Chapter 6 Reading YANCINA KO BUDURCINA COMPLET by Ummi Muhammad Usman.doc Arewa Novels

YANCINA KO BUDURCINA COMPLET by Ummi Muhammad Usman.doc

Author :  Ummi Muhammad Usman Category :  True Hausa Novels

Chapter   6 / 24

15K to 18K   out of 71.3K words

tamkar yadda zaki girmama mu ki kaunaci 'yan uwansa ki girmamasu kikula da addininki ki kula da mijinki.
Fatima nasan ke ba jahila bace iya gwargwado mun baki ilimi dan haka kinsan hak'k'in miji akan matarsa kiyi k'ok'arin ganin kin sauke hak'k'insa da ke kanki
Ki kula da damuwarsa a lokacin da yake cikin ta sannan ki kula da farin cikin sa alokacin da yake cikinsa ki shiga damuwa idan kin tabbatar yana cikinta kiyi amfani da tausasan kalamai dan ganin kin Kore damuwar da yake ciki
Ki nuna tsananin farin ciki ki alokacin da kikasan yana cikinsa
Ina rok'on Allah yai miki albarka yai wa rayuwar aurenku albarka dan Allah Fatima ki rik'e aurenki da daraja zanyi mutuk'ar farin ciki aduk sanda na tunaki na tuna kina gidan aurenki kina bautar ubangiji
Dan Allah Fatima ki kula cikin saninki kada ki tab'a sab'awa mijinki komai ze miki kiyi hak'uri ki jure watarana sai labari komai ze wuce kamar ba.ayi ba muddin kinyi hak'uri

Sannan inasan kisan abubuwan da zaki din gaci da sha domin ni.imar jikin ki dan mijinki ya sami nutsuwa da farin ciki daga gareki ba shaye shayen magungunan mata ne ke kawo ni imar jikiba domin kuwa ba ko wannene suke ingantattuba ki kasance mecin kayan itatuwa irinsu kankana kabewa kwa-kwa dabino Aya inibi da sauransu ab'angaren abinci kuwa ki dingacin naman da akayiwa kyaukyawan gashi me ruwa-ruwa ko farfesu me romo da abinda aka had'a da alaiyahu kabeji Ogun da sauren kayan ganyayyaki ki kula da shan madarar shanu domin tana da mutuk'ar amfani ajikinki sannan ki kula da shan ruwa domin yawan shan ruwa yana da mutuk'ar amfani wajen wanke dattin Mara
Ga ganyen magarya nan da garafuni tazargadi da zuma na zuba miki acikin kayanki na rubuta miki yadda zakiyi amfani dasu idan kin sami nutsuwa ki duba dan Allah Fatima ki kula da abinda na gaya miki.
Allah yai miki albarka tashi Ku tafi akoda yaushe kina cikin addu.ata inai miki fatan farin ciki me d'orewa a rayuwarki.

Na fashe da kuka saka makon tunawa da nasihar Umma gareni
In sha Allah zanyi k'ok'arin kula da dukkan abinda kika gayan Umma zan kuma zauna agidan mijina lafiya muddin raina yana motsawa a gangar jikina dan nasan hakan shine farin cikinki ni kuma farin cikin ki shine nawa.

Ina kwance ina tunani har barci ya sami nasarar saceni abinka da gajiyayya ban farka ba har saida aka shiga masallaci
Na tashi cikin salati tare da addu.ar tashi daga barci alhamdu dullahillazi ayana ba.ada ma amartana wa ilahir nushir cikin sauri na fad'a band'aki naiyo alwala nai nafula tare da sallahr asuba bayan na idar nai azkar nai addu oina bayan na gama karatun al kur anin da na Saba ina zaune zuciyata cike da tunanin inje in had'a masa kayan breakfast kokuwa in barshi
Tunanin nasihohin Umma ne yasani mik'ewa na fito na nufi kicin
Cikin yan mintina na gama had'a kayan breakfast d'in musamman da yake akwai wadatattun kayan electronic akicin d'in duk da bawani abu me wuya naiba shayine sai kunun gyad'a da farfesun naman kaza da soyayyen dankali da kwai sai bread dana gasa tunda bansan abinda yafi so ba

Naje na goge denning d'in da desta me tsafta na Jere kayan akai gwanin burgewa
Na tsaftace kicin d'in na wanke kayan dana b'ata na gyara na maidasu inda suke na fito falo na gyarashi na share na goge na dauko had'ad'd'un turarukan wuta masu dad'in k'amshi da Umma taimin na turare falon sannan na koma d'akina na gyarashi na canza tsarin abinda naga beyimin ba na shirya kayana acikin word dorup nai wanka da had'in turarukan wankan da Umma ta had'amin na shirya acikin parkistan ruwan hoda riga da wando na gyara gashina na nan na d'eshi natura acikin hula na sanya hijab d'in da ya dace da shigata na zauna akan kujera kwalli d'aya dake dakin na d'auki littafin addu.o ina ina duvawa dan ga dukkan alamu me gidan be tashi ba dan har yanzu k'arfe takwas da kwata banji koda motsin saba.

