Author : Jeeddah jao Category : A Books
[3/2, 5:44 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃 JASEENA🦃⚔ 2016
🐚Na Jeeddah jao🏵🐚
1⃣⏯5⃣
Gudu yake kan wani farin doki mai kyaun gaske da ka ganshi kasan a rude yake ,wata mata ce a bayanshi ta ‘kank’ame shi sai zare ido take yi yayinda shi kuma sai ‘kara gudu yake ,da an hau tudu ko tsauni sai matar ta sa ‘kara ta rike ciki da hannu daya, da ‘kyar ya samu wani kogon dutse ya shige ga dukkan alamu Matar na’kuda take yi domin dauke take da juna , ‘karar dawakai da yaji sun tukaro inda kogon yake yasa ya toshe wa Matar baki da hannun shi ganin tana kuka duk jikinta yana b’ari ,mutanen suka gama dube -duben da zasuyi sai wani daga ciki yace “sun yi nisa sosai!! Mu koma kawai ,a lab’en da suke babu wanda ya motsa har mutanen suka tafi sannan ya cire hannun shi daga bakin Matar da tuni na’kuda ya zo mata gadan-gadan, Allah cikin ikonsa ya jiyo ‘karan ruwa daga d’ayan ‘bangaren kogon ya mayafin ta ya nufi hanyar da gudu ,kafin ya dawo ma har ta haifu Yar cikin Jini Kwance a ‘kasa itama uwar haka ,ruwan da ke jikin tsumman ya d’an matsa a fuskar ta ta dan farfado ,shi da kanshi ya gyara yarinyar ya mik’a mata. Murmushi take yi tana hamdala amma hawaye ne zafafa ke bin kuncin ta ,ta sumbaci yarinyar sannan ta rufe idonta hannunta ta sa ta damk’e hannun mutumin wanda da ka ganshi kaga sadauki, tana salati rai yai halinsa.
🦂wani ‘kara mutumin ya saka wanda duk kogon sai da ya d’auka, ya kifa kai a cikin matar yana ta rusa kuka mai ban tausayi ,idanuwan shi suka rine kamar garwashi ya mik’e tsaye ya d’aga jinjirar sama cikin murya mai firgitarwa yace” masarautar KALAHARI !!! Sai na mayar muku jin dad’i da walwala !! Na lashi takobi!! da ikon Allah sai JASEENA ta zamo ciwon ido ga azzalumi JALALUD-DEEN!!!!
🐚 🐚🦂🦂🦂🦂🦂🦂🦂🦂🐚🐚
Asalin labarin
Masarautar Kalahari babbar masarauta ce wanda ake sakota a matsayi na farko cikin jerin masarautu, mai kuma cike da tarihi, mayak’a da kuma kayan ma’adanai na ‘kasa kamar su lu’ulu’u , gwala-gwalai da sauransu. Sarki Hameed shine ke mulkin Wannan masarauta, mutum ne jarumi ,mai tausayin talakawa gashi da kwarjini. Hameed shine d’a na biyu kuma na k’arshe gun mahaifin su ,ma’ana yana da wa mai suna JALALUD-DEEN ,wanda ya kasance baya son talakawa kuma shi duk abunda zai yi in dai don ya musguna ma talaka ne toh ya fi burgeshi, son zuciya gareshi , hakan ne yasa da aka tashi bada sarautar sai dattijawan gari suka zabi a bawa Yerima Hameed kasantuwar d’abiun sun daban ne kwata kwata JALALUD-DEEN bai chanchanta ya mulki Kalahari ba, a fuska JALALUD-DEEN ya nuna babu wani abu amma dai na ciki na ciki !!domin zuciyar sa tafarfasa takeyi kuma a nan ne ya k’udiri niyyar ganin bayan Hameed !!!
