A WUNI DAYA BOOK COMPLETE BY ESHAAAT.pdf

Author :  ESHAAT SMILER Category :  Hausa Book Store

Chapter   6 / 7

15K to 18K   out of 19.5K words

sauri sukace "mecece mafitar likita?"
"Ina ganin dole sai dai a raya d'aya d'aya
kuma ya mutu saboda yanda aka matse su da

k'arfi yasa komai nasu ya had'e, har xuciyar su
ma ta had'e ta zama amfani d'aya take yi, idan
ba haka ba kuma sai dai suci gaba da rayuwa a
haka har lokacin da wani zai mutu cikin su
sannan a raba",
Malan Liman (mahaifin Dj) yace "inna lillahi
wa inna ilaihi rajiun! Yaron yau kenan! Ka haife
shi baka haifi halin sa ba, kullun nasiha ta d'aya
da yaron nan akan yaji tsoron Allah saboda a
kowane lokaci mutuwa zata iya riskar mutun,
ashe abun da yake aikatawa kenan, ishara ce
Allah ya nuna masu tun a duniya, kuma ma Allah
yana son su da rahama tun da har haka ta
kasnace, da baya son su da rahama da haka zai
barsu suci gaba da aikata alfasha har sanda
mutuwar su zata zo, kuma ishara ce ga sauran
al'ummah masu halin iri nasu".
Alhaji Amiru (mahaifin Mc) yace "ka daina
wannan maganar malan, yanzu miye abun yi?".
Likita yace "kuje kuyi shawara a tsakanin ku,
duk yanda kuka yi zaku iya samu na Office d'in
shine na biyu daga gefen dama idan kun fita
daga nan" yana kaiwa nan ya fice hannun shi
rik'e da takardu.
Sautin kuka kawai kake ji a cikin d'akin,
iyayen kerry kuwa sai kallon ta sukeyi kamar ba
ita ba, a rud'e mom tace "Alhaji wannan ba
'yata bace, sun canja min 'ya wallahi, ni yarinya
ta lafiya lau ta baro gida babu abun da ya same
ta, saboda me za'a ce min wai itace wannan?
Ban yarda ba sun dai siyar min da yarinya shine
suka musanya min ita da wannan, 'yata bazata
tab'a cewa zata kashe ni ba" wasu zafafan
hawaye sukaci gaba da ambaliya daga fuskar ta.
Dad yace "haba Mom Kerry! Mesa zaki fad'i
haka? Baki ji abun da sukace ya samu yaran
bane? Bafa ita kad'ai ta samu matsala ba, yanzu
kika ji wani likita yana bayani akan abun da ya
samu wasu daga cikin yaran, kiyi hak'uri ki
daina kuka, ko birnin sin (China) ne zan kai
Kareemah indai zata samu lafiya, ki daina kukan
nan bana so kina yin sa",
Cikin damuwa tace "inda gaske ne ita

waccan mesa babu abunda ya same ta?" Tayi
nuni da Feenat dake zaune kusa da ummanta.
"Nace ki daina maganar nan fa, kiyi shiru
mana Kerry zata samu lafiya" (duk maganar da
zasuyi basa ambaton sunan Allah).
Shiru d'akin yayi cike da damuwa Dady yace
"tou wai ma menene asalin k'ungiyar nan tasu
ne?",
Alhaji Abdallah yace "nima dai tambayar da
nake wa kaina kenan, su wannan yaran har sun
san wai su fitar da wata k'ungiya a tsakanin su"
Feenat tace "yanzu kuwa zan baku labarin
asalin k'ungiyar *AREWA STARS* da dalilin
bud'e ta da kuma shugabannin k'ungiyar".
Hankalin kowa ya koma kan Feenat dake
share 'yar k'wallar data soma fito mata,
Hankali na ya tashi dana duba naga ruwan
biro na ya k'are gashi kuma ina son d'auko wa
fans rahoton komai, da sauri nacewa sis R. "Sis
kije ki siyo min pen yanxu dan kar labari ya
wuce mu",
Fuskar ta ta b'ata tace "ke sis Amrah kin
san fa biro tayi tsada yanzu, gaskiya sai kin
kawo kud'i na gaji da siye da kud'i na",
D'an murmushi na mata nace "ki karb'o bashi
zan baki kud'in idan mun koma gida". Murmushi
tayi sannan ta nufi hanyar shago domin siyo biro
d'in.
Ku biyo mu idan mun siya wata zaku jimu insha
Allahu.
(lol..)
*Amrah nd Rerbeeart sk novels📚*
YINI ÆŠAYA 26-33
By babymsh 08:38 No comments
[5:18pm, 16/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 26-30
"Asalin k'ungiyar ta samo tushiya ne tun muna
zana jarabawar jss, Shareef da Shareefat wanda

