Author : Billyn Abdull Category : Home Of Novels
haka??.
Tai saurin dafe bangon wani shago danjin tana niyyar faďuwa, ina ruwanka da inda zani nikam banason yawan shishshigi gsky,, amamakinta saitaga yayi murmushi tareda haďe hannuwansa a waje guda yana faďin sorry madam, amin afuwa natsaya ne narage miki hanya naga kina bu'katar hakan,, harararsa tayi tana wani lumshe idanu irinna 'yan maye, to idan banasofa?, sai incigaba da ro'konki harki amince kishiga motata beauty.
Murmushi tayi saboda jindaďin sunan daya kirata dashi, ta ce, "to muje ALLAH dai yasa karka sayar mini dakai,, buďe mata motar yay tashiga yana faďin ai ko sayar da kai nakeyi bazan saida na beauty ba irinki, dariya tayi tana faďin maza akwai daďin baki.
Tada motar yay sukabar titin batareda yayi maganaba.
Yajuyo yaďan kalleta yayinda sukayi nisa, beauty ina muka nufane??, taďan gyara zamanta ta ce, "muje zan rin'ka nuna maka hanya, okey yafaďa yana murmushi,, lafiya lau ta nuna masa hanya harzuwa gidan falmata yayi mamaki kwarai da gsk, azatonsa yanda take abigennan bazata iya komaiba, tafito tana masa godiya, ya ce, "yanzu nan haka zamu rabu ko number bazaki baniba??, taďan ta6e baki haba malam daga haďuwa yau saina ďauki no ďina nabaka??, ya murmusa A'a beauty kindai manta yauce haďuwarmu ta biyu fa, aikuwa na cancanta abani, kinga idan kinbani number ki duk sanda kika bu'kaci zuwa wani waje sainazo nakaiki, kinga kinsamu direba daga sama kenan.
Dariya sosai tayi tareda mi'ka masa wayarta tana faďin sarkin wayo gashi kaďauka, yauwa ngd sosai yafaďa yana kar6ar wayar tata mai 'kyawun gsk, number sa yasaka sanan yakira tata yay save ďin tasa atata sanan yayitata atashi,, sallama sukayi yaja motar yatafi suna ďagama juna hannu, itama saita shige gidan falmata tana murmushi, jinta take cikin wani farinciki mara musaltuwa.............
Ku biyomu.
©2017
Hikayarmu!!!!!!.
abba gana
&
bilyn Abdul
[16/02 11:48] bilyn Abdul: KUKAN KIRCIYA........
NA
MUH'D ABBA GANA
&
BILKISA IBRAHIM
{☆Bilyn Abdul☆}
Page1⃣1⃣&1⃣2⃣
Babu daďe tadawo hannunta ri'ke da ledar indome, sanda tadawo iya abu ta tashi dan haka tashige ďakinta itama, tana tunane2 yanda iya abu ta ruďe lallai awai wata magana a'kasa,, amma zatayi 'ko'kari tonota insha ALLAHU.
Hakadai tacigaba da tura indomi ďin badan tana mata daďiba, bayan tagama ci tafita wanko hannunta,, harta kai gab da 'kofa zata shige saitayi saurin jan birki danjin ana magana 'kasa2 a ďakin iya abu, ta matsa ahankali gefen 'kofar baba taji yana magana cikin ruďewa.
Abu!! data tanbayeki mikika cemata??.
Why malam bance mata komaiba saboda matu'kar razana da maganar ta sakani, iya abuce ke magana cikin rawar murya.
Baba ya ce, "lallai wannan magana takai arazana, to wai ya akayima wananan yariyar harta iya wanan magana??, kodai Nasuru ne ya kitsa mata hakan??.
Kai malam kaima kasan nasuru bazai faďaba, dan yanama abuja, nasan Nasuru bazaiyi irin wannan kato6ararba.
Baba ya sauke numfashi tareda yarce gumin daya wanke masa fuska, ahankali ya furta lallai idan mukayi sakaki tofa allura zata tono garma..........da sauri iya abu ta katseshi haba malam daina yimana wanan fatan mana, ai har abada babu mai tono mana daďaďďen sirrinmu, wanda dagamu sai ALLAH saikuma hajiya.
Baba ya jinjina kai, to ALLAH ya tabbatar mana zainabu.
