Author : Maman Annur Category : Top Hausa Novels 2025
shi da zaki yiwa mutane fi'ili waike mace ta gari,nima ta garin ce rainin wayo ne bazan dauka ba "
"Allah ya baku hakuri "
Sumayya taji ciwon a binda fareeda ta fada mata duk da gaskiya ne to Amma furicin nata ya yi mata ciwo,tabbas gaskiyar fareeda da ta ce bata da muhimmanci a rayuwar Amir.
Dakin ta koma don jin tashin hassan,A cikin dakin ta taradda Amir kallon ta yake yi tamkar ya samu TV. Share shi tayi taci gaba da uzirin ta sai can da yaga bazata yi mishi magana ba sai yace da'ita" Sumayya kada ki yarda da zancen matar can don Allah,domin kin San Ni dake soyayya ce ta hada mu ba zamu ta6a rabewa ba kuma zancen baki da muhimmanci a rayuwa ta wllh karya take ni kaina ban San me yasa wasu lokutan nake ganin ki a siffa marar kyau ba,Sumayya duk abinda yake faruwa wllh ba da sani na ba kiyi hakuri. Ni kaina ban San me yake damuna ba"
Kuka take haikan Wanda ba wani abu take tunawa ba illa soyayyar su da suka gudanar kafin shigowar fareeda rayuwar su.
Tasowa yayi ya zauna kusa da ita ya rike hannayen ta yana share mata hawayen fuskar ta cikin tausayawa da kalamai masu dadi,kukan ta daina ta tsayar da kanta a kan fuskar shi suka shiga kallon_kallo,gira ya daga mata yace "kiyi hakuri ki tayani da Addu'a Allah ya yaye mun abinda yake damuna"
Kanta ta gyada alamun zata taya shi da Addu'ar.
Hmmmm fareeda ce ta taho dakin Amir tana shiga ta taradda masoyan suna kallon love kana ganin su kasan sunyi missing junan su.Tsayawa tayi tayi turuss ranta duk ya 6aci har wani hazo-hazo take gani a cikin idon ta saboda tsabar kishin jaraba yana cinta.
Sumayya tana ganin kallon da fareeda take musu ai itama sai ta narke a jikin Amir ta fara nuna masa nata salon a wani hargitse fareeada ta fito daga dakin ta shiga dakin ta ta dauki hijabi da wayar ta sai mukullin dakin ta da ta dauka ta fice a gidan.
Bata zame ko'ina ba sai gidan su inda ta jewa mahaifiyar ta da zancen abinda ya faru har da Marin da Amir yayi mata,mahaifiyar ta ce tace mata su tashi su tafi gurin malamin su don da zafi-zafi akan daki karfe,tafiya suka yi mai nisa tukunna suka samu gidan malamin nasu,bayan ya musu iso suka shiga cikin zauren nashi.
Sun yi bayanin yanda suke so su samu nasara anan yace musu" to yanzu akwai wasu bayani da zan muku sai ku za6i daya a ciki"
"To ranka ya dade muna sauraro"
"Na farko dai a kwai lakanin da za'a masa zai zama jani talau ko mahaifiyar shi bata isa dashi ba sai abinda kika ce tukunna, sai kuma Wanda za'a yi musu su duka kowa ya tsani kowa,sai Wanda za'a yiwa yarinyar a Sanya mata warin ja6a"
"To malam kawai a yiwa yarinyar asaka mata warin ja6ar ta yanda ko ra6ar ta bazai yi ba"
Wasu surutai ya shiga yi tare da basu kullin magani Wanda zata zuba a ruwan wankan sumayya Amma saita yi dubara don in har wadda za'a yiwa sihirin ta gani da idon ta to ya karye abun zai koma wa maishi"
Godiya suka mishi suka ajiye masa kudi har kimanin naira 50k.
Cikin farin ciki suka dawo gida,sai can a shelake tukunna fareeda ta tafi nata gidan.
Tana shiga gidan ta taradda sumayya daga ita sai daurin kirji ta yafa tawul xata shiga wanka ai a sukwane tace mata "don Allah taimaka min zan kama ruwa kafin ki shiga wankan"
"Bismillah ki shiga"
Shiga tayi da sauri ko Addu'a bata yi ba saboda sharrin da take son bibiyar sumayya dashi.