suke twince ne masu k'aunar junan su da had'in
kai tsakanin su.
Tare ake kawo su makaranta kuma tare ake
zuwa d'aukar su, duk abunda Shareef ya samu
baya cin shi sai ya kawo ma Shareefat haka
itama take.
Ni kuma k'awata d'aya wato Afnan, duk da
nake marainiya baba na ya rasu tun ina
k'ank'anuwa ta hakan bai hana mahaifiya ta
kaini wannan babbar private School d'in ba mai
suna *SALDEFI INTERNATIONAL SCHOOL,* duk
yaron da zaka gani a makarantar to d'an masu
hali ne in banda ni da rufin asiri ne kawai kuma
mahaifiya ta tana so na samu ilimi mai kyau.
Afnan na k'auna ta sosai nima kuma ina
k'aunar ta, har gidan su an sanni nima kuma
gidan mu an santa. Sai dai kuma akwai
banbancin halayyya tsakani na da ita saboda ita
tana da son huld'a da mazan class d'in mu, tana
yawan yi min fad'a wai na kasa in waye har
yanzu gashi ina da kyau maza na son yi min
magana amma bana basu fuska, sai dai kawai
na mata murmushi idan ta fad'i haka.
Kwatsam wata ranar da zamu kammala zana
jarabawar jss muna zaune da Afnan akan
window sai ga wani yaro yaxo kusa damu,
hannu ya bata suka tafa kamar yanda suka saba
ni kuwa na b'ata fuska tamkar ban tab'a dariya
ba.
"Wai Afnan wannan k'awar taki bata dariya
ne ita?",
Kallon ta ta juyo gare ni tace "Feenat wai?
Tana yi mana me ka gani?",
"Kawai dai yanayin ta na gani haka, amma
ya kamata ta saki jiki damu tunda dai duk ana
tare" ya k'arisa maganar da kanne mata ido
d'aya.
Shareef da Shareefat ne tafe hannun ta rik'e
a nashi suka gitta ta inda muke, da sauri Afnan
tace ma yaron "nikam Shamow dama ina son
tambayar ka akan wancan yaran da suka
wuce?",
"Wai Shareef da Shareefat kike nufi?",

"Ban san sunan su ba, amma pls ina so ka
bani labarin daka sani game dasu, haka kawai
yaran suna burge ni da alamar saurayi da
budurwa ne"
Saurin dafe bakin shi yayi yana k'ok'arin yin
dariya "inji wa ya fad'a miki haka? Twince ne fa,
ke baki ga komai nasu iri d'aya bane? Yaran
gidan former Minister'n petroleum ne Alhaji
Ma'aruf Sale, yaran 'yan gata ne da kike ganin
su, suna k'aunar junan su sosai, kamar yanda
kika gansun can to haka suke ko a class, koda
yake ba class d'in mu d'aya dake ba saisa baki
san su sosai ba har kike fad'in haka, babu
malamin daya isa ko fad'a yayi ma d'ayan su,
idan kuwa wani malami yayi kuskuren haka tou
ranar baxai kwana a makarantar ba sai an kore
shi, kowa yana tsoron tinkarar su da sunan
magana saboda ko murmushi basu yi sai ga
junan su, nima tun farkon zuwan su makarantar
nan nake son masu magana amma hakan bata
yiwuwa saboda sun fi k'arfi na, akwai wani yaro
d'an ss2 daya ma macen magana wai yana son
ta wallhi baki ga yanda yaron ya wulak'anta ba
sai da ya bani tausayi, saisa kawai na hak'ura
na k'yale su, ni wallahi tsoron su ma nake".
Dariya Afnan ta k'yalk'yale da ita tana tafa
hannu "amma dai ka bani kunya guy, kai yanxu
duk tak'amar da k'wambon amma ka kasa
tinkarar wasu, ni kuwa wallahi sai na masu
magana sai dai duk abun da zai faru ya faru,
kowa yana ji da nashi ai, su idan uban su former
minister ne ni nawa Commissioner of police ne,
bari ma ka gani" mik'ewa tayi da sauri ta bi
bayan su tana k'ok'arin shiga gaban su, nima
nabi bayan su jiki na sai rawa yake dan bana so
wani abu ya samu Afnan.
"Hi" Afnan ta fad'a bayan ta shiga gaban su.
"Hello" Reesha ya miyar mata da amsa,
"Am Afnan by name", tare da sakin d'an
murmushi.
Kallon banza suka watsa mata kafin macen
tace "and so?",
"I just want you 2 to be my friends, ina

