Chapter 1 Reading SANADIN KENAN BOOK 4 BY SUMAYYA TAKORI.txt Arewa Novels

SANADIN KENAN BOOK 4 BY SUMAYYA TAKORI.txt

Author :  Sumayya Abdulkadir Takori Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   1 / 7

1 to 3K   out of 20.7K words








4







SUMAYYAH ABDULKADIR
Babbangoro2015@yahoo.com
Takorikabara@gmail.com
SADAUKARWA
Sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, Allah ya hada mu cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.

DON TUNAWA DA
Domin tunawa dake marigayiya Kakata kuma Goggo na HAJ. HAWWA ABUBAKAR WALI (Haj. Mai Mage ). You are evergreen in my memory Allah ya kai haske da rahma kabarin ki.

TUNASARWA
Ban yarda a kwafi wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ko karanta shi a rediyo ba tareda iznina ba, hakan zai kaimu ga tsayawa gaban hukuma, wadanda bansan inda kuke ba kuma zamu hadu a kotun Allah ranar da bawa bashi da abin biyan hakkin dan uwansa sai kyawawan Ayyukansa. Takori


FATAN ALKHAIRI
Fatan alkahairi gareku makaranta na da jimirin bin littattafaina ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke, nagode madallah da yabawarku. .

JINJINA
Littafin SANADIN KENAN! Ya jinjina miki AUNTY ZULAIHA ZUBAIR (Mrs late Tafidan Kano Hakimin Kura, SANADIN KENAN! Ya jinjina miki saboda gudummuwarki gareshi. Aunty Zulaiha Madallah Allah ya kara lafiya da nisan kwana.





