Author : Maimuna Tijjani Iyam Category : True Hausa Novels
da nake fuskarta akan jinkirin auren da Zakiyya tayi, gashi yanzu har ana maganar auran ƙannanta amma ita har yanzu shuru. Yanzu kema idan kika ce makaranta za ki cigaba dashi sai duk ku taru ku zauna a gida abin nema ya samu ace duk na hana ku aure ko meye?, burin kowacce uwa taga ƴarta a ɗakin mijinta nima akwai wannan burin a ƙirjina Na'ima karki bijirewa umarnin mahaifanki, kar ki hana su sauƙe haƙƙinki dake kansu na aurar dake. Sannan kar ki zamto ƴa ta farko da zata yi fatali da wannan al'adar".
Sosai maganganun Ummata suka kashe mini jiki dukkan gaɓoɓina suka yi sanyi ƙalau. Tabbas nasan irin ruwar gorin da Anty Zakiyya take sha daga matan gidan mu da hakan har Umma yake shafa wasu lokutan, ba zan so dukkan mu mu zamto hakan ba, sai da na yarshe hawayen da ya fara gudu a fuskana ba tare da sani na ba, na ce"Shikenan Umma in sha Allah bazan ƙara tayar da wannan maganar ba".
"Allah yayi miki albarka".
"Amin".
Na faɗa ina miƙewa na bar ɗakin idanun mutanen da na iske a filin gidan da ya dawo kaina, ya sanya ni saurin duƙar da kaina ina goge ragowar hawayen idona. Sanda na shiga ɗakin mu na iske su Bilkisu suna jira na muzo muci abinci na ce bazan ci ba na zube akan gado.
Har aka yi ƙiran sallan magrib na kasa tsinana komai zuwa bayan isha'i masu samarin da zasu zo musu zance suka fara shiri Bilkisu, Salma da Abasiya duk suka fice suka barni ni ɗaya kwal a ɗakin. Da hakan ya bani damar cin kukana babu bai dakatar dani. Sai da nayi don kaina sannan na tsagaita, Salma ce ta fara dawowa fuskarta tamkar gonar auduga sannan Bilkisu Abasiya ce ƙarshe.
Nan Salma ke faɗin saurayinta Abdallah ya ce shi kam ma jibi iyayensa zasu zo, Abasiya da Bilkisu kuwa sati mai kamawa. Ban tanka musu ba har suka ƙarishe zancen su don basu sanyo ni a ciki ba, ban basu hankali na ba sai tashin da Abasiya tayi ta ɗauko wani leda daga cikin kayanta tana sincewa.
"Abasiya meye wannan hakan?".
Salma ta tambaya suna aikawa junansu kallon kallo ita da Bilkisu.
"Maganin mata ne ɗazu Anty Hasina ta kawo min, zan fara amfani dashi kafin lokacin biki na zama zamzam".
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
________________________________________
Page 0⃣4⃣
Sake da leɓɓe nake bin Abasiya da take ɓaro zancen ko a kwalar rigarta, balle taji kunya fayyace wasu abubuwan da ido. Ban ɗauke idona daga gare ta ba sai sanda Salma tayi wani maganar da yaso sanya notunan kaina suncewa.
"Ƴar uwa za ki san min idan naga amfanin sa na sayi, da zarar Abdallah ya turo iyayensa zan amshi kuɗin gyaran jiki".
Sosai zantukan natan ya kuma shayar dani wani ruwan mamakin, yanda Salma take amsar kuɗin wajen Abdallah kai ka ce an riga da an ɗaura auren, haka nan ma Abasiya da Sagiru.
"Lafiyarki kuma ana magana kinyi shuru?".
Sai da na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya kana na ce"Mamaki kuke bani wallahi yanda kuke zumuɗi da rawar jiki akan auren nan kamar zaku kai kanku gidan mazajen, tun kafin kai ga ɗaura auran wannan rashin ajin har ina".
Tsirkar mini da tsaki Abasiya tayi tana miƙewa ta ajiye ledar cikin kayanta inda ta ɗauko, sai da ta dawo ta zauna kana ta furta"kyaji dashi ai tunda ke a hakan kina ganin wani aji ne da ke, yarinya in za ki nutsu ki ba wa Malam Yusuf kai bori ya hau kiyi a wuce wajen".
