Author : Sumayya Abdulkadir Takori Category : New Hausa Novels 2026
ta sauya ba, haka komai nasa bai canza ba. Amma Dr. Amina ta ji faduwar gaba matuka. Sai jin tausasan yatsun Ma'arouf ta yi cikin nata, ya rike ta gam ya ja ta sun fara taka matattakalar (upstairs) tare.
****
LAILAH JI-KAS
Lailah na zaune cikin daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon, ta dora kafa daya kan daya ta harde, ta ci ado da kayan Larabawa na kece raini har ta gaji. Remote din talabijin ne a hannunta tana sauya tasoshi.
Ta dago kai a yangace kamar yadda yake a al'adarta ta dubi masu shigowa ba tareda ta amsa sallamar da suka yi ba.
Sosai ta saki baki tana kallonsu, Ma'arouf ba zai taba kama macen da ba tashi ba. Wannan na nufin...... wannan na nufin....likitar Ameena wannan 'yar rainin hankalin ya aura???
An tabbatar mata Ma'arouf ya yi aure tana Saudiyyah, amma ba ta taba kawo Amina ba ce. Ta dauka iyakarta kenan sun rabu tunda Ameena ta warke. To yaushe aka kulla soyayyar wadda har ta kai ga aure tana gidan bata sani ba??? Ta tambayi kanta, bata kuma samu amsa daga kowanne sashe na zuciyarta ba.
Har suka zauna a kujera guda hannunsu na cikin na juna, Amina dai a tsorace ta ke ganin kallon kura ta ga nama da Laila ke mata. ta kawo karfin zuciya ta sanya wa ranta, tana murmushi, ta ce,
"Anty Laila, ina wuni? An dawo lafiya?"
Shiru ta yi mata ba ta amsa ba, har yanzu ba ta dauke ido a kansu ba, irin kallon nan na kun ci AMANATA.
"Wuce dakinki Amina ki huta, zan yi magana da ita".
Amina ta mike ta nufi dakin nata. Ba ta kai ga isa ba ta ji an shako ta ta baya, an yi mata wani wawan naushi a wuya, an maka mata wani irin abu a tsakar kanta da ya fi kama da kofin gilashi. Fasashshiyar Kwalba! Ta yi gaba luuu! Ta fadi a kofar dakin nata, tana jin sanda Ma'arouf ya yi magana da karfin gaske da iyakacin sautinsa,
"Lailaaa! Kina hauka ne? Kisa? Wallahi in ta mutu a bakin aurenki!".
Ya yi kokarin buga waya don kiran likita, amma ya kasa. Ya kuma kasa isa ga Aminan ya bata wani taimako saboda gigicewa. Hannunsa sai rawa yake yi, haka ilahirin jikinsa, wayar na subucewa yana sake dauko ta. Ita kanta Laila ta dan tsorata da ganin yawan jinin Amina da ke malala a kasa daga tsakiyar kanta, sai mazari ta ke yiamma ta maze, yadda take jin zuciyarta zata iya kashe Aminan kamar yadda ya fada in yaso itama a kasheta.
Ya samu ya lalubo lambar Dr. Isma'el (personal doctor) dinsa,jikinsa na cigaba da mazaridon kuwa Laila ta shammace shi, sanda tayi wuf ta mike bai ankara ba balle isar ta ga Amina kamar walkiya.
".....Ka zo maza-maza har upstairs Isma'el.......".
Babu tambayar ba'asi Dr. Isma'el ya amsa da; "Ga ni nanzuwa ranka ya dade".
Ya isa inda Amina take a kwance a kofar dakinta magashiyyan ya ciccibe ta ya kwantar a doguwar kujerar falon, bai damu da jinin da ya bi ya bata masa jiki ba. Ya soma yi mata firfitababu alamun numfashi a tare da ita. Bai kara bi ta kan Laila ba wadda ke tsaye a kansa tana kuka. Kukan da bai san maanar sa ba.
"Allah ya sa ban yi kisa ba zuciya ce, na shiga uku Ma'arouf ka yafe ni...".
Abinda take fadi kenan cikin rishin kuka.
Ko kallonta bai yi ba, firfita kawai yake wa Amina da gefen babban rigarsa idanunsa sun kada sun yi jazur. Abubuwa da yawa yake kissimawa a ransa da zasu faru da shi idan ya rasa Amina. A haka likitan ya iske su, bayan Ma'arouf ya ba da umarnin a shigo da shi.
