Chapter 19 Reading JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt Arewa Novels

JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt

Author :  Maryam Alhassan Dan Iya Category :  A Books

Chapter   19 / 22

54K to 57K   out of 63.9K words

dinta na nan ba, tashi yayi ya fito baiga sonia ba dan haka ya fice direct gidansu jawaheer din ya nufa inda ya samesu su duka a falo suna ta fira, shima zama yayi aka fara firan dashi, mama ta lura da jawaheer yake son gani dan haka ta kalleta tare da fadin jawaheer tashi ku dan zaga mana, tashi tayi shi kam dadi yaji, tashi yayi shima suka fita, wajan wata bishiya suka je a bayan gidan, zama sukai a kasa ya janyota jikinshi tare da fadin na rasa mai yasa bana son inga ina yin nesa dake, in nayi nesa dake sai in dinga jin wani iri, dariya tayi tare da fadin toh fah, toh mai yasa hakan ke faruwa? Yace shine nake so ki fadamin miye sirrin abun, hannunta ya riqo yana shafawa bata ce komai ba ganin haka yace jawaheer yau zan tafi dake koh? Da sauri ta dago tare da fadin dan Allah ka rufa min asiri, tamke fuska yayi yace kaman ya keba matata bace? Ina da iko inyi duk abunda naga dama dake babu wanda zaice min danme, tace hakane amma ai saika bari a kawo ni kaman yanda al'adanmu yake, yace ni bana son wani al'ada tunda ba addini bane, baki ta dan turo alaman taji haushi bata ankara ba taji bakinshi cikin nata, kissing dinta yake sosai tun bata mayar mishi da martani harta fara, sunyi wajan minti biyu suna tsotsan bakin junansu sannan ya saketa ta lumshe ido, ido ya zuba ma fuskanta yana kare mata kallo, lallai nayi dacen mata kyakyawa mai addini yar gidan mutunci, Allah na gode maka daka bani jawaheer a matsayin mata, gaba daya jikinta yayi weak bude idonta tayi taga ita yake kallo tayi sauri ta kuma rufewa dariya yayi tare da dagota daka jikinshi yace oya tashi muje yunwa nake ji, tace akwai abinci a ciki bari in kawo ma, yace nop muje akwai inda zamu ci, tace ok ina zuwa ciki ta shiga jim kadan sai gata ta fito ta canza kaya ido ya bita dashi komai jawaheer tasa yana amsanta, motarshi suka shiga shike tukawa har wani katon hotel ciki suka shiga, direct restaurant din hotel din suka nufa, masu abincin suka basu list na abincin suka nuna ba'a dade ba aka kawo musu, sunci sunsha sannan suka tashi wani daki taga ya bude gabanta taji ya fadi, amma haka ta daure ta shiga, bayan sun shiga kwanciya yayi akan gadon dakin tare da kallonta yace kunna min ac din, kunna mai tayi sannan ta sami waje ta zauna cikin kujeran dake dakin, kallonta yayi tare da bude mata hannunshi alaman tazo inda yake yi tayi kaman bata ganshi ba, ya lura da hakan yayi dan murmushi tare da tashi ya dauketa cak ta fara zillo amma ko a jikinshi kan gadon ya ajiye ta, tazo zata tashi ya janyota jikinshi tare da fadin muyi bacci, a hankali tace ni bana jin bacci, bai kulata ba sai kara manneta da yayi a jikinsa, bai dade ba bacci ya daukeshi yayi bacci sosai har wajan magrib tashi yayi tare da salati jin ana kiran sallah yasa ya tasheta da sauri tare da fadin tashi kiyi sallah, fita yayi ya nufi masallaci shima, koda ya dawo yaga ta ciro wani zanin gado ta yafa tayi sallah dashi, bayan ta gama yace su tafi, shiryawa tayi suka fita, bayan sun shiga mota yace mata gobe karfe hudu masu gyaraki za suzo, saiki zama ready suna tafiya yana mamin wakar da yasa na nicki minaj, har suka karasa kofar gidansu ya sauketa shima ya karasa nashi, koda ta shiga ta gansu a falo sai taji kunya amma sai basu nuna sun sam tana yiba, sai adda da tace sai yanzu bata ce komai ba ta sami waje ta zauna kusa da mum, tace mum gobe 4 masu makeup za suzo yace in shirya mum tace Allah ya kaimu, tashi tayi ta musu saida safe sannan ta wuce dakinta, tana sallah isha'i ta kwanta bacci.












