Author : Sumayya Abdulkadir Takori Category : New Hausa Novels 2026
ba, suka ce za su zo ta ce ba ta gayyatar gayyar naayya.
Wani cikin gidansu bai taba taka muhallin da ta ke ba, hatta uwar da ta haife ta, to juyayin me za su taya ta don yau ta ga juyin rayuwa? Da ma an ce ka taka duniya a sannu domin ba matabbaciya ba ce.
Kwanan Laila biyar a gidansu ko kofar dakinsu ba ta iya fitowa saboda habaicin su Laminde da dariyar ketar kannenta da yayyenta maza. Kuka ta yi shi har ta gode Allah, nadama kuwa ba irin wadda ba ta yi ba.
Ranar da ta cika kwana bakwai Inna Saade ta soma tila mata wanke-wanke da wankin kayan fitsarin kannenta da girkin gida in ya zagayo kanta, ta ce ba zai yiwu kina kwance a daki ina dafo abinci ina kawo miki alhalin kin fi ni karfi ba.
Ai shi zaman gida cudarni in cude ka ne ba irin gidan miji ba, shi ya sa ki ka ga ko mu da muke kauye lallaba aurenmu muke balle mai auren gwamna ta ce sai abin da ta ke so za ta yi?
Haka Laila ta ci gaba da rayuwa a gidansu cikin wani hali na tagayyara da fita hayyaci. Gaba daya ta zuge ta fita hayyacinta, fatar jikinta ta canza kala hatta gashin kanta ya san uwar dakinsa ta samu gigitaccen sauyin rayuwa na farat daya.
Ba irin kiran da ba ta yi wa Maarouf a waya, ba ya dauka sai ta koma yi masa sako (text) ko karantawa ba ya yi yake gogewa. Ga lokaci na tafiya tsoronta Allah tsoronta lokacin cikar iddarta.
Babban abin da ya kada ta hatta Hajiya Saude ba ta kara waiwayarta ba, kuma tana da labarin ya zo Ji-Kas har sau biyu a bakin kaninta mai bi mata. Haka Laila ta rungumi kaddara ta maida alamarinta ga Allah.
Kullum ta yi sallah sai ta roki Allah ya juyo mata da hankalin Maarouf, in hakan ba za ta yiwu ba tana rokon sa ya fiddo mata wani mijin cikin gaggawa mafi alkhairi a gare ta, ta yi aure ta huta da masifar gidan ubanta.
*****
A wannan satin Ameena karama ta zo hutun (third-term) daga makarantar da Babanta ya kai ta a Lagos. Ta tadda Antinta a upstairs’ tare da Babanta a gida daya kuma daki daya. Ta kuwa hau murna ba yar kadan ba. Kullum tana manne da Antin nata ko tsakiyar iyayen nata biyu tana sakin hira. Farin ciki ya cika ta ta rasa inda za ta sanya kanta don farin ciki.
Amina ta roki Maarouf da ya shirya musu zuwa Ji-Kas ita da Little za su je su yi wa Hajiya kwana uku.
Ya ce, Ni kuma fa? Haka za ku bar ni ni daya kamar maye Amina da Amina?
Kwana uku kamar kiftawar ido ne Your Excellency, na kwana biyu ban ga Hajiya ba, Ameena ma tana ta zancenta. Nayi-nayi ka dawo da Anty Laila ai ka ki saboda irin haka, mai mata daya fa aka ce aminin gwauro ne.
Nan da nan ya yi fuska, Kin jawo wa kanki fasa zuwa Ji-kas din, na kuma gane ba kya kishina ko kadan Amina. Ai sai ki dawo da Lailar tunda igiyar aurenta ai tana hannunki.
Na tuba, na bi Allah na bi ka, ba nufina kenan ba. Kawai na ga ya kamata zuwa yanzu a ce ka huce daga fushin da ka ke yi da ita, amma tunda hakan shi ne decision dinka ba ni da say Baban Ameena.
Da kyar ta shawo kansa ya sauko daga fushin nasa. Wannan ta sha faruwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba tun barin Laila gidan da dawowar Amina daga jinya a asibitin da Laila ta yi mata sanadin minor-surgery a cikin kai.
Idan Maarouf ya ce ba ta kishinsa a kan Laila hankalinta yana tashi. Domin da bacin rai yake fada, ko uwar da ta haife shi tunda ya nuna mata ba ya son zancen komen Laila ta daina yi masa sai ita?