Kunce kullin tayi ta zuba mata a ruwan yanda baza ta gane ba ta jima a tsaye sannan ta fita daga bandakin.
Sumayya shiga tayi ta fara zuba ruwan a jikin ta.tana gama wanka ta fito ta koma dakin Amir anan ta shirya yana kwance har barci ya fara daukan sa sai ji yayi acikin baccin sa wani abu marar dadi ya ziyarci hancin sa,bude ido yayi kadan sai yaga sumayya tasha kwalliya Amma wari yana fitowa a jikin ta
"Sumayya wai turare kika shafa ko kuma wani abu daban?"
"Hmmmm bbn twins kenan turaren da kake so ne na shafa ai"
" To wllh Ni dai bana jin kamshin turare ko daya illa warin mushen 6era da nake ji"
Gaban ta ne ya fadi tace furta Innalillahi.......,sannan tace masa"wari kuma ?" Idon ta yana mai zirarar da hawaye,aran ta take cewa
Wannna wace irin rayuwa ce daga wannan sai wannan Allah ka kawo mun dauki .
Hassan ta dauka takai daki sannan ta dawo ta dau Hussain shima ta Kai daki zama tayi ta ke tunanin me yake faruwa da ita ne? Ta yi tunanin yau matsalar ta takare ashe a yau din wata matsalar zata fito sabuwa.
Alqur'ani ta dauka ta fara karantawa tana yi tana kuka har dai taji ta ji salama a ranta,tayi addu'o'in ta tayi tawassuli da karatun da tayi akan Allah ya shiga lamarin ta Allah ya tsare su da yaran ta da mijin ta wannan wari da mijin ta ya shaka Allah yasa anjima kadan ya shaki kamshi a jikin ta.ta dade tana Addu'a sannan ta kwanta a kan gado sai bacci.
A cikin baccin ta ne tayi mafarki da fareeda tana janta kofar gida ita da yaran ta wai sai amir ya taho zai kwace su anan fareedar ta watsa masa wani bakin ruwa a fuskar shi ai nan da nan sai suka hadu suna Jan su sumayya sai da suka kaisu har karshen layin su sannan suka koma gida.
Farkawa sumayya tayi bakin ta dauke da Addu'a
Kanta taji ya Sara mata Addu'a tayi ta shafawa kan nata ta tashi zaune ta jingina da fuskar gado
Allah ka rabamu da sharrin fitinar kishiya
👏🏻👏🏻👏🏻
https://chat.whatsapp.com/LskntU56JpKIS3kUZmcwPV
ZAMAN 'YA'YA NA
Na Mmn Annurr
Page(15)
Suwaiba ta dage da neman kudi domin hakan ta fadawa Dan ta Abduljabbar " Babu maraya sai rago Abduljabbar mu dage mubaiwa mara Da kunya zanyi ko wacce sana'a matukar za mu samu rufin asiri a cikin ta kaima ka dage ku karasa karatun ku in shaa Allah a gabanmu a kwai nasara wacce za muji dadi har wanin mu shima ya ra6u damu yaji dadi"
"In shaa Allah Maman mu lokacin nasarar mu ya kusa zuwa yana daf damu"
"To 'yan Albarka Allah ya nuna Mana lkcn da Alheri"
"Amin" suka ce yaran nata.
Akwai wata makaranta a kusa da gidan kawun su Abduljabbar din in da suke da zama kenan to taje ta Kai takardunta ko zasu bata gurbin da zata ke koyar da yaran koda Allah zai sa lokacin daukan ma'aikata in tana da rabo sai asanya sunan ta.
Cikin ikon Allah headmastern ya amince aikwa godiya tayi masa sosai don taji dadi sosai.
Ta fara zuwa makarantar cikin ikon Allah da suka ga tana da himma da kwazo ga shi tana kula da aikinta yanda ya dace aikwa ana sanarwar za'a dauki ma'aikata headmaster ya kar6i takardun ta shine ya shige mata gaba akan komai har aka yi musu jarabawa da Ikon Allah sunan ta ya fito suka je akayi musu screening.
