Author : ESHAAT SMILER Category : Hausa Book Store
da sirfani da stones
a jiki, a daidai k`irjin rigar kuma anyi wani rubutu
da stones din an rubuta *"AM PLUS 1",* Sannan
aka zagaye rubutun da zanen flower daya k`ara
k`awata rubutun, daga bayan rigar tayi nan ma
naga an rubuta *"IT`S KERRY"* shima an
k`awata shi kamar yanda akayi ma na gaban,
"tir k`ashi!" Kawai na iya furtawa, ba komai na
fad`a maku akan kyawun rigar ba, idan nace sai
na zayyane maku yanda take duka tou za`a ci 10
pages ne, just close your eyes ku hango yanda
rigar take (lol..).
Da gudu wata budurwa ta shigo wadda da
ganin ta an san `yar aiki ce, fad`i k`asa tayi cike
da girmamawa kanta sunkuye alamar tana son
yin magana amma sai an bata izini sannan
zatayi.
"Go on" kerry ta fad`a cike da raini.
"Ma You have a visitor",
"Let her in" ta fad`a a tak`aice.
Kamar yanda ta shigo d`in haka ta fita, tsaki
Kerry tayi a bayyane wanda yayi daidai da
shigowar Deezee.
Amrah and Rerbee`art sk novels
Admins
ONLINE HAUSA READERSí ½í³š
YINI ÆŠAYA 5-6
By babymsh 08:27 No comments
[11:54pm, 19/09/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: í ½í²€
*A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
*~hannu biyu writers~*
Page5⃣
Har k`asa Deezee ta duk`a ta gaishe da kerry,
"Thank you" kawai ta fad`a tare da zama bakin
gado.
"Can I start?" Kerry ta tambaye ta cikin ladabi
kamar tana magana da babarta.
"Yes you can, ina son makeover na kirki
wanda baki tab`a yiwa kowa ko mai kama dashi
ba, zan baki naira dubu hamsin idan kika min na
kirki, pink, ash and black ne za`a had`a",
deezee lashe moneyí ½í¸œ tuni ta fara rawar jiki da
fara`a taji zancen kud`i, "fara saka kayan dan
kar ayi kuma wurin sakawa a b`ata wani abu",
"Good idea" kerry ta fad`a tare da zira
had`ad`d`iyar rigar a jikin ta.
Nan suka hau makeup baji ba gani, abunka ga
mutun kyakkyawa dama, babu kwalliyar ma tayi
kyau ina ga Deezee makeover ta mata.
*Karfe 4:45pm*
*~Gidan su Afnan.~*
Bayan ta gama kwalliyar ta duka ta saka
kayan ta d`aura after dress akai, nan fa ta fara
tunanin yanda zata fita, gashi kuma ta fad`awa
Momy bata da lafiya d`azu,
D`aukar wayar ta tayi ta kira MD, bugu d`aya
kuwa ya d`aga,
"MD ba kanta fa" ta fad`a bayan ta koma kan
gadon ta.
"Me ya faru ne `yan mata?",
"Na rasa kalar k`aryar da zanyi in bar gida fa,
gashi nama momy k`aryan banda lafiya da safe
dan kar inje islamiya„ ka bani idea pls".
Shiru yayi na wani lokaci kafin yace "to fa!
Bari zan kira ki yanzu".
Tsinke wayar yayi ya fara tunanin kalar k`aryar
da Afnan zatama momy, "yess" ya fad`a a
lokacin da wani tunani yazo masa, kiran wayar
ta yayi ringing d`aya ta d`auka,
"MB ya?" Ta fad`a rud`e.
"Idan kinyi kwalliya ki goge ta, ki nemi after
dress ki d`ora hijabi a kanta, ki k`irk`iri kukan
k`arya sosai kice baban su Esee ya mutu, yanzu
aka kira ki aka fad`a miki shine kike so kje, idan
tayi insisting zata biki jana`izar sai kisan yanda
zakiyi ki hana ta",
sosai taji dad`in wannan shawarar, "saisa
nake sonka MD, a duk *Arewa Stars* kafi kowa
brain mai kyau", daga nan ta tsinke wayar tana
mai jn dad`in shawarar da MD ya bata.
