JASEENA COMPLETE Book by Jeeddah jao.txt

Author :  Jeeddah jao Category :  A Books

Chapter   2 / 5

3K to 6K   out of 13.4K words

,sai kuma ta tabe baki ta ci gaba da lulawa……………


Jeeddah jao
[3/4, 7:41 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


2⃣1⃣⏭2⃣5⃣


Ta kai ak’alla minti talatin tana tafiya wani wajen ma sai ta sunkuya don ta wuce amma bata fasa ba har sai da takai wata Yar k’aramar k’ofa wanda aka toshe bakin da Yar ciyawa tasa hannu ta ture ciyawar dayake rana ta kusa faduwa Hasken wanda yay ja ya dalle mata ido sai kakkarewa take da hannun ta ,cikin dabara ta fito daga ramin dutsen ta tsaya ta jikin dutsen tana bawa idonta abinci domin banda dajin da yake gurin tana hango wani gini mai tsayin gaske ga kyau ,da gani kasan masarauta ce amma gaba yake da dajin shima ta hango shi ne don tana saman dutsen ne ta hango amma akwai wata siriryar hanya da ta bi gurin. Daji ne mai kyau don har yafi na inda suke kyau, da gudu ta juya tana dariya ta koma kogon bata yi wata wata ba sai gida Zainu na ganin ta yai tsalle ya koma kafad’ar ta yay zaman shi ita kuwa ganin yadda tayi datti yasa yasa ta nufi inda take wanka gefen Wannan ruwan tai ta wanke jikin ta tana wasa da ruwa ,k’iran da babanta yay mata ne yasa ta fita da sauri ta nufi inda taji Muryan shi ,fuska a turnuk’e yace “ina kika je?!!!” Nan ta fara kame kame ya juya ya barta gurin bai kuma cewa qala ba….


Cikin sand’a ta nufi d’akin ta, gami da turo k’ofar shi kuwa Hameed sai da ya gama kaifa takobin shi sannan ya wuce d’aki. Cikin dare ya kasa bacci domin jikinshi na bashi akwai abunda zai faru ,duk zuciyar shi sai bugawa take ya rasa dalilin faruwar hakan ,ya d’auki takobin shi ya nufi d’akin Jaseena wanda itama ba baccin take ba ,tana ganin shi ta tashi ta zauna tace ” baba na mai ya sameka? Yaya na ganka cikin daren nan? Murmushi yayi sannan ya kama hannun ta ya d’aura takobin ta daga kai tana dubanshi bai daina murmushi ba har Lokacin yace ” Jaseena !! Ko ma me zai faru yau d’in nan ka……….. Kafin ya k’arasa yaji motsi a waje tuni ya ce Jaseena ta fita ta bayan d’akin amma ta ture Wai itama zata iya fad’a ai kuma bazata tafi ta bar shi ba ,ya gaura mata mari wanda tsabar ta rikice sai da taga wuta🔥 ya ce ” nace ki tafi !!! Cikin kuka ta zari jakar ta na fata ta rataya zainu na biye da ita ta fice ta kofar bayan shi kuma ya fita don ya duba me ke wakana. Sauk’ar itace yaji a kansa wanda hakan yasa shi k’ara da zubewa a ‘kasa sumamme , duk abun nan da ya faru a idon Jaseena ne domin la6e wa tayi tana ganin duk abunda ke faruwa duk mutanen ta ga fuskokin su kasancewar Hasken farin wata duk ya mamaye gurin suka jashi suka tafi da shi ,nan ta zube tana wassu zafafan hawaye na takaici, a ranta tace ” toh ya akayi suka gano inda baba ya 6oye? 🗡……,