Da kayan aikinsa yake tafe don haka a take ya fara bai wa Amina taimakon gaggawa, har ta farfado. Ya cire kwalbar data nitse cikin kanta yayi dressing din wajen da ke fidda jinin, ya tsayar da gudunsa ya rufe da plasta. Ya dubi Ma'arouf da Laila mai kuka kashirban, Ma'arouf din ya ki ko kallonta hankalinsa da kulawarsa duk suna kan Ismael dake aiki kan Amina wadda ke kwance ido rufe. Nan ya gano bakin zaren, ya dubi Ma'arouf ya ce,
"Garin yaya? Yaya haka your Excellency? Wane ne da wannan danyen aikin? Wannan kan dole sai an je asibiti an yi hotonsa don mai yiwuwa akwai (Internal injury) na kwalbar, da nake addu'ar Allah ya sa bai taba kwakwalwarta ba".
Laila ta kara gigicewa, daidai da karuwar fushin Ma'arouf a kanta, ya ce da Doctor din,
"Je ka ka zo da (nurses) ku tafi da ita a ba ta duk kulawar da ta dace".
Cikin dan lokaci Dr. Isma'el ya yi waya asibitin cikin gidan, nurses biyu suka zo suka tafi da Amina. Aka barshi daga shi sai Laila a falon. Ya zauna cikin kujera ya tallabi fuskarsa da hannu bibbiyu cikin damuwa. Laila ta tsugunna a gabansa, ta kama kafafunsa tana kuka.
"Tunda ba ta mutu ba, don Allah kar ka sake ni, wallahi zuciya ce na tuba, zan zauna lafiya da ita insha Allahu".
Janye kafafunsa yayi, daga rikon da ta yi musu. Bai saki fuskarsa ba har yanzu, haka fushinsa bai sauka ba. Da kyar ya yi mata magana cikin muryar bada umarni,
"Hada kayanki Akilu ya kai ki gida Ji-kas sai na neme ki".
Laila ta rushe da kuka, "Na roke ka da Allah da manzonSa ka bar ni a dakina, in dai Amina ce na yi maka alkawarin za mu zauna lafiya".
Zuciyarsa ta so ta fara sanyi, sabida irin kukan da ta ke yi mai nuna nadamarta a fili. Amma ya yi rantsuwa cikin zuciyarsa sai ta je gida ko da bai sake ta ba.
"Hakuri na daya ne Laila, ki je gida sai na neme ki, amma ban sake ki ba, in kuma ki ka kara yi min musuraina zai kara baci, shiga ki tattaro kayanki".
Ba yadda ta iya, ta juya ta yi dakin nata tana share hawaye. Hankalinta a matukar tashe. Shi kuma ya kira Akilu a waya,
"Zo maza, za ka kai matar gidan nan Ji-kas".
Ta gabansa Laila ta wuce tanna jan akwatinta, ta yi lullubi da wadataccen mayafi, wanda a da ba ta amfani da irin shi sai raka-ni-gantali. Ta dube shi cikin ido da idanun neman afuwa, ya kauda kai don ba ya son ya ba wa tausayin da ke son rinjayar fushinsa dama ya yi tasiri.
Wannan karon ya yi aniyar daidaita mata sahu in har tana son ci gaba da zama da shi, to dole ta bar duk abin da ba ya so ta kuma zauna lafiya da zabin ransa. Ba ita dake cin alfarmar zabin iyaye ba.
Zaman hakurin da yake yi da ita inda tana da hankali adalci ne ya yi mata. Yaushe ta fara sonshi so na gaskiya da har ta san ta yi kishi a kansa? Kishin ma na jahilai da rashin imani.
Bayan tafiyarta ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai safah da marwah yake yi, yana son jin halin da Amina ke ciki wayar Dr. Isma'el na kashe alamar yana bakin aiki. Shi ba abun ya fita da kansa ya je asibitin ba.
Ya daure ya shiga (master-bedroom) dinsa ya yi wanka da alwala, ya yi sallah nafila ya roki Allah matsalar Amina ta zo da sauki.
Yana kan sallayar bai sauka ba bayan awa daya, sai ga kiran Dr. Isma'el. Da mugun sauri ya amsa wayar.
"Ya ya Isma'eel, is she o.k?"
"Eh, toh, shes conscious now,amma mun samuinternal injury, bayan na wajen, dole zaayi (minor-surgery) akwai bukatar ka sanya hannu, zan kawo maka takardun yanzu kayi signing.
Amma ranka ya dade ya kamata a dinga kula a kuma dinga tsawatarwa iyali idan sun aikata ba daidai ba irin wannan, this issheer rudeness,don dai matsalar ta cikin gida ce, amma da ba za mu barta ta tsaya a haka ba".
"Kada ka damu Isma'el, it's o.k, za a kiyaye zaa dau mataki. Yanzu ina Aminan? Ya ya yanayin jikin nata?"
"Alhamdulillahi ta farfado, amma za mu rike ta har muyi aikin ya warke, bari in kawo takardun maza".
