai ya kasa magana, kallon Mummy Mummy Zeey tai wadda da take ta huci tun dazu don ko data Kira baffa ta fada masa abinda ya faru bai yadda ba don a take yace sai dai ko ita Zeey din tasha wani Abu ne amma batul baxa ta iya sa mata maganin zubar da ciki ba, haka ma data kira Abie shima cewa yai a dai bincika sosai, wannan abin ba karamin kona Mata tai yai ba.
Ciki ciki Zeey tace "Mummy mai ya same ni"
A hasale Mummy tace"waccen shegiar kishiyar taki ce ta sa Miki maganin zubar da ciki kuma tayi nasara don cikin ya fita da kyar aka zaku aka tsayar da jinin ma".
Zaro ido Zeey tai kamar gaske tana dafa cikin ta tace "Mummy miscarriage nai? Kuma ita batul dince ta samin maganin".
Tsaki Mummy tai tace "toh Doctor yace abinda kika sha last ne a ciki aka sa maganin kuma Azlan yace zobon da ta hada Miki ne".
Fashewa da kuka Zeey tai tana matsa hannun sa dake cikin nata, cikin kuka tace "Yaya kana ji koh dama nace ma bata son cikin nn so hassada take min amma kaki yadda gashi ta mana asara Yaya".
Rarrashin ta suka shiga yi sida Mummy ita dai Mami tana gefe tana kallonsu, ba wani shaida mai karfi amma sun lakada ma yarinya laifi.
Da kyar suka samu tai shiru, fita yai ya Kira doctor ya kara dubata tabbatar musu yai ba komai zuwa gobe insha Allah ma za'a iya sallamar ta.
Ayi manage da wannan plz😢
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[25/09, 02:40] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 40
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃
*Mrs Dnah perfumes nd more*
*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*
*Muna Saida*
*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.
*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*
*Phone number*
+234 702 577 7778
Location kano
Bai Kara bin ta kan Batul ba har aka sallame su, Zeey sai kuka take tana fadin ita shiknn an rabata da cikin ta.
Haka suka koma gida da Mummy wacce tace zata zaunawa Zeey na sati daya, ta Kula da ita.
A kwana daya na zabge sosai sbd tashin hankali ko abinci na kasa ci, lokacin da suka dawo ina kallon su ta window sai lallaba Zeey yake har