Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
da ta ɗaurawa kanta zamarin kokuwa da ƙaddara, Allah ya sanya jumma'arta da nisa amma duk tabi ta ɗaurawa kanta damuwa akan zantukan da mutane suke yi, a shekarunta goma sha taran da take cikinsa.
Muryar yaya Majid da suka yiwa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya suka dawo dani daga nisan kiwon da na fara yi a zancen da nake yi da zuciyata.
"Zakiyya kukan meye kike yi? sai ka ce yau kika fara jin waɗannan maganganun, kamar yanda ni da Umma muka sha faɗa miki shi aure nufi ne na Allah kuma abinda ya hana ki mutuwa ki ya hana ki aure wato LOKACI. Matuƙar kina cikin bayin da Allah ya tsara akwai aure a cikin rayuwar su na duniya babu shakka sai kinyi Zakiyya".
Bata ce dashi komai ba illa sausauta kukan natan da tayi, shuru ya baƙunci ɗakin na tsawon daƙiƙun da basu gaza huɗu ba, kafin Anty Zakiyya ta kawar da shurun ta hanyar cewar"Yaya Majid ko ba yau kunnuwana suka basa jiyo min irin wannan zantukan ba, amma wallahi ban taɓa jin ciwo a raina irin na yau ba. Wai ace Bilkisu sa'ar ƙanwar bayata ce zata faɗi hakan a kaina?. Yaya Majid ni kuma ƙaddarata kenan haka Allah ya tsara min, yanzu ko tsakar gidan nan ban isa na fita ba sai a goranta min yaya suke zo nayi da raina?".
Ta ƙare zancen tana saka hannuwa tana tare ƙwallar da suka ciko mata kurmin idaniya a ƙoƙarin hana su kwaranya. Sosai yaya Majid yake fuskanto ta sai da ya tausasa muryarsa kafin ya shiga faɗin"Zakiyya ki sawa ranki dangana da haƙuri akan komai kinji?".
Kanta ta ɗaga masa, da hakan ya bashi damar miƙewa idanunsa a kanta yace"ni zan fita ki sanar da Umma in ta shigo".
"To a dawo Allah".
"Allah yasa".
"Amin".
Sai da na ga ya kai ƙofar ficewa nima na raka shi da addu'ar a dawo lafiya, ya amsa mini kamar yanda ya amsawa Anty Zakiyya. Ina jiyo sababin da Daada take surfawa a tsakar gida da ban san da wanda take yi ba, sai da na ƙare kwanciyana kana na fito nayi aikin da yake kallafe a kanmu na wanke wanke da shara.
Salma na iske har taja nata ta fara wankewa don haka nima na ɗibo na fara nawa, babu wanda ya tanka wani har muka gama. Na ware na sashin Hajiya Babba na kai mata babu kowa a filin sashin natan sai takalman su Abba da Baba da na hango yashe a ƙofar falonta, kaina tsaye nayi wuceta izuwa ga ɗakin girkin na ajiye kwanukan kana na ɗauki tsintsiya na fara share filin.
"Tunda yarinyar nan tayi nadama ni ina ganin kawai mu jira izuwa lokacin da Allah zai ba wa Habibun lafiya zai ayi wa tufkan nan hanci".
Zantukan Baba ƙarami da suka sauƙa a kunnuwana tamkar don naji ya yi su, kafin Baba ya karɓe zance a zafafe yake faɗin"Ummaru babu alamar nadama a tattare da yarinyar nan, don haka da zaran ya sama lafiya da kaina zan sanya shi ya sauwaƙe mata tazo gida ta zauna tunda hakan ta zaɓarwa kanta. Ai shi aure ɗan haƙuri ne da kuma kai zuciya nisa ba komai bane ake hawa dokin zuciya ba".
Kagagin kukan da Anty Kubra ta saka, cikin dushashewar murya tare da fizgo numfashinta take cewar"Baba dan Allah kuyi haƙuri wallahi ina son Habibu ina son aurena, don Allah kar ku raba ni dashi mutuwa zany.....".
Ban san meya hana ta ƙarishe ragowar zantukan da ta ɗauko ba naji tayi shuru, sautin kukan da take yi ya yawaita. Tagwayen ajiyan ajiyan zuciya na sauƙe tausayinta duk ya maƙale a raina, ina ƙara tabbatar da sahihancin wannan zancen na masu hikima"Nadama a ƙeya take".