Tunda Ameeda ta'iso wajen tsaye take kamar gunki, zuface keta ambaliya adukkan sassan jikinta, maganganun su iya abu sun rikita mata kwakwalwa, tarasa yanda zata fassara zancen nasu dan ta fahimta.
Da sauri tashige ďaki danjin motsin babanta zai fito, ta faďa saman katifarta tana fidda numfashi, afili ta furta wanne irin 6oyayyen sirrine su baba basa son nasani, minene ma'anar allura zata tono garma idan sukayi sakaki???, miyasa suke zargin kuma Nas shiyya sakata wanana tambayar???? Shin wai miya haďa Nas ma da sirrinsu??, kodai Nas yasan wani abu gameda family ďinsu ne???,, tadafekai tana jijjigashi kamar mai shirin hawa bori, hawaye suka fara silalowa akumatunta, itakam tana kallon rayuwa a baibai, lallai akwai mayan 'kalubale dake bibiyar rayuwarta ta baďini data zahiri,, yanzu tawace hanya yakamata tabi domin binciko boyayyen sirrin iyayen natane dasuke 6oye mata akan aslinsu da tushensu???, da sauri kanta yake sarawa kamar zai faďo 'kasa.
Jakkarta ta raruma tafara zazzagewa amma bataga abinda take nemaba, ta koma cikin kayanta, cikin sa'a tayi tozali da kwalbar sirob guda uku, da hanzari take 6alle murafan ta juye maganin abakinta, ta yarda kwalaben gefe dan bai ishetaba, kwalaben ďazu ta đauka tana 'kara kalacewa anan barci yay gaba da ita.
WASHE GARI.
Da'kyar taiya tashi tayi sallah tayi wanka tana cikin shafa mai kiran falmata yashigo ta ďauka murya aďashe tana faďin falmata ykk??.
Lfy lao Ameeda kema ykk?, ina lfya, dama sonake kizo kirakani wani waje dan ALLAH, okey babu damuwa dama shirin zuwa gidanki nakeyi,, to shikenan ina saurarenki.
Bayan wani ďan lokaci tafito saye cikin atanfa zani da riga ta yafa mayafi, atsakar gida taga iya ta gaisheta sanan ta ce, "zanje gidan falmata saina dawo.
Cikin rawar jiki iya tace to saikin dawo Ameedan baba, batabi takantaba tafice daga gidan.
Koda taje sai suka nufi inda zasu, gidan wata 'kawarsu sukaje sukai mata ALLAH yasanya Alkairi, dan tayi aurene itamadai irinsu ce ALLAH ne yay mata gyaďar dogo tasamu miji tayi aure.
Daga nan asibiti suka nufa domin yin dubiya, bayan sungama dubiya suka fito, arikice Ameeda taďago domin ji tayi karo da mutum lokaci ďaya suka ďago suna kallon juna, ahankali tafurta yi ha'kuri dan ALLAH.
Ko motsi baiyiba saboda shiga wani matsanancin ruďani, kallonta yakeyi ko 'kyafta ido bayayi, falmata taja hannunta suka bar gurin................
Ku biyomu.
©2017
Hikayarmu!!!!!!.
abba gana
&
bilyn Abdul
[19/02 13:21] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA.......
NA
MUH'D ABBA GANA
&
BILKISA IBRAHIM
(☆bilyn Abdul☆)
Assalamu alaikum.
muna mi'ko gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyanmu aduk inda kuke,, kuyi ha'kuri dabaku pages ďai2 damukeyi kullum, littafin namu gajeren labarine,, insha ALLAHU muna gab da kammalashi,, mungode da 'kaunarku garemu,,, luv u oll.
Page1⃣7⃣&1⃣8⃣
..........jikinta sai rawa yakeyi cikin kuka take bashi ha'kuri dan bataji daďin yanda tayi masa 'karyaba, kayi ha'kuri yayana wlhy badan banida gskya yasa na 6oyemaka sirrinaba akwai wasu dalilai masu yawa,, amma ina ro'konka da ka gafar ceni, insha ALLAHU wanan shine nafarko na 'karshe dazan yimaka 'karya akan abinda yashafi rayuwata, ta ďago tana kallonsa sai taga shikuma hankalinsa yana kan babanta dake tsaye a'kofar gida yana cin goro.
yayana!! tafaďa cikin sanyin murya, ahankali yajuyo yana kallonta cikin in ina ya ce, "beauty waye wancan??, babanane tafaďa cikin 'kwarin gwuywa.