Kafin a basu offer ma sunsha wahala har ta fitar da rai sai gashi ankira su an basu offer su a hannu,zo kaga murna agun su don har Azumi suka yi su ukun na nuna godiyar su ga Allah madaukakin sarki wanda duk ya dogara da Allah ya yi yakini mai kyau to hakika Allah zai shiga lamarin sa.
Anyi posting din ma'aikata in da aka kaita makaranatar da take zuwa take bolontary.sosai ta dukufa wajen ganin ta tafiyar da aikinta yanda ya dace shima karamin danta ta maido shi makarantar da take saboda mahaifinsu ya daina biya musu kudin makaranta,sati biyu daya wuce Abduljabbar yaje ya sanar dashi kudin makarantar su ya kare gashi har an korosu.
Budar bakin shi sai cewa yayi ai shi yanzu ya zare hannunsa daga lamarin su suje suwaiba ta biya musu.haka Abduljabbar ya dawo jikinsa duk a sanyaye yake sanar da ita abinda bbn su ya fada masa hakuri ta bashi tace dashi "kajure ka shanye duk wani wahalhalun rayuwa don cikar burin ka in Sha Allah ubangiji zai taimakeka duk wani Wanda kagani yana cikin daula to hakika in dai ka bibiyi tarihin rayuwar sa to zakaga yawanci sai ansha wuya tukunna ake jin dadi daga karshe don haka bana so zuciyar ka ta mutu katashi ka nema don gudun 6acin rai musamman yanda mahaifin ku yake da kudi Amma gashi ya kasa kula damu sai sharholiyar sa yasa a gaba mu hadu muke masa Addu'a Allah ya dawo dashi hanyar kwarai"
Karan message ne ya tashi suwaiba daga barcin da take na safe wayar ta dauko ta duba ganin sakon daga banki ne yasa tayi hanzarin dubawa
Alert ne na 90k Albashin su na farko,hamdala take yi sannan ta daga murya ta Kira Abdurra'uf da yake tsakar gdn nasu yana wanke uniform din shi na islamiyya.
"Zo nan Dan Albarka kaga Albashi aka Mana yanzun nan kudin ya shigo mini"
"Mama kice yau akwai sha'ani a gidannan hhhhhhhh wayyo dadi maman mu tayi kudi muma munyi kudi"
Dariya take mishi ganin murnar da yake yi don yaji batun kudi
"Mama wai nawa ne kudin ma?"
"Abdurra'uf 90k ne"
"Wayyo Allah mama naji dadi wllh yau zamuci dadi a gidannan hohoho yaya baya nan sai ya dawo mu kasafta kudin"
"Hmmmm yaro ni kuma ina ina to mai Dan uwa da zaku kasafta kudin " tana dariya take tambayar shi.
"Ai wllh Mama kudin nan kawai sai da kisa ido kiga yanda zamu yagalgala shi nida yaya domin shopping za muje muyi "
"Hhhhh to Allah ya kawo shi lfy sai kuje kuyi Mana shopping din maybe aljihunku a cike yake da kudi bansani ba"
"Kiji mama da wani zancen to ina nufin albashinki dashi zamuyi bishasha"
Suna cikin wannnan firar ne Abduljabbar yayi Sallama ya shigo, amsa mishi sallamar sukayi sannan Abdurra'uf ya labarta masa labarin jin Alert.shima murna yayi sosai kana yace mata "mama kinga sai a siyo kayan Abinci da sabulun wanki Dana wanka sai Dan abinda ba a rasa ba"
Itama ta goyi bayan shawarar da ya bada,Abinci ya ci ta bashi ATM din tace suje shida Abdurra'uf su yi siyayyar yanda ya dace .
Sun tafi wani shago da yake a tsohuwar unguwar su anan suka yada zango don sun saba da mutumin yana da kirki yakan Dan taimaka musu da bashi wasu lokutan,siyayya sukayi suka hada da manja karamar jarka,mahaifin su ne yazo shagon zai siyawa Aslamiyya pad bai kula dasu ba sai da ya kar6i pad din zai bada kudin sai Abduljabbar yace ba sai ya bada ba zai biya,kallon su yayi sannan ne ya kula dasu.
Hada baki sukayi wajan gaishe dashi" Baba ina wuni?"