Jeeddah jao🏵
[3/3, 7:07 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵 Jeeddah ja’o🏵🐚
6⃣⏭1⃣0⃣
Bayan an na’da Yerima Hameed a matsayin sarkin Kalahari sai Jalalud-deen ya fuskanci cewa matar sarki Hameed Sarauniya JASEENA tana dauke da juna biyu hakan ya tunzirashi ya kasa zaune ya kasa tsaye ko baccin kirki bayayi tsabar Kishi domin gani yake yi in har Hameed ya samu magaji to tabbas babu makawa ko ‘kamshin sarautar ma zai daina ji…………
🏵cikin Sarauniya Jaseena yana wata tara ,haihuwa ko yau ko gobe ,tana zaune cikin dakinta mai cike da kayan ado da k’yal-k’yali sarki Hameed ya shigo ,mutum ne mai tsayin gaske ga haske kyakkyawa ne wanda ba sai na tsaya misalta shi ba haka ma Jaseena kasantuwar a kasar masar ya auro ta , zama yayi kusa da ita yana zolayan ta suna ta hira ,basu ankara ba sukaji ‘kara a waje ,a tare suka mik’e cikin firgici Jaseena ta rike Hameed ta ‘boye ta bayan shi jiki na rawa yayin da shi kuma ya zare takobin shi 🗡ya rik’e yana dube-dube don yaga ko waye zai shigo Kwatsam sukaji an banke k’ofa kamar daga sama mutanen suka yo kansu nan suka kaure da fad’a ,gashi mutanen fuskar su a rufe da kyar ya iya fisge mayafin d’aya daga cikin su ,abun da ya gani ya matuk’ar girgiza shi !!! Amintaccen shi na fada ne Zakar da wasu wanda ya tabbata fadawan shi ne ,da yaga sarkin yawa ya fi sarkin k’arfi kaway ya figo Jaseena suka fita yayinda mutanen suka bi bayansu ganin Jaseena ta gaza yasa ya kwantar ta bayan wani k’aton tukunya yace yana zuwa ,cikin sand’a yake tafiya har ya isa gurin da dawakai suke ,fito kawai yayi wani kyakkyawan ingarma ya nufoshi fari ne fes ,ya shafa kan Dokin sannan ya haura shima ya nufi inda ya bar Jaseena,ya sameta yanda ya barta cikin ciwon na’kuda ,take ya umarci dokin da ya kwanta ,hakan yayi ma Jaseena daidai yanda zata samu sauk’in daidaitawa a saman dokin ,kafin su ankara sukaji harbi kibiyar ta chaki Jaseena ta gefen ciki ganin sun kusa far musu yasa ya fita a d’ari da dokin suma suka hau dawakai suka bi bayan su har suka samu suka shiga Wannan kogon dutsen……..
🦃🦃🦃🦃🦃 JASEENA. 🦃🦃🦃🦃🦃
Hameed ya d’auki gawar Jaseena ya fito bakin kogon ya tsaya , kasantuwar bai taho da komai ba daga shi sai takobin shi haka ya dinga tono da Wannan takobi har rana ta fito yayi gumi ba na wasa ba hannuwan sa duk sun salube sun ya’yyanke har saida ya gama tono ya sallace ce sannan ya binne ya d’au takobin ya koma cikin kogon ya zauna ya k’urawa jaririyar ido ,tsananin tausayin ta ya kama shi kasantuwar ta zo duniya ne lokacin da uwarta take gangaren barin duniya ,gashi shi bashi da abincin da zai ciyar da ita gata kuma abar tausayi kasancewar ta bak’uwa a duniya ,ya d’aga hannayen sa biyu yace ” ya Allah ga baiwar ka ta zo duniya lokacin da zalunci ya mamaye al’umma Kowa burinshi yaga shine a gaba ,Allah na rok’eka ka raya ta kan tafarki madaidaiciya kuma ka bata ikon kare hak’k’kin duk wani wanda aka zalunta a gaban idon ta ,ya Allah ka kareta da ikon kariyar ka!!!