yawan ganin ku a School d'in nan kuma kuna
burge ni, and I decided kawai na maku magana
yau, babana shine commissioner of police a halin
yanxu",
Da sauri Shareef ya sakar mata fuska jin ko
waye mahaifin ta yace "am Shareef and Shix
Shareefat, nyc to meet you",
"Nyc to meet you too dear, pls ko zan iya
zama frnd d'in ku in ba damuwa?",
Shareefat tace "why not? You can dear"
Murmushi Afnan ta masu tare da mik'awa
Shareef hannu suka gaisa sannan ta mik'a ma
Shareefat, nan ta masu introducing d'ina da
Shamow take suka hau hira kamar dama sun
saba.
Haka muka kasance mu biyar har lokacin da
mukayi hutun jss, Afnan na zuwa gidan mu nima
ina zuwa nasu, duk da talaucin mu bai sa ta
raina mu ba, tana yawan bani labarin Reesha da
Reeshat kamar yanda ta miyar masu da suna.
Haka ta k'agara hutun mu ya k'are saboda
sabuwar rayuwa da take burin yi idan mun
koma, Shamow kuwa shi yayi naming namu da
*5 STARS* saboda yanzu mun had'e kan mu
sosai kamar mun dad'e da sanin junan mu.
*Amrah nd Rerbee'art sk novels📚*
[5:25pm, 16/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 31-33
Ranar da muka koma hutu kuwa munyi farin ciki
saboda a class d'aya aka had'e mu, Shamow ya
kawo wata Friend d'in shi Nuratu yace "shix my
frnd wai tana da sha'awar kasnacewa a cikin mu
ne, shine nace zan kawo ta ku gani",
Reesha yace "tou muna da dokoki sai idan ta
aminta dasu sannan zata shiga cikin mu"
Da sauri ta d'aga kanta tana kallon shi,
"K'ungiyar mu duk wanda ya shiga cikin ta zai
mana alk'awarin bazai tab'a fita ba har sai

lokacin da mutun zayyi aure, sannan kuma duk
lokacin da muka yanke hukunci a abu babu
wanda ya isa yace a'a, zamu ringa tallafawa
junan mu idan wani yana buk'atar taimako, idan
wani zayyi *BIRTHDAY* dole mu had'a kai mu
faranta masa rai, kin yarda?",
"Ehh na yarda wallahi na amince"
"Good, miye Sunanki?",
"Sunana Nuratu Abdullahi",
"Kinyi register daga yanxu kin shiga cikin mu".
Nidai haka nan nake cikin k'ungiyar ba wai
dan ina so ba sai dan bana so na b'atawa Afnan
rai dan naga itace silar k'ungiyar.
Shamow yaji dad'i sosai yace "tou amma ya
kama ta mu canja suna ko?"
"Ehh ya kamata gaskiya" Reeshat ta fad'a.
"Why not mu saka *AREWA STARS?* wato
taurarin arewa", Reesha ya bayar da shawara.
Tafa hannu duka mukayi saboda sunan yayi
dad'i sosai.
*******
Haka mukaita k'ara yawa har lokacin da muka
kai mutun 15, daga nan Reesha yace a rufe
shigar da mutane haka nan saboda idan mukayi
yawa sosai abun bazayyi dad'i ba za'ayi ta
samun sab'ani. Hakan kuwa mukayi bamu k'ara
d'aukar kowa ba duk da akwai mutun uku da
sukayi requesting amma akayi rejected nasu.
Wata rana English teacher'n mu ya shigo
shine first period ya fara lesson mu kuwa muna
baya muna meeting akan *Birthday* d'in Iby
dake gabatowa, wani taku muka fara jiyowa na
takalmi tun daga farkon class, a tare muka
d'aga kai mukayi duba ga wata kyakkyawar
budurwa sanye da sabbin uniforms d'in ta, skirt
d'in ta ko guiwar ta bai rufe ba sai d'an hijabi
akan wuyan ta, hannun ta na jan wani d'an
trolley bag k'arami irin wanda ake saka
littattafan makaranta. Duka hankalin 'yan class
d'in ya koma gare ta saboda wani kallon raini da
take watsa ma kowa,
Baki ta tab'e tare da zare dark glasses d'in
dake idon ta tace "excuse"