🐚🕸🕸🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🐚


Kafin kace wani abu har gari ya waye Jaseena na idar da sallah tana goge takobin da Hameed ya bata kawai taji takun mutane ,cikin sauri ta haye wata bishiya cikin duhuwa zainu ma ya bita , a hankali suke magana tana jin su ,”sarki yace a duba ko akwai Dan sa ko kuma d’iya domin da ciki a jikin matar sa ya baro Kalahari !! Jin haka yasa Jaseena ta diro ta yi hanyan Wannan kogon wanda ke bayan ruwa mai zuba ta shige Wannan ramin Wannan karon har da zainu a tare da ita tana dirowa ta d’auki Yar ciyawar ta maida shi gurbin da yake ta fara tafiya tana bin Wannan hanyar da ta gani sai kalle kalle take yi zainu kuwa an samu bishiyoyi ya hau wancan ya kama wancan. Har lokacin bata daina kuka ba ,don tsoro take yi Kar a kashe mahaifin ta.. Gurnani ta jiyo ta gefen hanyar kamar na zaki ai kuwa Kwatsam yayi tsalle ya tare gabanta 🦁 ta tsaya chak a gurin ta zubawa sarautar Allah ido , bata ankara ba taga wani kyakkyawan sadauki a gabanta ya tsugunna yana shafa kan zakin ,damtsen shi ma. Kad’ai abin kallo ne shi kanshi kamar zakin yake ga gashi har Ka fad’a wata Yar farmalam ce a jikin shi wanda gabanta a bud’e take ya rataya kwari da baka a bayanshi takalmin ‘kafar shi kuwa na fata ne , ya mik’e yana kallon Jaseena sannan ya k’arasa kusa da ita ,hawayen da ya gani a fuskar ta yasa ta bashi tausayi saidai ba tare da yace komai ba ya ciro k’ullin gurasa a jakar shi ya bata ,kamar yasan tana jin yunwa. Da sauri ta wafce ta nemi guri ta nad’e k’afa ta fara ci ,chan sai ta tuna da mahaifin ta, hawaye na zubo mata sai chusa gurasar take yi tsabar ta zuciya ,har ya shak’e ta ta fara tari kamar dama jira yake , matashin ya ciro wata Yar gora na fata ya mik’a mata ta kar6a sai bayan ta d’an nutsu sannan ta dubeshi tace ” nagode !!👏🏽 murmushi kawai yayi ya yi mata nuni da hannu ma’ana ta tashi su tafi , nan ne ta gane cewa baya magana kuma ba kurma bane yana ji sarai amma baya iya magana ,saidai akwai kyau kamar balarabe , ta tashi ta bi bayanshi suka ci gaba da tafiya har suka k’ure Wannan dajin ,abin da ya bata mamaki shine wani tafkeken kogi ne a gurin saidai daga bakin ruwan ma kafi ganin masarautar ,jirgin ruwa suka shiga mai tuk’in yan ta fama da tuk’in shi kuwa sai wasa da ruwan yake yi…..,…….🦃


Jeeddah ja’o🏵
[3/17, 11:35 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚


2⃣6⃣⏭3⃣0⃣


Isarsu masarautar ,bai zame da su ko ina ba sai cikin hanyar fada ,yana gaba tana biye da shi cikin ranta tace ” yanzu har akwai masarautar da bawa zai dinga kutsa kai cikin fada ba tare da izini ba? ” bud’ewar wata k’atuwar k’ofa ne ya katse ta daga tunanin da take yi ,kai ya kutsa ba tare da fadawan sun Hane shi ba har ya k’arasa ya nemi guri ya zauna ……..🦃


Zubewa tayi itama tana kwasar gaisuwa kamar yadda yayi sannan ta gyara zama. Wani bak’in mutum ne wanda fuskar shi ba wani almuru don ko murmushi da yake yi kamar dole aka sa shi yake yi . ” yarima har an dawo ne!!? ” tambayar da sarkin yay masa kenan ,yayin da shi kuma saurayin ya gyad’a masa kai ,nan yaci gaba da yi masa kwatance da hannu irin na kurame ita dai Jaseena ta zuba musu ido cike da mamaki da kuma tambaya dake cikin zuciyar ta ” me yasa Yerima guda babu ko hadimai balle shiga ta alfarma?! ” don ita da tayi zaton bawa ne😄 gashi kuma kyakkyawan gaske amma mahaifin sai bak’i da muni 😂 ,ta d’an jinjina kai tace ” hala mahaifiyarsa ya biyo”
Maganar sarkin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga ” Yaya sunan ki baiwar Allah? ” shine abunda yayi karo da kunnen ta. A d’an rusune tace “Jaseena”. Sarkin ya d’an yi murmushi yace ” daga yau na baki masauk’i cikin masarauta ta domin Yerima Haidar ya sanar da ni cewa 6ata kikayi ,toh nan ya zama miki gida kina da iko ki shiga duk inda kike buk’ata a masarautar nan ! Tai ma sarki godiya sannan Haidar ya ja ta suka fice daga fadar ya mik’e da ita har wani hanya daban wanda ta yi nisa sosai da fada ga k’ofofi kala kala masu kyau da kwalliya ga fitilu masu haske abin ba’a cewa komai …..
Wani d’aki ya nuna mata ta sa hannu ta bud’e ta shiga da murmushin ta zainu na biye da ita ,shima murmushi yayi sannan ya juya ya fice daga wajen yayinda ta bishi da kallo kamar Yar k’auye.