🏵 Kukan Jaseena(sunan mahaifiyar ta ya maida mata) ne ya katse shi ya je da sauri ya dauketa ya rasa ta inda zai fara domin kuka take na fitar hankali ,kamar ance d’aga kanka sama kawai ya hango wani haske ya hasko cikin kogon kuma ba daga asalin k’ofar da ya shiga ba ne, ya mik’e ya nufi gurin dokin shi ma ya bishi kasantuwar kogon makeken gaske ne …..,
Abunda idon shi ya gane mishi yasa ya zaro idanuwa ya d’aga hannu yana godiya ga Allah .,……..,🦃
Jeeddah jao🏵
[3/3, 11:10 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔
🐚🏵Jeddah ja’o 1⃣1⃣⏭1⃣5⃣ Wata sabuwar duniya ce domin kogon nan zagaye yake da wani dutse wanda tsakiyar Wannan dutse ya kai girman rabin masarautar Kalahari gashi kuma jeji ne sosai mai yawan duhuwa ,kayan itatuwa kuwa babu kalar da babu ga ruwa yana gudana daga saman dutse tsuntsaye sai shawagi suke a gurin ,🕊🕊 , ‘kara da yaji ta wani 6angaren ya tabbatar masa akwai namun daji ciki kuma masu cike da had’ari🐅
🦃ya ja dokin sa har inda ruwan yake hannun shi d’aya kuma rik’e da Jaseena. Ruwa ne mai kyaun gaske ,yanda yake gudana ma abin kallo ne a nan ya dauraye jikin Jaseena dokin shi ma ya sha..nan ne fa Hameed ya fara sabuwar rayuwa daga shi sai dokin shi Zabil da kuma Jaseena wanda mahaifin ta ya maida ruwan kwakwa abincin ta, shi kuma yakan kama kifi ya busar don ya samu abin ci ,ko kuma y’ay’an itatuwa..haka suka yi ta rayuwa a jejin………..🦁
🦂bayan shekaru goma sha shida(16 yrs ltr)🦂
Zaune yake a fadar sa, su waziri sai zuba fadanci ake , wasu maza wad’anda da ka gansu kasan cewa magidanta ne sanye cikin kayan da basu fi a k’ira su da tsumma ba suka shigo fada gami da zube wa ‘kasa suna kwasar gaisuwa duk jikin su sai 6ari yake yi d’aya daga cikin su yace ” Allah ya baka nasara sarki !!! Mun kawo k’arar Yerima !! Ya takurawa y’ay’an mu ko diban ruwa basa iya fita saboda da ya gansu sai ya fasa tulun,shine muk………….kafin ya k’arasa yaji sauk’ar mari Tas!!!! Hakan yasa ya mik’e a firgice yaji an sake kwarfe shi ta k’afa take ya zube ‘kasa warwas !! Sarki ya ja tsaki Mtsew!! Yace ” ni zaku dubi tsabar idona Ku zo min da zancen banza Wai kun kawo karar Yerima? Toh baku isa bah !! Wato har an fara sa mishi ido kenan ? Ina so ku sani ,Rizwan Jini ne na sarauta yana da ikon taka duk wanda ya so kuma babu mai tanka masa ” ya dubi sarkin yak’i yace ” me kuke jira ne Amjad?!!! Aje a rufe min su a kurkuku da kuma horo mai tsananani!! Da sauri sarkin yak’i Amjad ya kama hannayen su ta baya ya tisa ‘keyar su suka bar fada yayinda Jalalud-deen ya koma kan kujerar sa yana maida numfashi kamar wani damisa 🐅
Sarkin yak’i Amjad yana fita da su yayi hanyar kurkuku dasu ,murya ‘kasa- ‘kasa yace sai dai ku yi hakuri da irin Wannan zalunci da ake muku ni na tabbatar cewa akwai ranar da zata zo idon Jalalud-deen sai ya raina fata kuma sai ya zama wulak’antace a idon jama’a!! Yayi d’an murmushin takaici dai dai lokacin sun iso mashigar kurkukun ya wuce chan ciki da su ,sun dad’e suna tafiya kafin su iso d’akin da za’a sa su ,ganin masu gadin na kallon sa ya sa ya hakad’a su ciki a fusace ,gami da rufo k’ofar ya juya idonsa cike da k’walla ya fice Daga kurkukun…..