Fitowar su Abba ya sa ni dai-daita nutsuwana, duk na rusuna ina gaishe su suka amsa mini a taƙaice suna ficewa, kafin iyayen mu mata suma suka fito daga ɗakin suma suka fice Anty Kubra ce ƙarshe fitowa, daga duba ɗa ya da nayi wa fuskarta na hango kumburi da canzuwar halittun fuskar. Ta gefe na ta raɓa ta wuce hakan ya ba wa ajiyan numfashin da nake dakon sa damar sauƙa.
Kafin na cigaba da sharan da nake yi sai da na share ko'ina, Hajiya Babba bata fito ba har na wanke banɗaki na shigo ɗakin natan bakina ɗauke da gajerar sallama. Amsa mini tayi tana daga kishingiɗe na zauna kusa da ita tare da yi mata sannu da hutawa ta amsa mini fuskarta tamkar gonar auduga.
"Hajiya ni kuwa ina son yi miki wata tambayar".
"Faɗi ina jinki Na'ima".
Musgutawa nayi ina lankwashe ƙafafuna waje guda, kana na ɗaura da cewar"Hajiya naga Anty Kubra ta fice tana kuka, gasu Abba ma duk sun fice rai a ɓaci. Dan Allah ki shiga maganar kar a raba wannan auren, a barta a ɗakinta kar ta fuskanci irin tsangwamar da Anty Zakiyya take fuskanta daga mutanen gidan nan".
Sai da ta saki ƙatotuwar ajiyar zuciya kana ta ce"Na'ima kenan Na'ima baiwar Allah duk abinda suke muku amma ke nufar ko wannen su kike yi da alkhairi. Lamarin Kubra babba ne ki taya ta da addu'a kawai kinji ko?".
A sanyaye na kaɗa mata kaina tamkar maraniyar ƙadangariya kafin na kai ga cewa wani abun, ta tari numfashina da faɗin"Saura kwana nawa ne sauƙar ku?".
Sai da na ɗan dara don ƙa'ida ce, tunda aka tsayar da ranar yaye mu daga islamiyya. Dukkan safiyar duniya na shigo sashin Hajiya Babba sai ta tambaye ni adadin ragowar kwanakin da suke rage.
"Saura sati uku Hajiya kullum fa sai kin tambaya".
"To ai gwara inna tambaya ni da zan aurar da jikoki har huɗu sa'i guda ai dole na tambaya, domin mun tattauna da iyayenku cewar da zaran kunyi sauƙar nan ba zaku wuce watanni biyu a cikin gidan nan ba, za'a yi bikin ku su Bilki duk iyayensu mata sunce suna da samarin da suke zuwa wajen su. Ke ce dai daman za a jira".
Sosai naji raina ya yi mini wani irin zafi kalaman Hajiya Babba ba kaɗan ba suka daki raina ba, tare da samun nasarar turbuɗe mini hasken annurin fuskata na wunin wannan ranar gabaɗaya.
"Lafiya dai takwara kin barni sai magana nake ni ɗaya kin yi shuru, tunanin meye kike yi?".
Furzar da iska nayi daga bakina haɗi da cewar"Hajiya nida ko tsayayyen saurayi ba na dashi, ayi nasu bikin kawai su da suke da samarin a hannu. Ni kuma idan Allah ya fito mini da miji koda na su Asma'u sai a haɗa ayi tare".
Sai da ta ƙare mini tanadin kallon tsaf tamkar mai son gano wani gaskiyar da na ɓoye kana ta ce"Na'ima aure shine cikar darajan ko wacce mace, kimarki ba zai cika ba inba a same ki a wurare ukun nan ba. Ko dai a tarar dake cikin gidan iyayenki, ko ɗakin mijinki ko kuma a iske ki a kabarinki, in sha Allahu kema Allah zai fito miki da miji kafin a kai ga lokacin sauƙar nakun".
"Uhmm".
Shine kawai abinda na iya furtawa a gare ta, daga hakan ban kuma fahimtar ragowar zantukan da ta ɗaura dasu ba. Har izuwa sa'ilin da Nurain yazo wai Umma na ƙira ta, tare dashi kuma baro sashin Hajiyan Babban sai da muka zo ƙofar ɗakinsu sannan na saki hannunsa ya shige nima na nufi namu.
