Chapter 3 Reading SANADIN KENAN BOOK 4 BY SUMAYYA TAKORI.txt Arewa Novels

SANADIN KENAN BOOK 4 BY SUMAYYA TAKORI.txt

Author :  Sumayya Abdulkadir Takori Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 20.7K words

tayi tana hailala don ta dauka bacci ne ya dauketa take mafarkin sa, saboda yadda zuciyarta ta dokantu da son ganinsa a lokacin. Shine ya bayyana a mafarkin ta.
bude idonki, ba mafarki kike ba, nima na kasa baccin. Ya russuna daidai kanta ya fada mata cikin kunnuwanta.
Da sauri Amina ta bude ido tana nuna masa Goggo dake sallah. Yayi dariya ya sumbaci bakinta zuwa wuyan ta sannan ya ja kujerar goggon ya zauna. Amina tayi suman zaune tana kallonsa a marairaice alamar rokon kada ya sake. Yace Ok? To ina kayan dadin da kika cin? Ta mike zaune ta dauko masa bokitin data ci ta rage daga kan locker ta mika masa. Ya karba ya bude ya soma ci. Ta sauko daga gadon ta isa ga firji ta bude ta dauko sassanyan zobo da kunun Aya wanda baa bude robar su ba da yake Goggo da sababbin robobi takeyi ta kawo masa. Zuwa dawowar ta mazauninta yaci meat pie ya kai hudu. Da kansa ya bude robar kunun ya soma kwankwada, sanyin kunun da gardinsa da ya ratsa shi ba irin na kowanne ordinary kunun Aya bane, wannan na professional Haj.Hawwa ne.
Daga shi har ita shiru sukayi yana ci yana sha sai da yayi kat! Yayi gyatsa yayi hamdala, da gaske ya azabtu da yunwar ashe. Shi kansa yayi mamakin yadda ya ci snacksdinnan da yawa, kunun Aya roba biyu zobo roba daya.Godiya ga Amina, wadda ta damu da cikin mijinta, wani abu da bai kara samu ba tunda ya rasa Aisha. Ko ya ci ko bai ci ba ba ruwan wani.Daga ido yayi yana kallonta da wata irin siga data sanyata sakin murmushi. Ta russunar da idanun ta.
Amina ta kawar da robobin daidai sanda Goggo ta shafa adduar ta ta juyo don ganin abinda nurse ke yi har yanzu a dakin, sai ta ga angon Amina da Aminarsa, suna hirar da bata san me suke cewa ba. Fuskokinsu dab da na juna, tana kwance a gadon asibiti yana zaune a kujerar mai dubiya. Kallodaya zakayi musu ka fahimci dab suke da su hadiye juna in suna iyawa.
Hajiya Hawwa ta mirgina kai tayi murmushi. Jikin su ne ya basu Goggo ta idar da sallahr ta. Mai yiwuwa tana kallonsu. Sai tsinkayota sukayi a bakin kofa zata fice. Da sauri Maarouf ya ja baya ya ce Goggo, don Allah kuyi hakuri,ta kirawo ni ne inci abinci. Goggo bata juyo ba tace kuma kuyi hakuri, ai da baka kirawo ni ba ka yi jinyar da kanka Yallabai yayi dariya yace don Allah Goggo ki dawo, wallahi na tafi. Bata tanka shi ba ta fice.Shi da Amina suka sa dariya ya bi bayan Goggo ya rufo mata kofar.
Kwanan Goggo uku a asibitin gidan gwamnati tana jinyar Amina, kaida ne Maarouf ya zo duba jikin nata sau uku a rana, da safe kafin ya shiga ofis, da rana in ya dawo da kuma da daddare kafin ya shiga barci, tun Goggo Hauwa na jin kunyar surukin nata har ta sake dashi, ta lura yanada saukin kai matuka kuma bai aje Amina nan kusa a zuciyarsa ba, don haka bata iya jure ganin su tare yana shigowa zasu gaisa ta nemi wurin fakewa don Maarouf ba ya jin kunyar kama Amina a gabanta da nuna mata kulawa mai nuna soyayyar sa gareta ba kadan bace.
Goggo ta kasance koyaushe cikin godewa Allah akan hakan, ta kuma amince wani jinkirin alheri ne, inta tuno yadda ta matsawa Amina akan aure ashe kyakkyawan rabon ta na gaba. Goggo kan daga hannu ta godewa Ubangijin ta.

