Author : Maman Annur Category : Top Hausa Novels 2025
mahaifiyar ta.
Duk da wannan kokarin hidima da take yi kwata-kwata mmn Aslamiyya bata gani ita fa bata ki ace suwaiba bata gidan ba saboda ita ma bata zauna da kishiya ba saboda haka bata son ganin aslamiyya da kishiya tafi son 'yar ta ta zauna ita kadai a gidan ta ita da 'ya'yan ta.
Kai jama'a kuji min mata keda 'yar taki ta aure mata miji duk bata ji ciwo ba sai ke da 'yar ki ta kasance haure, yo haure mana tunda sama taka taxo gidan ta fara baza bazarta .
Maman Aslamiyya ce take son kara maida Aslmiyya kan keken 6era "wai ta tashi tsaye wannan kashe-kashen kudin da matar nan take yi duk fa mijin ne yake bata don ayi amfani a cikin gidan Amma ke kina zaune baza'a tambayi me kike so ba haka kawai sai dai komai ace ita ni gaskiya bana son irin haka kina zaune za'a mai daki bora ita ta Zama mowa"
"Mama mmn Abdul fa tana kokari ni kuma banga laifin yin hakan ba duba da itace uwar gida sannan ko itace ta haihu to ni za'a baiwa kudin cefane da duk wani abun da ya dace a gidannan don haka ni daidan hakan na gani"
"Ke gidan ku nace ana nuna Miki Annabi kina rintse idanu, to ke bazai tambayi ra'ayin ki ba saboda itace uwar gida, toke yarinyar gida ce? Ki tashi ki farka daga nannauyan barcin da kike yi in ba haka ba wllh kina zaune zasu jone da junan su su koma kamar da, ke kwa sai dai kallo shawara ce nake baki a to"
"Hmmmm mama kenan bai kamata kice haka ba yanzu da na mutu me zanje in cewa Allah akan kuntata wa matar nan da muka yi ?karki manta fa dalilina har korar su yayi ita da 'ya'yan shi Amma hakan duk bai ishe mu ba sai mun sake fito da wata kitimirmirar kuma "
"To salamatu shikenan kin Zama sallamammiya na haifawa suwaiba kishiyar ki ke in ba haka ba ina fada Miki gaskiya kina kaucewa to shikenan nidai in ta kwa6e Miki kada ki nemeni tommm"
"In Allah ya yarda ma ba zata kwa6e mun ba"
Suwaiba tana daki ta kwanta don ta huta da Rana sai jin karar massage tayi a wayar ta aikwa tana dubawa taga daga bankine budewa tayi ai tana kwance sai gata a zaune domin albashin tane ya fado na wannan watan murna tayi sosai, Alhaji ne ya shigo dakin da sallama ya zauna ta ce masa"Bbn Abdul kaga Alert ne ya fado min"
"Alert kuma suwaiba?"
"Ehhh albashin mu na wannan wata"
"Ikon Allah aiki kika samu ban sani ba?"
"To fa wai dama ban fada maka ba kafin in dawo lokacin muna gidan kawun yaran nan na samu offer a wannan makarantar ta kusa d gidan sa"
"Ma Sha Allah ubangiji ya Sanya alkhairi Allah yasa mai amfani ne"
."Amin ya rabbi kayi hkr wlh mantawa nayi ban sanar d Kai ba"
"Babu komai ai yiwa kaine"
Da yamma ta shirya taje wani shago a nan kusa d su ta yi siyayya ta siyo atamfofi guda biyu sai rigunan jaririya guda biyu da yadi na maza ta siyo wa su Abdul , gurin tela ta wuce da yake yasan size din su Abdul din sai ta bashi ya dinka musu ita na da nata dinkunan guda biyu.
Gida ta dawo ta nunawa Alhaji rigunan yarinyar sosai yaji dadi yayi mata godiya.
Bayan tayi sallahr isha'i ne ta fito daga dakin ta ta nufi dakin Aslamiyya da sallama, amsa mata sukayi akace ta shiga.