K'ir k'ir k'ir ring d'in wayarshi ya katse masa daddad'an barcin da yake yi Aliyu ya bud'e idanunsa tare da addu.ar tashi daga barci ganin hasken rana ya hudo labulen ya shigo d'akin ya sashi saurin mik'ewa zaune tare da d'aukar wayar yakara akunne tare dayin cikakkiyar sallama daga d'aya b'angaren umar ya amsa tare da cewa lallai mutumina kana hutawa k'arfe takwas da mintina ashirin amma baka ta shiba bayan kasan aikin dake a gabanmu Aliyu ya shafi laulausar sumar kanshi yace afuwa wlh yau na makarane ban kwanta da wuri ba ga kuma gajiya dabata gama sakina ba da nai sallahr asuba barci ya kuma daukeni wayar kacema ta tasheni Kai ka shiryane
Umar yace yanzuma kaga na fito zan wuce ka sameni a office kawai idan ka shirya
Aliyu yace afuwa abokina dan Allah ka shigo ka jirani bazan dad'eba yan zunnan zan shirya kaima bazakaji dad:in tafiya Kai kad'ai ba tunda sauda yawa tare muke tafiya ka shigo nan ka bani minti goma yanzun nan Zan fito be jira jin abinda zeceba ya kashe wayar ya fad'a band'aki

Umar ya kalli agogon hannunsa tare da girgiza kai yaja motar zuwa harabar gidan Aliyun
Kai tsaye ya shiga falon da sallama babu kowa acikinsa ko ina a gyare a tsaftace ga wani sansanyan k'amshi yana tashi ya nemi guri ya zauna akan kujera ya lumshe ido yana shak'ar sassanyan k'amshin da ya cika falon

Aliyu cikin yan mintina yai wanka ya shirya cikin wasu bak'ak'en cot da farin takalmi sauciki gashin kansa kuwa zuwa kyaukyawan sajensa sunsha gyara sai k'yalli yake idanunsa kuwa sanye da Gila's irin na likitoci hannunsa na dama rike da jakar aiki dantsan hannunsa ya rataye fara kar d'in rigarsu ta likitoci yayinda hannunsa na haggu ke rike da wayoyinsa ya fito daga d'akin tare da rufowa ya nufi falo cike da tafiyarsa ta k'asaita yana ganin umar ya Saki murmushi yace sorry abokina na b'ata maka lokaci ko
Umar yai murmushi tare da mik'a mai hannu sukai musabaha yace ai girman Kane kai yanzu dole ai maka uziri domin da da yanzu ba d'aya bane tun da yanzu kun zama Ku biyu..
Umar yace kai ba wannan ba ma ya kwanan amanarka Aliyu yace tofa Allah yai dare gari ya waye zaka d'orane daga inda katsaya ai....
Sansanyan k'amshin da yaji ya bugi hancin sane ya katse shi ya d'aga kai ya kalli inda k'amshin yake fitowa ganinta dayayi cikin kyaukyawar kwalliya da daddad'an k'amshi a dedai wannan lokacin hakan ya tafi da shi dan sai da yaji gabansa ya d:an fad'i

Yaiwa ubangiji tasbihi mak'agin da ya halicceta tabbas yasan me kyauce be tabbatar da kyanta ba sai ayau da yai mata kyaukyawan kallo tabbas badan taimai k'ank'antaba kuma beriga ya mallakawa wata zuciyarsaba da yad'an ra b'ata badan komai ba saidan darajar Abba da kuma darajar kyawun fuskarta.
Ta k'araso cikin nutsuwa ta tsuguna akan carpet cikin ladabi ta fara gaisheshi ina kwana ya Aliyu yad'an kauda kai daga barin kallonta ya amsa lafiya lau
Antashi lafiya
Be amsaba illah mu kullin motarsa da ya dauka akan center table da ke tsakiyar falon..A??]
{


Please
Comments
Share



Mmn beby nusyA??]
{A??]
{A??]
{A??]
{




WhatsApp number 07010238476

Nasan ke
11/18/21, 11:00 PM - Fiddausi Yunus: ??c??c"YANCINA KO BUDURCINA??c??c



WRITING BY



UMME MUHAMMAD HASSAN

(Mrs Aliyu Jibrin Ali)


WNNAN BOOK D'IN NA KUD'INE 200 NAIRA DAN ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KIKARANTA MIN KO BANCE ALLAH YA ISABA KUNSAN HAK'K'IN WANI ABIN TAMBAYA NE .