In ma da nufin son harzuƙa ni tayi mini wannan zancen, tabbas haƙarta ta cimma ruwa don tunin naji zuciyana tazo mini har wuya. Idanuna suka ƙanƙance na shiga nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsata kafin nayi nasarar raba tsakanin haƙwara na ce da ita"Sai yau na san har yanzu baku san inda yake muku ciwo ba, in ce dai mutumin bai taɓa buɗar baki ya furta mini kalmar so ba, amma shine har kuke zancen na bada kai bori ya hau. Ke kuma Abasiya tun kafin lokaci ya ƙure miki ki san abinda kike yi, tun kafin a kai ga ɗaura auren har za ki fara shaye-shayen magungunan mata. Kinsan illar su kuwa? kinsan da meye aka haɗa su za ki hau bankawa cikinki su?".
"To don bai fito ya furta miki da bakinsa ba sai meye, ai dai naga duk makarantar babu wanda bai fahimci cewar malam Yusuf son ki yake yi ba, sai ki gaya min laifi don ke kin tunkare shi?. Kuma da kike maganar maganin mata har da kawo illar sa ban sani ba ɗin, ince dai ina ke kin sa ni yar iya".
Ban tanka mata ba naja bangona na rufu nayi kwanciya ta raba dare nayi ina saƙa da warwaran tunanai bartakai da suka ƙi barin ruhina cikin sallama.
Ban sama runtsawa ba sai bayan sallan asubahi, na komar da haƙarƙarina na wanka. Kamar a mafarki nake jiyo tashin muryar Salma tana ƙiran sunana na ware idona tar akan fuskarta.
"In ba za ki islamiyyar bane sai ki tashi ki sanar damu malama ba sai kin sanya mu latti ba".
Ban kula ta ba don sam na shafa'a da lokacin zuwa islamiyyar, na ƙyar na miƙe ina karanto addu'ar tashi daga bacci kamar yanda addinina na islama ya koyar dani.
Fitowa nayi na tarar Anty Zakiyya har tayi mini aikina na safe, don haka na wuce kai tsaye izuwa ɗakin Ummata na gaishe ta sannan na dawo nayi shiri.
Ko abinci ban tsaya ci ba don tunin Daada ta hau sababi na tsayar dasu don tsabar mulki da jin kaina. Ban tanka mata ba na fito muka wuce sashin Hajiya Babba muka gaishe ta sannan muka kama hanyar islamiyyar.
Yau nayi ƙudurin fahimtar abunda kowa ya gano saɓanin ni akan Malam Yusuf na ajin mu. Shi yake mana dukkan darrusan ajin mu, don haka na mayar da hankali yau fiye da kullum kullum.
Na lura ko yaya zai ɗago ya fuskanci ƴan ajin sai ya sauƙe ƙwayoyin idonsa a kaina duk da kaina yana duƙe kan littafin tauhidin dake buɗe a gabana, hakan bai hana jikina bani cewar idanunsa suna kaina ba.
Har ya gama darasin ya fara tambaya aka amsa masa kafin aka ɓarke da zancen batun sauƙan mu, kowa sai kawo nata shawaran da yanda taron zai kasance take yi, ni kuwa tunin na antaya cikin kogin tunanin da nayi nisan zango a cikinsa. Jin muryar malam Yusuf ta dokin ƙofofin kunnuwana ya sani saurin ɗagowa.
"Na'ima tunanin meye kike yi?, ana magana ke kinyi shuru?".
"Ba komai".
Na amsa dashi a gajarce ina basu hankalina da basu sausauta ba daga zancen nasun. Har aka gama aka tsayar da matsaya akan zamu yi ankon atamfa da kuma hijabi, sai kuma kuɗin da zamu fara tarawa wajen malam Yusuf da zamu yi amfani dasu wajen yin abincin walimar.
Ban tsuma bakina ba har lokacin tashin mu yayi, ƙarfe takwas na safe kowa ya fara haramar tafiya.
Nazo fita daga ajin Malam Yusuf ya dakatar ta hanyar ƙiran sunana dakatawa nayi tare da isowa gabansa.Yayin da ragowar ɗaliban duk suke ficewa, kashe mini ido Balkisu tayi yayin da tazo ficewa ta raɓa ta gefena ta fita.
"Malama Na'ima".
A sanyaya na amsa masa"Na'am Malam".
Sai da ya naɗe hannayensa dukka a ƙirjinsa kana ya ce"Naji ƴan uwanki duk suna cewar da sunyi sauƙa za'a haɗa da bikinsu, amma ke ban ji kina faɗin naki burin ba bayan haɗa karatunku".
