iznah Book Complete Hausa Novels By Mamughe.txt

Author :  Mamuhagge Category :  True Books

Chapter   10 / 19

27K to 30K   out of 54.8K words

ciki da Mamakin ganinsu suka tarbesu jafar ya kar6i abdulshakur dake hannunta daqyar ya yarda yaje gurin jafar din.

Abune ya fiddo da kayansu suka kwasa suka shiga ciki...

Cikeda farin ciki baffa ya tarbesu Dan kuwa duniya Yana tsananin qaunar 'yar uwarsa da ananonsa..

Nan da Nan suka baje a tsakar gidan Inna tafara kawo musu abinci da fura bayan hamma Yusuf yakaiwa Abu
Yana gamawa yakama hanya ya juya.

Cikin farin ciki baffa yakalli abdulshakur dake Kan cinyar Anano Yana cin dambun gyada yace,

Jafar kaga 'danku ya girma yayi wayo ko?
Cikin farin ciki yace,

Baffa ai saima ya girma yaxama soja tukuna...

Cikin farin ciki gwaggo tace,

Kamar kuwa kasan auren soja zasuyi Dan zancen nema yakawo mu Anano dai tasami miji babban mutum kuwa kuma soja ko acikin sojoji...

Baki jafar ya washe Yana kallon ananon data sunkuyar dakai su Yusuf ma duk bakin suka washe cikin farin ciki
Baffa kuwa kallon gwaggo yayi yamaida kallonsa ga ananon kafin yakalli inna dako bata fa'daba farin ciki ya bayyana afuskarta sbd kullum zancenta da fargabarta Taya Anano zata samu mijin aure tana tareda 'da ana Mata kallon ta haifi shege..

Jinjina Kai baffa yayi yace,

Hindatu waye wannan me sa'ar dayakeson auren ananon baffa.?

Hmmn aikaida baffa Anano dai Kam tayi sa'a itama Dan yaron akwai hankali da nutsuwa uwa uba sanin girma da darajar na gaba..

To hindatu yasan da maganar wannan yaron?

Yasani kuwa Dan da'aka kwantarda abdul din asibiti shiyayita Mana hidima..ataqaice dai baffa shine Wanda nake Zama gurinsa Wanda Mai 'dakinsa ta rasu...

Nan gwaggo ta 6alle tafara korowa baffa saqon Abba dakuma auren dasukeso cikin qanqanin lokaci..

Sosai baffa ya jinjina alamarin Amma dai zai jira zuwansu Abban jibi.

Da daddare haka ta saka hijabinta tai gidansu nusaiba acan sukasha firar yaushe gamo saidataga dare yayi tadawo gida bayan sunyi washe gari zasuje gidan ubaidah da'akai aurenta wata uku kenan.

Washe garima bata yini agidanba itada nusaiba suka yini gidan ubaidah Nantagaya musu duk abinda yafaru a wancan lokacin..

Da marairaice tadawo gida ta tararda abdulshakur ya daga musu hankali rashin ganinta Nan tayi Masa wanka itama tayi suka zauna shimfidar baffa daya dawo sallar magriba suka fara fira gwaggo da Inna kuwa Sai kaida kawon suyar Naman kaji da man shanu sukeyi na tarbon su Abba gobe.

Fira sukeyi sosai da abbanta anan ya tambayeta kotanason auren saheeb din ba 6ata lokaci tace eh,

Aiko washe gari su Abba da wuri sukazo Nan akai magana akakai qarshe suka bada ku'din aure da komai aka tsayar da Rana juma'a Mai zagayowa suka wuce.

Tunda aka tsaida ranar aka hanata ko fitowa tsakar gida kullum tana 'daki itada nusaiba data tare gidan har agama biki hakama ubaidah kullum tana hanya hardai bikin ya qarato daurin aure ya rage saura kwana uku..

Cikin qananan Kaya dark blue da facing cap dinsa ta soldiers yashigo palon
Kallo 'daya zakai Masa kaji yatafi da dukkanin nutsuwarka sbd yanda ya iya shiga kyawunsa da hasken fatarsa su fito sosai..

'dan risinawa yayi ya gaida Abba tareda komawa kusada mum asee ya zauna Yana kallon yanda fuskarta da idanuwanta suka kumbura sbd kuka da rashin bacci cikeda kulawa murya qasa yace,

Mum please kicire damuwar Nan indai akan tafiyar dazanyi ne.....