Shi kanshi malamin sai da ya tsorata da ita,
dan daga ganin wannan ba xatayi kunya ba, nan
ta hau yi masa bayani cikin British English nata
cewa Principal ya gwada nata nan class d'in
yace taxo, sosai turancin yarinyar ya burge shi,
take ya gwada mata baya yace ta zauna acan
saboda duk gaban a cike yake, bayan kuwa
mune kad'ai saboda kowa yana tsoron mu a
class d'in yasa babu mai iya tinkarar wurin mu
ya zauna.
*Amrah nd Rerbee'art sk novels📚*
A YINI ÆŠAYA 34-40
By babymsh 08:41 No comments
[12:31pm, 20/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 34-35
*We Dedicated this page to ```Pharty KK``` you
always pray for me, tanks alot for the caring,
Amrah loves youh muchí ½í¸í ½í¸í ½í¸*
A yatsine ta ringa kallon mu tana jira mu
matsa mata wuri ta zauna, kallon raini mu duka
muka bita dashi kamar yanda ita ma shi take
mana, har a lokacin English teacher'n mu bai
daina kallon ta ba, ganin mun k'i bata wuri yasa
yace "hey! Two of you let her sit down mana,
shix a new commer fa you have to welcome her",
Da sauri Afnan ta kalle shi tana k'ok'arin yin
magana ya d'ora yatsun shi akan lab'b'an sa da
nufin baya so tayi magana, gunguni ta hau yi
tare da matsawa ta shige jikin Shamow da
shima ya kasa kauda kallon shi daga kan Kerry.
Bayyanannen tsaki tayi tare da harar Afnan
sannan ta zauna teacher yaci gaba da lesson
d'in shi daga inda ya tsaya.
Da mamaki sai ga Kerry ta fiddo iphone 6s+
tana latsa, duk kan mu mun tsorata da ganin
wayar saboda zuwan wayar kenan Nigeria, ban
tab'a kallon ta a zahiri ba sai yanxu.
Bayan an tashi break fast duk aka fita aka

barmu zaune muna ta surutu, itama Kerry d'in
bata fita ba sai latsar wayar ta take yi, yaron da
muka aika ya siyo mana moi-moi ne ya shigo ya
same mu "naje wai yau ba'a kawo moi-moi ba
sai dai fried rice" tsawa Reesha ya daka masa
tare da fad'in "ba ance daga Crispy ake kawo ta
ba? na baka enough money ka hau mashin ka
siyo mana mana? Ko so kake har a dawo bamu
ci abinci ba?"
Da sauri yaron ya fita dan yana tsananin
tsoron Reesha, dama saboda aike yasa aka
d'auko masu hayar shi kullun yake zuwa
makarantar baban su yana biyan shi albashi duk
wata.
har a lokacin Kerry bata daina latsar waya ba,
kira ta latsa bayan an d'auka ne tace "mom ba'a
kawo min breakfast bafa" a shagwab'ance.
Ban san me aka fad'a ba daga d'aya
b'angaren sai naji tace "ok mom am waiting" ta
tsinke wayar.
Banda kallon ta babu abunda muke yi, daga
ganin yarinyar big gal ce, Afnan dai kallon raini
kawai take aika mata, ni kam burge ni ma tayi
saboda shix very classic, ga kyau da komai ta
had'a.
Kafin d'an aiken mu ya dawo aka kira Kerry a
waya ta d'auka "yes" tayi shiru daga nan kafin
ta kuma cewa "a kawo min mana ina class, ka
tambayi Principal yasan inda ya gwada min na
shiga ai, ni bazan iya fitowa ba" ta tsinke wayar
taci gaba da latse latsen ta.
Da rawar jiki principal ya shigo hannyn shi
rik'e da basket had'ad'd'en gaske, har k'asa ya
duk'a sannan ya mik'awa Kerry shi, "keep it
there" ta fad'a tare da nuna masa d'an nesa da
ita.
Ajiyewa yayi sannan ya fita yana d'an waigen
ta.
Da k'arfi muka d'auki shewa muna kallon shi,
a kunyace ya fita ba tare daya sake waiwayowa
ba.
********
Haka dai mukaci gaba da rayuwa da Kerry ba