*karfe 4:50pm*
*~Gidan su Feenat.~*
Ummah ce zaune akan sallayar ta tunda ta
gama sallar la`asar take zaune tana ta lazumi, a
hankali Feenat ta fito cike da tsoro ta duka har
k`asa, ta kasa fad`in komai jikin ta sai rawa
yake, har a ranta tayi nadamar shigar ta group
d`in *Arewa stars* sai dai kuma duk wanda ya
shiga baya fita kuma tasan haka, tausayin
ummanta take sosai yanda take k|ok`arin
tarbiyyantar da ita ba dare ba rana.
Ganin Feenat ta zauna kusa da ita kuma tayi
shiru yasa ta ajiye casbahar hannun ta tace
"Safeena ya akayi ne? Knzo kin tasa ni gaba
kuma kin kasa fad`in komai",
Da k`yar ta iya furta "ummah d`azu bayan
tafiyar Afnan ta koma gida ne ta kira ni wai an
kwantar da momy`n ta asibiti, bata da lafiya
sosai dan aiki ma za`a mata gobe,shine nake
son naje ganin ta",
"Ashsha kuwa abu bayyi dad`i ba, ya kamata
kam ki hanzarta ki gano ta, ki gaishe min da ita
sosai" ta ciro d`ari uku daga jikar ta ta mik`ama
Feenat tace "ki sai mata kayan marmari da
wannan ki kai mata, wannan d`ari biyun kuma
sai ki hau napep dashi" ta sake mik`a mata
wasu kud`in.
Wasu irin hawaye suka fara ma Feenat
ambaliya, sosai ta k`ara jin tausayin ummanta,
me yasa ta zab`i wannan rayuwar fiye da farin
cikin ummanta? Tunanin da take kenan a ranta,
"Tou ki daina kukan mana Feenat insha Allahu
zata samu lafiya, ki tafi ki kula da kanki kiji
tsoron Allah kuma", duk lokacin da Feenat zata
tafi wani wuri ko makaranta ne sai ummanta
tace mata taji tsoron Allah, takan yawan tuno da
wannan maganar a duk lokacin da zata je wani
party.
Amrah and Rerbee`art sk novels
Admins
ONLINE HAUSA READERSí ½í³š
[12:00am, 20/09/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: í ½í²€
*A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page6⃣
*Karfe 4:56pm*
*~Gidan su Afnan.~*
Tuni Afnan ta k`wak`ulo hawayen dole tana
mitsitstsikar ido kamar da gaske, ba wuya kuwa
idon ta yayi jajir, da gudu ta fita parlor tana
kiran "momy! Momy!!",
Momy`n na daga d`akin ta tace "gani a d`aki
na Afnan, lafiya!?"
"Ba lafiya ba momy" ta k`ariso d`akin tana ta
sauke ajiyar zuciya kamar da gaske.
Momy tace "lafiya? Me ya faru?"
"Momy baban su Ihsan Abdallah ne ya rasu
yanzun nan ta kira ni, bama a kawo gawar sa ba
wai sai gobe da yake hatsarin jirgin sama ne
sukayi",
Momy ta dafe k`irjin ta tace "mun shiga uku!
Allah sarki na tausaya masu, yanzu shikenan sun
zama marayu, in ko haka ne barin saka hijabi na
sai mu tafi tare",
Saurin katse ta Afnan tayi tace "noo momy ki
zauna kawai tunda ba`a kawo gawar saba,
nasan sai zuwa gobe za`ayi jana`izar shi kinga
sai kije goben, yanzu zanje inta bata hak`uri dan
nasan yanzu tana can tana kuka",
"To ba damuwa Afnan, Allah ya mashi rahama,
idan ta kama ma sai ki kwana acan tunda
mutuwa ta kauda komai",
Sosai Afnan taji dad`i amma a zahiri ta nunar
da wannan mutuwar ta tab`a ta sosai.
*Karfe 4:58pm*
*~Gudan su Ruky.~*
"Mamy har na shirya kin ganni nayi kyau?",
Ruky ta fad`a tana wani jujjuyawa a gaban
Mamy`n su.
"Kinyi kyau sosai auta na, ina mai tabbatar
miki da yau sai kinfi kowa haskawa a gurin, su
o'e da ba`a waye ba kuma a haka za`a k`are
fad`in Allah yace annabi yace kamar kansu farau
musulunci" ta k`arisa maganar tana kallon
Rumaysah, itakam ko a jikin ta, dan tasan duk
da tsanar da mamy ke gwada mata saboda bata
halayen banza bazai hana ta samun mijin kirki
ba, kullun tana ma mamy da k`anwar ta addu`ar
shiriya dan wannan hanyar da suka d`auka
hanyar kirki sam ba hanyar kirki bace.