Cikin gatse Abba dake karatun jarida yace,

Bayan auren nakane zakayi tafiyar ko kuwa?

Qasa yayi dakai yace,

Abba gobene tafiyar.

To matar taka ya kakeso muyima da ita..?

Shiru yayi cikin wani irin yanayi Dan kuwa baya iya yiwa mahaifinsa musu sbd shikadaine garesa Wanda zaibi yasamu Lada.

cikin sanyin murya yace,

Abba tafiyar aikice ayimin afuwa..

Kallonsa abban yayi saiyaji yabasa tausayi yace,

Shikenan Amma kafin katafi kayi qoqari yau Abu yakaika kaida zayyan kuje ka gaida iyayenta sbd karsuga bakajeba Kuma bakaje daurin aurenba..

To yace tareda miqewa yabar palon zuciyarsa na wani irin quna..

Vote🤨
Comment
Share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_





*27*
*Alhamdulillah banmasan ta yanda Zan gode mukuba Amma kusani mamuh taga qaunarku da kulawarku nagode matuqa,,,ku din nawane Nagani.. thank you so very much sweethearts more especially my wattpadians....*
*Mamuh  love you guys*.😍😍😍😍





Koda yabar palon direct motarsa ya nufa yabar gidan tareda kashe wayoyinsa gabaki 'daya.,

Zayyan Abba yakira yaqara yimasa bayanin inda zasu shida aminin NASA sbd yasani Sarai ba lallaine saheeb din yafada masaba.

Zayyan din nagama waya da Abba saheeb yakira Amma yaji suka wayoyinsa arufe
Dama yasan arina Kuma koba komai yasan zuwan saheeb din bamai yiyuwa bane yanxu
Dan haka Sai kawai yashirya shida Abu suka tafi batareda sanin abban bada saheeb suka tafiba...

Yau tun safe baqin kauye dasuka iso suka qarasa cika gidan Sai hayaniyar biki suke
itadai amarya tana 'daki tareda qawayenta Sai firarsu suke cikin farin ciki da kwanciyar hankali
Lokaci lokaci idan ta tuno dawa zata aura Kuma gobene saitaji gabanta yayi mummunan fa'duwa Dan 'yan kwanakin datayi agida jitake kamar karta koma tace tafasa
Sam yanxu batajin tsoron mum asee ko ka'dan bare na Kamal data gama rainasa kallon lusari ma take Masa Amma tsoron saheeb din acikin jininta Allah ya halitta Mata shi...

Kamar daga sama taji ana cewa ga angon Nan yazo gaisuwa
Ta lumshe idanu gabanta na tsinkewa Dan tasan saheeb bazai ta6a zuwaba Sai dai in Kamal n.....

Zumbur ta bu'de idanuwanta ta miqe Dan kuwa idan Kamal ne tonan asiri zaimusu anan kowa yagane kai da silar auren qilama har fiyeda hakan zaiyi.

Hijab ta dauko dogo tasaka tafito dakin su nusaiba suka bita da kallo
Tsakar gidan ma tana fitowa suka zubo Mata idanu ta Sosa Kai tareda waskewa ta 'dau buta ta nufi hanyar bayi tana satar kallon qofar shigowa
Cikin sa'a taga zayyan yaci ado cikin suturar alfarma yana shigowa tareda Yusuf da aliyu Dan harya gama ganinsu baffa yamusu bayanin aikine Mai qarfi yariqe saheeb shine ya wakilto shi kafin gobe suxo 'daurin aure..

Aje butar tayi tareda sakin ajiyar zuciya takoma 'daki ahankali ta zauna tareda godewa Allah ma dayasa saheeb din baixo ba.

Kudi sosai da Kayan dazata saka gurin sha'anin bikin zayyan yabayar kafin ya juya kusan da yamma Kuma harya tafi Bai gantaba tana 'daki.

Da dare gwaggo da wata 'yar qanwar Inna suka kawo wani uban lalle daya yini a kwa6e sukace daura Mata zasuyi ta kwana dashi
Kallo daya tayiwa lallai ta kalli gwaggo tace,

Gwaggo wannan lallan idan na 'daura na kwana dashi ko kofin Dana riqe saheeb bazai sake kallaba bare yaci abin hannuna...