Tafďijan yafaďa azuciyarsa, Ameeda ta ce, "koshima kasanshi ne??, A'a yafaďa a ta'kaice amma idanunsa nacigaba da kallon malam dauda.
Ameeda tabuďe motar tafice tana faďin to sai mun haďu gobe ko?, okey karki damu kijirani agida insha ALLAHU 'kar fe biyu zanzo miki da abu uwan mamaki, kinsan masu iya magana sunacewa KUKAN KURCIYA JAWABINE.......Ameeda ta'karasa da faďin "mai hankaline yake ganewa yayana, murmushi yayi tareda mi'ka mata dubu biyar ya ce, "sai kinjini, okey bye tafaďa tana ďaga masa hannu.
Koda tashige gida yadaďe zaune amota yana karema malam dauda kallo, daga baya yafice yabar anguwar, gida yaje yay wanka yanufi filin jirgi sai abuja.
Da wuri ya isa yauma mutanen gidan sunyi farincikin zuwansa, bayan yaci abinci ya huta, suka haďu afalon daddy, daddy ya ce, "Muzzaffar kace mana a kwai magana amma munjika shiru.
Muzzaffar ya murmusa, tabbas daddy akwai magana, dan yau na'kara gano abin mamaki kamar yanda na faďa maka awaya, inaso ka shirya mana tafiya kano muduka harda hajiya babba.
Bangane mikake faďaba Muzzaffar???, daddy zaka gane amma sai goben.........momy ta katse musu zancen da faďin a'a muje mu kaďai idan komai ya bayyana sai azo har inda take, kasan halinta sarai, kuma batason zuwa kano da kowa.
Gsky ne daddy yafaďa, yanzu saimu kwana cikin shirin zuwa kano insha ALLAH.
Washegari sukai 'kaura zuwa kano, dayake jirgi sukabi har saida suka huta agidan muzzaffar, kamar yanda yay mata al'kawari 'karfe biyu suka iso anguwar dan masallataima sunata sallar karfe biyu, amotar suka zauna babu wanda yafita sai muzzaffar, kansa tsaye yashiga cikin gidan saboda anyi masa iso, tunda yashigo iya abu tayi mutuwar tsaye, cikin in ina take nuna Muzzaffar Ameeda ina kika san wanan??.
Ameeda dake tsaye tana kallonsu ta ce, "iya Shinefa Muzzaffar ďin danake gaya miki, kumafa kece kikace ya shugo, ganin ta rikice da ganinsa sai Muzzaffar ya basar ya tsugunna har 'kasa yana faďin mama ina yini?, cikin rawar baki ta ammsa, baibi takantaba ya haye tabarmar da'aka shinfiďa masa ya zauna.
Ana cikin haka baba ya shigo gidan shima yarikitu da ganin Muzzaffar amma sai muzzaffar ya fuske ya'ki bada kofa koďaya ta alamun yasansu, nanma rissinawa yayi ya gaida baba, atsorace ya amsa tareda faďin yaro mike tafe dakai ne???.
Murmushi Muzzaffar yayi ya ce, "baba nidai sunana Muzzaffar nafito ne daga 'kasar kamaru, ALLAH ne ya haďani da Ameeda naji kuma inasonta, wani ďan aikine yakawoni Najeria saidai bansan ko inaba bankuma san kowaba akasar sai Ameeda dana fara karo da ita.
Ajiyar zuciya baba da iya abu suja lokaci ďaya itadai Ameeda duk kanta a ďaure yake, tana mamakin miyasa yayi 'karya??, bayan ita yafaďa mata iyayensa suna abuja.
baba ya ce, "yaro kana nufin kaiba ďan kasarnan bane??, eh hakane baba, niba ďan nan bane, domin a kamaru ďinma ba anan na girmaba a london na girma, lokaci ďaya suka washe baki iya abu ta ce, "masha ALLAH aimu wlhy sai kayi mana kama dawani damuka ta6a sani.
Ayya aidama haka rayuwa tagada mama, saikiga baka haďa komai da mutumba amma kuna kama da juna, nima haka mutane sukecewa ina kama da Ameeda sosai tamkar jini ďaya muka fito????.