SANADIN KENAN 4
S
u Jalan sunyi mamakin daular da suka ga 'yar uwarsuHauwa a ciki. Don a saninsu mijin ta bashi da komai har ya rasu, bayan gidan da suke ciki.Da mahaifiyarta ta tambaye ta murmushi ta yi, tace"SANADIN ilmin Amina ne".
Ranar litinin ita ce ranar da Amina za ta tare a gidan mijinta.
Kamin ranar ta kimtsa komai nata. Har Goggo na yi mata fadan ta ajiye tsofaffin kayan sawarta, ta fiya tsumulmula. Amina tayi murmushi ta ce,
"Goggo ki bar min su. Akowanne canjin rayuwa da na samu ina son in ke sanyayadda nake a baya in memory, kada in shagala, in manta da yadda na taso".
Goggo ta tabe baki, "Ai falsafa nan ta ganki ta barki".
Manyan motoci biyar Akilu ya kawo Shira, aka kwaso gaba daya dangin Amina manya da yara da matan Baffanninta kai har da wadanda ba dangin Iya babu na Baba aka dura su sai gidan Gwamnati.
Su Aisata kuwa motoci ne na alfarma daga maigirma Gwamna guda uku don su kadai jamaar Sierraleone.
A cikin gari kuwa dukkan abokan arzikin Goggo, Inna Zulai ita ce kan gaba, su Talatu masu aikin Goggo abu nasu maganin a kwabe su. Makotan Goggo na unguwar da suka baro da na sabuwar unguwa duk haka aka kwashe su Government House.
Sai a wannan lokacin mutane da yawa suka san waye ya auri Dr. Amina. Masu mamaki sun yi, masu gulma sun yi amma masu fatan alkhairi sun fi yawa kasancewar mahaifiyarta mutum ce wadda ta ke zaune lafiya da kowa, kuma ma'abociyar alheri, masoyanta sun rinjayi makiyanta.
Aka bude wa duka 'yan kawo amaryar guest house aka ce ango ya ce su zauna su huta har tsayin kwana uku. Murna a gurin 'yan Shira abin sai ya ba ka dariya. Shi kuwa ya sa aka yi ta cika su da liyafa iri-iri, sai da ya kure hadamar kowa, abinci suna gani amma sun kasa ci saboda koshi. Sun manta da wata Amina wadda aka kai 'upstairs' shagalinsu kawai suke yi.
Yan Sierraleone kuwa downstairs aka bude musu tareda alummar Hajiyan Jikas. Koda suka sada Amina da dakin aurenta basu ma zauna sun kwana ba suka koma gidan Goggo a motocin da suka kawo su, bayan an gabatar dasu ga Hajiyan Ji-kas.
Anty Laila ba ta kasar, ta je umrah, wannan karon da gaske Saudiyyan ta je ba Dubai bamusamman don ta yi addu'a Allahya ba ta haihuwa tunda likitoci sun kasa tsinana mata komai a Dubai, sai cin kudinta a banza, ta ga gara ta koma ga Allah don ta ji rade-radin Ma'arouf yana neman aure. Hankalinta in yayi dubunnai to ya tashi, sai dai duk kwakkwafinta an kasa gano mata wa zai aura saboda ba’a sa a (media) ba, yau satinta daya a can kuma sati biyu za ta yi.
Hajiyan Ji-kas da jama'arta da suka karbi amarya daga hannun danginta na uwa da uba suna nan a downstairs, washegari za su koma Ji-kas, Hajiya kuma Lagos za ta wuce.
Amina tana kusa da Hajiya lullube cikin laffaya, ta ki yarda ta zauna a dakinta da ke upstairs,self-content ne kamar duka dakunan wanda ke kallon na mai gidan, na Laila kuma yana nesa da nata sai dai duk cikin tafkeken falo daya suke.
Hajiya da 'yan uwanta da kishiyarta Lami hira suke, har dare ya soma yi. Hajiya ta lura Amina ta fara gyangyadi, ga dare ya yi wajen karfe goma sha daya na dare, ta ce,
"Tashi haka Amina, mu je in raka ki dakinki dare ya yi".
Amina ta turo baki cikin shagwaba, yadda ta ke yi wa Goggonta don ba ta bambanta Hajiya da Goggo, tana fadin,
"Don Allah Hajiya ki bar ni in kwana cikin mutane. Ni wallahi tsoro nake ji gidan yana da girma sosai, na yi miki alkawarin gobe zan koma".
Hajiya ta rasa yadda za ta yi da ita don ba ta so ta takura mata ta koma kukan nan da ta yi musu sanda suka banbaro ta daga jikin Goggonta. Kafin ta bata amsa ma Amina ta gyara waje a gadon ta yi kwanciyarta, barci ya sure ta.
****
Sanda angon ya shigo gidan, karfe goma sha biyu na dare ya yi. Wajen Hajiya ya fara dosa da takunsa mara amo, wanda yake yi cikin nutsuwa, ya shiga ne don ya yi mata sai da safe ya wuce wurin amarya.
Duk jama'ar dakin sun yi bacci, wasu a gado wasu a kasa, Hajiya ce kadai ido biyu, makure ta ke a can kusurwar dakin kan sallaya tana lazimi, ba komai Hajiya Saude ke roka ba daga wurin Ubangijinta face nema wa danta Ma'arouf dacewa a cikin wannan auren da zuri'a dayyiba, Allah ya kare mata shi daga duk mai nufinsa da sharri, ya ba shi alherin da ke tare da Amina ya nesanta shi daga rashin alhairanta. Ya sanya ta zamo marufar asirinsa kamar Aisha, ya kade dukkannin fitintinu daga cikin aurensu.
Jin murda kofarsa da sallamarsa ya sanya ta yi fatiha ta shafa. Bai shigo ba saboda mutane, daga bakin kofar ya tsaya rike da marikin kofar. Hajiya ta amsa sallamarsa fuskarta cike da yalwa. Ya ce,
"Hajiya ba ki kwanta ba?"
"Yanzu dai nake shiri, don gobe sammako za mu yi, zan je ganin Ameena a makaranta (an kai Ameena wata makarantar kwana ta yara 'yan firamare a Lagos) sannan na wuce Jikas".
"Ai booking din naki na rana ne Hajiya, ba sai kin yi sammako ba".
"A'ah, gara dai in yin don ta ji dadi".
Ya juya zai fita,
"Allah ya ba mu alkhairi Hajiya".
"Amin. Ga Aminar a nan ma bacci ya dauke ta".
Cak! ya tsaya kamar bai ji daidai ba. Hajiya ta yi murmushi.
"Na yi-na yi ta zauna a dakinta ta ki, wai tsoro take ji, abu kuma da gajiya ba ta san sanda bacci ya dauke ta ba".
Saura kadan ya ce,
Taso ta Hajiya, wannan wane irin abu ne? An taba yin haka?Amarya a ranar aurenta ta kwana da 'yan biki? To ni kuma fa? Hajiya kin daina sona da alama........!".
Dariya ta kusa kwace wa Hajiya Saude ganin ya kasa tafiya, ya kuma kasa magana. Sannan ya kasa juyowa. Ta yi niyyar tashinta wata zuciyar ta ce, 'kyale ta yau daya dai ta huta da gajiyar biki, yadda Maarouf yake rawar kafar nan da kyar zai barta ta runtsa, gobe mu bar muku gidanku ku karata'.
"Ka ce sai da safe kuma ka tsaya, ko in taso ta ne?"
Ya yi gaba yana fadin, "A'ah, Allah ya ba mu alkhairi".
Hajiya ta ce, "Amin".
Washegari da safe su Hajiya suka yi shiri suka wuce. Bayan ta raka Amina dakinta ta yi mata nasihohi a kan ta zauna lafiya da Laila, ta yi hakuri da ita kamar zamansu na baya. Ta yi musu addu'a suka tafi.
Gida ya saura 'yan Shira a sassan baki suna ta sha'aninsu. Ba wanda ya damu da ya zo inda amaryar ta ke ban da Ramma matar Baffa Bilya, ita kam ta zo taya Amina hira.

