Chapter 7 Reading JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt Arewa Novels

JAWAHEER HAUSA NOVELS BY MARYAM OBAM.txt

Author :  Maryam Alhassan Dan Iya Category :  A Books

Chapter   7 / 22

18K to 21K   out of 63.9K words

da fadin yes ke zai gani, matsowa tayi kusa dashi tare da fadin Allah yasa ba laifi nayi ba? Yanda tayi maganan cikin sanyin murya ya bashi dariya hancinta yaja tare da fadin bakiyi komai ba kawai yana son ganinki ne, ajiyan zuciya tayi tare da fadin yaushe zamu? Yace yanzu, tace ok ina zuwa dakinta ta shiga ta canza kaya tasa jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan tayi kyau sosai sak balarabiya, ga kamshi dake tashi a jikinta falon ta nufa lokacin data fito ido ya kura mata yana murmushi ganin irin kallon da yake mata yasa ta danji kunya, kaman ya lura da hakan yace sis kinyi kyau tashi yayi ya janyota tare da daukansu hoto yana fadin bani da pics dinki dama, ya daukesu da yawa sannan yace ta bashi wayanta, mika mishi tayi yayi dialing no dinshi cikin nata, sannan ya kalleta yace bani no dinki na kasarku, murmushi tayi tare da fada mishi ya rubuta, sannan yace suje, motarshi suka shiga wacce cikin motan kaman daki seat din motar ma kanshi abun kallo ne, ga tv har biyu a manne a motan dayan camera ne amma sai yayi kaman tv duk wani abu da akeyi a waje yana kallo ta ciki, jawaheer ta kara tsorata dashi domin tasan lallai m samir ba karamin mutum bane lallai haduwansu hadin Allah ne, Allah ya amshi addu'anta dole ace ganinshi tashin hankali ne amma sai gashi Allah yasa ta ganshi cikin sauki, wani hawaye ne ya gangaro mata, jin hannunshi tayi akan fuskanta yana goge mata, lokaci daya ta dago kai suka hada ido, sunyi wajan minti daya suna kallon juna, kowa da abunda yake sawa a ranshi, shine yayi karfin halin kawar da idonshi tare da janyota jikinshi yana shafa mata bayanta yana fadin jawaheer mai yake damunki? Cikin wata irin murya tace ina farin ciki da Allah ya hadani dakai cikin sauki, lallai haduwa na dakai akwai wani boyayy...... Shuru tayi domin taji abun ya mata nauyi, yace inaji akwai me? Tace babu komai murmushi kawai yayi tsayawan motar ne yasa ta gane sun zo inda zasu, fita sukayi m samir ya kamo hannunta zasu shiga tare tayi sauri ta janye hannunta kallonta yayi ba tare da yace mata komai ba, ganin irin kallon da yayi mata alaman tambaya yasa ta fara fadin kar dad yaga ka riqeni zaice banda kunya, murmushi yayi sai yaji ta burgeshi sosai, haka suka shiga cikin gidan koda suka shiga ya nuna mata waje ta zauna gina ta fito suka gaisa ta kawo mata coffee jim kadan sai ga dad da m samir, dad ido ya kura mata ganin suna isowa yasa ta tashi ta tsaya a tsaye har dad ya karaso dad yace ta zauna mana zama tayi a dan takure tare da gaida dad din ya amsa cikin sakin fuska tare dayi mata tambayoyi akan iyayenta tana bashi amsa dad ya yaba da tarbiyanta sosai kuma yaji ta burgeshi dan haka ya saki jiki da ita yana ta janta da fira sosai, suna cikin haka wayanta yayi kara dubawa tayi taga mum ce dauka tayi bayan ta gaida mum cikin harshen hausa tace mum zan kiraki tare da kashe wayan, tana gamawa m samir yace ta tashi su tafi, wata leda ta ciro cikin jakarta ta ajiye a gaban dad tare da fadin dad kayi hakuri babu yawa, dad rasa bakin magana yayi lallai yarinyar nan tana da kirki tarbiya ladabi sannan al'adunta abun burgewa ne, dad yana ta mata godiya, har mota dad ya rakasu tare da fadin ta kulan mishi da yaro sannan in komai yayi dai2 shima zai zo nigeria haka suka tafi cikin jin dadi, suna mota m samir ya kira sunanta jawaheer ta dago suka hada ido tayi saurin kawar da ido, kara kiran sunanta yayi alama ta waigo ta kalleshi, kin waigowa tayi, ganin haka yasa ya janyota jikinshi suna hada ido ta rufe idanta wanda hakan ya bashi daman kallanta dakyau tare da aiyana abubuwa da dama a ranshi......
