Baki su gwaggon suka sake Amma ita gwaggon tasan saheeb din zai iya yanda ta fa'da 'din Amma Kam yaza'akai amarya ba lalle kitso ma tun safe aka kirawo maiyi Amma ta murje idanuwanta ba kunya tace saheeb din bayason kitso.

Zama gwaggo tayi kusada ita tareda karbar robar lallen ta aje gabanta tace,

Anano Ina za'akai amarya ba lalle ba kitso saikace mugun aure..
Ki daure ko irin na 'yan gayune saiki 'daurashi kobai Kai safeba da tsakar dare saiki wanke Kinga fa kwana biyu zali tayi tana yanka Miki wannan salatif din irin zanen Yan gayu..

Kallon salatif din tayi taga yanda aka yankashi kamar za'a daura a qafar mutum biyar ta karba tareda ajewa gefenta tace,

To Zan daura da kaina gwaggo.

Suna fita ta jawo robar lallen ta daura a yatsun qafafuwanta Dana hannuwanta tana tunanin yanda komai na aurenta yazamo wani iri
Harta gama ta kwanta zuciyarta na wani iri.

Washe gari.
Tunda ta tashi sallar asuba takasa komawa ta kwanta jikinta gabaki 'daya a mace yake gashi 'daurin auren na safe ne qarfe goma..

Tun asuba gidan aka fara kaida kawon ayyuka har gari yayi haske lokacin 'daurin aure ya gabato su Yusuf da sauran samarin gidan suka shishirya tsaf
Tuni qofar gidan tafara cika da jama'ar daurin aure na qauyen.

Tunda suka hadu da Abba sallar asuba a masallaci abban cikin daurewar fuska yabasa umarnin shiri cikin lokaci daga haka ya tafiyarsa yabar saheeb din cikin wani irin yanayi...

Qarfe bakwai yamiqe yashiga toilet yayo wanka Yana cikin shiryawa zayyan tareda miqa Masa Kaya.

Ko kallon gefensa baiyiba ya wuce closet dinsa ya 'dauko wasu kayan...

Dariya zayyan yayi yace,

Banifa naKar zomonba rataya aka bani.....

Cikin milk Australian gezna yashirya tareda fesa turarensa ya fito Yana daura agogo wayoyinsa ya kwasa suka fito har lokacin fuskarsa a 'daure take..

Abba da sauran jama'arsa dama tuni suka wuce
Suna fitowa yaga motocin sojoji kusan goma ya sake 'daure fuska tareda watsawa zayyan wani mugun kallo suka shiga mota suka kwasa a guje suka dau hanya...

Kamal daya fito da gudu daga part dinsa ya daki iska cikin tsananin baqin ciki da qunar zuciya sbd tun jiya ya shirya zarewa motocinsu saheeb din burki Amma wani mugun bacci ya 'daukesa bayan yasha drink gurin mum...

Qyaci yayi cikin zafin zuciya yace,

Zaku dawo gidan daka Kai har ita idiot din zanyi maganin kowa har useless dattijon Nan daya ha'da auren har mum asee sbd bazai ta6a yafe wannan cin amanarba,,,, you'll all gonna pay for this idiots...



Qarfe goma da saura mintuna goma Sha biyu suka iso Nan qauye rikice da hayaniya sbd ganin sojoji mota mota kamar wa'inda sukazo kwantarda tarzoma...
Lokacinda saheeb din yafito yaqaraso ba baffa kawai yaji da'din ganin mijin Anano ba kaf su aliyu sunji Dadi Nan aka fara gudanar da 'daurin auren...


Tundata tayo wanka tazo ta shirya cikin doguwar Rigar wani tsadadden lace black Mai adon purple daya fitar da hasken fatarta matuqa Nan take tafito amaryarta ta shirya abdulshakur shima cikin adon sabbin kayansa da zayyan din yasako Masa shima.

Zaunawa tayi tareda 'daurasa Kan cinyarta tana basa sabuwar Madara da aka kawo Mata Tasha..

Kallonsu nusaiba tayi tace,

Anano kibani 'danki Mana kafin kugama cin amarci...