His Excellency bai shigo gidan ba saboda ayyuka masu yawa da suka tsare shi a office. Tunda aka fara hidimar auren bai dauki hutu ba sai yau. Wajejen karfe uku na yamma ya samu ya kira Amina a waya.
"Shirya kayanki da abubuwan amfaninki da za su yi miki kwana bakwai, za mu tafi Abuja".
Amina ta ajiye wayarta a gefe, twna mita cikin ranta, wace irin tafiya ce saboda Allah daga kawo ta jiya ko 'yan biki ba su watse ba? Sai kuma su nemesu a gidan su rasa? Abin da ta ke fadi a ranta kenan. Bata san shi yan bikin yakeson gujewa ba. Sun isheshi sun dameshi, yana son samun privacy hakannan da matarsa. Rabon da ya ganta tun kafin daurin aure. Hakan kuma bai hana ta bin umarninsa ba, ta samu babbar jaka ta shirya duk abin da ta san za ta bukata. Ya fi karfin ya yi hukunci, ta ce, a'ah! Ya fi karfin komai a gare ta!!
Ya sake kiranta a karo na biyu bayan ta idar da sallar la'asar. A gurguje yake fadin,
"Ki fito, direbana yana bakin falon karshe yana jiranki, zai taho da ke filin jirgi. Ba za mu hadu ba sai a jirgi, ina tare da jama'a sosai. Ina rokon kada hakan ya bata ranki, sai kin yi hakuri Amina, yanayin rayuwar tawa kenan. Are you o.k?"
Ta gyada kai kamar yana ganinta.
"I'm o.k, zan fito yanzu".
Da kanta ta turo jakar tata waje, bayan ta nade jikinta cikin wata lallausar laffaya fara mai ratsin shudi mai hasken sararin samaniya. Ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshi. Kamin ta isa downstairs wani ma'aikacin gidan ya zo don fita da jakarta, direban na jiransu ya karbi jakar ya sanya a bayan motar kirar 'porsche' ta shiga suka kama hanya tare da security dinta mace a gidan gaban motar.
A takaice Ma'arouf da Amina, ba su hadu ba sai a first class seats na jirgin Azman mai zuwa Abuja daga Bauchi.
Kar ki so ki tona zuciyar kowannensu a yayin da suka yi arba da juna domin ba za ki iya kididdige adadin farin cikin da ke cikinta ba.A lokacin da Amina ta zauna a kujerar dake daf dataangon nata. Karo na farko a tarihin rayuwarsu da ya kama hannunta ya rike cikin nasa.
Ji tayi tamkar magnet ya manne hanuwan nasu. Kanta ta sunkuyar,ta kasa hada ido da shi, tana mai karbar sababbin sakonnin farin-cikin dake shigowa zuciyarta, ba ta iya ta dube shi ba, amma wata rahma taji ta sauka aruhin ta.
Shi kuwa ajiyar zuciya ya ke saukewa da sauri-da-sauri, cikin ransa yana godiya ga mai tsarkin mulki, da ya nuna masa wannan ranar, wanda ya mallaka masaAminar nan da ya dadeyana so da kauna lokaci mai tsawo ba don isarsa ko mulkinsa ba.
Sun sauka a hotel din TRANSCORP HILTON da misalin karfe takwas na daren ranar. Gajiya ba ta bar Amina ta tsinana komai ba. Ta yi alwala ta yi sallar magriba da isha da ta riske su a hanya, a nan kan sallayar barci mai nauyi ya dauke ta.
Ta bude ido ne ta ganta tsakiyar wani ni'imtaccen gado, rufe ruf da lallausar (duvet).Da ta kara bude idon, ta juya sosai, a can gefe bisa wata yar kujera da dan tebir a gaban kujerar Ma'arouf ne yake cin abinci. Sanye yake da karamar t/shirt deep-bluesamfurin DKNY da bakin dogon wando samfurin Armani. Sosai yayi mata kyau irin na ranar nan data ganshi cikin kananan kaya, yau fiye da waccan ranar saboda harda hasken amarci tareda shi.Yayi wani fresh dashi (wanke hannu ka taba) inji zuciyar Amina. Suka kalli juna na 'yan sakanni tana daga kwance cikin duvet din, kafin ya ture tebir din duka ya taso ya tako har inda ta kekwance, tsayawa yayi akanta ya kama kallonta kamar a lokacin ya taba ganinta, gashin kanta da ya sha gyaran Aunty Jalan ya kwanta akan filon ya baje sai sheki yake, da Amina ta kasa jure kallon sai ta lumshe idanunta, siririyar fatar bakinta ta nuna alamar dan murmushi, hakan ne ya baiwa Maarouf damar sunkuyawa ya sumbaci saman idanun nata dake lumshe, ya tafi da gaggawa ya iso kan karan hancinta, kamin yacigaba da mikawa a urunce ya iso tausasan labbanta, anan ya ja birki yayi mata sumba mai tsayi da zurfi. Amina ta tsinci kanta cikin wata duniya da bata taba tsintar kanta a ciki ba.
Shi da kansa ya tuna Amina babu komai a cikin ta, ya dakata, sannan ya mike tsaye, hannun damansa ya mika mata ta kama cikin jin wata irin kunyarshi da bata taba ji a rayuwarta ba.
Tsaye ya mikar da ita ya shiga warware laffayar jikinta, ya saura doguwar rigar robar data bi fatar jikinta ta kwanta kalar (sky-blue). Gigicewa Maarouf yayi, wata irin gigicewa da bai taba yi akan diya mace ba. Yau ne ya ga zahirin Amina diyar Goggo Hawwa, ashe ba karamar ajiya Ubangiji yayi masa ba wadda bai taba tsammani ba???
Tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci wannan sura!. Ya cigaba da kissing dinta ta koina sannan ya rungumeta tsan-tsan a jikinsa kamar mai tsoron kada wani abu yaratsa ta tsakaninsu.
Sun dauki dogon lokaci a haka cikin sauraron bugun zuciyar junansu, kukan da akuyar cikin Amina ta soma yi ne ya ankarar da shi. Gabadaya ya dauketa bai dire ta koina ba sai a tebirin cin abincin.
A baki Maaroufya ke baiwaAmina abincin wanda a rayuwarta bata taba cin mai dadi da dandanonsa ba, tun tana jin kunya tana sunkuyar da kai har ta ware ta ci sosai, sai mamakin Maarouf takeyi soyayyarshi na kara kama zuciyarta, sai da ta tabbatar masa ta koshi sannan ya kyaleta ta shiga wanka, misalin karfe goma na daren ranar mai dumbin tarihi a garesu.
Ince zan tsaya wassafo muku wannan ranar da alamuran da suka wakana cikinta sai biro na yakare, takarduna su cika taf! Ba tare da na gama ba, idan ya kare yaya zanyi in kawo muku karashen labarin? Dr. Amina Mas'ud Shira,ta kira daren farkon ta da night of AMEENAH! Wato ita Aminar kadai ta san me ke cikin abinta. Abin sirri ne, sirrin ma ba dan kadan ba. Sirrin Maarouf da Amina.
Gane hakan dana yi ne yasa na soma ja da baya a hankali da birona da tarinfull-scaps dina har na fice daga TRANSCORP HILTON (murmushi).