A nata bangaren Amina ba rashin kishi ba ne, ba dai ta son zama kwarkwata fidda mai giji, ba ta so a ce a kanta wani ya shiga wani hali ko kankani, zuciyarta mai kyau ce maabociyar imani, idan akwai abin da ta ke kishi a duniya, to Maarouf Ji-Kas ne!Kishi kuwa wanda ko a tarihi babu irinsa. Amma na musulunci.
Ta kudire a zuciyarta ba za ta kyale shi ba, in dai ta samu faraga ta ganinshi cikin nishadi za ta ambato neman alfarmarta na a mayar da Laila ba don halinta ba. Tunda Annabi mai tsira da aminci ya ce, Imanin dayanku ba ya cika har sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa.
Tana so wa kanta Maarouf tana so wa kanta rayuwa da shi. Ta tsaya ma tana cewa tana sonshi bata baki ne, don haka tana kishin abinta. Sai dai ba za ta bari kishin ya dakusar da kaifin imaninta ba.
****
Sun isa Ji-kas lafiya ana kiraye-kirayen sallar magriba. Hajiya tana alwala sai ji ta yi Little ta dafe ta ta baya. Ta ce, Ho! yar nema, ni kada ki karasa ni.
Little Ameena na dariya ta ce da karfi, Hajiyan Ji-kas!.
Ta ce, Ni Saudatu sunana, ubanki ne Ji-Kas!
Amina da kishiyar Hajiyan suka yi dariya, Hajiya da jikanyarta kullum suka hadu sai sun ba da dariya.
Amina ta nemi buta ita ma ta yi alwala suka bi jamin sallar magariba daga masallaci. Hajiya ta rasa ina ta-ka-sa-ka, ina ta-ka-a-je da surukarta, inda duk ta mika hannu kwano ta ke janyowa cike da abincin da makota ke kawo mata da wanda mai aikinta ta dafa mata, fadi ta ke,
Zabi wanda za ki ci Dr. Amina, kin san nan kauye ne ba ma cin cima kala daya. Zabi duk wanda ki ke so.
Amina ta yi murmushi ta zabi burabuskon gero da miyar taushe wanda aka dafa wa Hajiya. Hira suke sosai kamar uwa da yarta yawanci duk a kan abin da ya shafi Maarouf ne da siyasarshi.
Ana haka Amina ta sako zancen Laila, Hajiya ba za ki roki Baban Ameena ya maida Anty Laila ba? Saura kadan fa ta kare iddarta. Bana so su rabu kwata-kwata a dalilina.
Hajiya ta girgiza kai,
Ko kusa, kada ki kara sanya wa ranki da ke cikin dalilan rabuwarsu. An samu sabanin halayya tsakanin Maarouf da Laila, mun ganganda (rushing) wajen tabbatar da aure a tsakaninsu ba tare da binciken halayya ba, inda za ki san ba ke ce sanadi ba hatta iyayenta da yan uwanta ba sa jin dadinta, sanda tana gidan yaron nan. Sawun barawo naki alamarin ya taka don haka ki daina damun kanki.
Zan tsaya kan ya maida ta din amma ba yanzu ba, sai ta kara tarbiyyantuwa. Don labari yana zuwar min kala-kala tana can nadamar rayuwa ta ishe ta duk surfen gidansu da sanwar gidansu ita ta ke yinta, kin ga ko ai Laila in mai hankali ce dole ta shiga karatun ta-nutsu.
Amina ta langabar da kai, Ni tsorona Hajiya kada iddar ta kare wani ya fito ya aure ta.
Hajiya ta ce, To ba shi kenan ba?Allah ya hada kowa da rabonsa. Ni yanzu na daina gaggawa a kan aure Aminatu.
Dole Amina ta yi shiru don ta fahimci daga Hajiyar har danta sun hau doki guda, ba za ta iya sauko da su ba, sai ranar da Allah ya nufa.
Da za su kwanta ta canza zuwa kayan barci masu kauri ta daura zanin atamfa a kai, ta kakkabe wa Hajiya gado, kayan da ta tara tsibi guda ba ninki bayan ba masu dauda ba ne, ta ninke mata su ta shirya mata a sif, lungu da saqo na dakin Amina ta bi ta kakkale shi tana mamakin wace irin mai aiki ce Tambai da a kicin da dahuwar abinci kawai ta ke aiki?