Murmushi tayi ta bu'de baki zatayi magana shigowar hamma Yusuf da goron daurin aure cikin gidan Yana fa'dar andaura ne yasa bakinta nauyi gabanta yayi mummunan fa'duwa..

Rintse idanuwanta dasuka kawo ruwan hawaye tayi
Su ubaidah kuwa fita sukayi tsakar gidan Sbd cewa da akayi ga angon Nan shigowa ya gaida iyaye Mata.

Sake rintse idanuwanta tayi lokacinda taji qamshin turarensa har cikin dakin ya shiga hancinta.,

Jiki a mace ta miqe daukeda abdulshakur ahannunta taje bakin window tana tsaya Yana qarasa shigowa tsakar gidan gabaki 'daya Kuma Kai tsaye cikin idanuwanta nasa idanun suka fara sauka...
Saurin barin bakin windon tayi zuciyarta na bugawa da sauri takoma bakin gadon ta zauna da sauri.

Cikin qarfin hali ya gaggaisa dasu yafito sbd tsananin zafinda zuciyarsa ke Masa musamman ma yanxu daya ganta itada bastard son dinta.
Sosai zayyan da Abba sukaita sakin kudi suna rabawa maroqa da Yan qauyen har aka watse suka juyo da niyar Sai washe gari za'a Aiko motar daukar amarya.

Koda suka koma tuni gyaran part dinsa yayi Nisa sbd fitar da komai da akayi akayo odar sabo bedroom dinsa ne kawai ba'a ta6aba sbd gudun laifi hakama ba laifi mum asee ta Tara jama'arta anyi taro na musamman na auren 'danta..kaman yanda take fa'da.

Baidawo gidanba Sai dare Koda yadawo angama gyaran komai part din ya canxa sosai saidai hotunan nafeesat ko daya ba'a daukeba suna Nan maqale inda suke saima gogesu da'akayi aka mayar..

Bedroom ya wuce ya shige toilet yayo wanka yaxo ya kwanta...
Asuba nayi yayi wanka ya shirya ya nufi masallaci acan yasanarda Abba tafiyarsa qarfe bakwai na safen..

Cikin sakewa Abba yayi Masa adduar Allah ya tsare Dan dama shidai burinsa ayi auren yananan..

Yana komawa 'daki ya harhada abinda zai buqata ya sake shiryawa cikin qananun Kaya black da blue leather jacket yafito daidai isowar zayyan dazai kaisa airport
Ya shiga mota suka wuce..

Jirginsa na tashi zayyan yadawo gida yahau Shirin zuwa 'dauko amarya sbd shine zaije.

Qarfe goma aka sata ta shirya baffa ya zaunarda ita yayi Mata nashiha shida gwaggo duk da da ita zasu koma
Hakama su Yusuf kowa yayi Mata tasa kalar nasihar..

Sosai jikinta ya mutu da nasihar su baffa Dan ma basusan wane irin aurene ba tayi.

Babu abinda ta 'dauka Sai kayan da zayyan yakawo Mata
Qarfe biyu zayyan ya iso qarfe uku suka juyo daga ita Sai gwaggo da nusaiba ubaida mijinta Bai bartaba Sai jafar dake gaba...

Tunda suka dau hanya jikinta ya qara saki tsoro da fargabar yanda zata ha'du da saheeb din take.

Gab da magriba suka iso Nan su mum asee da wasu baqinta suka tarbesu a aladance suka rakasu har part din saheeb har cikin bedroom din nafeesat dayake amatsayin nata yanxu..

Gwaggo 6angarenta ta nufa tareda nusaiba sbd basusan saheeb din baya gariba..

Bata tsaya wani dogon jiraba sbd tasan ba kamar kowane aurene wannanba dazata jira ango ta miqe jiki asanyaye tana kallon tsari da haduwar kayan dakin da'aka canza tana qara mamakin inda aure yakawota harta fa'da toilet tayo wanka tazo ta bu'de akwatinta ta canza Kaya tayi sallar la'asar dabasuyiba da magriba..

Tana idarwa taji ana knocking qofar bedroom din
Gabanta yayi mugun fa'duwa jikinta na saki ta miqe ta bu'de cikin fargaba.

Asabe tagani tareda wata sabuwar Mai aiki budurwa tasaki fuska suka gaisa asabe tace,

Abincine mum asee tace akawo..

