ZAMAN TASHA COMPLETE BY UMMY AYSHA.pdf

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 19

30K to 33K   out of 55K words

Masha Allah Baba kanshi Yace dake waje dan yaji zazzakar murya ta
a'cikin waya....



Rafel yafita ya durk'usa akan gwiwar shi ya fara ma Baba godiya kamar anyi abun angama..
"Baba ya mikar dashi tare da nuna mai bakomi yana masu fatan alkhairi."
Sukaman Sallama cikin farin ciki suka tafi.!

Washe gari muka hau machine d'in Baba sabo mukata fi Studio Rafel, haka muka dage mukayi
wakar mu cikin farin ciki da jin dad'i, dan sosai ni kaina ni kejina a saman gajimare..



Bayan sati d'aya Ammi ta sauka, tasamu d'an ta Namiji mai kama dani sosai..Ranar suna
a'kasa mai suna Aminullah, zoka ga murna wajen Ammi ta haifi Dan Albarka, d'an da ba
lau-layi." sosai Baba ma yayi murna nikai na ba a'barni a'bayaba har kaya nasai ma Aminu nai
ma Ammi d'inki mai masifar kyau naba ta, haka ta amsa ba gode bare nagode a'ranar soye
Ammi ta zauna zata fara soye nazo zan kamama ta ta kwabeni, tare da cewa ban isa in samata
hannu acikin aikin sunan Dan Albarka ba.. Haka na koma gefe na raku be ina jiran Baba yafito
daga toilet mu koma shagon mu, Bayan yafito ya cema ta kibata ta yimaki mana!


Ammi Ta ce" ban'so, ina amfanin hannuwa na .

Baba Ya ce" Uwata muje! Haka ya tasani gaba muka fito. Muna fitawa mota na fakawa," Rafel
ne da kanan shi Fahad suka fito ko wannan su bakin su a'washe sukayo kai na, Fahad harfa
daka tsalle ya rungume Yayan shi Ya ce" Yaya fad'a mata.."

Rafel yayi dariya Ya ce" Baba abamu wuri muzau na."

Baba ya bud'e shagon muka shiga suma suka shigo "Rafel ya zube kasa ya fara kwararo ma
Baba Addu'a, tare da fa�in Baba wallahi abu ya samu karb'uwa ya kar kace ya fiddo key din
mota Ya ce" Baba ga Abun da aka bamu guda biyu na d'auki da'ya na ba Moopy daya, sai
kuma kud'i million d'aya gasunan zan dauki rabi inba ta rabi..
Baba ya jin jina Abun tare da jin farin ciki a'ranshi Yace lallai Uwata an'fara abu asa'a, Allah
yayi jagora, amma anan wajen bakai rabon adalci ba gaskiya ina na shikuma dan uwan naka ?

Rafel ya sosa kai" Yace Baba har na barmai wannan motar ni zan dauki sabuwar, kana ku�in
danasa mu zan bashi wani abu."

Baba "Ya ce " ba haka za aiba!! kai ka dauki dubu dari hudu, kaba Moopy dari ukku, shima
a'bashi dari ukku.. Haka kam akai Fahad harda duka wa yaman godiya, rana daya sun samu
manyan kyautu'tuka," nace masu bakomi."
Rafel ya fiddo wasu Paper's yasa ke ba Baba "Ya ce "Baba wannan ma wata kwangilar ce muka
samu zamu sake wasu wako'kin". Baba Ya ce "kai Masha Allah! Allah yasanya Alkhairi ya
kiya'ye halshen ku.. suka amsa suka mana sallama muka rabu cike da farin ciki..

Baba ya kalleni" yace Uwata kinga Abun Allah ko.
Insha Allahu saikin zama Abun da Duniya zatai alfahari dake, yanzu mu kulle shagon nan muje
wajen ginin ki muji akwai wani Abun da ake bukata, kinsan ku�in sunfara kasa yanzu bai fi
million d'aya ba, dan ma munfitar dana tafiyar mu hajji.
"Nace to Baba duk yanda kace."