*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 18




















Gaba daya ya gama karema jikinta kallo yayin da duk wani sassa na jikinshi ya mutu wani irin yanayi ya shiga mai wuyan musaltuwa jawaheer tana da kyau na bugawa a jarida tana tarbiya wacce za'a so ace mutum ya sameta a matsayin mata sai dai kash baya jin sonta, idanshi ne ya sauka akan lebanta wanda kallo kawai zakai mata ka gane yana da laushi ido shima ya lumshe tunawa da ranan da yayi kissing dinta, bai taba shiga cikin wani irin hali mara misaltuwa ba kaman ranan duk da ba'a hayyacinta ya mata ba, inda tana cikin hayyacinta kuma da yardanta hakan ya faru da ya zaiji?.... Karan wayan jawaheer dinne yasa ta bude ido wanda shima yayi dai2 da bude nashi caraf suka kara hada ido wanda wannan karan sun kasa daukewa daka kallon junansu har wayan ya tsinke, shidai yasan baya son jawaheer sonia yake so amma yana jin wani abu a tare da jawaheer wanda bayaji akan sonia..... Karan kiran nata ne ya kuma katsesu wannan karan dauka tayi taga mum dinta, tace mum ...... Mum tace inata jira ki kirani kinki kira ya maganan dawowan naki gobe? Kallon m samir tayi taga yana danna waya, tace mum gobe zan dawo amma bana tunanin abuja zan sauka,mum tace kaman ya ina zaki? Tace yola zani mum tace what?... Kina da hankali kuwa uban me zakiyi a yola jawaheer wlh zanyi mugun saba miki, ki tabbata gobe kin sauka a abuja inba hakaba zaki hadu da fushina wlh, tace mum pl...... Kit mum ta kashe wayan jawaheer kallon wayan ta tsayayi tana mamaki toh miye abun zafi dan tace zata yola, bama an barta tayi wata daya bane a nan ai bata ma kai wata dayan ba, jin hannun m samir tayi a kanta yana fadin what r u thinking sis? Murmushi ta saki tare da fadin babu komai, a hankali ya furta nagode da kyautarki da kika ba dad dina i really appreciate it, bata fuska tayi tace nima fa dad dina ne, yaji dadin magananta, domin yana son dad dinshi duk wanda yake son dad dinshi toh shima yana son shi, a haka har suka karasa gida gidanshi ya shiga itama ta shiga nata.










