Author : Maman Annur Category : Top Hausa Novels 2025
fari ne sosai sai shigar tasu ta dace da juna.
Anyi photuna Amarya da Ango sannan da abokan ango da kawayen Amarya,bayan wani lkc kawayen Amarya suka fita daga baya suka shigo kowacce da kaskon turaren wuta mai kamshi wanda Amina mamu take yi turare ne mai kamshi da kama daki .nan da nan guri yadauki kamshi mai dadi kawar Amarya karima da wasu kawayen ne suka fara raba kayan kamu irin su turaren wuta wanda Amina mamu ta hada da kanta da lalle mai kyau sannan da key holders gaskiya abun ya kawatar domin a tsanake ake gudanar da komai.
Bayan angama kamu ne aka maida amarya d kawayenta gida sai kuma gobe in shaa Allah .
Washe gari Juma'a bikin farko inda kawaye suka hada wa sumayya shagali sunce dinner za'a yi sun kama gun da zasu gabatar shima sun sha hidima domin amare ankon farin lace suka yi ita kuma amarya tasa jan lace gaskiya fadar irin kyawun da suka yi ma bata baki ne domin akan kan ka in ka hasko abun to zaka kiyasta kyan ne a idon zuciyar ka .sun rarraba cake da samosa da spring roll,sun sha picture Kala kala kamar ba gobe dare ya fara yi inda kowa aka maida shi gdn shi taro kuma sai na gobe in Allah ya so.
Yau take Asabar inda za' a daura Auren sumayya Abba Hadi da Mubarak Ali hashim (Amir) .
Da misalin karfe 11 na safe aka gudanar da daurin auren akan sadaki Naira dubu dari biyu lakadan ba Ajalan ba .aifa nan maroka suka fara kakatin nasu suna kada ganga suna tayi da bakin su.
Bakin Ango yaki rufuwa Sai gaggaisawa ake da jama'a ana masa Allah ya sanya Alkhairi yana ta godiya sai fama yake da babbar riga Bangaren sumy Amarya ana daurawa gaban ta ya shiga dukan tara tara tana cewa shikenan itama ta shiga sahun matan aure Allah kasa inyi biyayya kamar yadda aka umarci mace ta yiwa mijin ta biyayya .Gudar da aka yi ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi Allah ya sanya alkhairi ake mata tare da ftn samun zaman lfy da zuri'a dayyiba.
Da yamma sun sha kyau sosai sun yi kwalliya kowa kaga ni ji da kansa yake yi a cikin kwalliyar su to bb laifi domin sunyi kyan d ake tunani koma fiye da tunanin mai karatu.
Taro ya watse domin shirye shiryen Kai Amarya ake yi inda aka sanya ta taje ta sake wanka mai shafa lalle ta shafa mata wani kaya naga kanwar umman ta ta dauko mata shadda ce da akayi wa dinki na kece raini doguwar riga ce akai mata aka sa mata hijabi aka feshe ta da turare masu kamshin dadi hannun ta aka kamo aka Kai ta dakin Abba don yin nasiha kamar yadda yake a dabi'ar mu ta mallam bahaushe nasiha suka mata ta ratsa jijiyoyi da jiki sannan aka farfada mata dubarun xama da miji da dangin miji .sosai sumayya take kuka saboda ko bulaguro bata taba yiba dan haka rabuwa da iyayen ta sai ta zame mata tamkar an rabata dasu ne har abada.Allah yayi miki albarka ubangiji Allah yasa gidan kine Allah yabaku zuri'a dayyiba ,ku tashi kuje dakyar aka janye ta daga jikin umman ta suka kaita cikin mota suma suka shiga aka kaita gidan ta.