Har Dr. Ismael ya iso gumi kawai yakeyi a zaune. Bai san yana son Amina har haka ba sai yanzu da take cikin wani hali da yake ji da zai yiwu da ya maido da ciwon jikinsa. Laila zata dandana kudarta yadda gobe ko da kyauta aka ce ta kwatanta rashin hankali irin wannan cikin gidannan bazata soma ba.
Ya yiwa Ismael umarnin shigowa, ya kawo takardun har inda yake cikin girmamawa, ya karba ya rattaba hannu. Mintuna talatin suka dauka suna zare kwalbar data nitse cikin kan Amina amma alhamdulillahi bai tabi kwakwalwar ta ba.
Karfe takwas na dare sukayi waya da Ismael ya tabbatar masa zai iya zuwa ya ganta yanzu. Asibitin nan cikin gidan gwamnati yake don haka akwai tsaro sosai.
Amina na kwance lamoo!A gado, bayanta jingine da filo, ta sha katuwar plasta a ka. Maarouf ya murdo kofar ya shigo, idanunsu suka sarke dana juna, sun dauki lokaci suna kallon juna kafin hawaye ya cicciko idon Ameena. Ya karasa jikin gadon ya kama hannun ta ya ja farar kujera ya zauna a saitin kanta.
Zaiyi magana ta kai tafin hannunta ta rufe masa baki ta san hakuri ne zai bata akan laifin da ba nasa ba.
Don Allah kada ka sake ta na ji sauki wallahi na ji sauki. Kaima ka yi laifi da tuntuni baka fada mata ba, da bazata dauki alamarin da zafi haka ba.
Ido ya zuba mata ya kasa cewa komai, wace irin mutum ce Amina?Wace irin kyakkyawar zuciya gareta? Yake tambayar kansa.
Me kike so yanzu? Me zaki iya ci? Ya kawar da maganar data yi masa don bashi da amsar da zai bata, babu bayanin da zai yi mata ta fahimci irin zaman auren da yake yi da Laila Jikas wanda babu emotion ko affection a cikin sa da har zaa zauna ana tattauna muhimman alamura da suka shafi rayuwar juna, zaman auren kawai akeyi don ya zama dole.
Amma yau an zo wani limit da yake jin wannan mugun zaman ya kare, babu wanda ya isa ya tankwara zuciyarsa ta sake zama da Laila har ita Aminar kuwa. Bashi da sauran abin nema a wata diya mace, duk abinda ya rasa a Aisha ya sameshi a tareda Amina har ma fiye da ita, ko baayi haka ba ya yanke shawarar kawo karshen zaman nasu don yiwa kansa da ita kanta adalci, yana tsoron kada ya tashi ranar Alqiyama da shanyayyen barin jiki. Zai bi hadisin Manzo (SAW) wanda yace;
Ku auri abinda yayi muku dadi daga mataye daga dai-dai har hurhudu, idan kunji tsoron bazaku iya adalci ba to ku zauna da daya. (Bukhari).
Ba abinda nake so, Goggo kawai nake so a dauko min don Allah!
Ya dan fiddo ido damuwarsa ta karu kina so a tayar mata da hankali Amina? Ba kankanin abu ke tada hankalin Goggo ba, tanada juriya,idan bata zo ba bazan iya cin komai ba.
Bai yi musu ba wannan karon, ya fiddo waya yana magana da daya daga cikin direbobinsa tunda Akilu ya tafi da Laila Ji-kas.
Amina na ganin Goggo ta shigo sai kuka, Maarouf yayi kasa da kai ya russuna ya gaida Goggon ya fita, zuciyarsa cike da damuwa, kukan Amina na tada tsigogin jikinsa.Ga nauyin Hajiya Hawwa da yazo ya baibayeshi, ace matarsa ce ta aikata wannan taaddancin yana zaune ma ai sai aga sakacinsa. Ba kuma yadda zaiyi ya hana Amina fadawa Goggonta tunda ta riga tazo.
Cikin nutsuwa Hajiya Hawwa ta zauna a kujerar da Maarouf ya tashi, ko hankalinta ya tashi babu alamun hakan akan kamilalliyar fuskarta. Ta kai hannu ta dafa kafadun Amina don an nade kan da bandeji.
Yi hakuri daina kukan ki gayamin me ya faru daku? Kunyi hatsari ne a hanyar Abujan? Amina ta girgiza kai Goggo ai na gaya miki, Anty Laila ce, kofin gilashi ta kwantsa mini aka. Goggo ta girgiza kai babu mummunan rauni to? Akwai Goggo amma an cire kiyi hakuri, nasan zai dauki mataki Hajiyarsa ma haka, Allah ya kiyaye gaba Allah ya baki lafiya. Tun yaushe rabon ki da abinci? Wallahi Goggo tun a Abuja don a jirgi ma ban ci komai ba. Ni sai da na ganki ma na ji yunwa.