Wasu atamfofi Umma ta fiddo mini dasu ta ce na kaiwa wata aminiyarta da ke nan bayan layi, na ce wai saƙonta ne na wajen Hajiya Sa'adatu. Hijabina na saka na sundumi ledar zannuwan na fito dai-dai sanda Asma'u da Habiba suke fitowa cikin shirin zuwa makaranta kasancenwar su tasu ƙarfe sha biyu ake zuwa bayan ƴan firamari sun taso.
Kallon Asma'u nake yi na ce"iyee har da hodarki a fuska cau abin ki".
Murmushi ta sakar mini tana juya mini idanunta Habiba tayi caraf ta amshe zance"Ai Anty Na'ima wai ita a hakan malam Garba take so, banda wahalar da kai mutumin da aka ce yana da mata har ɗa ɗaya".
Haɓata na riƙo ina ƙara shan ruwan mamakin da zantukan Habiba suka shayar dani, kafin wata dariya ta suɓɓuce mini sai da nayi son rayina kafin na ce"To kika sani ko zata je a ta biyu".
Harara ta watso mini ta finciko hannun Habiba suka fice fu, taɓe baki nayi cike da mamaki wai su ma sun san soyayya yaran nan da suke aji biyu a ƙaramar sakandiri.
A zaure na iske Daada da Anty Hasina da ban sa sanda tazo gidan ba tsaye cirko cirko, tana tsegumta mata abinda ya faru da Anty Kubra. A cikin zancen nasun nake jin wai Habibun ya ɓoyewa iyayensa gaskiyar lamarin tare da ƙin sanar dasu ita ce ta turo sa daga beni, Baba ƙarami kuwa yace da zaran ya warke sakinta zai sanya Habibun ya yi.
Tsumi-tsumi na wuce ta gefensu bayan nayi musu sannun da bata sama amsuwa ba. Gidan Aminiyar Ummata Baaba Asabe na nufa na kai mata saƙon da zan taho har da bani kuɗi wai na hau adaidaita, bayan ɗiyarta ta gama jeranta mini saƙon na gaishe mata da Anty Zakiyya.
Kamar wacce bata so haka nake tafiya a cikin layin nasu mai ƙarancin mutane, kamar daga sama naji an dafo ƙafaɗuna ta baya na juya a gaugauce cike da son ganin wanda ya yi mini hakan. Wangale baki da hanci nayi ina bin Khadija Salisu ƴar ajinmu da muka gama ƙaramar makarantar sakandiri tare da ita, sanye cikin sabbin uniform dal, kalan ruwan samaniya ga safanta da tasha wanki tayi tas da ita.
"Khadija Salisu ke ce?".
Na faɗa har yanzu idanuna suna kanta, ta ɗan juya idonta kana ta amsa mini"Nice Na'ima ya kike ya su Bilki?"
"Duk lafiya ƙalau".
Tare muka fara jerawa muna tafe tana labarta mini, sunan sabuwar makarantar babbar sakandirin da ta jona kuma iyayenta sunce da zaran ta kammala makarantar koyan aikin asibiti za a kai ta.
Sosai nayi mata fatan alkhairi muka rabo akan zata kawo mini ziyara, duk saurin da nake yi har ƙafafuna suna harɗewa cikin zanina gani nake yi tamkar ba tafiya nake yi ba. Banda burin da ya ɗara na isa gida na amayarwa Ummata zantukan dake cikina.
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page0⃣3⃣
Kiciɓus nayi da Anty Hasina tana fitowa daga sashin su Abba kasancewar nasu sashin ne a farko sai zaure tsakanin nasun da na Hajiya Babba, inda ɗakin yaya Majid yake. Namu sashin muda iyayen mu mata shine a ƙarshe.
Abasiya tana biye da ita goye da Abdul a bayanta. Hanya na basu suka wuce nayi wa Anty Hasina Allah ya maida ta gida lafiya, ban sa rai da samun amsa daga gare ta ba. Haka nan ban mayar da hankalina gare ta ba domin abinda dake kaina a wannan lokacin ya ɗara nata.
Umman su Salma da yake ranar girkin ta ita na iske zaune a tsakar gidan, sai faman cika da batsewa take yi. Ban bi ta kanta ba nayi wucewa na izuwa ɗakin Ummata. Tsawan da Anty Zakiyya ta doka min ya sanya ni dai-daita nutsuwata lokaci guda ina kai duba na gare ta.