Yanzu karfe 8 na dare a kasar spain amma zukata biyu sun kasa sukuni domin kuwa ko wanne yana burin ganin dan uwansa, jawaheer tana mugun san ganin m samir cikin daren nan, haka shima ta gefenshi babu wacce yake burin gani sai ita amma shi a nashi ganin ya danganta hakan ne da daukinshi na zuwa nigeria kuma itace zata kaishi, tashi yayi yasa riga ya fita, tana kwance tana tunanin m samir taji ana mata nocking tashi tayi taga ita sai rigan bacci dai2 gwiwanta ta nufi kofa, tana budewa taga flower a wajan amma babu kowa, dubawa farayi ko zata ga mutum, amma bataga kowa ba dan haka ta dauki flower din tayi shuru lokaci daya kuma ta shiga ciki dashi, dan karamin kwalin data gani ta dauka ta fara karantawa kaman haka..... *Hey am hare missing you u r d best sister in d world* ido ta lumshe domin yanzu tasan waya ajiye mata wani irin farin ciki taji yana shiganta, wayanta taji yana kara da sauri ta nufi bedroom dinta ganin number din da yake kiranta yasa ta dauka da sauri amma saita tsinci kanta da kasa magana, muryanshi taji yana fadin kinyi kyau cikin night gown kiyi bacci da wuri kin san gobe zamu tafi, tace ok yanzu zanyi bada dadewa ba, murmushi yayi tare da fadin ok sis good night tare da kashe wayan, wani irin murmushin murna tayi tare da rungume wayar a jikinta sai kace m samir dinne a gabanta ta rungume haka, ranan bacci tayi cikin nishadi haka shima ta gefenshi.












Washe gari tun karfe 7 jawaheer ta dan ta makara da sauri ta shiga toilet tayi alwala sannan tayi sallah tare da neman gafaran Allah, bayan ta gama ta shiga toilet tayi wanka tasa wata doguwar riga, tare da hada sauran kayanta, tana gamawa kiran m samir ya shigo wayanta dauka tayi da sauri tana gaidashi amsawa yayi cikin murmushi tare da fadin zan turo a dauki kayanki 9 zamu wuce tace ok, basu dade da gama wayan ba taji nocking dan haka ta nufi kofan ta bude security dinshi ne suka shigo suka kwashe kayanta yayinda suka rufe komai na gidan da farin kyalle gudun kar kayan suyi kura tunda za'a bar gidan, bayan sun gama ta bisu suka tafi gidan m samir tare a falo ta ganshi shida dad dinshi cikin girmamawa ta gaida dad din nashi ya amsa cikin sakin fuska tare dayi musu addu'an samun nasara akan abunda zasu nema, fira suka farayi har 9 din yayi suka fito inda dad din m samir yake ta fadama jawaheer ta kula da m samir domin ya yarda da ita, tace insha Allah, da haka har suka nufi Airport, nan mutane suka fara ihu ganin m samir yayin daya rike jawaheer a makale dashi yan jarida nata dauka domin suna ganin budurwanshi ce duk yanda sukaso yace wani abu amma bai ceba koda suka zo shiga jirgi daukanta yayi ya daurawa sannan shima ya hau suka haura tana gaba yana binta a baya, daka shi sai security dinshi guda goma suka shiga jirgin aka rufe domin private jet ne, kusa da jawaheer ya zauna basu dade da zama ba masu aikin jirgin suka zo tambaya mai suke so, kallon jawaheer yayi yace ta fadi abunda take so, coffee tace kawai shima yace a kawo mai coffee din, kallon juna sukayi sukai murmushi wanda a dai2 lokacin jirgin ya daga domin zuwa nigeria....... Hmmmm ku biyoni dan jin yanda zata kaya ga m samir a nigeria








*maryam obam*




*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 19














Sai wajan karfe biyu jirginsu ya sauka a airport dake yola, fita sukayi, suka fara tafiya yayin da security dinshi ke zagaye dashi, nan mutane suka ganeshi musamman matasa nan aka fara ihu tare da daukanshi hoto, yana ta daga musu hannu,haka har suka samu suka fita, motoci ne makil a waje sodoji ne da yan sanda suka zo daukansu da motoci na alfarma, tare suka shiga mota daya shida jawaheer, sannan security dinshi suka shiga sauran, hotel aka kaishi kai tsaye dan sun so su fara kaishi government house yace a'a su kaishi inda zai sauka yana son hutu, hotel din gaba daya aka mishi booking babu kowa a ciki sai su kadai an zagaye hotel din da jami'an tsaro, domin kuwa kasar spain ta bada ajiyan m samir ga gwamnatin nigeria, shugaban kasa da kansa yasa governor din yola yayi mishi komai da komai, jawaheer kam abun mamaki yake ta bata koda yake ba abun mamaki bane dan he is a biggest celebrity in d world wannan ba komai bane, sai da yakai jawaheer har dakin da zata sauka sannan shima ya shiga nashi mai kallon nata dakin, yana shiga ya fada toilet dan yin wanka, koda ya fito daka wanka, yasa boxer tare da daura jallabiya yayi sallah, koda ya idar cire jallabiyan yayi, kwantawa yayi dan ya huta, bai dade ba bacci ya daukeshi.