Goggo tayi murmushi bansan yaushe zaki girma ba Amina, me kikeso ki ci? meat-pie da cakezobo da kunun ayarki murmushi Goggo ta sake yi ta ciro wayarta daga purse din hannunta ta kira Ilya ta gaya masa Amina na asibiti wai zata ci meatpie da cake, zobo da kunun Ayansu, ya jajanta ya kuma tabbatarwa Goggo yanzu zai kawo dama yana cikin gari.
Cikin dan lokaci Ilya ya kawo cikin bokiti, Amina ta shiga ci hannu baka hannu kwarya.
Ya tambayi Goggo abinda ya faru ta sanar dashi. Ilya ya shiga tsokanarta“raguwa kawai, mai tsoron kishiya don me baki bude kwanji kin rama ba? Amina bata kula shi ba, a ranta fadi take baka san Anty Lailah ba, (shes super warrrior) labarinta kake ji ina ni ina gwada yar kashi da ita ta karairayani a banza! Sai da ta koshi ta rufe ragowar tace.
Goggo na ragewa Baban Ameena wannan, nasan shima tunda muka dawo bai ci komai ba, baki ga yadda yake cikin damuwa ba har ya fini damuwa”.Goggo tace to Amina! Ilya ya kama haba yana kallonta bakinsa fal magana amma bai furta ba, sai taji kunya ta rufe fuska tana dariya. Goggo tace ah toh mutum yayi rashin kunyarsa ya nade kayarsa shikadai ba! Ilya yace wallahi kuwa Goggo, oh! Su Ameena dadi miji ta galla masa harara.
A daren Maarouf na shirin kwanciya, hankalinsa ya kwanta ganin Amina ta samu sauki kiran wayarta ya shigo. Ya mika hannu ya dauko wayar daga inda take ajiye gefen gadon sa ya manna a kunnensa ya makale da kafadar sa yana kakkabe shimfidar gadon da dukkan hannayensa biyu zai kwanta.
Yaya akayi my patient? Bakiyi bacci ba har yanzu? Nayi zaton tun dazu kinyi bacci a cinyar goggo kina bukatar hutu. Amina tace ni bana kan cinyarta, gata can ma a gefe sallah take yi. Yaya zan iya runtsawa alhalin nasan baka ci komai ba? murmushi yayi, zuciyarsa na yi masa wani irin dadi tunda kin samu sauki sai naji na koshi, babu yunwa a tare da ni Amina gashi ni kuma bazan iya bacci ba baka ci komai ba wallahi mai dafa min abincin ya kwanta already, bazan iya kiransa yanzu ba, amma nayi miki alkawarin zan sha tea inada kettle da lipton da Zuma a dakina bana shan sukari. Na rage maka abinda naci, zaka iya cin cimar gidanmu? murmushin sa ya fadada why not? Zobo, Cake, da meat pie din Goggo ko? tayi smiling tareda kara manne wayar a kunnenta ta lumshe idanunta. Yadda suke maganar goggo dake gefe bisa sallaya bata jin su. A ina ka sani? Wa ya gaya maka? Ya kada kafada kamar tana ganinsa ina ruwanki? Babanki Turaki bai hana ki bin kwakkwafi ba? Ta zarce da murmushin zuwa dariya kamar inyi tsuntsuwa ta sama inzo in ganka.
Maarouf yaji zuciyarsa ta dauke shi ta cilla shi wata hamada mai cike da koramu na madara da Zuma sabida jin dadin kalaman Amina. Sai ji tayi ya kashe wayarsa.
Ta ciro wayar daga kunnenta ta duba sosai, ya kashe. Ta shiga mamakin me yasa ya kashe toh? Ko kalaman data fada ne suka bata masa rai? To amma me tace na bacin rai din? Ta daga ido ta dubi agogon dakin karfe goma sha biyu na dare. Idanunta suka soye ta kasa bacci sai kissime-kissime take yi a ranta na abinda ya sanya rabin ranta kashe mata waya.
Ji tayi ana knocking kofarsu, lokacin goggo tayi sujjadah, ta dauka nurses ne don haka daga kwancen tace Yes!.
Ya bayyana a dakin mutum biyu da suka rako shi suka tsaya daga waje, wanda bata taba kawowa ranta gani a lokacin bane, Maarouf Ji-kas ne.
Cikin matsanancin mamaki da alajabi, so, kauna, da bayyanannen farin ciki take kallon sa. Ya daga mata gira ya karaso gaban gadon nata ya mika mata hannu. Gani, bani abincin.
Shudin wandon jeans da farar shirt mai rubutun marks&spencer ne a jikinsa. Sassanyan kamshinturaren (givenchy) ya bakunci hancinta. Rufe ido