"Ince dai lafiyar ki Na'ima?, za ki shigo ɗaki kamar an jefo ki ko sallama babu".
Sai a sa'ilin na tuna banyi sallama ba na dafe goshina nace"Afuwan mantawa nayi".
Banta tanka mini ba don bata cika yawan zancen ba illa ɗauke kanta da tayi daga gare ni. Hakan ya sa ni faɗin"Ina Umma?".
Ba tare da ta kallo ni ba ta ce"Tana sashin Hajiya Babba".
Ban tsaya sauraran ragowar zancen natan ba na figi jiki zan fice ta cafko hannuna"Ina za ki?, ki jira ta ta dawo suna tattaunawa ne".
Ba don rayina yaso ba haka nan na koma na zauna lokaci bayan lokaci Anty Zakiyya take kallo ni, ko kaɗan naƙi bata damar da zata jefa mini wata tambayar. Tufka da warwara kawai nake yi cikin raina waye zan fara tunkara da wannan zancen?, duk tunanin da yake kai kawo a ƙalbina Umma ita ce mutum ta farko da raina yafi samun nutsuwa akan na fayyace mata ƙudurina nason komawa makaranta. Bayan ita kuwa wata zuciyar ta kitsa mini na sanarwa yaya Majid tun shi har karatun NCE ya kammala.
Shine mutum na farko da ya ciri tuta a gidan mu, yayi zurfi a boko saɓanin mu da dukkan mu madakatan mu ƙaramar sakandiri. Su Anty Halima da Anty Maimuna kam ma basu yi ba gabaɗaya, sai dai dukkan ƴan gidan mu mahaddatan al-ƙur'ani mai girma ne da kin sauƙe bakya wuce watanni biyu a gida za'a aurar dake.
A cewar su Abba ilmin boko da ƴaƴa maza ya dace, kuma domin su aka ƙirƙire shi ba ga ƴa mace ba. Don ita dukkan rayuwarta ƙanƙani ce ba kamar su ƴaƴa maza da suke cin gajiyar kansu kuma suke riƙe da gida ba. Wannan dalilin ya sanya bama wuce ƙaramar sakandiri a karatun zamani.
Sosai na sauƙe ajiyar zuciyar da ta jawo hankalin Anty Zakiyya izuwa gare ni ta ce dani"Ke lafiyarki kuwa Na'ima?".
Har ga Allah ban ji daɗin katse mini zancen da nake yi ni da zuciyata da tayi ba. Cuno baki nayi na miƙe na bar mata ɗakin nayi komawa ta ɗakin kwanan mu tare dasu Abasiya. Ina shiga na zube akan katifar mu ina karatan wasiƙar jaki a raina, ban sanda bacci ya yi nasarar ɗebe ni sai ji nayi kamar a mafarki ana taɓo kafaɗata tare da ƙiran sunana.
A hankali na soma buɗe idona kafin na wangale su tar akan fuskar Bilkisu, ganin ta ya sanya ni sirkar da tsaki don har yanzu haushin ta nake ji akan furcin da tayi akan Anty Zakiyya. Kamar tasan zancen da nake yi a raina ta ce"Allah ya ba ki haƙuri Ummanku ne ta ce a tada ki har lokacin salla zai ƙure".
Ban ce da ita ko kanzil ba, illa miƙewa da nayi na fice nayo alwala Umman su Salma ta baje kwanuka sai rabawa ƙananun yaran abincin take yi, tare da basu zazzafar kashedi akan duk wanda ya sanye miyarsa ba zata ƙara masa wani ba sai dai yaci haka.
Alwalan na kammala na dawo ɗaki na shimfiɗa sallaya na fuskanci alƙibla na tada sallah, har na iddar Bilkisu tana zaune bakin katifar ta jawo bahon kayanta tana ta dube-duben da na gaza gano abinda take son ganowa. Addu'ata na shafe da yake cike da roƙon Allah yasa ƙudurina ya samu ƙarɓuwa.
"Na'ima dan Allah kiyi haƙuri akan abinda ya faru ɗazu kinji?".
Yatsina fuska nayi don daman nasan dole zata bani haƙuri, ko kaɗan bama iya ƙarar da wuni ɗaya ba tare da mun yi faɗa da ita ba, amma kafin mu kwanta mun shirya.
"Ba komai amma kar ki ƙara yi mini irin hakan bana so".