Shiga tayi dakin suka gaisa ta mata ya saukin jikin sannan ta Mika mata rigunan jaririyar kar6a tayi ta fito dasu daga cikin ledar tana dubawa cikin farin ciki ta dubi suwaiba tace mata "na gode mmn Abdul Allah ya saka Miki da alkhairi Allah ya jikan mahaifa na gode sosai"
" Babu komai ai nima 'ya ta ce babu godiya a tsakanin mu"
Maman Aslamiyya aka nuna wa kayan tace "kai kinyi kokari 'yar nan yanzu a zamanin nan da kaya suke tsada har kika iya ciro kudi kika siyo wannan rigunan 'yan dubu uku uku gaskiya mun gode Miki Allah ya saka Miki d alheri"
"Babu komai mama nima na gode"
Bayan fitar suwaiba daga dakin Aslamiyya ta dubi maman ta tace "haba mama wannan fa bai dace ba tsakani da Allah idan ba zaki mata godiya cikin farin ciki ba ai bai dace kice mata wai rigunan 3k ba, to wannan rigunan da na shiga kasuwar kwari kwanaki na taya zan siya lokacin da aka mun scaining aka ce mace zan haifa ita na fara taya wa rigunan kudin su kowacce 10k ce kinga ta je ta kaso Mana kudi har Dubu Ashirin bai kamata a wulakanta ta ba fisabilillahi "
" Ummm to wancen rigunan sune original wadanda kika gani Amma wadannan daga ganin su jabu ne ba kwari za suyi ba"
Shiru tayi ta rabu da ita don wlh ba taji dadin abinda maman ta yiwa mmn Abdul ba, ita fa ta janye makaman yakin ta don Zama lafiya yafi Zama Dan sarki"
Fareeda ce ta shirya taci gayu zata je unguwa, tana taunar cingum ta fito daga daki ta fara wake-waken habaici har ta fita daga gidan murmushi sumayya tayi don inda sabo ta saba da gidadancin fareeda.
Bata zame ko ina ba sai gidan malamin su inda taje masa tana yi masa magiya akan ya taimaketa ruwa yana neman 6alle mata.
"Fareeda kin yi abin da Aljanin da ya Miki aiki ransa ya 6aci sosai don haka Ni bansan me zan yi Miki ba"
"Ran malam ya dade ka taimaka mun Kai kadai nake da yardar zaka mun abinda nake so "
"Hhhhhhhhh kin makaro Amma bari in tambayi Dan kunama idan zai Miki aiki"
.
"Yawwa mallam a taimaka mun ko nawa ne zan bada"
"Angama"
Wasu dalasimai yake karantawa a haka har ya shafe kusan mintuna biyar. Sai da ya gama kirarin da yake wa aaljani Dan kunama tukunna ya dago kansa yace mata"kinci sa'a yace zai Miki Amma da sharadin sai kin kawo masa jinin jikin ki a jikin tsumma tare da jinin kishiyar taki shima a tsumma ko wanne ki kulle daban-daban don kar ayi kuskure"
Godiya tayi masa ta ce babu matsala sai ta dawo . Gidan su ta wuce ta sanar da mahaifiyar ta yanda suka yi da malamin nasu murna tayi tace mata" haka nake son ki 'yata mun Sha wahala na zauna ZAMAN 'YA'YA NA a baya yanzu kwa ai dole mu shana mu fito gari ke dai kice ya baki mallakar da yake hadawa da kan maciji da kuma karin kunama ta yadda in dai ya hada Miki shikenan kin mallake Amir da uwar sa.
Gida ta koma don bata son Amir ya dawo bata nan saboda za tace masa ne bata fitan ba sai gobe saboda bata jin dadi yau din.
Washe gari da safe ta tashi ta ciro tsumman da tasanya a jikin ta don tarar jini saboda jinin da ya zo mata a daren jiyan, kulle shi tayi a leda sannan ta adan sai kuma ta shiga ko kwanton ina zata sami na sumayya jinin ita da ba shiri suke ba, to koma suna shiri ta yaya zata samu Amma za ta jira anjima tayi shawara da zuciyar ta.