Baba ya tashi ya fiddo mashing dinshi na haye muka tafi har goruba, muna zuwa muka iske
Alhaji nan tsaye yana daukar gidan dake opposite da nawa photo, yana ganin mu ya k'araso
wajen Baba yana maida wayarshi, suka gaisa.. "Yace ma Baba wallahi kana raina yanzu nike
da burin kiran ka.."
"Baba Ya ce" ikon Allah Alhaji Allah yasanya muji alkhairi.
Alhajin Yabce" ameen Alkhairin nama, Wallahi kaga gidan d'ana yau an'kammala shi
kasancewar jibi zai shigo nageria, to an samu kaya da yawa wanda sukai saura nace ma ma
aikatan nan,su kwasa suciga ba da gina ma Mufeeda, to kaga cikin ikon Allah abu yayi har sun
hada komi penti ya rage.
Baba yasaki baki yana kallon Alhajin "Yace Alhamdulillah wai kana nufin cikin wata daya har an
kammala gina gidan nan ?

Alhajin yayi dariya tare da "cewa k'araso kagani" yayi gaba muka bishi a'baya yana zuwa ya
tura kyauren yashiga muka bishi Masha Allah nace ganin yanda gidan ya mugun tsaru komu
an'sanya harda shukoki masu maseefar kyau da wajen arbana motoci, gidan baki d'ayan shi flat
guda ne.. Haka muka shiga d'aku nan muka ga falo biyu ne sama da kasa, daga sama akwai
dakuna biyu k'asa ma d'aki biyu a tak'aice dai wajen ya maseefar hadu wa dai-dai da benen

gidan abun kallo ne .

Baba ya duka ya fara ma Alhaji nan godiya, tare da dauko key d'in motar da a'kabani yaba
Alhajin" Ya ce "Alhajin yace kasama ta Albarka yau aka kawomata shi.

Sai naga Alhajin yayi kicin-kicin da fuska tare da cewa ma Baba wai kana nufin saurayin ta
yamata kyautar mota?

Baba yarike haba" Ya ce all6ah yakiya ye Alhaji taya saurayi zaima budurwa kyautar mota a'a
Wallahi waka ta fara shine sukayima wani dan siyasa wakar yabasu kyautar Abun."

Alhajin yarike baki tare da cewa yo malam ai wajena akasai motocin nan wallahi, kason
sana'atane, tabbas Sanata bello awaje na yake sayen motoci shekaran jiyama ya aiko aka
dauki wayannan guda biyu ko, kai nakau yi maki murna ashe ke ki kayi wannan wakar data
zaga'ya Duniya cikin sati d'aya nikai na dabana sauraro nakau saurari wakar nan wallahi, Allah
ya'kara basira.
Baba yace ameen Alhaji.

Alhajii yami komin key din "Yace Dota Allah yasanya Alkhairi, wato sabon gida sabuwar mota
ko?
Nakar ba nai dariya muka fita! Baba kece man Alhaji to yanzu wazai yi fentin dan gobe zan
kawo kudin.

Alhaji Yace ba matsala kawai kaba da gobe ma war haka zaka iya zuwa ka iske an'gama.

Baba yazaro dubu dari ukku da a'kabani yaba Alhajin tare da cewa ina fatan sun isa..

Alhaji Ya yi dariya tare da zarar dubu dari da hamsin yamikoma Baba dari da hamsin, "Yace
"wayan'nan sun isa, dan ma za a'hada da wayarin din nepa da sunyi yawa".

Baba Ya ce "to Masha Allah! Allah ya'kara zumunci sai goben in munzagayo.

Alhajin Ya ce" bakomi Allah yakaimu'

Muka hau machine zamuyo gida muna yaba mutuncin mitumin" nace Baba gaskiya mutumin
yasan ya gudum'muwu sosai"Baba Ya ce" ai Uwata badan Abun da ya bada ba da ina tabbatar
maki da cewa Wallahi sai million din nan tashige, babu Abin da zamu mashi sai fatan gama wa
da duniya lafiya, ko bayan raina Moopy ban amince kiyi watsi da mutumin nan ba, ki �aukeshi
tamkar Uba kin ji ko?" nace to shikenan Baba Insha Allah ".
Munyo nisa da tafiya munzo Kofar Durbi "nace ma Baba wow Baba kaga wasu daka dakan
kujeru a'cen da gadon su..

