KUKAN KURCIYA COMPLETE DOCUMENT by Billyn Abdull.txt

Author :  Billyn Abdull Category :  Home Of Novels

Chapter   4 / 6

9K to 12K   out of 15K words

kina bu'katar ganina sainazo??, sassanyar dariya tayi aini kozaka kasance dani koda yaushe zanso haka, amma yanzu kaga kayi aiki kagaji dan haka kaje gida kayi wanka kaci abinci ka kwanta ka huta.
Murmushi yayi tamkar yana gabanta, murya 'kasa2 ya ce, "ina gwauro yaga duk wanan gatan beauty!!?, dariya Ameeda tayi sosai, wlhy kanada abin dariya, yanzu dakanka kake kiran kakanka gwauro??.
Shima dariyar yayi, to aii gsky ce beauty, kinga da inada mata da yanzu kafin na isa gida an haďamin ruwan wanka, idan nayi kuma ga abinci yana jirana, kilama saboda gata abani abaki, to amma yanzufa?, dole duk abinda nalissafo nizanma kaina.
Ameeda ta gyara kwanciyarta to yayana kadage kayi auren mana musha biki, kaga idan kayi aure to koda yaushefa ina gidanka ina taya aunty na aiki da hira kafinkadawo.
Tofa yafaďa yana murmushi, beauty to idan kuma kece kika zama matar tawafa???, ido tazaro da sauri kamar tana gabansa, tabďija yayana bar wananan zance kaji yanzu dai bari nabarka sai anjima,, kafin ya farga ta kashe wayar gaba ďaya, yayita kira amma akashe, daga baya saiya ha'kura yanufo gidan falmata kawai.
A 'kofar gidan falmata yay fakin yasamu yaro ya ayka dan akira masa Ameeda, shigar yaron babu daďewa suka fito da falmata, saida ta gaisheshi sanan ta ce, "ai tana gida yauma batazo nan gidanba kwata2, cikin mamaki yake kallonta ya ce, "dama tanada wani gida bayan wannan??.
Lah bata ta6a gaya makabane, ainan gidanane nikuma 'kawartace, kai ya girgiza to shikenan, dan ALLAH kozaki iya yimin kwatacen gidanne??, babu damuwa ai bawani nesa baneba, kwatance tashiga yimasa, ta ce, "damma inada ba'ko dana rakaka kawai.
Babu damuwa yafaďa yana tada motar, bankwana yay mata yatafi.
Yazo gaf dazai fita layin ya haďu da motar Nas, bin motar yayi da kallo harta shige wanan ai Naseer ne mikuma yakeyi anan anguwar??, kardai ďan isakan yaronnan yazo yayta 6ata 'ya'yan jama'a a garinnan??.
Da yayi tunanin yabi bayansa saikuma yafasa ya hau babban titi yanufi gida, yama fasa zuwa gidansu Ameedan kenan.


Bayan kamar kwana biyu da faruwar hakan saisuka sake haďuwa da Naseer a anguwar, amma shi Nas baiga Muzzaffar ba, Muzzaffar ya ce, "Beauty dan ALLAH kinsan wancan guy ďinne??, cikin damuwa ta kalleshi ta ce, "miyasa kamini wanan tambayar ne??, saboda naga kina ganin shigowar motarsa kika kwantar da kujerar baya, kuma kin matu'kar shiga ruďani.
Ajiyar zuciya taja tareda zubo da hawaye daga idanunta, ta ce, "karka damu dashi, a'a beauty dolene nadamu dashi dominkuwa nasansa nasan koshi waye, irikice take kallonsa cikin tsoro kuma, a ina kasansa dan ALLAH????.
kansa ya maida ga titi yana faďin kifara sanar dani ala'karku sanan saina sanar dake nima,, cikin rawar baki tace shinefa saurayina danake gaya maka ďinnan, hazbinallahu wani'imar wakil yashiga ambata, arikice ya ce, "Ameeda yau inaso ki kaini ainahin gidanku.
Nanma cikin tsoro take kallonsa ta ce, "badaga gidan namu mukeba yanzu,, kansa ya girgiza tareda yin fakin agefen titi, juyowa yayi sosai yana kallonta, Ameeda banan bane ainahin gidanku, nan gidan 'kawarkine falmata, amma idan kin bani dama yanzunnan zan kaiki ainahin gidanku inda mom & dad naki suke, yana gama faďa yatada motar.
Gaba ďaya zufa ta wanke jikin Ameeda, tanajin kunyar 'karyar datayi masa gsky,, amma ba laifinta bane rayuwace tamaida ita haka.
Tiryan2 yaringa bin hanya kamar yata6a zuwa babu indà ya tsaya sai'a 'kofar gidansu Ameeda, yajuyo yana kallonta beauty ga gidanku nan.................