To daga ita har Hajiyar sun kwana biyu ba za su iya wannan (neatness) din ba. Ta sawa ranta alkawarin zuwa Ji-Kas akai-akai da kula da Hajiya kamar yadda za ta kula da Goggo, ta wanke mata bayi kal sai sheki da tashin kamshi yake kamar ba bayan gida ba.
Ta kuma koya wa Tambai yadda ake wankin bayi na zamani ta gane sosai. Hajiyar sai albarka ta ke sanya mata har suka kwanta barci.
Washegari ita ta yi wa Hajiya girkin rana da na dare. Har zuwa ranar da za su taho ita ke yi wa Hajiya girki da shara da gyaran bangarenta.
Babu abinda Maarouf bai sanya mata ba na saukaka rayuwa, amma ba sa samun kulawa yadda ya kamata sakamakon Tambai din ta kwana biyu, kuma girman kauye ce.
A kwana ukku da Amina ta yi Hajiya Saude gani ta yi sassanta ya dawo sabo kal. Ta yi kewar su ba kadan ba bayan komawarsu Bauchi. Kowa na gidan ya yi kewar Amina don mutum ce mai saukin kai da dadin muamala duk yayan Baba Liman sun saba da ita.
****
WATA SABUWA
Bayan Little ta koma makaranta da sati biyu aka bugowa Babanta waya daga ofishin shugabar makarantarsu cewa ba ta da lafiya. A take ya tsallake abin da ke gabansa ya shirya musu tafiya Lagos shi da Amina. A Clinic din makarantar suka riske ta a kwance ana kula da ita. Ya karasa jikin gadon jikin sa na kyarma ya dafa kanta ya tambaye ta me ke damunta?
Cikin sassanyar muryarta take masa bayani.
Daddy watarana in na zauna ba na iya tashi tsaye sai an daga ni.
Hankalin Amina da na Maarouf ya yi mummunan tashi.
Ameena little ta cigaba da cewa,
Cikin kashin kafata in na tsugunna sai in ji kamar zai tsage, sannan kafafuna suna karkarwa in na dade a tsaye.
A take Amina ta janyo ta ta soma dudduba ta, to babu kayan aiki a tare da ita, don haka ta nemi izinin Maarouf na son yin magana da Dr. Turaki.
Shi ya kira shi da kansa ya hada su. Amina ta gaya masa matsalar da ta biyo bayan warkewar Ameena. Suka yi magana irin tasu ta likitoci. Ta mika wa Maarouf wayar ya ce da shi su zo da ita asibiti a duba ta sosai. Makaranta ta ba da izni suka taho da Ameena Bauchi.
To a binciken su shi da Amina da sauran likitocin bangaren su na ATBU Teaching Hospital sun gano matsala babba a tare da Ameena. Sun gano cewa kashin kafarta na hagu bai gama yin kwari ba, yana bukatar wani irin gashin wanda ba su da injin yinsa sai a waje.
Dr. Usman ya ce ya san wani asibitin da suke irin wannan aikin a Vienna (Austria) wadanda sukawarkar da EFCC Lamido Nasir (Babban Goro) da kuma wani a Jeddah (Saudi-Arabia).
Maarouf ya zabi na Jeddah, ko ba komai bai karya (patriotism) dinsa na yin alaka da kasashen Turai ba. Ya soma yi musu shirin tafiya Jidda shi da Amina da Ameena.
Ranar wata asabar jirgin KLM ya daga dasu zuwa Saudi-Arabia. Madinatul-Munawwara suka wuce kai tsaye don fara yin umrah musamman akan Allah ya basu saar abin da suka zo nema, daga Madina suka wuto Makkah suka yi cikakkiyar umrah, duk adduoinsu a kan lafiyar Ameena ne na neman nasara a kan aikin da za a yi mata.
Sannan suka isa asibitin da suka zo a Jeddah (Solayman Faqeeh) aka fara yi wa Ameena(Radiotherapy)na musamman. Amina ta ja gefe tana kuka fuskarta cikin mayafinta kawai saboda tausayin Ameena. Yarinya karama tana shan azabar da bata misaltuwa a yan kananan shekarunta da basu kai goma ba.
A duk lokacin da ta ga ana yi wa Little therapy din nan ba ta iya daurewa sai ta yi hawaye kamar ba likita ba. A karan-kanta yanzu in zaa bata trillion ba abinda zata iya kara iya yiwa Ameena. Ba don komai ba sai don tausayi da sarewa. Daga ita har ubanta tausayinsu take ji har batasan wa tafi tausayi ba tsakanin yar da ubanta. Amina keda ciwon a jikinta amma zata iya rantsuwa Maarouf zai fi so a dawo da ciwon jikinsa in har zata samu lafiya. Tana ganin yadda baya iya barci tun saukar su a Saudi.