****
Yana sane ya kashe wayoyinsa tsawon kwana uku don ya san dole za a neme shi kan batun Laila. Ba ya zuwa ko'ina a kwanaki ukun nan, wakilai yake turawa. Daga (office) sai gida manne da Aminarsa. Hajiya da ta gaji da nemansa sai ta kira layin Amina, ta ce ta hada ta da shi.
Ba yadda zai yi don yana zaune a wajen. Ya karbi wayar ya soma gaida Hajiya cikin ladabi, ba ta bari sun gama gaisawar ba ta jefo masa tambayar da take dauke da ita.
"Me ya hada ka da Laila? Ta zo wajena ban barta ta karasa wajen iyayenta ba. Nayi-nayi ta gaya min me ya faru ta ki. Sai kuka ta ke tana fadin in nema mata afuwa a wajenku".
Da ba Hajiya ba ce kashe wayarsa zai yi, amma wannan ita ce mace mai daraja ta farko a gare shi. Ya gaya mata duk abin da ya faru, a yau kuma ya bude baki ya sanar da ita irin zaman da yake yi da ita tun aurensu. Ya ce, saboda rashin kaunarta da tausayinta ga Ameena ya dauko Dr. Amina ya kawo gidan. Don haka ita ce SANADIN aurensa da Amina ko ta ina aka je aka dawo.
Da ta bi yadda yake so su rayu shi da ita da tilon yar sa, shi da ba mai ra'ayin kara aure ba ne. To ta kwashi wasu dabi'u da halaye na kawayen banza da matan bariki ta daura wa kanta. Shi kam, ya gama aurenta zai aiko mata da takardarta don ko ta ce za ta canza ba zai iya adalci tsakaninta da Amina ba, kuma Annabi (S.A.W) ya ce a zauna da daya, in ba za a iya adalci ba. A karshe ya ce,
"Hajiya ki barta ta tafi gidansu, yanzu ne ta san ke mutum ce da za ta amfane ta? Ta taba zuwa har inda ki ke haka siddan ta gaishe ki tunda na aure ta? A matsayin ki na wadda ta haifa mata miji?
Ta taba jin kan abin da na haifa a lokacin da take bukatar Uwa mai tausaya mata? Ta taba nuna min kauna ta hakika ban da ta in na ba ta kudi? Laila ba matar zama ba ce Hajiya, don Allah kada ki takura ni in maido ta ta fita daga raina gaba daya. Ki barta ta je gida don Allah na sake ta saki daya......".
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel... Ma'arouf ni za ka bai wa aiken saki? Ka yi min adalci kenan? In don ta ni ne duk abin da ta yi min na yafe mata, na yi mata uzuri tunda ta yi nadama kuma ta kara jaddada min ba za ta sake duk abin da ba ka so ba, za kuma ta zauna da Amina lafiya.
To na yafe mata duniya da lahira, ko tsoron surutu ba ka yi a ce don ka yi aure ka saki uwargidanka? Ce ne ka maida ita maza-maza tun wani bai ji ba bayan ni".
"Sai ta ji na sake ta Hajiya wallahi sai ta ji, ba ni ita a wayar".
Tunda ya rantse jikin Hajiya ya kara yin la'asar, ba ya rantsuwa koda wasa, tabbas yau an kure hakurinsa, ita kanta ta san halin Laila ba mutuniyar kirki bace, ita ma dattaku ne kawai a matsayinta na uwa gyara ne nata ba bin bayan daya ba. Tunda kuma ya rantse ba za ta so shi da kaffara ba.
Lailan ta kuma sabule mata da a yau ta ji bata kaunar jikarta tilo a duniya;Amina diyar Aisha.Daga bakin da bazai yi mata karya ba. A sanyaye ta mika wa Laila wayar wadda ke zaune gabanta dirshan tana tikar kuka, tana kuma jin duk abinda suke tattaunawa tana mai yarda da kuskurenta.
"Ma'arouf don Allah ka yi hakuri na tuba, na bi Allah na bi ka......"
"Na sake ki saki daya. Kije gida kawai. Allah ya hada kowannenmu da Alherinsa.
Wayyo Allah Maarouf ka yimin rai, ina son ka, ina kake so insa raina.....???
Sai a lokacin ta lura ya dade da kashe wayar hannunsa.
Hajiya ta rasa kuzari, ta kasa yin komai akai, a karshe da Laila ta yi kuka ta gaji ta umarce ta data yi hakuri taje gidan nasu kawai kafin tayi tunanin yadda zata shawo kansa.