Idanu suka zazzaro tareda haďa baki wajen faďi kuma???.
Ya ce, "ai ikon ALLAH kenan kawaidai kamace, ya za'ayi muzama jini ďaya bayan tana Najeria ina kamaru koma nace london, wanan shine karo na farko dana ta6a zuwa 9ja.
Ajiyar zuciya suka 'kara saukewa sukace eh gskyar ka kuma.
Ya ce, "to nazo neman aurenta ne indai zaku bani, amma inaso asadani da ainahin iyayenta.
Iyayenta kuma???? suka haďa baki wajen faďa suna kallon juna.
Muzzaffar ya ce, "eh ina nufin kanin baba ko yayansa tunda sune masu ďaura aurenta.
Eh kayi gaskiya yaro suka faďa suna sauke ajiyar zuciya.
Muzzaffar yasake faďin saidai abinda yabani mamaki ko kaďan bakwa kama da ita anya kuwa ba sato................da sauri sukace satowa kuma yaro??????, nanama suka faďa suna dafe 'kirji.
A'a bahaka nake nufiba, ina nufin kota sato kamannin wanine a danginku???.
Ohhhhhh yaro kace wani abu, tana kamane da kanwar kakar baban babana ce.
Ayya ammadai tayi 'ko'kari data ďakko gida, dan ance duk wanda yabar gida gidafa ta barsa, saidai inane asalin 'kauyen naku, dan can yakamata akai kuďin aurena.
Kallon juna sukayi Yaro kauye kuma???,,, suka faďa suna haďa baki.
Eh baba wai ina nufin asalinku, dan inaso na auri 'yar dangi mai asali kuma.
To to to wannan magana da girma take yaro.
Miye girmanta baba???, kodai dangin kune a abuja dan naga kamarsu da Ameeda, tayi kama sosai dasu.
Abuja kuma yaro???? suka faďa kamar zasuyi kuka.
A'a kukwantar da hankalinku nifa nayi muku hannunka mai sandane, yanzu ina tareda iyayena zasu shigo idan kun basu izini dan sunaso ku gana kamar yanda al'adar kasarmu kamaru take kenan, dan gobe idan ALLAH yakaimu zamu juya kamaru.
To sushigo mana bari asaka musu tabarma.
Duk abinnan da akeyi Ameeda tana zaune kamar gunki tana kallon alamomin rashin gsky kuru kuru a idanun iyayennata, lallai yau akwai abubuwan mamaki masu kamada almara agidannan, ita harma tarasa yanda zata fassarasu.
Shin kodai ya Muzzaffar yasan wani abu gamedasune??, miyasa yakema iyayenta wanana tambayoyin ma wai??, miyasa sukan rikice aduk lokacin da yay musu tambayar ne???, gaba ďaya takula sun fita hayyacinsu..
Amota ya tarar dasu momy, ya kallesu yana murmushi, dady ina fatan kunajin duk yanda mukayi ta waya???, kwarai kuwa ďan kirki muna jinku, inagadai dukkan hasashenmu yazama gasky kuma ALLAH yakawo mana 'karshen damuwa ta shekara ashin da biyu dasuka wuce.
Murmuahi yayi To ALLAH ya tabbatar iyayena, yanzu kamar yanda kukaji sunce ku shigo.
To suka faďa suna fitowa.
Duk wanan tanbayoyi da Muzzaffar yakema su iya abu wayarsa a kunne take, dankuwa kiran daddy yayi ya ajiye wayar komai sunaji har aka gama.
Da sallama suka shiga gidan, iya abu da baba suna zaune yayinda Ameeda take zaune a inda suka barta kamar dutse.
Tunda suka rangaďa sallama suka shigo kallo ya koma sama, dominkuwa tuni su iya abu sunyi mutuwar zaune, ko yatsun hannunsu sun kasa motsawa, Ameeda ta mi'ke zummbur dan tun shigowar muta nen biyu gabanta yake dukan uku2 tamkar zai fito waje, jinta take tamkar ba'a duniyaba, sai kawai ta yanke jiki tafaďi awajen batareda daliliba.
Da gudu Muzzaffar yayi kanta yana kiran beauty! Beauty!!!. Ina beauty ta suma, jiki na rawa momy ta 'karaso wajen tana jijjiga Muzzaffar da Ameeda dake jikinsa.