A makkah da madinah a masallaci yake kwana. Anan jeddah kuwa bisa dardumarsa. Da gaske Allah ba ya hada maka komai a rayuwa, in ya baka wannan sai ya jarrabeka da wancan, shi kuma Maarouf Ji-kas ga ta inda allah yake jarrabarsa (ciwon Da).
Ganin halin da take kasancewa in sunzo asibitin tare sai Maarouf ya daina zuwa asibitin da ita, ya gwammace ya zo shi da wadanda suka rako su (securities) dinsa. A hotel din da suka sauka (Aljamjoum) yake baro ta ya zo asibitin da masu tsaron lafiyarsa.
Ba su fara samun nutsuwa ba sai da manyan likitocin na asibitin (Doctoor Solayman Faqeeh) suka tabbatar musu kafafun Ameena sun samu waraka cikin yardar Ubangiji, amma zai iya yiwuwa wani lokacin ta yi fama da dan ciwon kafa kadan-kadan, da zarar ta yi complain din hakan sun rubuta magungunan da za’a bata ta dinga sha a take ciwon zai daina.
Sai a lokacin ne Maarouf da Amina suka samu lokacin junansu, aka biya bashin soyayyar da aka ci kwana da kwanaki wanda tashin hankalin ciwon Amina ya mantar dasu.
Sun yi honey-moonmai tsayawa a zucci fiye da na farkon aurensu a Transcorp. Wata guda da rabi suka kwashe a Saudi-Arabia sannan suka tattaro suka dawo gida Nigeria.
Daga airport kai tsaye direban da ya kwaso su Ji-kas ya wuce da su. Maarouf bai kwana ba ya koma Bauchi su kuwa suna tare da Hajiya har tsayin kwana uku. A nan ne Amina ke yi mata bayanin matsalar da ta fidda su Jeddah. Hajiya Saude ta ce, Kai! Wato dan Adam har ya mutu ba zai huta da kaddarorinsa ba, Allah ka kara mana lafiya bakidaya, Allah ya kara miki lafiya mai dorewa Amina.
Da suka koma Bauchi da wata daya aka mayar da Ameena makaranta bayan ta kara samun kyakkyawar kulawa a hannun Antynta.
****
Watarana Amina na gyaran tsofaffin takardun ta na makarantar sakandire wani karamin littafi ya fado, ta dauka ta goge shi tana dubawa, a ciki ta ga lambar waya a kasa an rubuta Hafsa Datti. A take ta tuno kawarta ta makaranta Hafsa. Murmushi tayi tareda yin hamdala ta roki Allah ya sa ta samu Hafsa a wannan lambar wayar, bazata taba mancewa da Hafsa ba, ta dade tana fado mata a rai batasan ya zatayi ta riske ta ba, abinda ta sani kawai shine a Abuja take. Da gudu ta dauko wayarta ta shigar da lambobin.
Sai da ta gama abincin ranan His Excellency ta shirya komai a inda yake cin abincin tayi wanka ta kintsa a lokacin bai dawo daga office ba ta harde a hakimar kujerar falon ta ta soma kiran lambar.
Kira na daya, na biyu ta ji lambar ta shiga, ta fara ruri. Addua kawai take Allah ya hada ta da Hafsa Datti a wannan gabar na rayuwarta. Wata mutum daya cikin masoyan ta na hakika da bazata manta gudummuwar da suka bata a rayuwarta ba. Sannan tana bukatar aboki bayan yan uwa da dangi, aboki saanta wanda zata ke tattauna wasu alamuran dashi bayan Goggo.
Assalamu Alaykum.
Taji muryar wata kamilalliyar dattijuwa ta amsa.
Amin waalaikumus-salam . Ina yi ni?
lafiya lau yammata, daga ina? Ban dau muryar ba kuma bansan lambar ba.
Sunana Amina Masud, daga Bauchi nake magana, ni kawar Hafsa ce da mukayi makarantar sakandire tare. Don Allah ko zan iya samun magana da ita?
Allah sarki, Amina ke ce! Yau Allah ya hada Hafsa da Aminar ta. Kullum tana zancen ki, tana rokon Alla ya sada ku watarana kun rabu ba tareda karbar adireshin juna