??.\???aLOVE STORY HOT ROMANTIC



Please matan aure kad'ai banda yan Mata duk budurruwar data karanta babu ruwana.



Ya Allah kajik'an iyayenmu kaiwa rayuwarmu albarka ka shirya mana zuri.a ameen??R0???_



PAGE2??_/Q9??_/QC?&
{3??_/Q0??_/Q
Ta kalli umar tace Ina kwana ya umar ya amsa cike da Fara.a lafiya lau Fatima ya gajiyar tafiya da kwanan bak'unta tai dan murmushi tare dayin k'asa da kai tace alhamdullh

Aliyu ya kalli umar tare dacewa tashi muk'arasa kada muyi latti umar ya mik'e yana cewa nanawa kuma ai mun riga da munyi kuma nasan zamu sami cunkosan majinyata yanda muka kwana biyun nan ba mujeba .

Ya rataya jakarshi yana shirin fita daga falon cikin sanyinta ta tsaida shi da cewa um... um... dama sai tai shiru ya juyo ya kalleta tare da zuba mata manyan idanunsa farare k'al masu mutuk'ar kyau da d'aukar hankali

Ta sunkuyar da kanta cikin sauri saka makon wasu irin abubuwa data hango acikin idanun
Cikin ishashshiyar maganarsa yace kinga idan zakiyimin magana kiyimin ita sak banasan inda inda tace dama na shirya maka kayan breakfast ne kuma naga bakaci ba zaka fita
Ya sake ware manyan idanunsa akanta yana me mamakin furicinta cikin kaushin murya yace nagaya miki Ina buk'atane ko angayamiki ni zan iyacin jag??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????walgwalanki.
Ta girgiza Kai cikin sauri

Yaja tsaki tare da juyawa ze fuce daga falon cikin taushin murya tace adawo lafiya Allah ya bada sa.a ubangiji ya dawo da kai gida lafiya
saida ya d'anyi Jim sannan ya fice daga falon batare dayace komai ba ya shiga mota suka fice daga harabar gidan.


A haka rayuwata taci gaba da kasancewa cikin zak'i da mad'aci nikad'ai nake rayuwata cikin kewa da kad'aici babu me zuwa inda nake babu wani da nake gani inji dad'i kullum zuciyata cike take da damuwa da tunani ga kewar gida da k'aunar ganin ummanmu bani da abokin hira da ya wuce alkur.ani babu inda nake zuwa dan tunda nazo gidan kimanin wata biyu da kwanaki ko bakin get d'in gidan ban tab'a zuwa ba kullum Ina zaune cikin kewa da kad'aici dan megidan ma ban fiya ganin saba idan ya fita tun safe sai dare wataren ma banajin fitarsa kan ya dawo kuma nayi barci
Ya umar kuwa sai dai inji maganarsa a harabar gidan shima be fiya shigowa ba

Yau kimanin kwanakina 70 da shugowa cikin garin abuja yau na tashi cike d tsananin kewar gida Ina zaune a falo na tasa photos d'inmu ni da ya Ibrahim Umma da abbanmu Ina kallo cike da kewa zuciyata cike da tausayin halin da ya Ibrahim yake ciki Wanda babu Wanda yasani sai Allah nayi nisa acikin tunanin d'an uwana kamar daga sama naga mutane a tsaye akaina
matane su su uku manya- manya sunci kwalliya sanye da kayan dake bayyanar da surar jiki namik'e tsaye cikin d'an murmushin yak'e dan na tsorata da ganin su
Nace sannunku da zuwa Ku zauna mana gaba d'aya suka zubomin idanu yayinda d'aya daga cikinsu ta k'araso kusa dani tafara zagayeni tana k'aremin kallo sanye nake da atamfa super holand ruwan zuma d'inkin riga da skirt duk da d'inkin be wani kamaniba amma ya zauna ajikina sosai nayi kyau mutuk'a musamman zaman waje d'aya ga cima me kyau jikina ya kuma murjewa fatata ta kuma gogewa sai shek'i take da daukar ido na sakeyin d'an murmushi a Karo na biyu ganin irin kallon da suke min ya wuce na addini nace Ku zauna mana bari in kawo muku ruwa ko nai saurin daukar hijab d'ina dana ajiye a hannun kujera nasa dama ganin ni kad'aice shi yasa na cire shi