Acan kuwa tuni fitsari ya ji'ke wandunansu iya abu da malam dauda, tuni sunshiga cikin kogin kwadamin ruďani da kiďima, lallai yau kashinsu ya bushe, lallai yau itace ranar tonan asiri, lallai yau itace rana dubu ta 6arawo ďaya kuma tak tamai kaya, lallai yau itace rana mai firgitarwa, lalai yau itace rana ta cizon yatsa da ambatar dana sani.
Lallai yau itace ake kira da 'karshen tuka tuki tikkk.
Adai dai wanan lokacinne kuma Naseer yashigo gidan ko sallama babu, tofa shimafa mun lura 'kamewa yayi atsaye tamkar bishiyar da aka dasa awaje ďaya, gaba ďaya zufa ta gama wanke masa dukkan sassan jikinsa, jiyake tamkar ya saki kashi atsaye, lalaikam idan zomo na yawo tofa kerema yana yawo tabbas wata rana za'a haďu, yau itace ranar zadata girgiza mutane masu ďunbin yawa, wasu zasu rasa daula, wasu zasu rasa aure, wasu zasu rasa aiki, wasu zasu rasa mutunci, wasu zasu rasa girma, wasu zasu bakunci gidan yarinema, tofa tabbasa Nas yana ganin kila yana cikin masu ziyartar gidan yari, dan yau ranace mai kamada ranar hisabi amma na duniyyyyyyyya.
Tofa wai miye sirrin wanan rikita2ne???, wai miye abinda ake tsoron yafarune??, wai miye dalilin shigar mutane masu yawa cikin ruďani haka?????, miye tsakanin su muzzaffar da Ameeda ne???, miye tsakanin Nas dasu muzzaffar ne???, waishin ma waye muzzaffar???, waye Naseer???, suwaye su iya abu?????, wacece Ameeda??????, miye matsayin momy & daddy awanana bada 'kala???, miye kuma ya haďa wanana ahali akarkashin runfar rikici ďayane??????????...
Mukaďaine masu baku wanana amsar, dan haka ku kasance damu........................
Ku biyomu.
©2017
Hikayarmu!!!!!!.
abba gana
&
bilyn Abdul
[19/02 13:31] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA........
NA
MUH'D ABBA GANA
&
BILKISA IBRAHIM
(☆bilyn Abdul☆)
Page1⃣5⃣&1⃣6⃣
.......Tunda tashiga falmata ke binta da kallo dan ganin wata fara'a mara kangado datakeyi, ta zube saman kujera tana lumshe idanu dan barcin bai gama isartaba, falmata data kasa ha'kuri ta ce, "Ameeda wai miye sirrin farin cikinki ne???.
Murmushi Ameeda tayi tana kallonta hummm 'yar uwa yaumafa sake haďuwa da guy ďinnan nayi, shimane ya kawoni har 'kofar gidanan.
Falmata ta saki baki tana kallonta, kai haba??, ALLAH kuwa, zama falmata tayi kusada ita tana faďin to ya akayi yasan gidanku??, k ahanya ya ďakkoni yayin zuwana nan gidan, kai kawai falmata ta jinjina ta na faďin to ALLAH ya jishemu alkairi.
Haka rayuwar tacigaba da gungurawa yayinda da Muzzaffar yashiga rayuwar Ameeda sosai, koda yaushe suna ma'kale da waya, ko kuma su haďu awani wajen dan bata so Nas yagane tana tare da wani, cikin hikima yake janye ra'ayinta daga barin shaye2, idanma tasan zasu haďu bata shan komai kwata2, yauma tana zaune aďakinta sai wayarta tafara ruri, takai hannu ta ďauka dan ganin sunan Muzzaffar, cikin muryarsa mai daďi ya ce, "assalamu alaiki beauty, saida tayi murmushi sannan ta ce, "wa'alaikassalam yayana, ykk?, ya aiki??.
Alhmdllh wlhy, yanzuma gani ina shiri tashi daga aikin, kefa kina inane??, gabanta ne yafaďin dan batasan yazata cemasaba, tunda suka haďu baisan inane gidansuba kullum a hanya suke haďuwa ko gidan falmata, shi azatonsama nanne gidansu, yaďan yi gyaran murya yana faďin yadai beauty??? koba'kya gidane??.
Ajiyar zuciya taja ta ce, "ina gida zakazo ne??, eh indai