Sai da na ƙara duƙar da kaina ƙasa ina ƙare ƙarfin riƙon da nayi wa jakata nace"E Malam haka ne dukkanin su bikin tare da walimar sauƙar mu za'a haɗa".
Bai bani damar ƙarisawa ya katse ni da cewar"ke kuma fa?".
"Malam ni bani da wani tsayayyan saurayin da nake kulawa a halin yanzu".
Jinjina kansa ya yi kawai ya harhaɗa littattafansa, da hannunsa ya yi mini alama akan muje na fice ya sanyawa ajin makullin sannan muka fara tafiya. Waige waige na fara yi ko zan hango su Balkisu amma ko mai kama dasu babu, hakan ya ƙara tunzura raina nayi ƙwafa da hakan ya sanya Malam Yusuf yi mini kallo ɗaya kafin ya ce dani"Lafiya kuwa?".
"Babu komai".
Sai da ya yi taƙaitaccen murmushi kafin ya ce"Sun tafi ƴan tafiyar nakin ko?".
Ban iya cewa dashi komai ba, sai ji nayi ya kuma cewar"bari na raka ki har gidan".
"A'a malam nagode zan tafi kawai,wataƙil wani uzurin ne ya kama su shiyasa suka tafi ba tare da sun yi haƙurin jira na ba".
"Rakiyar tawan ce bakya so?".
Kaina na girgiza masa, "To jira ni na ajiye littattafan nan a ofishina na fito".
Bai jira ta cewa ta ba ya nufi ofishin malaman da suke jere da juna ya murzawa nashi makulli sannan ya shiga, cuno baki nayi don har ga Allah ya shiga rayuwata a wannan sa'ilin, har ya dawo ban gusa ba daga inda ya barni tsaye.
"Muje ko".
Tafiya muka fara yi a jere har muka fice daga cikin islamiyyar, jifa-jifa nake amsa zantukan nasan da na lura baya gajiyawa da yinsu, haka nan rashin tankawa ta bai hana sa dakatawa ba.
Har cikin layin mu ya kai ni ya tsaya nisa kaɗan da gidan mu. "To na kawo ki har gida na sauƙe alƙawarin ko?".
Ya ƙare zance yana murmushi, kaina na gyaɗa masa da hakan ya bashi damar ɗaurawa da"To sai gobe a gaishe da mutan gidan".
"Zasu ji nagode".
Na faɗa ina ɗaukar miƙaƙƙiyar hanyar da zata kai ni har ƙofar gidan mu, ba tare da na karya kwana ba. Ina tafe ina ƙunci ni ɗaya har na isa gida. Ɗakin mu na nufa ina yaye hijabin dake kaina.
Salma da Balkisu suka shiga kallon juna suna ƙunshe dariyar dake cikinsu, tsaki na tsirkar mai dogon zango ina naɗe hijabina kafin na ajiye shi cikin bagon kayana na ce"kwaji dashi ai munafurcin banza".
Daga haka na fice daga ɗakin na nufi na Ummata, tun kafin na kai ga shiga nake jiyo tashin sheshsheƙar kuka, har na ƙarisa shiga cikin kwaridon ɗakin da Umma ta sanya labule ta masa tsakani da ainihin uwar ɗakin.
"Malama bazan iya cigaba da zama da Abban Walida ba, zan koma ƙauyen mu duk da kuwa bani da wasu tsayayyun dangin a yanzu, na rasa kowa nawa a rikicin ta'addanci boko haram".
Sune zantukan da suka sauƙa a dai-dai ƙofofin kunnuwana, na kuwa baza kunne cike da son sauraran ragowar zancen, Umma ce ta ɗaura da cewar"Maman Walida ko wani aure da irin nashi matsalar sannan shi mai ɗaki shi yasan inda yake masa yoyo, amma tabbas matsala irin naki tana buƙatar waliyan ku su shiga ciki, a yi masa gargaɗi da jan kunne domin tabbas ya aikata ba dai-dai ba. Kuma ya wuce iyakarsa a wani wajen aka ce namiji ya sanya hannu ya duki matarsa haka siddan babu laifin tsaye balle na zaune, abin baƙin cikin har da yi mata tsirara a kan idon yaranta wa iya zubillah".