Da kafar dama ta shiga bakin ta dauke da bismillah sannan sai da ta karanta Ayatul kursiyyu da Addu'ar shiga gida sannan ta shiga cikin gidan dakin ma da za a shiga da ita saida ta yi bismillah tashigar da kafar dama sannan ta shiga .Abakin gado aka ajiye ta sannan sauran 'yan uwa suka dan gyaggyara mata wasu abubuwan a gdn sannan suka mata sallama suka tafi kuka ta saki tace ita dai kanwar ummar ta ta zauna su kwana 😳 gdn ku nace sumayya ja'ira dan iyayen ki kin taba ganin an kwanar wa Amarya a gd ? Sai kace al'adar mutanen yobe a a baza a fara a kan muba muma da haka muka girma .kawar ta karima kadai aka bari itama idan an rako ango sai su maidata gida .
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA
Na mmn Annur
Page (4)
TALLA
INA KUKE MA'A BOTA KWALLIYA DA SAN CANCAREWA DA SHIGA TA KAMALA SHIGAR DA IN KIKA JE WURI BABU MAI MIKI KALLON DAWA MUKA ZO,
HAJIYA TA KIZO KI GWANGWAJE KANKI DA YARA DA MAI GIDA DA KAYAN MU DOMIN MU DIN MUNYI FICE WAJAN KAWO MUKU KAYA MASU KYAU MASU QUALITY WANDA IN KIKA SIYA BAZA KIYI DANA SANI BA.
MUNA DA LACES, SHADDA, ATAMFOFI MAYAFAI, SARKOKI, TAKALMA NA MAXA DA MATA, ZANNUWAN GADO, LABULAYE, TARE DA TURAREN WUTA NA GARWASHI,
MUNA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI.
GA MAI BUKATA YA TUNTUBI WANNAN NUMBER 09069615587
dan Allah idan baki shirya siyan kayan muba to babu bukatar kira ko chatting don 6atawa juna lkc.
Ngd.
Bayan an rako ango Abokan shi sun musu nasiha sosai dan gane da kowa ya yi kokarin sauke nauyin da Allah ya dora musu.daga haka su kayi sallama suna yiwa ango tsiya,karima suka yiwa magana suka tafi inda Amarya ta fara sheshshekar kuka hakuri ta bata tace da ita gobe in shaa Allah da wuri zata zo haka dai suka rabu suna masu kewar junan su .
Asuba ta gari Sumyn Amir.
Garin Allah na wayewa sumy ta fito ta shiga kicin tana duddubawa wai ita za ta girka musu break fast,fitowa yayi yace tayi hakuri ta zo su tafi daki zuwa anjima za'a aiko daga gidan su to tace masa suka koma daki don bacci take ji .ko minti biyar ba a yiba bacci yayi awon gaba da su basu tashi farkawa ba sai wajan 10 am.
A gurguje suka yi wanka suka shirya kana ganin su kaga amarya da ango sosai sumy tayi kyau wani sky blue lace ta sanya tare da tsara daurin dankwali na zamani zama sukai suna fira gwanin ban sha'awa yana tambayar ta irin abubuwan da take so da wanda bata so zayyano masa tayi shima ta tambaye shi abun da yake so da wanda baya so shima sanar da ita yayi .basu wani dade suna firar tasu ba akayi nockin kofar gdn su tashi yayi ya je dan ya bude tambaya yayi yace waye? Nice yaji muryar kanwar shi ,bude gidan yayi tashigo hannun ta dauke da kula ta abinci ,karbar daya yayi itama ta karaso da dayar a hannun ta
Shiga dakin suka yi sumayya ta karasa ta karbi na hannun mijin nata ta ajiye a kasa itama ta'iba ta ajiye na hannun ta xama tayi suka gaisa da yayan nata sannan ta ce aunty sumayya ina kwana ? Itama amsawa tayi cikin sakin fuska da walwala sannan ta tambaye ta mutanen gidan su ,lfy Alhmdllh tace da ita .shiru suka yi daga bisani sumayya ta tashi taje kicin da kulolin ta bude su wow tace ganin abunda take so wato funkaso da miyar taushe wadda tasha nama da kayan kamshi zuba musu taushen tayi a cikin kwanon kass sannan ta zuba funkason a food flask ta kawo musu
Kwantaina roba ta dauko tare da ruwa a cikin ta don dauraye hannu bayan sunci abicin ne sun gama sai Amir yace ta'iba ta tashi su tafi yana so yaje ya gaisa da baki aikwa nan sumy tace wllh tsoro take ji gida ita daya kawai yaje yabar ta'iban su zauna ta dauke mata kewa ,to yace mata .sukayi sallama ya tafi gidan su ..