Ita ko jawaheer tunda ta shiga dakin take jinta wani iri na farko dai ba yunwa takeji ba dan taci abinci a jirgi, sannan ita ba rashin lafiya ba, gadai ta nan ne dai, wannan ne zuwanta yola na farko duk da ya kasance garin iyayenta ne shi, amma bata taba zuwa ba, sau da yawa takan rasa mai yasa iyayenta basa son koda firan garin yola ayi musu, musamman ma mum tafi tsanan mahaifar tata, lallai akwai wani abu amma kodai miye kiyayyar tayi yawa haka, dan murmushi tayi tare da fadin may be ma ba wani babban abu ya faru ba suka dauki karan tsana suka sama garin tare da watsar da danginsu gaba daya dama ance fulani nada riko, tashi tayi itama tayi toilet tayi wanka, sannan ta fito tasa kananan kaya riga da wando, tare dasa hijab dinta dan yin sallah azahar, bayan ta idar ta dauko wayanta tasa sim dinta na nigeria, kaman jira ake kiran mum dinta ya shigo wayan kin dauka tayi dan tasan indai ta dauka tasan tana yola sunanta sorry, amma da tayi tunanin rashin fadama mum din nata zai iya daga musu hankali suyi ta tunanin tana ina, dan haka kiran na tsinkewa ta tura ma mum message kamar haka..... *mum na dawo nigeria amma kiyi hakuri ina garin yola nida m samir muka zo, mum ki tayani da addu'a burina ya cika a kanshi duk da nasan kina min, tana gama rubutawa ta tura mata* koda saqon ya shiga wayan mum ihu ta saki tare da tafa hannu tana fadin lallai jawaheer yau ta wuce gonarta ta nunamin ban isa da ita ba, dad dake zaune kusa da ita yace haba bilkisu miye haka mai kuma ya faru? Kasa magana tayi sai miqa mai wayanta tayi amsa yayi shima ya karanta, salati yayi tayi tare da fadin mai yasa jawaheer zatai haka? Mum tace dole in tafi yola ina tsoran kar tarihi ya mai maita kansa, dad kallonta ya tsayayi tare da fadin koma dai miye kiyi mata addu'a sannan maganan zuwanki yola bai taso ba zanje da kaina in dauko ta, mum tace a'a tare zamu tafi, ganin yanda ta dage yasa dad fadin zasu tafi taren amma gobe da safe, mum badan taso ba dan taso su tafi yau din nan kar abunda take boyewa ya fito fili.












Washe gari tun karfe biyar su mum suka nufi airport dan mum ta matsa sosai,koda suka je airport din saida suka jira dan jirgin karfe 7 zai tashi, kallo daya zaka ma mum kasan tana cikin tashin hankali yau itace zata yola wanda a kalla shekara ishirin da wani abu da suka wuce rabonta da mahaifarta Wani irin hawaye mai zafi ne ya zubo mata a ido, shiga jirgi aka farayi suma suka tashi suka shiga, nan aka rufe jirgi ya daga zuwa garin yola.