🐚🐚🐚🏵 🏵🐚🐚🐚


Yau kwanan Jaseena uku a Wannan gari wanda ko ita kanta bata san sunan garin ba ,Haidar kuwa kusan kullum da safe sai ya lek’o don ya duba lafiyar ta ,haka take wuni ita kad’ai sai zainu yana d’ebe mata kewa kasantuwar Haidar bai cika dawowa da wuri ba in ya dawo ma sai gari ya waye yake duba su….” Yau kam sai na fita na zaga gari!!” Cewar Jaseena kenan tana ta faman gyara zaman dogon rigar da ta saka ,sai duba kanta take ta madubi don bata saba saka irin kayan nan ba ,ita kanta ya mata kyau ,sannan ta dauki mayafin wanda da shi da kwalin tata duk d’aya ta yafa a kanta ta nannand’e ta fice zainu na binta a baya kamar yadda ya saba , tana tafiya tana faman tattare riga don yadda yake Jan ‘kasa a haka har ta bar fada ,tana ta kalle kalle ta tsaya can ,ta ta6a wancan , tana cikin haka har tayi nisa da masarautar a can nesa ta hango wasu mata guda uku kowacce da tulu sun sha ado sai ture -turen juna suke a kan hanya suna ta raha……
Cikin sauri Jaseena ta k’arasa inda suke ,tana iskesu ta sa hannu ta ta6a kafad’ar daya daga cikin su duk suka juyo suka k’urawa Jaseena ido sai kuma suka bushe da dariya suna nuna ta da yatsa 👉🏾 hakan yay matuk’ar bawa Jaseena haushi ta yamutsa fuska tace ” toh me nayi kuke min dariya !!😠. A tare suka tsare kamar da gaske sannan suka sake bushe wa da dariya ,wata Yar siririya sosai tace ” ke kuma Wacece haka !? Ko rigar ma bata iya sak’awa ba Yar k’auye kawai!! Suka juya suka ci gaba da tafiya yayinda ita kuma Jaseena ta tsaya Kallonsu har suka shige ta daina hango su ma……………🦃


🏵Jeeddah ja’o🏵
[3/18, 9:58 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚


3⃣1⃣⏭3⃣5⃣


Duk Wannan abun da ya faru Haidar na tsaye yana kallon ta ,shi ma kanshi ta bashi dariya kawai ya tsare ne,kwata – kwata rigar baibai ta saka shi bayan haka kuma gaba a baya ,duk da hakan da tayi yay matuk’ar yi mata kyau amma ba daidai bane shi yasa matan ke mata dariya….


🎗Nan ta nemi k’ark’ashin wata y’ar bishiya ta zauna tana ta 6ata rai harda d’an hawayen ta ,tace ” ai yanzu da baba ne bazai min dariya ba cewa zai yi yayi min kyau !! Toh ma miye laifin kayan nan tunda dai ba tsiraici na bari a fili ba!!!Mtsew!!!” Take ta zabura ta mik’e tace” Baba!!!”


🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸


Kwance yake cikin wani matsatsen d’aki mai duhun gaske duk ruwan datti ta nan yake biyo wa ,ya tashi ya mik’e tsaye sai kai kawo yake a d’akin yana cizon le6e ,duk tunanin shi ya koma kan y’ar sa Jaseena addua kawai yake yi Allah ya sa Kar su gano ta ,Allah yasa basu kamata ba duk da yasan k’arfin damtse na y’arsa da kuma wayo irin nata. ” HAMEED!!! K’iran da waziri Zakar yayi masa kenan , hakan ya sa shi juyawa cikin sauri fuskar shi a d’aure. ” kamar yadda muka kamoka kamun wulak’anci haka zamu kamo d’iyar ka da kake tak’ama mai k’arfi ce mu wulak’anta ku a bainar jama’a !!! Hhahhah !!!!! ” Zakar kenan yayi Wannan magana ,bai ankara ba yaji an shak’e wuyan shi har saida idanuwan shi suka fito kwala kwala ,ya kasa magana. Hameed kenan !! Yana cikin kurkuku ma amma k’arfi na nan !!💪🏼. Wasu masu gadin gurin su biyu ne suka tunkari inda suke da ‘kyar suka cire waziri daga rik’on da Hameed yay masa sukayi waje da shi ,yayinda shi kuwa gogan ya koma ya zauna yana maida numfashi 😤………….
👑. 👑
A tsayen da take tana tuna halin da mahaifin ta zai shiga a Kalahari taji durowar abu ta bayanta tuni ta zari wata y’ar wuk’ar ta ta juya zata kai hari ,hannu ya sa ya tare ,wuk’ar ta yanke shi a hannu. Tana juyawa taga ashe Haidar ne 🙄ta zare ido,a rikice ta cire gyalen da ta rufe
kanta ta raba gida biyu ta d’aure masa yankan da tayi sai bashi hak’uri take yi ,ga dukkan alamu bai ji zafin ciwon ba sai murmushi yake mata ,jiki a sanyaye ta nemi guri gefen bishiyar ta raka6e tana y’ar hawaye….
Wata murya mai dad’in gaske da ratsa zuciyar duk wani mai sauraro taji yace ” Jaseena!! Ai barin kashi a ciki baya maganin yunwa ,inaga lokaci yayi da zaki sanar da ni matsalar ki wata’kila na nema miki mafita ko in taimaka miki!! Kinga dukkan mu nan ko wanne yanada matsalolin da yake neman mafita amma 6oye su bazai amfane my da komai ba har lokaci ya k’ure mana !! A firgice ta juya tana neman inda akayi maganar amma ta rasa domin ta lura babu Kowa a gurin sai Haidar da har Lokacin murmushi kawai yake yi rik’e da hannun shi yana kallon ta da kuma mamakin yadda ta rikice tana neman wanda yayi magana………


Ta dawo gaban Haidar tana kallon cikin idon shi tace ” bakaji wani yayi magana ba ? Baka ga wanda yayi ba?” Murmushi ya sake yi sannan yace ” ni nayi miki magana Jaseena !!” Nan ta tabbatar tabbas shi ne yayi magana ,kafin ta ce komai ganin yadda ta saki baki kamar wawuya yasa ya fisge hannun ta yabi wata hanya da ita sai cikin wani daji dake gefe da gurin ,kan wani gungume ya nuna mata ta zauna ,yace ” eh nine nayi magana ! Kuma ke kad’ai ne kika san hakan ko sarki bai sani ba ,kuma ina so ki rik’e shi a zuciyar ki ,duk Lokacin da kike buk’ata muyi hira to kizo nan amma Kar ki kuskura wani yasan ina magana !” Kai kawai ta girgiza mishi cike da mamaki har lokacin ta kasa nutsuwa…,……….🦃


🏵Jeeddah ja’o🏵
[3/19, 12:16 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚


3⃣6⃣⏭4⃣0⃣


“Dama kana magana ne?” Shine tambayar da ta fara fita daga bakin Jaseena. Haidar yayi wata Kyakkyawar dariya yace ,ina magana amma banda iyayena babu wani mahalukin da yasan hakan ko sarki Hasheem da kika gani bai sani ba ,duk da shine silar dawowa ta hakan !! Duk Wannan maganganu da yake yi babu abunda Jaseena ta fahimta duk ya dagula mata tunani , Ta mik’e tace in na fahimce ka ,kana so ka ce min kai ba d’an Wannan sarkin bane ? Kuma akwai abunda kake 6oye masa a matsayin sa na wanda ya yi rainon ka?
Wata dariya ya saki mai ban mamaki yace ” Jaseena duniyar tamu zagaye take da azzalumai masu bak’ak’en zuciya da son abun duniya !! Zan baki labari na da kuma dalilin da yasa na zama haka ,amma kafin na baki labari ina so ki min alk’awari babu wanda zai san ina magana a cikin masarautar nan ko da wasa ne! ” Jaseena ta furzar da iska daga bakinta tace ” inshaa Allah bazan bari Kowa ya san da Wannan zancen ba !! Sirrin ka zan killace shi kuma na bashi mazauni na musamman a zuciya ta !!” Murmushi yayi yace na gode !! Amma yanzu muje in nuna miki gari ,gobe zan sanar da ke tarihi na in Allah ya yarda ” Jaseena ta d’an 6ata rai tace” me yasa bazaka fad’a min yau ba? ” murmushi kawai yayi yace ” muje ” ya tashi ya mik’e ita ma tabi bayan shi har ta sa k’afa zata tafi sai tace ” kai ka je !! Ni zan gyara riga na, ba tare da ya tanka ba yayi tafiyarshi ita kuma ta juya rigan ta gyara tsaf sannan ta fito daga duhuwar da take …
Tsaye ta same shi a gefen Wannan bishiyar yana jiranta ” na gama mu tafi” shine maganar da ta ratsa kunnen sa ,ya juyo ya k’ura mata ido kamar ya had’iye yace ” muje” ya fara tafiya ta bi bayanshi sai fama da doguwar rigar takeyi duk ta mata nauyi ta tattare rigar har guwiwa hakan yasa ta bata sauri sai ta d’an ruga ma take iske Haidar duk da ya ga yadda take fama da rigar wanda hakan ya bashi dariya matuk’a amma ya kafse kamar bai san ma tana yi ba .


⚜kasuwar garin ya fara kai ta ,sai kalle kalle take yi ,Kwatsam ya bi da ita layin sayar da tsuntsaye ,su Jaseena an samu abun yi ,nan ta dinga bin keji keji tana ta dariya kamar pagal (mahaukaciya) shi dai haka yake a tsare sai tafiyar shi yake in taga yayi nisa sai ta sa gudu ta taro shi ,ga shegen surutu kamar aku ta sha gaban shi yana tafiya ita kuma tana tafiya da baya baya ,” kai nace ka d’an tsaya mana sai sauri kake yi ko baka ji na ne!! ? A garin ja da baya ta banke wata budurwa ta d’ebo kwai a kwando ta fad’i k’asa kwayayen suka fashe ,a gurin ta daskare ta kasa magana ,budurwar ta mik’e tana karkad’e jikinta yayinda Jaseena ta sunkuya tana kwashe mata wayanda basu fashe ba sai hak’uri take bata. Murmushi yarinyar tayi tace ” babu komai !! Ba kece wadda muka gani dazu zamuje deban ruwa ba?” Jaseena ta d’an d’aga kai alamar tunani tace “🤔 ” Eh nice !! Ina sauran guda biyun suke?” Yarinyar tayi murmushi tace suna can gida ni sunana Jauda , ke kuma fa?” Ni kuma Jaseena! Shine amsan da Jaseena ta bata .


Ta juya sai dube dube take yi bata ga Haidar ba murya can k’asa tace “toh shi Wannan ina ya tafi ne?!” Murmushi Jauda tayi tace ” tun yaushe ya tafi!! Kizo mana mu tafi tare zamu nuna miki cikin gari ni da yan uwa na !” Da ‘kyar Jaseena ta yarda ta bi ta suka tafi………….


🏵Jeeddah ja’o🏵
[3/21, 9:24 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


4⃣1⃣⏭4⃣5⃣


Suna tafiya tana mata hira har suka isa wani babban gida ,ginin mai tsayi ne sosai ga kyau kuma tare suka shiga kai tsaye hanyar d’akin girke -girke suka nufa yarinyar ta ajiye kwandon kwai din ,a d’ayan 6angaren kitchen din kuma wayannan yan matan nan ne da suka mata dariya tare da

2 / 5