Da yamma sumayya tana zaune a tsakar gida kusa da kicin din su na waje tana Shan iska kasancewar yau ana zafi kawai saiji tayi wani kamar an jefo mata mashi tarewa tayi da hannun ta aikwa sai gani tayi ashe wuka ce har ma ta yanke ta a hannun ta. "Innalillahi wannan wukar daga ina haka?"
Fareeda ce ta fito daga kicin tace mata "subhanallahi wlh ban gani ba naje in jefa ta a cikin kwando ashe nan ta iyo kiyi hakuri ba da gangan na Miki ba. Ganin fuskarta ta nuna kalar tausayi sai sumayya tace " babu komai ai tsautsayi ne"
Kyalle ta dauko ta goge mata hannun tayi hanyar inda suke zuba shara kamar ta jefar Amma sai ta linke tasa a ljihun rigar ta ta wuce daki, ranta fari kal domin cikar muradin ta ya kusa.
A leda ta Sanya taje tasa a jakar ta gudun karta manta shi ma.
Washe gari da safe ta shirya ta fita gidan malamin ta wuce tace mishi "gashi mallam naka sauran aikin ya rage"
"Kai ashe kema shedaniya ce ta lamba daya ma to kinyi kokari"
Dalasimai ya karanta sai ga wasu layu da garin magani a hannun mallam ya bayyana , bata yayi yace mata "wannan garin maganin ki tabbatar kin zuba mata a cikin ruwa Tasha to zata rikice don da kanta zata bar gidan ki shi kuma wannan layar ki binne a inda kika San ita da mijin zasu tsallaka idan kinyi wannan aikin sauran duk mai sauki ne"
Godiya tayi ta ajiye mishi 50k ta tafi gida ko gidan su bata je ba burin ta kawai taje ta aiwatar da kudirin ta .
Karku manta free book ne.
[7/4, 9:12 AM] Maman boy: ZAMAN 'YA'YA NA
NA MMN ANNUR
YAA HAYYU YAA QAYYUM ina rokon ka da sunayen ka tsarkaka da suffofin ka kyawawa yaa rahmanu yaa raheem ka cikawa mmn Afrah burikan ta na Alkhairi ka shirya mata yaran ta ka basu ilimi mai Amfani ka jikan mahaifan ta kasanya su a cikin Aljannar ka madaukakiya.
Ameeen yaa rabbi.
Page(22).
Alhamdulillah sauki ya fara samuwa jikin Aslamiyya yayi kyau tunda har nannadewar hannu da kafa dinnan babu duk sun koma dai dai, A haka maman ta tace taron suna za suyi saboda su samu kudin suna dama fatara take.
Kai kaji tsiya wai da kudin suna za tayi arziki dadi na da talaka wani lokacin bai iya samun guri ba, in banda abun mmn aaslamiyya ita ba ta jinyar 'yar ta take ba,hmmmmmm takamar ta kudin Alhaji Adnanu to mai kudin ta kar6e sai muga yanda zaman zai kaya.
Gobe ne za suyi taron suna inda yarinya taci sunan babar Alhaji Adnanu wato Rukayya za ake Kiran ta da Ummy. Yarinya Masha Allah kamar ta da Abdurra'uf sak hatta yatsun kafar ta Dana hannun ta iri daya ne, suwaiba idan ta kalli yarinyar sai taga kamar lokacin da ta haifi Abdurra'uf, jini ba karya ba kamar ta 6aci . Shi kanshi Abdul din zuwa yake ya dauki kanwar tashi yayi ta kallon ta musamman da mmn shi tace mishi kamar su daya da kanwar tashi.
Yau take suna maijego ta tafito fess da ita ga Ummy an Sanya mata rigar wajen suwaiba sosai rigar ta mata kyau har da bandana aka Sanya mata kalar rigar, Milk ce da pink color tabarakallah kamar a sace. Yayin da Aslamiyya Tasha wani dakakken leshi ja Wanda tayi order a gurin mmn Annur Tasha sarka da Dan kunne da Abin hannun ta mai kyau Wanda ta siya a gurin mmn Afrah, gaskiya maijego tayi kyau. Kunsan ance maijego tafi Amarya kyau saboda ita sabon jini ne yake gudana a jikin ta.