Washegari tun da safe gidan ya kacame anata gyare gyare duk da ba taro za'ayi a gidan ba, lokaci kadan gidan yayi kyau ga kamshi na tashi tako ina, jawaheer sai wajan 10 ta fito adda ce ma take ta buga mata kofa sai yasa ma harta fito, bayan ta fito adda tace mutum ya kwanta yaita bacci har yanzu, tace kai adda bazaki bar mutum ya huta ba wlh, adda tace malalaciya ni ban taba ganin amarya mai son jikinki ba anya ma zaki dinga dafa mai abinci kuwa? Jawaheer tace haba girki sai kace zamaninku salati adda ta saki tace amma ko wannan zamanin naku ba abun arziki kuka koya ba, toh a ina zai dinga cin abincin? Tace wajan saidawa adda taita bala'i wai taya zata bae mijinta ya dinga cin abincin saidawa saboda lalaci, su mum kam babu abunda suke sai dariya, dinning ta nufa ta zuba abinci ta fara ci, sallamanshi taji idonshi na kanta ganin irin kallon da yake mata yasa ta sakar mai murmushi, adda data lura dasu tace mutum dai ya kalli gabanshi kar yaje ya fadi, shi kam ba hausa yake jiba, jawaheer kam ta gane dasu take, dan haka ta kawar da kanta daka kallonshi, taci gaba dacin abincinta, gaida su mum yayi da mama suka ansa sannan ya gaida adda da fadin ina kwana adda? Amsawa tayi da lafiya qalau, itama jawaheer gaidashi tayi da fadin morning, amsawa yayi ba tare daya kalleta ba, zama yayi kusa da mama yace ya kwanan kasar? Mama tace alhmdlh ya shirye shirye? Yace an gama komai babu abunda ya rage, tace toh alhmdlh Allah ya taimaka, ya amsa da ameen khlil da dad da muhd da kabir da umar ne suka shigo cikin gidan, gaisawa sukayi sannan suka zauna anata tattaunawa yanda abun zai kasance samir yace ya gama shirya komai karsu damu, jawaheer bayan ta gama cin abinci barin falon tayi ta nufi dakinta, kwanciya tayi dan bata koshi da baccin ba adda ta tashe ta, amma sai dai kuma me gaba daya ta kasa baccin sai tunani, yau itace a matsayin matar m samir, tashi tayi ta fito falon ta kalli samir tace plz ina aka sauke baki zarah na can tace tare da kawayenmu zasu zauna, gashi ina bukatarta a nan, yace zaku hadu ai daka wajansu nazo nan, na bada kayan da za susa ankai musu ma, tace ok tare da komawa ta zauna akan kujera kusa da adda, m samir tashi yayi ya wuce haka sukai ta fira.












Wajan 5 masu makeup suka zo, saida tayi alwala kafin ta zauna aka fara mata, ana cikin makeup din aka kira sallah, saida tayi sallah akaci gaba, kwalliya ake mata na kece raini, wedding gown aka sa mata, jin kiran sallah isha'i yasa tace a cire mata abun kanta tayi sallah, haka suka cire tayi sannan suka kara gyara mata, wow fadin irin kyau din da tayi bata lokaci ne, bazai ma iya faduwa ba, bayan an gama aka rufe mata fuska suka fita cikin wata dangareriyan mota suka shiga da ita, a ciki ta sami samir shima yasha suit fari irin kayanta fari, kallonta yayi tare da fadin wow my princess kinyi kyau sosai, murmushi tayi ba tare da tace komai ba, driver yaja mota suka tafi bayan sun karasa dangareren hall din tare suka jera da kawayenta da suka sa black gown mazan ma haka har cikin hadaddan hall din, zama kowa yayi inda karan kida ke tashi masu rawa nayi, amarya da ango akace su fito su zo suyi rawa, hannu ya miqa mata ta miqa mai nata suka fara rawa gwanin sha'awa zarah taki yarda tayi rawa da kowa saboda khalil na wajan, bayan amarya da ango sun zauna nan aka fara basu gift suna amsa, cikin masu bada gift din harda sonia wacce taba zarah ta amsa tayi godiya, murmushi sonia tayi tare da komawa ta zauna, anci ansha gaba daya kayan aka kwashe akai mota dasu, yanda aka tsara daka dinner zai tafi da ita, ita bata ma san hakan aka tsara ba, saida aka gama suka shiga mota, wani dangareren gida suka nufa bayan mota ta faka yace ta fito fita tayi sukai ciki, gidan ya hadu sosai a falo suka tarar da gift din da aka basu, gaba daya anyi raping dinsu, gasu manya wanda sonia ta bata ta dauko shine karamin ciki, zata bude samir ya amsa ya fara budewa zobuna ne guda biyu masu shegen kyau ko wanne an rubuta S&J ma'ana samir da jawaheer kamo hannunta yayi yasa mata daya shima yasa nashi, tunda yasa mata ta zauna a kasa murmushi yayi tare da kokarin dagata amma tayi wani irin wurgi dashi wanda saida ya bugu da bangon dake kusa dashi, cikin tsoro da mamakin irin tureshi din da tayi ya fara kokarin tashi nufanshi tayi ta shake mai wuya tare da fadin yau zan kashe ka, lokaci daya kuma ta saki dariya tare da kara jefar dashi wannan karan akai ya bugu harda jini ya fara zuba, dariya ta saki mai karfi tare da sauti gashin kanta duk ya mimmike tsaye........ Toh fah muje zuwa
