*****












Sun mori (honey moon) na tsayin kwana bakwai yadda ya kamata a wannan hotel wanda babu na biyunshi a Nigeria. Sun kara fahimtar juna, so da kaunar junansu ya kara habaka da shaharar da a da, bai yi ba. Sun dinke zukatan junansu cikin na juna sun zama daya. Kowanne ya shiga tababar yadda zai rayu, rayuwa mai inganci ba tare da dan uwansa ba.
A Transcorp suka ajiye tarihin. A can suka baro shi kamar kar su baro, Ma'arouf Ji-kas ya yarda Allah ya sako Amina cikin rayuwarsa SANADIN tashi Ameenar ne don ta gyara ta, ta maye mashi gurbin Aisha, ta wanzar da farin ciki a rayuwarsa wanda ya rasa tun gushewar Aisha. Ta wanke bakin cikin Laila Ji-kas da yake kwana yana tashi da shi. Ta kawo sauyi mai albarka daga rayuwar kadaicin da ya tsinci kansa a ciki tun bayan rashinAisha. Ita din ALHERI ce, kuma AMANA a gare shi (sunan wasu littattafan Takori).
Isowarsu gida ke da wuya tun kafin su isa dakin barcinsu wani mai share-share ya sanar da Ogan nasa, Anty Laila ta dawo.
Fuskarsa ba

1 / 7