Matar dake kusa da nice ta dakatar dani cikin isa tace da kata malama bashi muka zo sha ba dan daga ganin mu kinsan a wadace muke munzo ganinki ne sai kuma muka ganki ba yanda muka zata ba
Taja tsaki tace gaki da suffar cikakkiyar mace sai kuma na ga baki cika macen ba tunda kina zaune da mijin da baya sanki baya muradinki baya kaunar ganinki kin zamar mai tamkar k'a dangaren bakin tulu a karki a kar tulu a barki ki b'ata ruwa ko da yake ba wannan ne ya kawomu ba na zone inyi miki bushara da shugowata cikin gidannan sannan inyi miki albishir da rayuwar kunci takaici gami da ba k'in ciki tad'anja numfashi tare da cewa sorry yarinya Ina mutuk'ar tausayawa rayuwarki akan katsalan dan d'in da tai na shigowa tawa rayuwar in tabbatar miki zaki d'and'ana kud'arki na shugowa rayuwata daki Kai dan babu wata 'ya mace da zqta shugo rayuwata da haider in kyaleta ba tare dana durk'usar da ita ba
Idan baki saniba Ina so ki sani haider na Hindu ne ita kad'ai kuma mutuk'ar muna tare da shi to babu shi babu wata 'ya mace acikin duniyar nan

Shawara d'aya zan baki ki tattara yanaki yanaki ki barmin cikin gidana tun kamin ranar da zan shigo dan mutuk'ar aka ce miki yau nazama matar haider
Haider ya zamo mallakina to bolar gidanshi ta fiki daraja agurina bey na barki lafiya

har ta juya ta tafi Ina kallonta fuskata sake babu wani alamun b'acin ran maganganunta a tare dani har ta kai bakin k'ofa cikin sanyin murya na tsaida ita da cewa bakiji ba
Taja ta tsaya tare da juyowa ita da yan koran nata cikin murmushi nace da ita inai miki maraba da shugowa cikin gidan haider d'inki a ko wanne lokaci sannan Ina so kisani babu abin tausayi irin mutumin da baisan damar Saba balle haggunsa shiko k'unci gami da takaici babu me shigarsa face mutumin da besan Allah da ya halicci shi ba bare ya bauta masa Ina maraba da duk wani k'alubale da zezo daga gare ki na barki lafiya inai miki fatan alkairi na juya na shige d'akina nasa key na barsu anan

K'awayenta sukaja hannunta suka fita daga cikin falon
Ruma ta dafa kafad'ar Hindu tace a gaskiya Hindu na tausaya miki domin a yau na tabbatar haider ba aurenki ze ba
Ki duba kiga mutumin dake da mata kamar wannan kyaukyawa ga kyan k'ira ga k'uruciya me zeyi dake domin duk abinda kike ta k'ama dashi yarinyar nan tafiki

Domin duk yadda nake ji da kaina da kuma burin danaci na yarfata daci mata mutumci wlh tunda muka shiga na ganta kwarjininta ya bugeni sai naji nayi lak'was
Lubabatu tace kikayi lak'was ruma konayi lak'was ai ni Hindu da zakiji shawarata da sai ince ki hak'ura da haider kibar mata kije kici gaba da harkokinki kada ki manta yanzune maza suke rububinki saboda kina musu duk abinda suke so ki tsaya ki mori rayuwarki dan idan ma kinyi auren bazakiji dad'in saba dan yadda kika saba yin yadda kike so maza suke sakar miki k'udi to shifa bazaki sami yadda kike soba

Lubabatu tayi dan murmushi taci gaba da cewa kuma yadda haider d'innan naki yake da mutuk'ar tsantseni me zakice da shi ranar daren farkonku shi yana tunanin ya dauki dalleliyar budurruwa cikakkiya me rufaffiyar k'ofa
Yazo da rawar k'afa
K'ofar da yake tunanin saiyayi fama kafin ya shigeta tashin farko sai yaji zuruf ya shigeta

Lubabatu da ruma Suka kyalkyale da dariya tare da tafawa ruma tace dole kiyi tunanin amsar bashi kafin zuwan lokacin dan wallahi Ina...

Hindu ta d'aga mata hannu tace ya isa dan Allah haba kundameni duk cikin Ku babu me kawo mafita sai tarin matsaloli ni babu ruwana da kyan matarsa ko wani Abu da take dashi.