tare da mun san ko sunan ta ko tasan namu ba,
ko k'ala baya had'a mu da ita, babban abunda
ya bani mamaki bai wuce yanda take da sharp
brain ba, so da yawa idan ana lesson hankalin ta
baya ma wurin malamin amma da zarar ya
tambaye ta sai ta bashi answer, su kansu
malaman suna mamakin k'walwa irin tata. Wani
lokacin har Iby yana cewa zayyi mata magana
amma sai Afnan ta hana shi.
Gata da yawan waya da maza, kullun aka
tashi daga skul sai tayi AP da namiji kuma
manyan yara take tarayya dasu.
Da haka har muka kammala SS 1 zamu shiga
SS 2, bayan an dawo hutu ne muka fara ganin
sauyi daga Kerry, saboda kullun tazo sai ta bimu
one by one ta bamu hannu mun gaisa har da su
Iby kamar yanda taga muna yi dasu. Wani
lokacin har fira take k'ok'arin jana dashi saboda
ta kula duk na fisu sauk'in hali.
Bayan sati biyu da dawowa hutu ne ta tare
ni wai tana so ta shiga group d'in mu, dana
fad'awa su Reesha yace "ai an riga da an rufe
shiga k'ungiyar mu, wasu ma suna so amma
mun hana su shiga" Iby ya katse shi da cewa
"kai guy yarinyar nan fa big gal ce, wallahi tunda
ta yarda duk wani jiji da kanta ta nemi mu saka
ta is good kawai a saka ta d'in, sauran wanda
suka nema mutun hud'u ne ko uku suma sai a
saka su, kaga mun cika 20 kenan daga nan sai
mu rufe d'aukar kowa, koya kuka ce?"
Mu duka muka had'a baki mukace "hakan
yayi"
Reesha yace "to shikenan ayi hakan"
Washe gari na shaida ma Kerry komai, taji
dad'i sosai ta kuma bayyana min hakan, bayan
anyi break tayi introducing kanta a wurin mu
muma muka mata namu, tun daga nan ta shiga
cikin mu har ya zamo kamar ma itake leading
namu, har Reesha sai abunda Kerry ta fad'a
yake ji saboda kusan komai itace take mana,
idan wani party za'ayi itake d'aukar nauyin
komai na party'n, ko abinci muka daina siye sai
ita take siya mana.

Wani lokacin ma idan muka rasa idea'n
k'aryar da zamuyi a gida mu fita itace take fad'a
mana yanda zamuyi dan duk ta fimu k'walwa.
Haka rayuwar mu taci gaba da kasancewa,
amma a koda yaushe ina yawan neman gafarar
Allah saboda ina cin amanar ummanah, duk
lokacin da zan fita sai tace min inji tsoron Allah,
haka kuma aduk lokacin da na mata k'arya naje
wani wuri nakan tuno da furucin ta, lokaci d'aya
naji bana son rayuwar da nake ciki, na tsani
kaina a doron k'asa. Wannan fitar da mukayi ta
k'arshe ma sai da nace baxanje ba amma Afnan
tace inhar banje ba sai ta tona min asirin
abubuwan da nake yi a

6 / 7