Jawaheer tunda tayi sallah asuba, tayi wanka tasa wata doguwar riga gaba daya tun jiya bata cikin yanayi mai dadi, ta rasa dalili ga gabanta dake ta faman fadi, jin nocking tayi dan haka ta tashi jiki a sanyaye ta bude kofar murmushi ya sakar mata yayin data lumshe ido dan kamshin turarenshi ya bugan mata hanci wanda yake kara sa taji ya narkar mata da zuciya, wani irin kyau taga ya karayi yi mata sosai, duk da bawai wani canji yayi ba hasali ma riga da wando ne jikinsa kaman kullum kananan kaya, duka babu wanda yayi ma dan uwansa magana sai itace tayi karfin halin fadin morning, bai amsa ba sai hannunta daya kama sukai dakinshi tare, bayan sun shiga ya zaunar da ita, ido ya kura mata tare da fadin jawaheer maike damunki? Daga kai tayi ta kalleshi taga shima din ita yake kallo dan haka tayi saurin yin kasa dakai tare da fadin babu komai kawai.... Sai kuma tayi shuru, jin muryanshi tayi yana fadin kawai me? Tace gabana keta fadi ban taba jin irin yanayin da nakeji yau ba, murmushi yayi tare da fadin ki yawaita fadin innalillahi wa inna'ilaihira jiun, kai ta daga alaman toh sannan ya kalleta tare da fadin zamu anguwan da dad dina ya fadamin tunda bakya jin dadi ki zauna muje mu dawo, kai ta girgiza tare da tashi tace a'a tare zamu duk inda zaka a cikin kasar nan ina tare dakai,murmushi yayi tare da jan hancinta sannan yace kinyi breakfast? Kai ta girgiza alaman a'a wayan dake dakin ya kira ya fadi abunda yake bukata, bai wani dade ba aka kawo abunda yace, tea da chips nd egg aka kawo, tare sukaci sannan suka fita, motocin da aka kawo su jiya nan suka shiga inda jawaheer ta fada musu inda zasu tace guyuk in anje kuma ace gidan liman, kai tsaye driver din suka nufi hanya, hannun jawaheer na rike dana m samir yana kallon garin yanayin garin ya mishi kyau in yaga abu bai gane ba saiya tambayi jawaheer ta fada mishi, da haka har suka iso anguwan, babu laifi anguwan nada kyau, da tambaya har suka isa kofar gidan, koda suka isa jawaheer ce ta fito tace bari ta fara shiga, yace a'a tare zasu, haka suka shiga cikin gidan,babu laifi gidan yana da kyau duk da ba wani girma gareshi ba, sallama jawaheer tayi, wata yar dattijuwa ta amsa tace waye? Ku shigo, bayan sun shiga jawaheer taga tsohuwar fuskanta dauke da glass dam taji gabanta ya buga da karfi domin sak fuskan mum dinta sai dai kuma wannan tsohuwa ce ita ta girmi mum dinta sosai lokaci daya ta shiga rudani.......




















*maryam obam*


*JAWAHEER*






*STORY AND WRITEEN BY......*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*


*wattpad @maryam-obam*


*WWW.Maryamobamnovels.com*








https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/










*DEDICATED TO.....*


*Nafisa mrs dan malikin kawo*


















Page 20














Muryan matan ne ya katse jawaheer daka duniyar tunanin data fada, tace sannunku ku karaso mana, wani karamin falo ta kaisu wanda daka gani an ware shine dan ajiye baki, falon sai kamshin turaren wuta yakeyi, jawaheer dai bin matar take tayi da ido, domin abubuwa ne fal a cikin ranta, fita tsohuwar tayi jim kadan sai gata da ruwa ta kawo musu, pure water mai sanyi, sannan ta zauna tare da fadin bismillah, m samir kallon jawaheer yayi wacce idonta nakan wannan tsohuwar,kafin yayi magana yaji matar na fadin sai dai ban shaida ku ba, cikin harshen hausa take magana, m samir bai san mai take fada ba dan haka ya kalli jawaheer tare da fadin tayi mata bayani, jawaheer tace da fatan mun sameki lfya hjy, amsawa tayi da fadin lfya qlau, sannan jawaheer tace

7 / 22