🗡🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🗡
Gudu take a kan dokin sanye da bak’in dogon wando mai fad’in gaske ta sama , ta ‘kasa kuma a tsuke,rigar jikinta na cikin dogon hannu ne da shi kuma sak’awa akayi da auduga na saman kuma da fata akayi shi bak’in mayafi ne rataye a kanta wanda har ya zagaye fuskar kamar wanda tasa nik’ab baka ganin komai sai girar ta ,idon ta da kuma saman zirin karan hancinta , takalmin k’afarta ma na fata ne ,ta rataya wata y’ar jaka a jikinta sai wani dan biri da ke zaune a kafad’ar ta yana ta fama da ayaba🐒…..
” Hyaaaa!!!” Ta fada gami da bugan dokin ta baya ,yayin da shi kuma ya kara gudu. Sun dad’e suna tafiya kafin su isa mashigar garin tana isa ta sauk’a daga saman dokin ta kama linzamin suka ci gaba da tafiya basu zame ko ina ba sai kasuwar garin nan ta wuce gun wani mai saida ganyeyaki na magani ta mik’a masa jakar , ya karba ya Ciro kad’an daga ciki ya shinshina sannan yayi murmushi ,yace ” yayi kyau Jaseena !! Wannan na’a na’a mai kyau ne !! Ya sa hannu cikin aljihun shi ya Ciro sulalla ya muk’a mata ta kar6a ta juya abunta ba tare da ta ce k’ala ba ……..
Cikin kasuwar ta sake kutsa kai tana ganin yanda Kowa ke gudanar da alamuran sa cikin kwanciyar hankali ,kai tsaye ta nufi gun mai shinkafa ,ya auna mata ta kar6a kawai ta jiyo hayaniya bata ankara ba ta hango dawakai kusan biyar sun dumfaro inda suke ,da wasu matasa a kai sai 6arna suke ,guda daya daga cikin su ya sha ado da kaya irin na alfarma shi ya fi Kowa ma ta’adi a cikin su suna ta buge mutane ,suna zubar musu da kayayyaki ,ta gefen Jaseena suka wuce gami da banke wata mata mai juna ta fad’i ‘kasa kayan marmari da ta siyo ma duk suka zube ,a fusace Jaseena ta dubi mai shinkafan tace “Wannan kuma su waye haka kamar mahaukata ??!!! Mai shinkafa ya zaro ido yace ki rufa ma kanki asiri baiwar Allah!! Wannan shine Rizwan d’an sarki Jalalud-deen !! Ta juya ta sake kallon hanyar da suka wuce tana wani irin murmushi na k’eta ” a ranta tace lallai yau kakarta ta yanke sak’a!!! Mai shinkafa ya ce ” amma baiwar Allah kina garin nan kice baki san Yerima Rizwan ba? Murmushi kawai tayi ta d’auki shinkafan ta sa a Jakarta ta juya ba tare da ta kalle shi ba balle ma ta bashi amsa ,ta nufi gun matar da ta fad’i kasa wanda duk an zagaye ta ana kallo kuma babu wanda ya ma je kusa da ita don ya taimake ta…………….🦃
Jeeddah ja’o🏵
[3/3, 10:16 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔
🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚
1⃣6⃣⏭2⃣0⃣
Kutsawa tayi cikin taron mutanen da k’arfin hali ta samu ta shige inda matar take ta d’aga ta tana yi mata Sannu yayinda sauran mutanen suka watse daga gurin Kowa ya fara tattare 6arnar da akayi masa amma da ka gansu kasan a tsorace suke duk da Jaseena ta fuskanci hakan bai sa ta ko girgiza ba ta d’aura matar kan dokin ta sannan ta ja akalar dokin suna tafiya matar na mata kwatance har ta kaita gidan ta, ta kuma taimaka mata har cikin gida ,wanda ba girma gareshi ba amma sai tsafta ,wani gadon kara ne gefe guda ta hango ta ja matar har gurin ta zaunar da ita sannan ta tashi ta nufi d’ayan 6angaren gidan don nema wa matar ruwa, akayi sa’a ta samu ta d’ebo mata….