Keeee Baba yaja burki muka juyo muka dawo wajen masu kujeru nan, kamar wasa muka shiga

muka tambaya suka hadamana kud'in harda na gadon dubu dari takwas, sosai muka yaba da
saukin su dan sun maseefar hadu, harda dinning dinsu Baba yazaro kudin nan yace gobe za
akwashi kayan zamu ciko sauran.
Nasaki baki ina kallon Baba nace haba Baba mizanyi da wayannan Uban kayan saikace
Amarya?

Baba yayi dariya "Yace Wallahi Uwata jinki nike kamar jaririya sabuwar haihuwa.
In Allah ya yarda bazan bar Duniyar nan ba saina ga Rayuwar ki ta ingan ta. na share hawayen
idona namai godiya muka hau mashin din mu muka tafi.

Washe gari ina gama dunkunan wata Hajiya data kawoman na bata, Baba Yace infito mu
wuce.. Haka nafito muka biya muka ba masu kaya cikon su Baba Yace a'biyomu da kayan,
haka suka loda ma motar su kayan ta biyo bayan mu har Gidana.

Muna zuwa muka an'gama fenti gidan yayi fess, akamasu fenti kala d'aya dana gidan dan
Alhajin nan, wato farin fenti sai get din akasa baki, ba k'aramin haska Unguwar gida jan nan
sukai ba muka shiga mukaga ba kowa sai wani saurayi tsaye fari sol mai maseefar kyau ya
zubaman idanuwanshi, na sakar mai harara dan baifiye son ana kallo na ba, ya nuna kanshi
alamun dashi nike? na d'agamai kai "ya Langwabe kanshi alamun shagwaba..Ba k'aramin
kyau salon yamai ba banson sadda nasaki murmushi ba na juya gefe .

Baba ya k'araso wajenshi tare da bashi hannu saurayin yaki mikamai saima dukawa da yayi ya
gaida Baba har kasa.. Baba ya amsa cikin farin ciki Yace amma kai D'an Alhaji. ne ko?

Saurayin ya saki murmushi tare da cewa eh Baba nine d'anshi na biyu, suna na Imran, daddy
Ya ce " in tsaya yason zaku k'araso, yana cen Gidan Big bro gobe zai zo ana ida sanya kayan
dakina.

Baba "Ya ce to Masha Allah, Allah ya kawoshi lafiya" ya amsa da Amin.

Baba yace inba damuwa zamu shiga a'zuba kaya.

Saurayin yarike baki "yace wane kaya bayan wanda aka zuba d'azu?

Baba Ya ce" kaya kuma?kai ba nan ba dai wannan yanzu nasawo su.

Saurayin zai magana sai ga Alhaji ya k'araso cikin Gidan da han zarinshi, ya kalli Baba Ya ce"
malam yana ganku da kaya haka?

Baba yace wallahi Alhaji bayan tafiyar mu jiya muka saye su shine yanzu muka biya aka taho
dasu.

Alhajin Ya ce" ikon Allah daba kai saurin saye ba dan nazubama ta wasu yau-yau dinnan suma
a'kagama d'aurawa dan bana nan bane, kana aka tsallaka aka sama Babana nashi .

Baba yasaki baki yana kallon Alhajin.

Alhajin Ya ce" kumuje ai sai asanya palon kasa tinda wayan cen sama aka dorasu..

Haka mukabi shi saman bene Masha Allah na fara cewa, sadda muka shiga falon yasha fenti
mai maseefar kyau onion color da milk, wajen yabada ma'ana ga fitulu an sanya wajen yayi
kwal tamkar rana... Alhaji yahaye sama muma muka bishi har muka k'arasa , woow na furta da
karfi har saida Baba yajuyo dan yadauka wani abu yasaman, wasu daka-dakan kujeru ne farare
sol Royal masu masifar kyau, ga wata katuwar plasma data mamaye bango guda harda show
glass, a tak'aice yah Ammar yanda kason �akin amarya harda gado yasaman fari sol mai
kwalliyar pink color..Banson sadda na ruga na rungume Alhajin nan ba, da banta ba tsayawa
nai maganar data wuce gaisuwa dashi ba, nafara mai Addu'a tamkar yanda nike wa Baba na,
tare da fatan Allah yabani Abun da zanmai wanda zaishi farin ciki.