Key`n motar mamy ta d`auka sannan ta fice,
nan ta kira Triple A ya fad`a mata a inda za`ayi.
*Karfe 4:59pm*
*~Gidan su Iby.~*
har a wannan lokacin Iby na zaune ya rasa
yanda zayyi ya d`auki d`aya daga cikin motar
yayan sa, ganin yake girma ya fad`i idan ya hau
mashin ya tafi, barin kuma a dam d`in Ajiwa
za`ayi party`n ba cikin gari ba, sand`a yayi a
hankali ya shiga d`akin Mukhtar, ya samu baya
nan tunda ya tafi masallaci bai dawo ba,
makullin camry CE ya d`auka cike da murna ya
tafi.
*
*Karfe 5:15pm.*
*_~AJIWA DAM~_*
A daidai wannan lokaci ne kowa ya hallara a
bakin ruwan ajiwa, an k`awata gefen ruwan da
kyakyawan decoration, abunda yafi komai kyau a
wurin shine yanda kowa ya saka kaya ash, pink
and black, ga wani sauti da yake tashi a hankali
a hankali, Kerry uwar birthday kuma tana cikin
mota bata fito ba har sai DJ ya gano wak`ar da
zata shigo da ita.
Muje zuwa (inji Asea Bashir),
This is just the beggining.
Amrah nd Rerbeeart sk novels.
Admins
ONLINE HAUSA READ
YINI ÆŠAYA 7-8
By babymsh 08:28 No comments
[5:09pm, 20/09/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: í ½í²€
*A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page7⃣
Wak`ar *broken angel* aka saka a lokacin
shigowar Kerry, cike da k`asaita ta fito daga
motar ita da saurayin ta Triple A, hannun su
sak`ale da juna suna wani taku kamar basa son
taka k`asa,
Ihu duka wurin aka d`auka take suka fara
fiddo wayoyi suna snapping nasu, tafi kake ji
sosai wurin da k`arfi, kai da kagan su kasan
suna cike da farin ciki tsantsar shi, banda Feenat
data ware kanta gefe cike da haushin zuwan ta
wurin.
*karfe 6:30pm*
A lokacin ne za`a yanka cake, nan aka hau tafin
yanda Triple A ya kama hannun Kerry ya d`ora
akan cake d`in, hotuna sosai suke d`aukar su
kuma a lokacin ne hotunan sukafi yin kyau
saboda rana ta fad`i hasken flash lights yafi fita
da kyau.
Sautin kiran sallar magrib ne yake fita
kad`an kad`an daga wani masallaci nesa da dam
d`in, da alamar dai can cikin garin Ajiwa yake.
Feenat ce zaune tana tunanin yanda za`ayi tayi
sallah, can wata dabara ta fad`o mata, a bakin
wani famfo taje tayi alwala ta bud`e handbag
d`inta ta zaro hijabin ta ta saka, can daga gefe
inda ba`a jin kid`an ta koma tayi sallar ta
sannan ta dawo cikin mutanen.
*k`arfe 7:30pm*
Cashewar su suke sosai kowanen su ya kama
partner d`in shi, a hankali na fara jiyo wani sauti
mai had`e da wani irin kuka_kuka kamar kukan
shanuwa ko alade, sukam da yake sunyi nisa a
casun su har yanzu basu fara jin shi ba, tun
sautin yana fitowa kad`an kad`an har ya fara
yawaita, sautin wak`a na fita daban sannan na
wancan kuka kukan ma yana fita daban, sai
kuma yanda kururuwar take k`ara tashi sosai.
Feenat ce keta bige hannun MD dake faman
shafar gabanta har yana k`ok`arin kai hannu
cikin rigar ta, kunnen ta ta kasa sosai dan yanda
sautin abun yake fita har ya fara yin yawa, ido
ta fara zarowa í ½í¸³ tana kasa kunnuwan ta cike da
tsoro da fargaba, da k`arfi ta buge ma MD
hannun shi wanda yasa shi dawowa hayyacin
sa,
Da sauri ya koma wurin Reeshat dake rawa
ita da MC, rungumo ta yayi ta baya ya fara
shafar ta a hankali, nan sukaci gaba da
romancing juna cike da jindad`i.