Can na gano suwaiba ta fito cikin dinkin ta da ta bada aka mata doguwar riga ce aka mata dinkin zamani wato na manyan hajiyoyi su ma su Abduljabbar sun Sha nasu gayun da dinkin su.
Sai uban jagorar mai gayya mai aiki yasha shadda blue tayi masa kyau harda babbar riga sai walwala yake Musamman abokan sa suka zo taya shi murna inda suka masa kyautattuka na kudi.
Taro yayi taro masu aikin girki sai fama suke a gurin tukunya masu suyar nama suma sai aiki suke, raguna biyu ya yanka manya, can na hango mmn Aslamiyya tasha atamfar ta an mata riga da zani rigar tasha stone babu laifi tayi kyau itama.Amma duk da haka kyashi da hassadar ta sai da ya bayyana akan suwaiba da 'ya'yan ta, Wanda su basu San tana yi ba.
Anci ansha an koshi kowa ya watse inda maijego ta rattara kudaden ta data samu da kayayyakin barka ta je ta nunawa Alhaji Adnanu yayi mata ftn alkhairi sannan taje ta nunawa suwaiba itama tayi mata Allah ya Sanya alkhairi ya raya ummy akan sunna.
Fareeda ta aiwatar da duk shirin da malam ya bata kuma an samu nasara domin sumayya tana tsallakawa taji jiri yana neman kayar da ita, Zama tayi tana salati fareeda tana kusa don taci burin koma meye zai faru sai dai ya faru Amma dole ayau takeson burin ta ya cika.
"Sumayya lfy kwa naji kina salati?"
"Jiri nake ji"
"Sannu bari in dauko Miki ruwa kisha,kinsan wani lokacin karancin ruwa a jiki yana Sanya jiri, shiyasa ake son muke yawaita Shan ruwa"
Ina sumayya fa jikin ta ya fara rikicewa don har wata karkarwa take you kamar mai ta6in Aljannu .
Ruwan ta bata nan da nan ta ma manta ba tayi Bismillah ba haka ta kafa kofi a bakinta ta fara kwankwadar ruwan kamar wadda tayi kwana daya bata hadu da ruwan ba.
Bayan ta Sha ne sai kuma taji hankalin ta ya tashi bata son zama a wajan da take, dakin ta ta koma ta zauna ,tana Zama amir shima ya shigo gidan ya nufi inda ta zuba maganin nan ya tsallaka yana tsallakawa ya nufi hanyar dakin sumayya ya daga labulen dakin ya kalleta ta kalleshi,tana son yi mishi sannu da zuwa Amma bakin ta ya gagara buduwa sai kauda Kai tayi daga kallon shi.
Dakin sa ya nufa ya zauna yana tunanin wannna zaman kwawar da sumayya take ya isheshi shifa baya son ganin ta a gidan sa ya tsaneta.
Ruwa da abinci fareeda ta Kai mishi tare da yi masa sannu da zuwa cikin kissa da kisisina sai da yaci Abincin ya koshi sannan ya karkace jiki ya kwanta a wajen saboda wannan maganin da ya tsallaka kansa yaji yana juyawa don haka yayi tunanin ko gajiya ce da bacci.
Yana kwanciya bacci awon gaba dashi sai mafarki yayi wai ga sumayya nan ita da wani kato a dakinta suna zaune suna fira suna dariya kamar dai mijinta, aikwa yana shiga dakin ya cakumi wuyan mutumin yace "masa ka tashi ka fice min daga gida,mema ya kawo ka gidana kana gardi dakai?"
"Kai da baka damu da sumayyan ba, ka sani sumayya tawace, jiran wani Abu guda daya nake yi da ba haka ba da tuni na dade da dauke ta "
Farkawa yayi saboda xungurin da fareeda ta mishi ganin yana bacci yana ambatar sunan sumayya,tunanin ta ko maganin bai ci jikin sa ba shiyasa.