"In sha Allahu ba zai sake faruwa ba".
Ta faɗa tana ɗan murmusawa na bi ta da kallo kafin na ce"wai ke ɗin meye kika nema ne?".
Ta juya mini idanunta kamin ta ce"Kayan da zan saka da yamma nake dubawa, Zaidu ne zai zo na ma rasa wanin kayan zan sanya wallahi. Ki ara min wannan jar atamfar nakin mana ƴar-uwa".
Kallon uku saura kwata na watsa mata"Lalle ma kuwa in dai da kayana za ki zance, to tun wuri ki ƙira shi ki sanar dashi kar yazo don bazan bada ba ehe".
Marairaice murya tayi tare da ƙara lanƙwasata ta shiga cewar"Haba Na'ima yanzu ba za ki taimaka min ba?, kin san fa su Baba sun ce kowacce daga cikin mu ta sanar da wanda yake zuwa wajenta, in da gaske yake yi ya turo iyayensa ana gama bikin sauƙar mu ayi komai a yi a gama".
Bana ƙaunar cigaba da sauraran ragowar zantukanta don haka na miƙe na ɗauko kayan na jefa mata nayi ficewa ta izuwa ɗakin Umma. Tana zaune kan sallaya tana lazimi na iske ta ganin hakan ya sa ni yiwa kaina mazauni kusa da ita, kuma shafa addu',ar tare sannan nayi mata bayyanin yanda muka yi da Baaba Asabe na nuna mata kuɗin adaidaitar da ta bani.
Kafin na shiga in-da-in-dan yanda zan fara bayyana zancen cikina, na lura duk idanunta a kaina suke don haka nayi sauri cewa"Umma ina wannan ƴar ajin namun, Khadija Salisu wacce take zuwa wajen su Bilkisu?".
Ɗaga kanta sama tayi alamar tana son tinano ta kafin ta ce"na gane ta aure tayi?".
Taɓe baki nayi"A'a Umma ita kam ai in gaya miki makaranta ta cigaba dashi, ɗazu da ina dawowa na haɗu da ita a hanya zata makaranta. Umma yasin kika ganta sai kin ƙara raka ta da wani kallon sha'awar".
"Masha Allah hakan ma yana da kyau".
Iya abinda Umma ta furta kenan a gajarce da ya rage mini ƙwarin gwiwa na ɗan tsagaita. Kafin na aro jarumta da ƙarfin hali na yafawa kaina na ɗaura da cewar"Umma shine nima na ce in munka yi sauƙan nan, kafin Allah ya fito mini da miji ko za ki yiwa su Abba magana na ɗaura da karatun na-na-na-na nawaan".
A rarrabe na ƙarishe zancen ƙarshe tamkar yaro mai koyar magana, sakamakon kallon ƙurillan da Umma take bina dashi tunda na fara maganar har na kai aya. Hakan ya sanya ni yin ƙasa da nawa ƙwayoyin idanun ban yi gigin ɗagowa ba har izuwa lokacin da muryarta suka sauƙa a ƙofofin kunnuwana.
"Na'ima".
Ta ƙira sunana a kausashe, can ƙasan maƙoshina na amsa hakan ya bata damar ɗaurawa da"Kinfi kowa sanin al'adar gidan nan da kuma yanda ake ɗabbakata. Babu yarinyar da take wuce matakin ƙaramar sakandiri a karatun boko kuma ba za'a fara a kan ki ba, ko ɗazu zancen da muka yi da Abban ku shine idan akwai wanda yake son ki, ki bashi damar fitowa ya gabatar da kansa kafin a kayi magana ta gemu da gemu, domin sauran ƴan uwanki duk nasu samarin zasu turo iyayen su cikin sati mai kamawa. Don haka kema ki nutsu ki san wanda za ki fitar a haɗa ku tare kamar yanda kuka taso a tare".
Ko garwashin dake ƙasan tukuban gashin tsire bai kai zuciyata ɗaukan zafi ba a wannan lokacin. Idanuna suka ƙafe sam na kasa sakin hawayen da suka cika mini kurmin idaniyata, har izuwa lokacin da naji hannayen Ummata a bisa nawa cikin taushin murya take cewa dani"Na'ima kin san komai dake faruwa a cikin gidan nan, bakya buƙatar ƙarin bayani kina gani irin ƙalubale da gorin