Bayan ta tabbatar matar ta samu nutsuwa sai ta tashi zata fice ,hannun ta matar ta rik’e ta ce ” nagode baiwar Allah !! Amma yaya sunan ki ? Ta juyo da murmushi tace ” “Jaseena ” matar ta d’an jinjina kai ta ce ” amma ke bakya tsoro labari yaje kunnen Yerima Rizwan cewa kin taimaka wa wanda ya wulak’anta? Zai ce kin raina mar hankali ,sannan ya sa a miki horo mai tsanani ,kuma gashi ke yarinya ce bai kamata kina k’arama ki jefa kanki cikin had’ari ba !!! Murmushi kawai Jaseena ta sake yi tace ” Kar ki damu umma !! Ni ma ba kanwar lasa bace !!!in yana ji da sarauta nima ina ji da ita !!🗡 ke dai ki kula da kanki kuma ki daina fita ke kad’ai domin hakan ba k’aramin had’ari bane” tana kai Wannan ta juya ta fice gamida rufo k’ofar gidan ,matar ta bita da kallo ,a ranta tace ” yau naga mace mai kamar maza!! Yanzu har a masarautar Kalahari akwai macen da zata iya tsallake dokar Yerima ?? Ta girgiza kai ta koma ta kwanta.
🐚 kasuwar ta k’ara komawa ta gama saye-sayen da zatayi sannan ta juya ta bar garin , da la’asar ta isa kogon su ta shige ta nufi inda tasan kullum mahaifan ta yake motsa jiki da yamma ,wani d’an fili ne ya zagaye da itatuwa a nan ya ke koyawa Jaseena dabarun yak’i ,da gudu ta nufi inda yake ta zari wani sanda suka fara fad’a cikin raha har suka gaji suka bari.
🔥wuta suka hura tana taya shi gasa kifi sai zuba take yi don duk abunda ya faru a Kalahari sai da ta zayyano masa shi dai bai ce ‘kala ba ya ci gaba da gasa kifin ,ganin ba sauraron maganar ta yake ba ta mik’e ta nufi wata duhuwa mai siriryar hanya ,gaba kad’an ruwa ne ke sauk’a ta saman dutse birin ta wanda take k’ira da suna Zainu yana nan kan kafad’ar ta yayinda take Kutsawa cikin duhuwar 🌳 kukan damisa ta jiyo hakan ya sa ta wata Yar siriryar dariya ta kama wata reshe kamar biri tana lek’o inda taji kukan ,domin takan ji kukan ne tun tana Yar yarinya amma bata tab’a yin gaba da Wannan gurin ba kasantuwar daga Wannan dutsen mai ruwa babu wani guri a gaba balle ta ce ko daga chan ta jiyo k’ara. yau de ba Jaseena bace zata fita ,mahaifin ta Hameed ne zai fita duk da ranta bai so ba amma tasan bata isa hana shi fitan ba ,kamar kullum ya debi ganyeyaki a jaka ya ja Zabil suka fice …..tana cikin wasa da zainu su kama Wannan reshen su saki wancan Kwatsam ta sake jin Wannan kuka na damisa ,ai kuwa nan ta k’udiri niyyar sai ta gano duk inda Wannan ‘kara ke fitowa !!! Diro wa tayi daga saman bishiyan tabi hanyar da ta jiyo karan kamar kullum de bakin dutse take riskar kanta amma yau tace bazata juya ba sai taga menene a bayan ruwan da yake zuba kuma zata nemo inda Wannan damisa take
; Hawa tayi kan dutsen duk ruwa yana ta jik’a ta a hankali ta mika k’afan ta gaba taji dai ya zauna ai kuwa sai ta kutsa kai ,zainu kuwa tun da yaga ta shiga ruwa ya koma gefe yana kallon ta itama bata biya ta kanshi ba tai shigewarta………….
Wata Yar siriryar hanya ce a ciki sai duhun tsiya amma don rigima ta shige sai tafiya take ,har tayi tsakiya ta juya tana kallon hanyar da ta baro