****

An sallami Amina ta koma gida amma baa kwance bandejin kanta ba, Amina zata iya rantsuwa cewa ciwon nan a jikin ta yake amma Maarouf ne yake jin zafin sa.
Har dakinta nurse ke zuwa tayi mata dressing din ciwon kullum.
Sai kasancewarsu su kadai cikin makeken gidan mai rassa daban-daban ya zama wata hanya ta kara dankon soyayya da fahintar juna, aminci da kauna mai karfi a tsakaninsu. Amina ya zamanto bata da damuwa, koyaushe idanMaarouf ya shiga office zama take ta kira Goggonta da yan uwanta na gida dana kauye dana Sierraleone su sha hira ko ta tura mota a dauko su su wuni tare, duk wanda ke da nasaba da Amina komai kankantar ta to kuwa yana shan inuwar data ke ciki, wannan a fili yake, hannunta a bude yake kullum cikin bayarwa take da yiwa alummar data shafe ta hanyar cin abinci.
Hatta Yayanta Hafiz kuma tsohon masoyinta Amina tasa Maarouf ya dauke shi daga kamfanin mtn da yake aiki ya maida shi bankin GT. In ma tanada damuwa to na rashin practising aikinta ne.Ta taba yiwa Maarouf zancen tanaso ta koma aiki don bata iya zama waje daya ba ta komai ba, kuma ba ta son tsoma hannunta cikin siyasa.
"Ina matar Jikasda zuwa aiki? Kin taba jin wata matar gwamna na aiki a Nigeria? Ko zan amince da komawarki asibiti sai ranar da bani da nauyin kowa a kaina muka bar wannan gidan na aro muka koma gidana na Fati Mu'azu".
Dole Amina ta hakura ba don ta so ba, ta maida hankali ga bautar aurenta, domin neman dacewa wajen Ubangiji, don a duniya kam ta yarda ta gama dacewa. Alfarmar auren miji na gari irin Ma'arouf Habibu Ji-kas ba karamin dace ba ne. Ta kowanne fanni da diya mace ke buri.
Duk da an ce kowanne dan Adam tara yake bai cika goma ba, a wurinta ita nata mijin ya cika har ya wuce ya isa goma sha tara!!!Matsalarta da Maarouf bazai wuce yawan tafiye-tafiye ba wanda ba yadda zatayi da hakan yanayin rayuwarsa kenan a haka ta ganshi ta aure shi, ba kuma kowacce tafiya ce yake iya yi da ita ba wata tafiyar bata bukatar rakiyar ta.
Kullum Tana kitchen,safe, rana da dare tana girka masa abinda zai ci da hannunta, tafi gamsuwa da hakan, bata ga amfanin ta ba in zata harde kafa a gefe gardi ya shigo ya shiryawa mijinta abin ci ya gama kalle kwalliyar ta ta gefen ido,ta fannin His Excellencyfadar farin cikinsa da hakan bazai misaltu ba. Kullum zaka ganta da littafi da biro tana tsara time-table na abinda zata dafawa maigidan nata, ko ka ganta gaban talbijin tana murdo tasoshin girke-girke na kasashen duniya tana jotting.