Itakam Feenat sosai hankalin ta ya tashi, nan
ta fara tunanin to wannan kururuwar ta mecece?
K`ok`arin magana take masu amma muryar ta
bata fita saboda sautin wak`ar dake tashi.
"Na shiga uku ni Safeenat! Wannan k`arar ta
mecece? Kar dai namun daji ne zasu cinye mu"
ni kuwa Amrah nace in namun daji ne ma ai da
abun yazo da sauk`i saboda akwai hanyoyi da
yawa zaku iya guduwa.
Sosai wannan k`arar take k`ara yawaita, a
hankali sautin speakers d`in ya fara canjawa
yana komawa irin wancan sautin na kuka,
Reesha ne yace "oh common! Dj wannan kukan
daka kunna mana fa? Abeg ka canja shi mana,
abu kamar kukan jaki", Sally dake rungume da
Reesha tayi dariya tace "wuce jaki ma wannan".
Amrah and Rerbeeart sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERSí ½í³š
[5:22pm, 20/09/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜:
í ½í²€ *A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page8⃣
Sautin ne ya k`ara d`aguwa sosai, Dj`n ma
hankalin shi ya soma tashi, shidai a iya sanin
shi bashi da wannan sautin a duk wak`ok`in shi,
k`ok`arin wucewa ya fara yi amma d`if! Wayar ta
d`auke, dvd d`in ta mutu, ga hasken fitilar duka
ya mutu, sai wannan sautin da yake ta k`ara
yawaita.
Feenat jiki sai rawa yake, ta ambaci sunan
Allah amma sam ta kasa, ga wani irin mugun
duhu daya mamye wurin, Dj ma hankali ya k`ara
tashi, Sally tace "mun shiga uku! Wa ya kashe
mana hasken?",
Reesha yace "kila dai cikin samarin nan ne wani
ya kashe ta, shegu maza! Iskanci yayi dad`i
kenan",
Cike da tsoro da rawar murya Sally tace "wannan
ba kashe shi akayi ba, kaji sautin da yake tashi
fa, na shiga uku ni Saleemah" sai hawaye sharrrr
a kumatun ta.
Wata irin k`ara da k`arfi speakers d`in sukayi
wanda yasa lokaci daya kowa ya dawo hayyacin
sa, tsoro duk ya kama su, wani irin iska mai
had`e da guguwa ya fara tashi, Kerry uwar
birthday tuni hawaye sun cka mata ido, wayar ta
take ta nema amma ta rasa inda take, ita dai
tasan akan table ta ajiye ta a lokacin da zasu
yanka cake amma kuma yanxu ta duba nan
babu ita, can daga nesa ta hango hasken ta
alamar ana kira saboda wannan muguwar k`arar
bazata bari k`arar waya ta fita ba, hannun ta ta
zira zata d`auko amma sai taga wayar ta k`ara
yin gaba kamar anja ta, k`ara zira hannu tayi
amma wayar ta k`ara tafiya, binta taci gaba dayi
ana jan wayar har saida tayi nisa sosai ta fara
fita daga cikin mutane, har tabar baki d`aya
area`n da suke party.
Ihu dukkanin su suke, daga mai kiran dady
sai mai kiran momy amma babu mai kiran sunan
Allah, sannu sannu kukan nan ya k`ara yawaita,
da suna jin murya d`aya ne amma yanzu ya
zama muryoyi da yawa babu adadi.
"Tashin hankali" na fad`a a raina, tuni biro na
ya kufce ya fad`i tsananin tsoro da fargaba, ban
san a ina yake ba dole sai Sis ta siyo min wani.
Muje zuwa, ba`a fara komai ba yanzu za'a fara
inji Amrah.
Amrah and Rabeeart sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERSí ½í³š
YINI ÆŠAYA 9-10
By babymsh 08:29 No comments
[8:02pm, 21/09/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜:
í ½í²€ *A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page9⃣
*'Karfe 9:00pm*
*_AJIWA DAM_*
Iya rud'ewa da kid'ima yau *AREWA STARS*
sunyi ta, kuka suke su duka 19 d'in banda Kerry
da tabi wayar ta, hankali tashe Feenat ta ringa
kiran "Ummah! Ummah!! Ummana kizo ki
taimake ni, alhakin ki ne Ummana, kullun
k'ok'arin ki ganin kin bani kyakkyawar tarbiyya
amma bana d'auka, ina watsi da duk tarbiyyar
da kike bani, yau gashi nan muna ganin abunda
muke shukawa", sosai take kuka duk ta fita
hayyacin ta.