Ku biyomu.
















©2017




Hikayarmu!!!!!.
abba gana
&
bilyn Abdul.
[24/02 17:32] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA..........








NA
MUH'D ABBA GANA
&
BILKISA IBRAHIM
(☆bilyn Abdul☆)








Page1⃣9⃣&2⃣0⃣


.........Bayan an yayyafama Ameeda ruwa ta farfaďo, ya Muzzaffar ya zaunar da ita, ruwa dady ya mi'ka mata tasha tana hawaye, cikin kuka ta ce, "ya suwaye waďannan dan ALLAH???.
karki damu 'kanwata ashirye muke damu sanar dake komai, dan haka ki kwantar da hakalinki.
Dubanta ta maida gasu iya abu dake durkushe sunata rawar jiki harda kuka, ahankali ta matsa kusadasu tana faďi iya miyake faruwane agidabnan??, shin kunsansu ne?? Idan kun sansu suwaye su??.
Babu wanda yabata amsa acikinsu saima rawar jikinsu dake 'karuwa, ta ďauke kai daga garesu ta maida kan Nas dake tsaye shima tamkar gunki daka gansa kasan arikice yake, jira kawai yake yasami hanyar dazai arce amma babu dama, dan tuni polis sun dunkare 'kofar gidan.
Waya daddy yayi tareda faďin kushigo ku kwashesu dan yanzu zamu koma abuja acan zamuyi komai daya dace.
Okey sir suka faďa suna ďirarowa cikin gidan tamkar tururuwa, tamau aka dam'ke iya abu da malam dauda da Naseer aka yayibesu sai mota, 'kofar gidan cike yake da al'ummar annabi sai kallo da dariya akema su iya abu, su mutane azatonsu wajen kwaďayin 'yarsu ta auri mai kuďi suka kwaso wanda yafi 'karfinsu, mota aka cimimiyasu suna kuka da ro'kon ayi hakuri babu wanda ya sauraresu saima wani ďansanda daya kwalama iya abu bakin bindiga a 'kafa, tako daddage ta kwala ihu.
Acikin gidan kuwa tuni Ameeda ta ruďe tana kwasar kuka dakyar suka lalla6ata tayi shiru, momy ta ce, "idan kinada wani abin bu'kata ki ďauka dan daga nan har abada bazaki sake zuwa gidanan ba, cikin mamaki Ameeda take kallonta amma babu damar tambaya dan tana tsoron kar itama asaka 'yan sanda cimimiyar ta yanzunan.
Kayanta ta haďo dady yakama hannunta haba baby indai sutturace abinda kike bukata kawai to kibarta mu tafi komai kike bu'kata zamu yimiki da izinin ALLAH kinji.
Kai ta jinjina tareda ajiye jakkar kayan ta ďauki ďan abinda ba'a rasaba suka fice, har yanzu mutane suna tsaytsaye a kofar gidan dan su iya abu ana motar 'yan sanda, suna shiga motar polis suka take musu baya sai abuja garin naira.
Koda suka iso 'yan sanda wucewa sukayi dasu iya abu polistion sukuma suka wuce gida.
Aljannar duniya ameeda tafaďa azuciyarta, gaba ďaya tazama 'yar 'kyauye, taga gida tamkar baza'a mutuba, saida momy takamata ta zaunar sannan, mizzaffar sai dariya yake mata, tana kallonsa amma tayi burus dashi tanabin ko ina da kallo, ruwa 'yan aikingidan suka kawo musu tareda kayan motsa baki, ďaya acikin 'yan aikin ta rissina tana faďin momy akawo abincine??.
Momy ta girgiza mata kai, a'a magajiya abarsa saimunyi wanka sanan, to hajiya afito lafiya.
Muzzaffar yami'ke yana faďin kunga nayi nana.
Momy ta ce, "to saura kuma ka kwanta barci, kanayin wanka kazo kaci abinci, karki damu momyna kibani minti talatin.
Kai ta ďaga masa tana dariya, saida ya haye samansa sanan ta kama hannun Ameeda tana murmushi babyna zomuje kiyi wanka kinji, itadai ameeda tamkar makaho da ďan jagora haka takebin momy har zuwa ďakinta.
Yasalam ameeda tafaďa azuciyarta, bedroom ďin yatafi da imaninta wani abin kallo sai a bathroom tamkar wajen cin abinci, bayin ya haďu, itadai haka tayi wanka tafito, saimada momy tanuna mata yanda zatayi sanan.
Bayan futowarta momy ma tashiga wankan, bayan ta nuna mata kanayan kwaliya dakuma kayan sawa data ajiye mata akan gado.
Tashirya tsaf cikin jar doguwar rigar mai adon fararen duwatsu abinka ga fara tayi mata ďas kamar dan ita akayi.
Momy ma tafito tashirya, sukayi sallar la'asar dan tama ďan shige lokacinta.
Afalo suka tarar da ya Muzzaffar da dady suna jiransu a dinning.
Momy tazauna kusada dady, itama ya Muzzaffar ya nuna mata kusadashi, babu musu taje tazauna, aka haďama kowa abinci agabansa sanan sukai bismillah suka hau ci.
Itadai ameeda akunyace takecin abincin har saida daddy yay mata magana, babyna kodai dakaina zan baki abincinnan dai?, hannu tasa tarufe fuska tana dariya a'a dady zanci da kaina.
To yakamata kam, kisaki jikinki baby nan gidankune, bakida inda yafinan kinji, dummm taji kanta yayi, wai ita wane irin ruďani ake shirin sakatane??, tagaza gane wanan rikitaccen al'amarin??, ya Muzzaffar ya ta6ata, taďago tana kallonsa da ido yay mata alamar taci, ďan murmushin ya'ke tayi tacigaba dacin abincin.
Su momy suna kallonsu.