Sumayya tashi tayi ta dauko wayar ta ta nemo gun photuna ta baiwa ta'iba tana ganin pic din bikin su
Kallo ta kunna gami da mikewa a kan doguwar kujera ta dan kwanta tana tunanin gidan su Allah sarki su umma ta nayi kewar ku sosai .
A kwan a tashi babu wuya a gun Allah sumayya ta samu ciki sai dai yana wahalar da ita sosai ga yawan amai gashi bata son miya a abunci ko za tayi girki to sai ta toshe hancin ta da dankwali take samun damar yanka albasa ta yi miya .sai kwadayin tuwo dumame kai ko brush tayi sai ta wuni tana amai sai dai a nemo mata aswakin darbejiya to fa aranan zata wuni lfy ,
Cikin sumayya ya shiga wata na uku sai aka kara samun wani fi'ilin laulayi domin dan cikin ta zarnin fitsari yake so dadin shi take ji har wani ajiyar zuciya take yi yayin data shaki zarnin nan
Kai jama'a wllh iyaye mata suna cikin yanayi kawo kan laulayi rainon ciki da tsufan shi zuwa haihuwar shi ,ranar da kake so ka rabu da cikin wato ranar da zaka haihu tofa shima anan gixo ke sakar domin ranar akwai fargaba da tashin hankali,wata tayi nakuda mai tsayi wata kuma gajerar nakuda tofa ba nakudar ba fasowar kan dan jaririn Kai tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki ubangiji kasa mu gama haihuwa lfy ka rabamu da samun tangar da a cikin ta .wllh baka taba sanin muhimmancin iyaye sai ka haifi naka musamman mace ,kaiii ni dai kam haihuwa tana bani tsoro ybangiji yasa mudace Amin.
Gida yau take son zuwa idan ta wuni a can daga nan sai ta wuce gidan iya bbr Amir itama ta gaishe da ita,
Bayan taje gida ne murna ta kaure tsakanin iyayen biyu da tilon diyar tasu sai farin ciki suke dan ganin ta cikin kwanciyar hankali suna nan nan da ita mutuniyar uwar shagwaba nan fa ta narke musu sai shagwaba take yi san ranta.
Bayan sallahr la'asar ne tace musu gdn su Amir zata wuce daga can zasu wuce gida
Sallama ta musu dakyar ta tafi tana mai jin rashin dadin rabuwa d iyayen nata
Napep ta tare ta mai kwatancen gidan bayan ta sauka ne ta dauko jakarta da kullin kayan daddawa da kubewa d kuka sai man shanu sannan ta baiwa mai napep kudin shi.
KOfar gidan ta karasa gami da yin sallama ,amsawa akayi ai ta'iba tana ganin itace ta raho da gudu ta rungumeta hajiya iya tana mai hararar ta tare da fadin saikin kayar da ita irin wannan gudu haka ai saiki jimata ciwo ,sumayya ce tayi murmushi tace wa hajiya laa hajiya bb komi ai ta'iba tawa ce munyi missing din juna ne shiyasa nima sai dokin inxo in ganku nake .dariya hajiya iya tayi ,taji dadin furucin surukar ta ta don hkn ya nuna macen arziki ce .
Sannu ta mata tace ta karaso ta zauna ,zama tayi suka gaisa take tambayarta mutanen gidan su lafiya tace mata sannan ta mika mata sakon umma ,godiya tayi mata tace kai naji dadin wannan kyauta da tabani kai Allah yasaka da alkhairi nagode sosai.