Bayan kwana biyu taga masoyan sun rage azar6a6i akan junan su shima yanzu baya ma tambayar twins,Kai rabon da ya gansu ma kwanan shi uku don haka ta shirya don Kara kaiwa malam ziyara ta musamman sannan ya Kara mata wasu aikin da yace zai yi mata bayan tayi amfani da wannan layar da maganin.
Da yamma bayan Amir ya fita daga gidan sai ta shirya ta fita ba tare da ta tambaye shi ba saboda yanzu yazo hannu shi yasa duk inda take son zuwa za ta tafine ba tare da ta tambaya ba.
Zuwan ta gidan malam sai da ta jira saboda layi kusan mutum biyar ne a gaban ta, tana zaune har layi yazo kanta ta shiga gurin malamin nasu suka gaisa take sanar da shi tayi amfani da maganin kuma taga kyan sa domin yanxu ko 'ya'yan sa baya tambaya balle uwar 'ya'yan.
Maganin ya harhada mata da Wanda za ta Sanya a gabanta da danyen nama ake hada shi sai ayi inserting dashi idan yayi kwana biyu a jikin ta sai ta dafa masa ta bashi yaci sannan da wani kullin magani baki a leda amfanin sa idan dare yayi zata turara gaban ta dashi to da zarar Amir ya shigo dakin ta shikenan zance ya kare domin mallaka ce tayi masa da daurin baki sannan ta ce a hada mata da wannan maganin da ya ta6a bata Wanda idan ta shafa masa a jikin sa yayin da zata taya shi shafa mai ajiki to duk macen da zai gani zai ganta tana tafiya da kanta ne kafafunta a sama wannan lakanin kawa har sumayya aka yiwa saboda ya daina ganin ta daya da fareedan ya zamana ita da babu duk daya. Haka ya hada mata su ta taho a hanya ta siyi danyen nama na 1k ta karaso gida ta za6i tsokoki kamar guda uku dai dai yanda zasu shiga jikinta ta bade su day maganin nan ta cusa a jikinta, sauran ma duk tayi amfani da su a daren ranar sai da ta aiwatar da aikin malam hatta da Wanda zata ahafawa Amir a jiki saida ta yi masa dubara yana fitowa daga wanka ta shafa maganin a hannun ta ta dauko mai ta shafa masa a kansa da bayan sa sai sauran jikin sa.
Wani ikon Allah da yadda ya tsarawa bayinsa rayuwa a lokacin da yaso a take a gurin sinadaran maganin suka fara aiki a jikin sa har sai da ya ce mata ta kwanta a dakinsa shi tsoro yakeji kada ta tafi ta barshi, haka akayi kwa kwana tayi a dakin washe gari haka ta fito ta Sanya sumayya aikin tsakar gida kuma tayi saboda aikin sihirin jikin ta.
Yau ne danyen nama ya cika kwanakin da aka diba masa fito dashi tayi taga duk yayi kore har wari yake yi Amma ahaka don rashin imani da kazanta ta dafa shi ta zuba akwanon miyar Amir ta bashi yaci harda sanya mata albarka tayi masa girki da nama.
Wayyo Allah masoya sumayya da kungan ta a halin da take da kun tausaya mata domin sumayya ta Zama kantace yadda kusan bawa da mai gidansa haka ta Zama shi kanshi Amir din ya Zama kan tace mijin hajiya domin sai abinda tace musu a gidan suke yi haka za ta hada wanki tabasu kuma dole suyi wannan yana sa6i wannan yana dauraya rayuwar dai abin tausayi.
Umman sumayya ce ta zo gidan don duba 'yan biyu aikwa tayi mummunan gani domin yaran tagani duk sun kazance babu wanka kayan su duku -duku ita kanta sumayyar ta wani fige ta lalace gashi an hado mata uban wankin kaya kuma daga ganin kayan kasan ba nata bane na fareeda ne.Umma har kuka tayi ganin yadda aka maida mata 'yar ta kwaya daya tilo jikokin ta ta