*maryam obam*


*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 55-56
















Riqe kanshi yayi da yake ta zubar da jini, a wannan karan baiyi yunkurin tashi ba, sai kallonta da yake da ido, yana mamakin maiya sameta lokaci daya haka, kodai aljanu gareta? Kai anya inma aljanu ne...... Ganinta yayi a tsugunne a kusa dashi tana dariya mai karfi magananta yaji ya canza kaman ba nata ba, gashin kanshi ta danqo da karfi duk da yana jin zafi baiyi kokarin hanata ba, haka ta dagashi sama ta kuma yin wurgi dashi tare da fadin zan kashe ka, ka shiga gonar daba taka ba duk cikin turanci take maganan, lokaci daya kuma tasa kuka mai ban tausayi, samir kam tunda tayi wurgi dashi ya bugi wani glass bai san inda kanshi yake ba, jin ruwa yayi a kanshi da sauri ya bude ido ganinta yayi tana dariya ga idonta ya rune yayi baki sosai, ga gashin kanta duk ya mimmike a hankali ya sauke idanshi akan komai na falon duk ta faffashe komai na falon komai ya wargaje ga jini itama na zuba a jikinta alaman taji ma kanta ciwo, da sauri ya tashi da nufin ya riqota amma ina wani irin ihu ta saki tare da shako mai wuya lokaci daya kuma tayi 'kasa tana surutai ganin ta sakeshi yasa yayi kokarin fita dan ya kira security dinshi su taimaka a kamata ji yayi ta janyo shi tare da wurgar dashi a kasa, tace kar kayi tunanin yin wani abu duk wanda ya shigo cikin gidan nan saina kashe shi, matsawa tayi daka inda yake ta zauna akan kujeran falon tana kallonshi tana dariya, shi kam gaba daya ya firgita da ita ya rasa ma abun yi, bai kara yinkurin tashi ba ga dariyan da takeyi babu dadin ji, ga tsoro, ganin karan ya isheshi yasa ya yankura ya tashi ganin ya mike yasa ta nufoshi amma wannan karan addu'a ne a bakinsa harta karaso inda yake tana kamashi ta sulale kasa tabata yayi yaga alaman kaman ta sumene da sauri ya dauketa yayi wani daki da ita ya rufe da key, fita yayi daka gidan cikin daren direct gidansu ya nufa, nocking yayi aka bude mai, mum ta tsorata da ganin dan nata jiki duk jini, tace samir lafiya maiya sameka? Bai iya furta komai ba sai shiga falon da yayi ya zauna yana maida numfashi kowa dake gidan ya fito, hankalin kowa ya tashi na ganin irin halin da yake ciki, mama ta matsa kusa dashi tana fadin samir maiya sameka ina jawaheer accident kukayi? Kai ya girgiza alaman a'a yace mama jawaheer ta sami tabin hankali itace tamin duk wannan abun, kowa dake wajan ya tsorata mum tace kaman ya labarin abunda ya faru ya basu, kowa yayi shuru yana jimami, mum tace ai sai muje gidan muga halinda take ciki sannan a kira dr, tashi sukayi da mum da dad da muhd da mama sai adda, suka shiga mota samir na tuki har gidan, salati kowa yasa da suka ga yanda falon ya dawo an wargaza komai dake falon, jin karan ihunta yafi komai daga musu hankali tare da gunjin kukanta, dr yace bari ya dubata, dakin suka nufa samir ya bude kofar, aiko suna shiga idonta ya sauka akan na samir da gudu ta cafkeshi tana fadin saina kashe ka wa yace ka kira mutane? Sakinshi tayi kuma ta saki dariya tare da kallon dr ta nunashi da hannu alaman ya fita daka dakin, ganin haka dr yayi saurin fita har zufa yake dan tsoro, kowa dake wajan ya tsorata da ganin yanayin data shiga, musamman ma da sukaji yanda take magana kaman ba ita ba, samir kam kuka yakeyi ganin yanda jikinta yake zubar da jini duk taji ma kanta ciwo sosai, matsawa yayi kusa da ita amma tayi baya da karfi tare da kwashewa da dariya mai sauti, kara nufanta yayi wannan karan bata matsa ba yana tabata tayi wurgi dashi su dad sukayi saurin riqoshi, fita sukayi sukai sauri suka sama dakin key, buga kofar tai tayi da karfi, shuru sukai a falo su duka, maman jawaheer kam ita da mum babu abunda suke sai kuka, adda ce tayi gyaran murya tace kunyi shuru ku dukanku ya kamata a nema mafita fah, dad yace inaga mu kaita asibiti, mum tace kana