"Lfy kalau ku daga ina kuke? Kar ku sake ku kar6i bashin sa saboda ni yanzu ba biya muku zanyi ba saboda haka kuje kuce mata kada ta kara turo ku shagon nan kar6ar bashi"
Mai shagon ne yace masa" Alhaji baka ji yaron wajen naka yace kabar kudin pad din zai biya ba? To ai ba bashi suka kar6a ba kaga duba nan duk siyayyar nan daka gani to kudi zasu bani yanzun nan"
Alhjai Adnanu mamaki yayi yana tsaye suka mikawa mai shagon ATM ya zari kudin sa ya basu ATM din su.
"Baba ka gaida gida mu muntafi"
Su Alhaji Adnanu antafi duniyar tunani ko ji baiyi ba sai juyowa yayi yaga wayam har sun 6ace masa.mamakin da yake yi shine to waya basu kudin nan da sukayi wannan uwar siyayyar haka,lallai suwaiba kar fa ta fara bin maza saboda cikar burinta na Zama da 'ya'yan ta.
Pad din ya kaiwa Aslamiyya aikwa fada tashiga yi mishi akan ya dade bai kawo mata ba don wulakanci yasa ta zauna zaman jiran shi.shidai shiru yayi mata don abinda yake damun shi ma ya isheshi,wani lokacin in ya zauna tunanin 'ya'yan sa da yake kauna to kwa ranar zai wuni da ciwon kaine Amma wani lokacin idan taga kamar asirin jikin shi yana neman karyewa to itama kara kaimi take yi.
Sun isa gida lfy suka bata labarin sun hadu da baban su wai yake cemusu kada su kar6i bashi don ba biya zaiyi ba,dariya tayi tace in Sha Allah yanxu kam muda cin bashi wai don muci Abinci in Allah ya yarda takau.kayan ta shiga budawa sarai kaya sunyi domin kwa ko ita ta je da kanta iya abin da zata siyo kenan,canji ta dauka a cikin Jakarta har na 5k tace su kaiwa kawun su yasha fura,aikwa suna kawowa yazo da kanshi yamata godiya yace "suwaiba bayan Abinci da kuke bani kuma harda dawainiyar kudi haka? Gaskiya yayi yawa da an rage"
" A a kawu ba za'a rage ba muma fa ka taimake mu a lokacin da muke bukatar taimako don haka ko nawa zan baka ban fadi ba"
" To nagode suwaiba Allah ya saka miki da alkhairi ya shirya miki yaranki ya juyo da hankalin mijin ki gareku "
"Amin ya rabbil alamina nagode kawu"
Nama ta aika aka siyo musu na 2k suka ci."oo mama yau dai wllh wani gata kike nuna mana"
"To banda abinka Abdurra'uf in ban nuna muku gata ba wa zan nunawa? Ku kadai gareni fa kuma ni kadai gareku to ba dole mu hadu mu hade kanmu ba "
"Hakane wllh mama Allah ya nuna Mana lokacin da zamu jiyar dake dadi maman mu "
"Amin "
Alhaji Adnanu yau dai ya wuni sukuku bashi da kuzari,domin akan kanshi yasan bai kyauta wa suwaiba da yaran ta ba gashi bai tambaye su inda suke da zama ba balle yaje ya dubasu duk da wani 6angare na zuciyar shi yana hana shi hakan
"Gaskiya ban kyauta wa suwaiba ba kudin nan da nake facaka dashi ba nawa bane na suwaiba ne Amma bata ta6a tambaya ta ba akan in bata kayan taba,Amma dai zan nemeta ta dawo gidan nan saboda 'ya'ya na ina kaunar su sosai "
Bai San a fili yake zancen ba ashe Aslamiyya taji duk abinda yake fada,"to ba saikaje ka dawo da itan ba da kasan da haka ka koresu don munafunci shine zaka zauna kana wani zantuka marasa amfani"
"To laifi nayi don na zauna ina tunanin iyalina? "
"Bakayi laifi ba Adnanu Amma ka kusa daina tunanin su "
Aslamiyya gurin bokanta ta koma ya sake juyar mata da hankalin mijin nata aka dasa masa tsanar yaran nashi da suwaiba,al'amarin dai babu dadin kallo.