Tunin Maman Walida ta kuma ɓarkewa da wani kukan da nake jiyo sautin sa yana ratsawa har cikin kunyar kaina, kafin tayi nasarar jawo numfashinta da yake maƙalewa a ƙirji ta furta"Malama bani da wanda zai ɗauka min mataki, bani da iyaye duk sun rasu haka nan ma dangina duk sun ƙare rikicin faɗan boko haram shi ya rabo mu da ƙauyen mu, ya sanya danginmu warwatsuwa iyayena suka rasa rayukan su. Ni kaɗai na shigo garin nan da Abban Walida na fara haɗu ya taimake ni tare da bani wajen zama a cikin gidan su, bayan na sanar dashi da kuma iyayensa labarina da musabbabin barowa ta ƙauyen mu. Ya nuna ra'ayi a kaina har aka ɗaura mana aure dashi a nan ƙofar mai unguwa ba tare da mahaifiyarsa ta so ba, tun satin farko na amarcina a gidan Abban Walida ban ƙara samun farin ciki ba, baƙin ciki da ƙunci suka ƙara samun gurbi zaman daram a cikin raina".
Sosai ta saki kukan da ya zo mata a lokacin, sai da ta tsagaita kana ta cigaba da faɗin"Malama wallahi idan naji ana cewar ana samun farin ciki da walwala gami da kwanciyar hankali a gidan miji. Wallahi gani nake yi kamar ƙarya ne ko kuma shi mai faɗan kawai ya faɗi son ransa ne, domin ni duk ban taran da wannan jerin ababaɗen a cikin gidan nawa auren ba. Rashin dangi da gata su suka haɗo suka durƙushe min rayuwata, wallahi Malama cikin ƙirjina nawa akwai damuwowi masu tarin yawa da in bake na furtawa su ba bana jin nauyin da ƙirjina yake min ya rago".
Ina iya jiyo tagwayen ajiyan numfashin da Umma ta sauƙe kafin ta kai ga furta"Maman Walida tabbas wannan lokacin za ki ga gatanki, domin kina da Allah sarki da ya haramta zalumci akan kansa kuma ya sanya ta haramun a tsakanin bayinsa. In sha Allah da zaran Malam ya dawo zan faɗa masa komai sai kuje wajen mai unguwa ayi komai a gabansa, idan ba'a samu sulhu ba kuma bai amshi laifinsa ba ko takardarki ne sai ya bak......".
Saurin katse Umma Maman Walida tayi cikin sautin muryarta dake bayyanar da taci kukan har ta gaji take faɗin"A'a malama ko meye za'a yi banda saki, wallahi in ya sake ni bansan inda zan tafi ba a yanzu bani da wajen zuwa ƙauyen namun ma ba kowa bane ya koma".
Rawar da ƙafafun suka fara yi suna barazanar gaza ɗaukar nauyin gangar jikina, ya sanya ni saurin jansu na fice izuwa namu ɗakin na kuwa yi sa'a babu kowa.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".
Shine abinda yayi nasarar fitowa daga bakina, ina ƙara jinjina girman lamarin Maman Walida tun tasowar mu muke mata kallon mahaukaciyar da ta daɗe da rasa hankalinta. Babu irin aikin wahalar da bata yi domin ciyar da kanta, mijinta da ƴaƴanta har ma da iyayen mijin, sai da muka girma muka gane ba mahaukaciya bace tsabar talauci da ƙangin rayuwa ce ta mayar da ita hakan. Wayyo MATAN AREWA waye zai taimake mu?, kaf AREWA mun rasa.
MATAN AREWA
©Maimumah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 0⃣5⃣
Na daɗe a haka har sai da naji kaina yana sarawa da matuƙar ƙarfi, kafin na yunƙura dafe da goshina da nake ji tamkar ayi mini ajiyar wani abun mai nauyi a tsakiyar kaina. Sosai lamarin Maman Walida yake nuƙurƙusan rai da ruhina, duk da ba yau ne karo na farko Umma take samun ziyaran irin waɗannan matan ba ko wacce da iriyar nata matsalar.
Amma sai naji wannan ta fi ko wanne riƙe mini zuciyata, Ta ina zan fara kawo gyara a cikin al'ummata?, Wata zuciyar tayi saurin raya mini ta hanyar karatu ne kawai haƙata zata cimma ruwa, Babban burina raina tun ina ƴar ƙanƙanuwa nake da sha'awar zamtowa ƴar jarida, haka nan marubuta suke burge ni fiye da yanda kalmomin da baki kan iya furtawa.