Ta d'anja numfashi tare da rausayawa tace kada kumanta ku kukace maza suna yayina suna kuma rububina Ashe kuwa Ina da abubuwan so atare Dani Wanda maza suke k'auna
Dan haka kuyimin shuru nasan hanyoyin warware matsalolina
Idan zaku tafi kuzo mutafi idan kuma nabarku anan to kunga tafiyata
Gaba d'aya suka shiga mota taja suka fita daga harabar gidan.

A kishingid'e yake acikin falo yana karatun jarida yayinda lokaci bayan lokaci yake duba agogon hannunsa ya dauki wayarsa dake ajiye agefensa yai kira tare da karawa a kunne assalamu alaikum yace bayan yaji an d'aga daga d'aya b'angaren umar ya amsa da wa.alaikas salam Aliyu yace wai baka sami dawowa bane tund'azu nake jiranka muwuce office najika shiru?
umar ya amsa na dawo tun jiya ban shigo da wuri bane shiyasa ban nemeka ba
Kaga nafito ma yanzu haka Ina hanyar gidanka ganinan k'arasowa ya kashe wayar
Shima rufe jaridar hannunsa yai ya mik'e ya shige d'aki dan shiryawa.

Umar ya shiga falon da sallama babu kowa aciki sai tashin sansanyan k'amshi yake ya nemi guri ya zauna Aliyu dake futowa ya amsa mai sallamar tare da k'ara sowa kusa dashi ya zauna ya mik'a mai hannu sukai musabaha yana cewa kabarosu lafiya yasu ammi?
Umar yace duk sunanan lafiya suna gaisheka da iyali
Aliyu yace Ina amsawa sosai da sosai ai na so zuwa in gaishesu sai kaimin wayo ka gudu ka barni da tulun aiyuka

Umar yai murmushi yace ai ko ban hanaka ba kaima yakamata ka Hana kanka zuwa saboda matarka tunda da da yanzu ba d'aya bane idan muka tafi wa zaka barwa matar taka acikin gida ita kad'ai

Aliyu yai d'an tsaki yace tofa allah ya dawo da Kai zaka d'ora daga inda ka tsaya to tashi mu tafi tunkan ka cinye mana lokaci dan....

Sallamar da tayi ta shigoce ta katse shi tana sanye da duguwar rigar materials brown me taushi ta d'ora dogon hijab da ya rufe mata komai nata

Ta durk'usa d'an nesa da su tace ya umar Ina kwana
Ya amsa lafiya lau Fatima ya zaman kad'aici dan dai nasan yana damunki ko ya fad'a yana murmushi
Aliyu ya mik'e yana cewa yakamata mutafi ko kada muyi latti
Ganin sun mik'e ya sani kuma tausasa murya nace ya Aliyu ga abincin breakfast na shirya akan danning ya juyo y kalleta tare da watsa mata harara yace wai saunawa zangaya miki ba zanci jagwalgwalann ki ba amma kink'i dena dafawa to daga yau sai yau idan kika kuma yimin zancen abincinki sai na b'ata miki rai wawuya kawai.A??]
{




Please
Comments
Share


Mmn beby nusy.A??]
{A??]
{A??]
{A??]
{



WhatsApp number 07010238476
11/18/21, 11:00 PM - Fiddausi Yunus: ??c??c "YANCINA KO BUDURCINA??c??c



WRITING BY


UMME MUHAMMAD HASSAN

(Mrs Aliyu Jibrin Ali)



WANNAN BOOK D'IN NA KUD'INE 200 NAIRA ZAKU BIYA KUD'INKU TA ACCOUNT 3048536089 KO KATIN WAYA MTN KO AIRTEL DAN ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTAMIN BOOK KO BANCE ALLAH YA ISA BA KUNSAN HAK'K'IN WANI ABIN TAMBAYANE.


??.\???aLOVE STORY HOT ROMANTIC



please matan aure kad'ai banda yan mata duk budurruwar data karanta babu ruwana.



Ya Allah kajik'an iyayenmu kaiwa rayuwarmu albarka ka shirya mana zuri a ameen??R0???_



PAGE 3??_/Q1??_/QC?&
{3??_/Q2??_/Q
Ko angaya miki zan iyacin jagwalgwalonki
Na sunkuyar da Kai sakamakon hawayen da suka tahumin cikin rawar murya nace kayi hakuri dan Allah
Yaja dogon tsaki tare da ficewa daga falon
Duk abinda ke faruwa umar na tsaye yana kallonmu bayan fitar sane ya kalleni yace kiyi

6 / 24