Ya d'agoni tare da zubaman idonshi Ya ce" karki damu Dota, kinson haduwar jini?to haduwata
daku haduwar jini ce Allah ne yahadamu daku dan mu taimaki juna, wannan gudum muwatane
ina maki fatan Alkhairi Allah yakawo miji nagari.
Na dukar da Kai bance komiba, daga bayan mu naji ance Ameen Daddy yama kawomata gani
nan tsaye.
Muduka muka juya muka zubama saurayin da Ya ce mana sunanshi Imran ido.


Alhajin Yayi dariya Ya ce" baka gajiya da zaulaya Imran, wato bazaka ma jira Yayan ka ya
faraba kamin kafara ko?

Imran ya sosa kai Ya ce "Allah Daddy indai zakaban inaso wallahi.

Daddy Yayi dariya tare da cewa to bari kaji nason malam bazaima Maman shi auran dole ba,
dan haka gaka gashi Daddy yajuya zai fita.

Baba Ya ce" a a alhayji katsaya ayi komi gaban ka nidai in nine banda matsala nidai na bada
mamana kina son shi ko?..

Banson sadda na ruga toilet na rufe ba dan sosai kunya takamani bantaba jin wani Ya ce" yana
sona ba, saida naji ma tsaye kana naji ana bugawa," na bude kofar ina dire kafafuwa cikin
shagwaba nafara fadin haba Baba yazakaban kunya gabansu..

Bashi bane yar shagwaba!!!

Da sauri na dago kaina idona yasauka a kyakyawar fuskar Imran,
Nai saurin sunkuyar da kaina k'asa tare da fara wasa da yatsun hannuna. Dan kunya takamani
nasanya Baba ne.

Imran Yace Mufeeda dan Allah ki kalleni kiman magana.

Na d'ago dara-daran idanuwa na nasakasu anashi,cikin lokaci naji zuciyata ta aminta da Imran,
araina ina yaba tsarin halittar da Allah yamashi.

Imran yace Moopy kina sona?...��


Carasss 💃💃💃💃💃
Am happy today Wallahi I love you all my fans 🥰🥰😘
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: ��💘��💘��💘��💘
ZAMAN TASHA
💘��💘��💘��💘��
NA UMMY AYSHA
��💘��💘��💘��💘


🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=
mo

*⚜�©J.A.W📚🖌�*




🅿�3�⃣9�⃣&4�⃣0�⃣

""Moopy ta kalleshi bata cemai komi ba saima k'ok'arin bi ta gefen shi Tayi tawuce.


Imran yasha gabanta tare da fad'in "ban CAN'CANTA ba ko Moopy?shiyasa ko Amsa bazan
samu ba ko?
Na ka�amai kaina tare da "fad'in ba haka bane, dan Allah kabar ni in wuce kawai.

Imran "Yace shikenan Moopy" ya bani hanya na wuce zuciya ta fal da tausayinshi dan da gani

zayyi saukin kai.?
Ina fitowa nagaa Baba na'karasa wajen shi nai tsaye ina sunkuyar da kaina kasa.

Imran ya fito tare da k'arasowa wajen Daddy shi dake tsaye gefe "Yace muje Daddy bata Sona.

Wata irin kunya ta kamani da har ban son sadda "nace kai Imran kaji tsoron Allah ba.
Cikin sauri ya kalleni tare da fadin Moopy kina nufin kin amince?.

Na rufe fuskata tare da komawa cikin palon.

Sosai su Baba sukaji Dad'i wato lokaci guda ko ince rana guda Allah yahada ni da Mijin
aure..Nan Baba da Alhaji suka tattauna Alhaji ya buk'aci ayi komi cikin lokaci, Baba ya
nunamai baida matsala Insha Allah duk yanda Yace.