Sumayya dai yanayin da ta tsinci kanta babu dadi domin mafarkin da tayi to shine ya faru a gaske wai fareeda tana neman yi mata duka ita ala dole sai ta zane sumayya, sosai abin ya daurewa sumayya Kai ganin fareeda ta nufo ta da bulala wai saita Zane ta wllh indai bata bar mata gida ba."lallai fareeda baki da tunani ke yanzu ke ce yakamata ki fadi hakan ko kuma Ni yakamata in fada ? Kada ki manta ni kika tarar a cikin gidan nan don haka wllh wllh wllh kika kuskura wannna gajirabil din hannun naki mai kama da hannun samudawa ya ta6a Ni to kwa jikin ki zai gaya miki ,ina kyaleki ne saboda wasu dalilai to amma tabbas ya kamata in fyato dake daga hancina "
"Sumayya ke kinsan Ni ba sa'ar ki bace ko to kiyi a hankali wllh Zane ki zanyi a cikin gidannan banxa bora wadda bata da zuciya miji yana wulakanta ki Amma kin nace kin zauna"
"Hhhhhhhh fareeda kenan to ai ke ce banxar wadda bata ramin kanta sai dai na wani ke fa mugun halinki ne ya rabaki da tsohon mijin ki to amma da yake kanki na dankaline shiyasa ba zakiyi hankali ba ki San Annabi ya San duniya ,a a sai dai kici gaba da Abinda kika ga dama ,to kiyi watarana wllh ko ance kiyi baki isa kiyi ba domin abinda kike takamar dashi ya koma gidan sa Wanda yafi jin dadin zama aciki"
"To muzuba mu gani shege ka fasa"
Suna cikin yin fadan ne Amir ya shigo gidan wani kallo da ya aikawa sumayya Saida hanjin cikinta ya kada"wai hayaniyar me nake ji haka acikin gidana ?"
"Baby wannan yarinyar ce zata Raina min hankali zagina take yi,wai saina bar mata gidan ta tunda ita na tadda a cikin sa"
" Wllh bbn twins ba haka akayi ba wai bulala ta dauko zata dake Ni"
"Ke dalla malama kimana shiru kina bude baki kina cika Mana gida da wari wllh sumayya idan kika kara buda wannan tsatstsaman bakin naki sai na Zane ki din tunda kin Raina mutane,don Allah ji ta wai wannan macece jiki duk wari sai mugun hali da bakin kishi tasa a gaba Amma bazata gyara jikin taba kina mace Amma kina barin jikin ki da wari?"
"Innalillahi yanzu irin cin mtuncin da zaka min kenan Amir nice nake warin ? Sakayyar da zaka min kenan?"
"Wllh idan baki tafi dakin kiba to tabbas zan iya 6allaki haka kurum ki zauna kina mana wari a gd sannan ga warin baki gaskiya inaga gara inje in sanar da 'yan gidan ku abinda kike yi na kazanta mace har mace Amma kin zauna kina mana warin ja6a a cikin gida"
Daki ta shige take kuka tare da ambaton Allah."Allah kasan abinda ake min acikin gidan nan ya rahmanu ya rahima ya hayyu ya Qayyum kaji tausayina ka tallafa min ka yaye mun abinda yake damunaYa rabbi ka warware duk wani kulli da yake jikina da jikin mijina"
Tashi tayi ta dauko ganyen magarya da tazargade ta hada su a guri daya ta shiga karanta ayatul shifa baya ta gama ne ta rufe dakin ta da mukulli ta cire kayan ta, addu ar ta fara Sha cikin hannun ta sau uku,sannan ta shimfida wani Zane ta hau kanshi tayi wanka da wannna ruwan maganin da tayi addu'a acikin sa,hatta da cikin gashin ta Saida ta zuba wannan maganin bayan ta gama wankan saita bari jikin ta yabushe da wannan tsakin maganin aikwa nan take jikinta ya fara kaikayi kamar tayi kuka Saida ta bari ta daina kaikayin sannan ta goge tsakin maganin ta sa kayan ta ta kwanta bacci.
Kuyi hakuri da wannan ina busy ne shiyasa kwana