Ƙarƙarfan ajiyan zuciya mai matuƙar sauti, na sauƙe wata zuciyar tana cewa dani yaudaran kaina kawai nake yi. Miƙewa nayi na fito waje na wanke fuskana da nufin ko zan ji sauƙi sarawan da kan nawan yake mini. Idona sam na gaza kawar dashi daga ƙofar ɗakin Umma, kana nan zuciyata take kwaɗaita mini son sauraran ragowar zancen Maman Walida.
Miƙewa nayi zan koma ɗaki sallamar yaya Majid suka a kunnena. Amsawa nayi sannan na gaishe shi ya amsa. Ya ce na kawo masa abincinsa ɗakinsa, ɗakin girkin na nufa da zummar ɗauko masa naga babu kwanon abincinsa.
Girkin Ummansu Anty Kubra ce, don haka na ɗauki hanyar ɗakinta bakina ɗauke da gajerar sallama, sai da nayi baki uku ina shirin yin na huɗun aka amsa.
Gaishe ta nayi ta amsa mini cikin halin ko in kula, kana na ce"Umma daman abincin yaya Majid ne ya ce a kai masa, kuma naga kamar kin manta ba ki zuba masa ba".
"Ba mantawa nayi ba abincin ne bai isa ba shiyasa na zubawa ƙananan yaran".
Tana gama faɗin hakan ta sakin labulen ta koma ɗakin, yanda muka yi da ita naje na sanarwa yaya Majid, bai wani damu ba domin ko ƙananan yaran gidan mu sun san halin Umman su Anty Kubra.
Sashin Hajiya Babba na nufa, kamar kullum na iske ta tana sallar walaha, yiwa kaina mazauni nayi gefe da ita kaɗan har ta iddar da sallan.
"Takwara kece, har kun taso kenan?".
"E wallahi Hajiya mun taso".
Daga haka nayi shuru ina wasa da yatsu hannuna, na rasa yanda zan fara fuskantar Hajiya da wannan zancen, sosai naji ya yi mini nauyi akan harshena, domin nima kaina na san nazo da sabon abu a cikin ahalin namun.
Ban sa ni ba ko fahimtar yanayina, ne ya sanya ta cewa dani"Lafiya kuwa? ko wani abun kike son faɗa?".
"Hajiya wata magana ce ta kawo ni".
"Ina jinki Na'imatu".
Gyara zama nayi ina lanƙwashe ƙafafuna waje guda kana na ce"Hajiya sauƙar mu sai matsowa take yi, kamar yanda iyayenmu suka zarta za'a haɗa walimar sauƙar da bikinmu, gashi ni kuma har yanzu Allah bai fito mini da miji ba. Shine na ce ko za ki yiwa su Abba magana ko makaranta ne na kom...".
Ƙarƙarewa zancen tayi ta maƙale mini a hanyar maƙoshina, sakamakon kafe ni da ido da tayi. Ƙasa nayi da ƙwayoyin idona ina sauraran lugudan dukan tara taran da ƙirjina yake yi, ɓal ɓal ɓal.
"Na'ima".
Cikin rawar murya na ce"Na na na'am".
Sai da ta sauƙe numfashi"Na'ima kin zo da baƙun lamari mai girma zuwa yanzu bana ce da ke komai ba. Amma tabbas za ki fuskanci ƙalubale shawarata gare ki shi ne, ki nutsu ki fidda miji kafin wa'adin da iyayenku suka ɗebar muku ke da ƴan-uwanki ya cika, domin tabbas babu abinda zai dakatar da auren nan". Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauƙe, duk yanda naso dauriya da ƙarfin hali gami da son ƙarfafa kaina, ta hanyar matse ruwar ƙwallar da suka wadaci kurmin idaniyata. Lamarin faskara ya yi sai da ƙwallar suka fara gudu gefen da gefen fuskana.
"Ke macece Na'ima aure shine abinda yafi dacewa dake, karatu na ƴaƴa maza ne domin sune suƙe riƙe da iyali kuma muke ƙarƙashin kulawar su, ki zamto macen ƙwarai ga mijinta abar alfahari ga ƴaƴanta".
Sosai naji bakina ya yi mini nauyi ta yanda naji ko kalma ɗaya bazan iya furta mata ba, kaina kawai nayi nasarar ɗaga