Dahaka dai suka gama cin abincin suka tashi, dady ya haye samansa sukuma suka zauna suna 'yar hira, wadda duk anayine dan ameeda tasaki jikinta.
Momy taje ďakin daddy, ta ce, "Alhaji nifa yau tareda baby zan kwana nayimaka yaji, yay murmushi a'a hajiya ainima ban yardaba saidai tazonan mukwana tare, murmushi momy tayi ta ce, "to inaga hakan zaifi sau'ki kam.
Ranar agado ďaya ta kwana da momy da dady, sukasakata tsakkiya, (araina nace kai 'yan boko sai abarsu, wananan gandamemiyar budurwar za'a kwana gado ďaya da ita in bandadai.........baridai nayi shiru, ALLAH yashiryemu).............


Ku biyomu.




Washe gari bayan sun kammala breakfast suka nufi polistion, itadai duk abinda ake ameeda binsu kawai take da kallo cikin mamaki, tarasa gane kan wannan lamari, har yanzu bata fahinci inda suka dosaba, gashi kowa ya'ki bata damar tambaya, dahakadai suka 'karasa, tunda suka shiga 'yansanda suke 'kamewa daddy, watodai afahimtar ta daddy ďansanda ne kuma babba, shiyyasa yaja rundunar 'yansanda har kano suka yayibosu, towai misuka yimusu?, mi iyayenta sukai misu ne?, komadai miye ai yanzu zata gani, wani 'kayataccen office suka isa, mutummin dake saman kujerarsa ya mi'ke tareda sarama daddy, daddy yay masa umarni daya zauna, suma duk suka zazzauna asaman kujerun da aka 'kawata office ďin dasu domin saukar ba'ki, wanda suka tarar a office ďin yakira waya taraeda bada izinin shigowa dasu iya abu.
Babu daďewa aka shigo dasu kallo ďaya ameeda tayi musu hankalinta yatashi, daka gansu kasan sunci ďan karen duka, duk raunuka ajikinsu, dareďaya sunyi wujiga2 kamar waďanda suka shekara akulle.
Gaban dady da momy suka zube suna kuka da ro'konsa gafara, alhaji dan girman ALLAH kayi mana rai wlhy ka 'kara barinmu awajennan kashemu zasuyi, wlhy munyi nadamar abinda muka aikata, kuma ashirye myke mu faďa muku gskyar lamari, dan ALLAH kace karsu kashemu.......dakatar dasu dady yayi tahanyar ďaga musu hannu, ruf suka rufe bakinsu tamkar ruwa yacinyesu, office ďin yay tsit, dady yay gyaran murya tareda faďin musa ai inaga kawai zamu tafi dasu gidan dan kes ďin nagidane, dama nabari kakawosu nanne dansu dan nasan kai tsaye bazasu amsa laifinsuba sai sunji wuya, musa D.P.O yace babu damuwa sir bari nasa akai makasu, ai tun daren jiya suka faďi laifinsu kuma sunce basu kaďai bane suma sakasu akayi.
Dady yajinjin kai ya ce, "shiyyasa nace zamu je gida dasu dansu nuna mana waďanda suka sakasu ďin dady yafaďa yana mi'kewa.
'Kara cimimiyar su iya abu akayi zuwa wani haďaďďen gida shima babu nisa da gidan dady, dady ne yafara shiga, da wata dattijuwa yafara karo, dakaganta kasan ba 'karamar masifaffiya bace, dan ko sallamar dady acinkushe ta amsa masa kuma cikin yanayin masifa, doguwace fara 'kya'ky'kyawa, tahaďu sosai dan tafi momy 'kyau nesa ba kusaba, daddy yazauna yana faďin ya gidan??, ta yatsine fuska tareda ta6e baki, yaukuma mafarkinmu akayi da sassafen nan??, ďan murmushi kawai daddy yayi dama sainayi mafarkinki nake zuwa ganinki, ba jiya dasafe nabar gidanba, nanma baki ta ta6e ai nasan idan kana gidan 'yar gold mantawa kake da kwa da komai, yanzuma da safennan sayeed yayo waya wai yana bu'katar kuďi, dady ya haďe fuska wane kuďi kuma yake bu'kata? Kofa sati uku banyi da tura masa dubu ďari biyarba, shin kuďin abincine??, bare ace suyakeci? Haba alhaji yanzu dan ALLAH dan yace yanason katura masa kuďi saiya zama abin faďa, sukenanfa ALLAH yabaka su biyu dukiyarnan fa tamkar tasuce tunda idan kamutu sune zasu gada, bare kace za'aci da ha'kkin 'yar gold, murmushi dady yasaki tareda gyara zama nibama wannan yakawoniba hassana, ta watsa masa kallon rainin hankali to da wacce kazo??, kodami kazo ashirye nake dakai alhaji ta'kare maganar cikin 'kufula.