Fira suke dayake hajiya iya bb ruwanta mace ce mai san mutane shikenan sai zaman nasu yy dadi domin sumayya bata da kiwar aiki sarai dagewa tayi ta yiwa hajiya iya ayyuka .sai sanya mata albarka takeyi da yi mata fatan sauka lfy.
Bayan sumaiyya ta koma gida ne sai ta tarar da Amir ya riga ta dawowa har ya musu shimfida,sannu yayi mata ya hada mata ruwan wanka don ta karfi a jikin ta.
Godiya ta mishi kana ta je tayi wanka.kwanciya take son yi amma abu ya gagara marar ta ciwo bayan ta ciwo ta rasa ina ne ma gun da yake ciwon sai salati take gami da fadar lahaula wala quwwata illa billah.Amir hankalin sa ya tashi ganin halin da sumayya take ciki ai nan da nan ya shiga makotan su ya kira hajiya deluwa don taga ni shin haihuwa ce ko kuma wani abun ne na daban,
Hjy deluwa tsohuwar ungozoma ce tasan kan aikin ta na goxanci ,tana ganin halin da sumayya take ciki ta tabbatar da haihuwa ce asibiti tace su tafi saboda gudun matsala gashi kuma haihuwar fari ce ,na'am yayi da shawarar ta hjy deluwa ,makocin sa ubale mai adaidaita ya samu yace ya taimaka masa iyalin sa bb lfy yana so ya kaisu asibiti,da to ya amsa ta koma gida ya dauko key suka rankaya asibiti tun sumayya na gane wasu abubuwan har ya xamana bata gane kowa duk ta galabai ta.sannu yake mata bayan an sauke su ne nurses suka taho da gadon daukan marar lfy aka shiga da ita labour room aifa ciwo nan ya dawo gadan gadan ba a dau awa biyu ba sumaiyya ta haihu Allah ya azurta tasu da kyautar yara biyu 'yan maza kaii masha Allah yara da uwar su gwanin sha'awa domin sai da aka gyaresu sannan aka yiwa su Amir albishir.
Murna kamar suyi me hjy deluwa kam ciki ta shige ta xauna kusa da sumayya tana mata sannu sannan ta dauki yaran ta yi musu addu'o'i ,dakin hutu aka ce wa Amir ya shiga a miko masa yaran hamdala ya shiga jerawa Allah madaukakin sarki da wannan kyauta da ya musu ba tare da yayi shawara da kowa ba .
Bayan an miko yaran ne Amir ya kura musu ido yana jin kaunar yaran nashi a cikin jinin jikinsa godiya yayi ta jerawa rabbi sarki ga gara misali,Addu'a yayi musu kana yayi ta daukan su a photo sosai ya shagala a gun yaran nashi.
Ba'a dau lokaci ba aka basu sallama suka dawo gida,Amir da kanshi ya hura wuta ya hadawa sumayya ruwan wanka na jego hajiya deluwa ta taimaka mata suka shiga toilet ta mata wanka na musamman tare da gasa ta sosai ita kanta sumayya taji dadin wankan duk wani ciwo na jikin ta yayi kaura ya tafi sai dai abun da ba'a rasa ba.
Kan kace me dangi sun zo ganin twins don a dangin su Amir ba'a taba haihuwar 'yan biyu ba kai koda 6arin su ba a ta6a yiba.kowa sai San barka yake yi ana ta yiwa sumayya barka da arziki Allah ya raya yasa masu taimakon musulunci da musulmai ne Allah ya bada lfyr shayarwa Amin.
Siyayya ta musamman Amir yayi wa mai jego da yaran sa,domin kayan barka ne aka musu shi na musamman ita kanta mai jego akwati seti daya yayi mata sai twins suma kowa da akwatin shi kayan su iri daya kai hatta da zobe na zallar ruwan azurfa iri daya ne sai dai stone din jiki da ya ban-banta hassan shine stone din shi "ja" sai hussain nashi stone din fara kowa an sanya mishi a yatsan shi na tsakiya hannun yayi kyau kamar dan su aka yi zoben
Atamfofi aka zuba wa sumayya guda biyu sai lasuna biyu shadda daya material guda biyu da mayafi sai hijabi jalbab guda biyu sarka da dan kunne d abun hannu ,gaskiya babu laifi Amir yayi bajinta kaya sunyi babu karya adai dan talaka a wannan zamanin sai dai muce Alhamdulillah .