Cikin kan'kanan lokaci shak'uwa mai yawa tashiga tsakanina da Imran a'koda yaushe muna tare
a waya har Gidan mu yakan zo muyi zaman mu shago, bai tab'a tambaya ta miyasa bana
zaman gida ba dan nafahimci mutum ne mai saukin hali baida yawan surutu a'kan Abin da bai
shafeshi ba.
Imran Shi ya mana cuku-cukun komi har mukaje K'asa mai tsarki nida Mahaifina mukayi ibadar
mu cikin natsuwa na roki Allah yazaba'man Abun da Yafi Alkhairi dan'gane da rayuwa ta da
Imran, ko kad'an ban yiwa Ammi Addu'a komi ba dan har gobe nidai ban yarda itace Uwata
ba...Haka muka gama ibadar mu muka dawo gida.
A ranar da muka dawo ko bacci bamuyi ba saboda masifar Ammi haka tai ta bala'i tana cema
Baba na tsohon banza, ya turani karuwanci na samo kud'in da muka tafi Makka.. Da yake
shima dan Duniya ne haka ya bini muka tafi ba ko kunya, sosai take ai'banta Baba nako ma
gefe ina kuka jin Yan da Ammi ke wulak'anta Baba da yayi shuru kanshi a'kasa.
Aminu ya rar'rafo wajena nasa hannu zan dauke shi ,Ammi ta bugaman butar kar'fen dake
hannunta take goshina ya fashe, bakin cikin hakan yasanya Baba yin kanta zai kai mata duka ta
goce cikin tsautsayi kafar Baba ta zame take ya fadi faduwar datazomai da tso'tsan da yayi silar
zama Ajalinshi. Moopy ta fashe da kuka tana ganin yanda Baba yayi kamar a'lokacin Abun
yafaru..

Ammar da idon shi ya koma kamar kuli dan girma dan sosai yake kuka kamar Yaro, ya bude
baki zai magana saiji sukai an fyace majina daga bayan su, da sauri suka juya sukaga Tsohuwa
zaune Tayi rashe -rashe bayan su tana kuka, ko kallabi babu a'kanta, jin sunyi shuru Tsohuwa
ta d'ago kanta tace cigaba Dan Allah yar Caɓas....

Moopy ta share hawayen idon ta, tace Inna gida zan tafi mangari ba yakawo kai, kuma lokacin
Sallah Yayi zan dawo wani lokacin..

Tsohuwa ta tashi ta ruga da gudu ta rufe kofar tare da dan'na key, sai da ta tabbatar k'ofar ta
rufu sosai, tazaro key din tana gwadaman Moopy "tace in kin tashi ki É—auka a'nan ta
nunamata dan bantan ta dake cikin zane, ta bude Aljuhun ciki ta sanya, tare da rushewa da
wani mahaukacin kukan da yasa Irfan ya fito da sauri ya k'araso yana tambayar ta ko lafiya?..
Tsohuwa "Tace matsa cen shege da kumburar'ra fuskar ka kamar giginya, Uban mi zaka iya
yiman Azzalumi mai cutar marainiyar Allah, matsa kaban waje tasa ke sakin kuka" cikin kuka
Tace "nace kici gaba.."

Moopy da tin shigowar Irfan taji jikinta ba Dadi dan ta tsani Abun da zai K'ara hadata zama waje
daya da mugun nan," Tace kiyi hakuri Inna ina buk'atar tafiya a'kwai abunda zanyi..."

Tsohuwa "tace ke banason iskanci, karki ga ina lallashinki yanzu na baki kashi, ke kika kawo
kanki ko Aljannun ki suka kawoki, A A zakiman iya shege, sha kurumunki nima Aljannu na zan
san ya su mai daki kinji...?


Moopy ta tashi tsaye tana kuka mai cin rai, ta nuna Irfan da hannu "tace muddum mutumin nan
na cikin palon nan bazan iya furta ko kalma d'aya data shafi rayuwa ta gaban shi ba, Wallahi sai
dai in kwana a'nan ta fad'a a fusace.

Ba k'aramin tsoro ya kama Tsohuwa ba, dan bata manta a'bunda akai mata ba, har yanzu bata
iya d'aura kallabi, dan mugun ciwo kanta ke mata, ga kuka tana tayi kan yasake tsukemata.

Tsohuwa "tace kiyi hakuri kai Irfanu koma É—aki kan in'sanya taci Uban ka"

Irfan yayi tsaki tare da shigewa �akin shi yayi kwance yana wani tinani dan gane da bayyanar
Moopy mawakiya, Fatan shi dai Allah yasanya kamin lokacin fuskar shi ta sace..

11 / 19