Kallon k kika sani yay mata sanan yaďauki wayarsa yay kira, kushigo kawai yace ya kashe, tami'ke tsaye afusace, wakuma ka kawomin har cikin gida, kaifa nakula kullum rainin hankalinka 'kara yawa yake, wlhy Alhaji har yanzu ina nan amatsayin hassanata daka sani, babu abinda yarage ahalina.............maganar ta kakare mata ama'koshi dan ganin masu shigowa, saikuma jikinta ya hau rawa dataga su iya abu, gabanta sai dukan tara2 yakeyi, tadaka musu tsawa kai kukuma daga ina? gayyar tsiya arna a idi, babu wanda ya kulata saima neman gurin zama dasukayi, Nasir ne 'karshen shigowa falon, ta gwalalo idanu tareda faďin Nasir kaikuma daga ina?, ina kasamo waďannan kara da kiyashin? Gaba ďaya aruďe take maganar, baice mata komaiba yanemi guri shima yazauna.
Dady ya kalleta ya ce, "hassana yakamata kizauna, da'karfi tace bazan zauna ďinba munafuki, to wannan gayyar dakayomin ta micece??, tsawa dady yadaka mata tareda faďin karki zauna ďin, ai zaki zauna da tsiya, ana cikin haka saiga wani dattijo shima yashigo, shimaďin arazane yake bin mutanen falon da kallo, yanan tsaye wata tsohuwa tashigo tareda wani dabaikai su dady girmaba, saikuma mata su uku sumadai da'alama akwai dangan taka tsakaninsu da dady dan naga kama, sudai nakula kowa hankalinsa akwance yake.
Duk guri suka nema suka zauna, hajiya hassana ce kawai a tsaye, da'alama tana samun hanya arcewa zatayi waje, saikuma dattijon nan dayaketa zufa da rawar jiki, sai kulmawa su iya abu idanu yakeyi, falon yay shiru babu abinda ake sai kallon kallo musamman ma Ameeda da kanta yake shirin tarwatsewa saboda mamaki wanan irin taron dangi haka duk na miye??.....maganar dady ce ta 'katseta, sallama yay musu tareda godiyar halartar kiransa dasukayi, kowa ya amsa.
Tsohuwar nan ta kalli dady tareda faďin Hamza ina kasamo wannan yarinyar??, ta nuna ameeda, naga ita kaďaice ba'kon ido afalonnan gashi? kuma ina jin wani abu gameda ita""..
Dady yace mama ai akantane akai wannan taron, insha ALLAHU yanzu zamu fiddaku aduhu.
Kallonsa ya maida gasu iya abu ya ce, "abu munason jin wani abu daga bakinki keda malam dauda, malam dauda yay saurin 'kar6e maganar da faďin wlhy alhaji banida laifi kona sisin kwabo, kaga wanan munafukar ya nuna iya abu, to duk wani kulli ita tasanshi tareda hajiya matarka da alhaji Tasi'u yayanka da matarsa, saikuma abokanka uku da 'kanwarka matarka hajiya sadiya, saikuma Nasir kanin matarka, duk wani bayani abakin waďannan mutanen dana lissafa zaka sameshi dan sune suka kulla abinsu, nima saboda hakane aka danneni da asiri nakasa ta6uka komai arayuwata.
Dady ya ce, "malam dauda su waye abokannawa??, malam dauda ya ce, "alhaji safiyanu da marigayi alhaji lawan da alhaji mansur......atsorace dady yake kallonsa saikuma yazaro waya da sauri batarda yayi maganaba ya hau kiransu ďaya bayan ďaya da bu'katar son ganinsu, cikin minti goma sha biyar suka iso kusan atare, ba abunda sukayi zaton ganiba kenan dan haka dasuka shigo duk sai suka rikice bayan sun gama bin falon da kallo, dady ya ce, "kuzauna mana, amnafa kuyi ha'kuri bansanar daku dalilin kiranba.
Tsohuwa ta katse musu zance da faďin wai mike faruwane, nifa sai "kara rikitar dani kukeyi da sakani aduhu,, kiyi hakuri mama yanzu zaki fahimci komai, abu bismillah...ina kika samu wannan ďiyar??????.
Ďagowa tayi tana kallon ameeda, muryarta na rawa ta ce, "hajiya ce tabani.......................