Yau take suna an yanka manyan raguna guda biyu an radawa yara suna hassan shine Ibrahim sai Hussain shine Abdullahi za'a kira su da hassan da hussain din su.
Can na hango mai jego da yaranta ana daukan pic da sauran mutane maijego ta dankara wani hamshakin lace wanda Amir ya siye su a gun mom hibba don kayan ta indai ka siya to babu dana sani domin kaya ne na daukan wanka duk wanda ya kalli sumayya yasan ta sa suttura mai kyau da tsada ta zama big mama hannun ta da wuyan ta yasha kayan alatu ita kanta sarkar a gun maman Afrah ya siye ta gaskiya bb laifi maijego ta yi kyau ita d yara sai dai muce allah ya raya mana
Kyautattuka ta same su a gun mutane da dangin su an raba kayan suna da calendar mai dauke da hotunan 'yan biyu a jiki su karima musa anxo gidan Amir anyi wankin ciki domin taci ta koshi tasha lemuka San ranta tayi guzirin wasu domin bb a House.
Taro ya watse anbar mai jego da yaran ta sai mai mata zaman wanka kanwar baban ta Aunty saratu mace mai kirki da dattaku tana kula da sumayya da yaran bata gajiya da hidimta musu Amir yana yawan cewa ki rage ayyukan nan Aunty saratu nima fa na iya wasu abubuwan sai dai tayi dariya tace aikin ai danshi na zauna da babu ai da na tafi gidana nima
[6/6, 10:26 PM] Mom mashkr & Afrah: ZAMAN 'YA'YA NA
Na mmn Annur
Page(5)
Wannan page din dukan shi na sadaukar wa mutane biyu mutanen Amana masoya a gare ni baki na bazai iya ba zai iya wassafo kaunar su a gareni ba,Fa'iza Abubakar (mmn Afrah) marubuciyar littafin 'YAR ZAMAN WANKA d KAZAMIN MIJI'
Sai Hajjaju mutanen saudiyya Bilkisu Badamasi (mmn meenal)
Allah yasa Amintar mu ta dore har gidan Aljannah.
ASLAMIYYA
Aslamiyya likkafa taci gaba inda ta samu wani Alhj Adnanu yake kashe mata 'ya'yan banki nan fa take cin karan ta babu babbaka domin har kayan daki ya canja wa innar ta karima irin matan nan ne masu dagawa musamman da taga an canja musu kayan daki sai ta fara feleke idan tasan kai ba mai kudi bane to fa ba zata saurare kaba kai ko a cikin kawaye ba kowa take hulda da shiba ita a cewar ta masu kudi sune da duniyar talaka kwa yana duniyar ne amma ba jin dadin ta yake ba.
Yau dai sun shirya da Alhaji Adnanu domin kaita shop rite don yin siyayyar kwalam d makulashe,anan ne ta hadu da tsohon saurayin ta Kasim yana xaune a kofar shop rite din inda kasim yake sanye da uniform na shedar cewa gadi yake musu a nan din
Wani kallo ta bishi dashi wanda shi bai ma san tana yi ba kallon kurar da ta dauko su ma bayyi ba aiko ta shaka da yawa ita anata tunanin zai gigice ya shiga wani hali idan ya ganta d Alhajin ta. Bata san cewa Kasim shi baya zafafa abu idan ya janye a kan abu to ko da zai shiga damuwa baya waiwayar abun duk yanda ya kai da son Aslamiyya kwata kwata ta fice masa a ranshi
Shiga ciki sukayi sukayi siyayya ta kece raini har innar ta ta daukarwa kayayyaki gun biyan kudi suka karasa aka musu total din kudaden kayan Atm ya zaro daga aljihun shi ya mikawa