A hankali guguwar nan ta fara isowa inda
suke, k'ura ce mai had'e da wasu irin k'ananan
halittu wanda bazasu iya misaltuwa ba, da
yawan gaske suke ta zuwa wurin su, ga wannan
kukan mai muryoyi da yawa shima yana ta k'ara
yawaita, ga kuma duhu shima babu wanda ke
iya ganin ko tafin hannun sa.
Wurin Eseeee k'warin suka nufa da mamaki
naga sun k'adaddabe ta baki d'aya kamar yanda
zuma kema mutun idan ta kama shi. Sosai take
kuwwa tana ta k'ok'arin murje su daga jikin ta
amma sai k'aruwa suke, da mamaki wannan
halittun suka ringa shigewa a cikin fatar Esee
suna yawo ciki kamar wani bororo, har cikin
kanta suka shiga suna mata yawo akai, banda
soshe soshe babu abunda take, take gashin
kanta ya fara kakkaryewa yana fita har sai da
baki d'ayan shi ya fita kanta ya koma swal, in
banda yawon wannan halittun dake cikin kan.
Fatar jikin ta ta fara zagwanyewa tana barin
tsokar ta baki d'aya kamar wadda ta k'one,
kamar gari haka fatar ta ringa murmusa a k'asa,
take Esee ta fad'i wurin bata a hayyacin ta.
Reesha da Sally kam har yanzu basu saki
junan su ba, cike suke da tsoro da fargabar
wannan al'amarin,
Can suka ji wannan halittun sun dawo kan su,
yanda suka ma Esee suma haka suka masu
kuma har a lokacin suna manne da juna basu
rabu ba hannun Reesha a cikn rigar Sally kan
k'irjin ta.
Fad'i sukayi a tare suma basa a hayyacin su.
Da wata irin dariya da k'arfi naji wata
muryar da tunda babata ta haifeni ban tab'a jin
ko makamanciyar ta ba,
Wannan k'warin ne suka hau dunk'ulewa guri
d'aya, d'aya na cin d'aya har suka zama guda
d'aya babbar halittar da babu halitta mai girman
ta a duk doron k'asar mu ta Nigeria.
Nan ta hau jijjigar jikin ta saboda duk inda
bai gama had'ewa ba ya had'e.
Idon ta ma jaa ne tamkar garwashi wanda
hasken idon kawai ake iya gani a duk fad'in filin.
Afnan ce b'oye a bayan wani katako wanda
jikin shi duk k'usoshi ne ta lafe jikin ta sai rawa
yake, da k'arfi taji an buga ta jikin k'usoshin duk
suka caccake ta, take jini ya fara ambaliya daga
jikin ta, tun daga nan itama ta fita hankalin ta
da alama suma tayi, bata kuma sanin abunda
yake wakana ba.
Nan ma wata dariyar ta kuma yi da k'arfi
wadda tafi waccan ma tsanani.
Ruky wadda tuni ta sume tsananin tsoro da
tashin hankali da k'arfi halittar nan ta d'auki
Ruky ta d'aga ta sama ta nanata k'asa, take
kuwa Ruky ta farfad'o, sake d'aga ta sama tayi
ta jefar sai kan wani dutse, take jini ya fara
ambaliya daga kanta itama ta sake sumewa.
Dj da Mc kuwa had'a su tayi da karfi ta
matse su sai ga hannun Dj ya b'ullo ta bayan
Mc, hannun Mc kuma ya b'ullo ta cikin Dj,
wulwula su taci gaba dayi sannan ta jefar dasu
daidai kan dutsen da ta jefar da Ruky, take suma
suka sume.
Dariya mai had'e da sautin kuka ta fasa
lokaci d'aya, wanda yasa sauran da bata kashe
ba suka k'ara tsorata da ita, dan cikin su har da
wanda ya saki zawayi daga zaune akwai, a
ransu kuwa banda dana sani babu abunda
sukeyi, ni kuma Amrah nace maganin irin ku
kenan, wata k'ila wasu idan suka ji labarin ku
koda halin su ne zasu daina, basu san aron
lokaci bane Allah ya basu amma sun kasa
ganewa, yau gashi sun had'u da daidai dasu,