Ku biyomu.


















©2017






Hikayarmu!!!!!!!.
abba gana
bilyn Abdul
[04/03 10:46] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA.........












NA
MUH'D ABBA GANA
&
BILKISA IBRAHIM
(☆bilyn Abdul☆)










Page23&24


.......gaba ďaya falon suka maida kallonsu ga iya abu, dady ya ce, "wace hajiyar? Ta ce, "hajiya hassana, gaba ďaya falon suka ďauki sallallami tareda tafa hannye, tuni hajiya hassana ta zauna jagwaf tana zufa, dady ya ce, ta yaya tabaki ita?.
Iya abu ta matso hawaye sanan tafara bada labari daga tushe.
Kamar yanda kuka sani hajiya hassana itace matar alhaji ta farko, sunkai tsawon shekara ashirin ALLAH bai basu haihuwaba, gashi kuma ALLAH ya azurta alhaji da tarin dukiya, yana cikin damuwa ta rashin haihuwa amma baita6a yin'kurin 'kara aureba, har saida mahaifiyarsa ta taursasashi, alokacin 'yan uwa sun goya masa baya da'kin amincewa dan bayason 'kara aure saboda 'kaunar dayakema matarsa hajiya hassana, saidai dukda haka acikinsu akwai masu goyama mama baya, akan alhaji ya 'kara aure, ba 'karamar fama akayiba kafin ya yarda ya 'kara aure, ya auri hajiya saliha wato momy, tunda ya auri hajiya salaha zaman lafiya ya 'kaura agidansa ta 6angaren hajiya hassana, kwata2 bata 'kyaunar tabuďe ido taga hajiya salaha agidan, abinda yasa duk nasan wanan shine tun ina yarinya aka kawoni wajen hajiya hassana amatsayin 'yar aiki daga 'kyauyen kokai, hajiya hassana tanada faďa sosai da kalolin shirya makirci iri2, to sai akayi sa'a halinmu yazo ďaya, ganin haka yasa tasakani cikin lamuranta sosai, duk wani mugun abu na asiri kona tsafi dazata kulla akan alhaji to da sanina harma da taimakona, ganin na kwarance awajen mugun hali yasa hajiya tasa dauda mai gadi ya aureni dan bataso nayi nesa da ita ko kaďan, dauda baya sona alokacin amma saida muka shiga muka fita yasoni, alhaji yabamu BQ Muka zauna, babu daďewa da aurenmu ya auro hajiya saliha.
Wanan aure ba'karamin girgiza hajiya hassana yayiba dan

4 / 6