ganin yanda take fusge fusge ba bari zatai a kamata ba, shuru sukai kowa yana tunanin yanda za'ayi samir yace ina zuwa dad tashi yayi ya bude kofar shiga yayi tare da addu'a a bakinsa kaman dazu tana tabashi ta sume da sauri ya ciccibeta akai mota da ita suma tashi sukayi suka shiga akai asibiti da ita, ana zuwa aka sata akan gado, aka daure mata hannu da kafa dan dr din yaga yanda takeyi kafin yabar gidan, ana gama daureta kam ta fara fisge fisge, tare da ihu, kowa dake wajan saida ya tausaya mata, dr suka mata alluran bacci amma sam baccin yaki zuwa haka taita ihu mai karfi, dukansu haka suka kwana babu bacci, hankalin kowa a tashe yake musamman ma samir da yake jin jawaheer din kaman ranshi a yanzu, har rama yayi na lokaci daya, haka itama ta kwana tana ihu, duk wani abu an mata ba'a ga wata matsala ba kwakwalwanta an gwada lafiya qalau babu wani ciwo, hankalin kowa ya tashi sosai, adda tace nifa wannan ciwon ban yarda na asibiti bane gaskiya a kira malami, mum tace adda bari muga mai za suce, adda ta fara masifa ai matsalanku kenan abu gashi a fili inba aikin sihiri ba taya magananta zai canza sannan kuce ciwon asibiti ne ni wlh ku kira malami tun kafin abun ya girma, ganin yanda take ta bala'i yasa dad yama samir magana akan a kira malami, samir dad dinshi ya kira dabai san maike faruwa ba, bayani ya mishi a waya dad din yana ta salati, yace gashi nan zuwa, bai dade ba sai gashi da mlm sun zo, malamin yana daya daka cikin manyan malaman kasar spain, dakin da jawaheer take aka kaishi kallo daya ya mata yayi murmushi tare da fadin a kwance ta, dr din sukace a barta in aka kwanceta akwai matsala, yace toh su basu ita a mayar da ita gida, suka ce sam saita sami lafiya tana karkashin gwamnati ne yanzu tunda a kasar ta fara ciwon, saida samir yayi magana aka kwanceta ta fara zabure zabure mlm ya fara addu'a ihu ta fara tare da sumewa, yana ganin haka ya kalli samir yace dauketa ka kaita mota, hakan yayi suka bar asibitin gidan suka koma, akan kujeran falon ya ajiyeta malam din yace ya kwantar da ita a kasa, yace a bashi cup da ruwa samir da sauri yayi kitchen ya dauko cup da ruwan roba, ya miqama mishi, budewa yayi ya zuba a cup din yayi addu'a sannan ya miqama samir yace gashi ya shafe mata jiki dashi, amsa yayi ya fara shafa mata a jiki wani irin nishi takeyi mai karfi tana jijjiga jikinta malam din yace yaci gaba karya tsaya har sai yace ya daina, haka yaita shafa mata tana nishi daka karshe ihu ta fara mai karfi malam din yana ta addu'a yana tofa mata shi kuma, lokaci daya ta fara ihu mai karfi kowa dake falon ya tsorata dajin irin ihun da takeyi musamman m samir dake jin ciwon kaman a jikinshi yake, ido ta bude daya kara kadawa yayi baki, hannunta take ta kokarin dagawa amma ta kasa idon malam din ya sauka akan hannun zoben hannuta ya gani da yake kaman hayaki da sauri ya kamo hannun ya cire mata zoban wani irin ihu ta saki tare suka suma ita da m samir yana tsaye ta fadi tim, a kasa hankalin kowa ya kara tashi malam ya koma kan m sami yana shafa mai ruwan addu'a shima yana karatu shima hannun nashi ya kalla yaga zoben irin na jawaheer din cire mai yayi wani kara dakin yayi mai karfi, zuba ya fara keto musu su duka mlm din ya kalli su mum yace bari su farka mu gani anyi musu mugun sihiri ne, amma mun godema Allah abun ya hada da zoben dake hannunsu a ciki akasa sihirin bayan sun sa ne abun ya kamasu yanzu sai su dinga kula sosai domin inda abun ya dade samir zaiji tsanan jawaheer a ranshi sai su kara dagewa da addu'a, sai fadin alhmdlh suke bacci suke sosai mum tace bari ta kira masu aikinta suzo su gyara falon haka akayi aka gyara falon wajan da suke kwance kuma a haka aka barshi har su tashi, mlm din yace zai tafi yayi addu'a yace gashi in sun tashi a basu susha sannan yace a hadashi da wani ya amso musu maganin

19 / 22