*****
Laila ta isa gidansu yamma lis almajiri dauke da katuwar akwatunta, mahaifinta ta fara arba dashi a kofar gida ya shimfida tabarma yana kishingide yana sauraron radio, tun daga nesa ya hango ta tana tafe amma ya sawa ransa ba ita bace mai kama da ita ce, ina Laila ina tafiyar kasa da dirkeken akwati haka kamar mai barin gari?
Bai tabbatar itace ba saida ta tsugunna a gabanshi tana gaishe shi tana share hawaye da gefen gyalenta. Muryarta ba ta fita sosai saboda kukan da ta ci. Dagaci ya ce, Laila ce?
Ta ce cikin dusasshiyar murya, Ni ce Baba.
Ya ce, Lafiya kwaram-kwaram da yammacin nan kamar korarriya?
Da farko Laila ta so ta boye wa mahaifinta gaskiyar cewa, Maarouf ya sake ta, sai kuma ta yi tunanin gara ta gaya masa ko ba komai Maarouf na ganin girmansa idan ya nemi alfarmar ya maida ta dakinta zai yi masa. Don haka ta bude baki ta ce, na dade a garin nan, ina gidan mahaifiyarsa, mun samu sabani ne. Jiya kuma ya sake ni. Amma saki daya ne. Don Allah Baba ka je ka ba shi hakuri.
Dagaci ya gyada kai cikin matsanancin takaici, Ya yi kyau. Na tabbata halin naki na tsiya da ki ke shukawa a gidan da giggiwarki ce ta ishe shi. Ga gidan nan tunda zamansa ki ke shaawa kafada daya da uwarki sai ki shiga ki yi ta zama ki ji in zaman gidan dadi ne.
Amma ni ko sawuna ba zai taka inda Maarouf yake ba balle in wani ba shi hakuri alhalin ban san me ki ka shuka masa ba. Haka siddan yaron nan yaron kirki ba zai sallamo ki ba, da ma ina jin wai-wai a kan wulakancin da ki ke wa yan uwanki saboda Allah ya rufa miki asiri. Duniya ta fi bagaruwa iya jima Laila, ga gidan nan ki zauna haka kawai ba za ki zo ki daga min hankali ba ina zaman-zamana lafiya.
Ya nuna mata hanyar cikin gida, ya ce, Wuce ciki.
Sabon kuka Laila ta sakar wa Babanta, fadi ta ke,
Wallahi ba abin da na yi masa Baba, sabon aure ya yi shi ya sa ya sake ni.
Maigari ya ce, Yanzu na ji magana. Ya yi sabon aure kin yi masa tashin hankali ko? Saboda gidanku ba mata uku ris ki ka tashi ki ka gani ba. To madallah wuce ciki na ce ki gama idda ki auri wanda ba shi da mata. Kada in kifta ido in bude in sake ganinki a wajen nan duka za ki sha wallahi.
Tana kuka ta ja akwatinta mai tayoyi ta shige cikin gidansu kamar ta dora hannu a ka ta zabga ihu.
Matan gidan uku duka suna tsakar gida har mahaifiyarta, kowacce da sabgar da ta ke yi. Mahaifiyarta ce mai girki, don haka talgen tuwo ta ke yi, mai bi mata Larai tana tankaden garin kuka.
Sai amarya Laminde ita kuma tirken awaki ta ke sharewa. Ga kannenta nan matasa da kanana kowa abin da yake yi daban. Jin karar akwatunta duksuka juyo suka dubi hanyar shigowarta.
Babar Laila Inna Saade ta washe baki amma ganin yanayin Lailan sai gabanta ya fadi ta bar abin da ta ke yi ta shige daki, ta fi so ko ma mene ne ta ji shi a daki ita kadai ba gaban wadannan masu son ganin hanjin nata ba.
Kai tsaye kuwa Laila dakin mahaifiyar tata ta wuce. Ta jefar da akwatin gefe ta samu waje ta hada kai da gwiwa ta ci gaba da kuka. Inna Saa ta ce,
Ke lafiya? Mutuwa aka yi?
Laila ba ta amsa ba sai hadiyar zuciya.
Tambayar duniyar nan Innar ta yi Laila ta ki gaya mata komai har ta fusata ta fita ta kyale ta. Kishiyoyin kuwa abin nema ya samu tattaunawa suka shiga yi tsakanin Larai da Laminde.
Wannan akwatin dai ko saki ko yaji. In ji Larai.
Laminde ta ce, Ko kuma an nado mata dankaren duka ba, an koro ta. Ahayye!
Ita dai Inna Saa ba ta tanka musu ba ta wuce murhunta ta ci gaba da tukin tuwonta zuciyarta a jagule.
A daren ranar Laila ba ta runtsa ba sabida cizon sauro, ga Innarta ta hada ta shimfida da kananan yayanta sun jike ta sharkaf da fitsari. Bargon da ta kwanta a kai kuwa jinsa ta ke kamar karzuwa saboda kaushinsa a fatar jikinta.
Wancan zuwan da ta yi da Maarouf ya dage sai ta kwana biyu karbar matar gwamna Inna Saade ta yi mata, gadon audiga ta bar mata ta kwana ita ta kwana a kasa da yake an san bakuntar arziki ta zo. Sai yanzu ta shiga nadamar rashin gyarawa Innarta daki a lokacin da ita ta ke cikin kololuwar daular rayuwa.
Washegari da safe kuwa koko da dumamen tuwo Innar ta dangwara mata a gabanta ko uffan ba ta ce mata ba, cike da haushin ta ki gaya mata abin da ya kawo ta ta barta da kishiyoyi suna yada mata habaici. Shi ma Dagaci bai yi wa kowa zancen Laila ba ya ja bakinsa ya yi shiru, harkokinsa kawai yake yi.
Sai da Laila ta kwana uku a gidansu ganin ba wanda ya zo biko, sannan Maigari ya gaya wa uwarta sakinta aka yi. Hadiyar zuciya ne kawai Inna Saade ba ta yi ba, amma ta fashe da kuka mai karfi wanda ya janyo hankalin abokan zamanta suka zo kofar dakinta suna tambayar ko lafiya?
Ko kula su Inna Saa ba ta yi ba, amma maigidansu ya gaya musu Laila aure ya mutu don shi a wurinsa duk an zama daya. A fili suka jajanta suka wuce dakunansu farin ciki fal zuciyarsu suna labarta wa yayansu har wadanda ke gidan miji sun aika musu.
Yan uwan Laila, Asiya da Sadiya in ban da Allah ya kara ba abin da suke yi, ba za su taba manta wulakancin da ta yi musu da za a yi (swearing in ceremony) na mijinta

3 / 7