Kallon kulolin hannunsu tayi kafin tace,

Su aje dining
suna ajewa suka fice ta fito palon cikin fargaba ta nufi qofar kicin tabita qofar kicin din ta fa'da dakin gwaggo..

A zaune ta tarar dasu suna hutawa tazauna gefen nusaiba tareda gyarawa abdul kwanciyarsa tana  cewa,

Nusy ga abinci acan kixo muje mudauko saimuci anan..

Muguwar harara gwaggo ta watsa Mata tana cewa,

Kedai wlh anyi gantalaliyar amarya Mara kunya,
Yanxu da ace saheeb din Yana gari haka Zaki taho kibarosa?
To Allah tsaya kiji matuqar kikace wannan zaryar gantalin Zaki riqayi zuwa Nan kayana Zan ha'da nakoma gida tunda dama Dan kina ganinane,
Abinci mun Riga munci ki tashi maza ki koma 'dakinki..

Miqewa tayi jiki a salu6e ta duqa ta 'dauki abdulshakur ta sa6a akafada ta Fice gwaggo tabita da harara ko Abdul dinma Dan taji asabe tace bayanan ne yasa tabarta ta tafi dashi.

Washe gari tunda safe nusaiba da jafar suka wuce Abu driver Abba yasa yamaidasu..

Bayan kwana biyu
Qarfe goma da rabi ta shiryo cikin wata dark blue atampar super exclusive batareda tayi kwalliyar komaiba Amma duk da haka sosai tayi kyau cikin shigar ta fito ta riqeda hannun abdulshakur dake koyan tafiya ta nufi gurin gwaggo suka gaisa tabaro abdul din ta nufi part dinsu mum asee.

Tana kaiwa qofar part din da Kamal tafaracin karo ya tsaya gabanta Yana watsa Mata wani mugun kallo zuciyarsa na mugun tafasa...

Dauke Kai tayi tareda ra6asa zata wuce a zuciye ya fixgota tadawo baya
Bata tsaya Bata lokaciba ta yanka Masa wani lafiyayyan Marin dayasa su mum asee qarasowa cikin wani mugun yanayi..

A zafafe ya 'daga hannu zai sakar Mata Marin yaji anriqe hannunsa ya juyo cikin zafi yaga zayyan tareda Ahmed zubair Barr Kuma PA na saheeb..

Kallonsa tayi cikin daure fuska tace,

Ka dawo hankalinka idanma gushe maka yayi kasan da matar babban soldier kake
Ka gode Allah baya gari da baka qara marmarin ko kallon matarsaba bare ganganci ta6awa....

Ba Kamal kawaiba hatta mum asee da zayyan sunyi matuqar mamakinta bare Ahmed daya fito da idanuwa ganin matar saheeb din ta yanxu taci uban marigayiya Dan nafeesat sanyi qalau take.....hmmm lallai akwai rigima tafe Amma Bari yagani...

Gyara tsayuwa yayi tareda kallon mum asee yace,

Mum asee dama maganar ku'din da ake bayarwane na duk wata na biyan ma'aikatan gidan da bills na gidan nakeson sanin sabon lissafinku tunda oga yayi aure yanxu Dole lissafin zai qaru.

Kallonsa tayi a wulaqance tace,

Banda wannan lokacin kaje ka qara dubu 'dari asama......

Zaro idanuwa yayi tareda gyara zaman medical glass dinsa yabude baki zaice to cikin 'daure fuska Anano ta katsesa da cewa,

Wayene Mai biyan bills din?

Oga saheeb ne madam..

Nawane?

Dubu 'dari biyu ne duk wata madam....

Sake daure fuska tayi tareda satar kallon zayyan ya gyada Mata Kai a fakaici saita juyo ta kalli Ahmed din tace,

Cancel wannan lissafin sbd nice matar saheeb nice Zan riqa bada duk wani lissafin abunda ake buqata matuqar daga dukiyar mijina zata fito daga yau kaje jibi zan nemeka idan nagama lissafin nakumayi magana baby anjima....

To yace tareda juyawa yabar gurin Yana danne tsananin mamiknsa
Zayyan ma bayansa yabi Yana jinjina alamarin....
Hmmmnn su saheeb baby manya.

Suna barin gurin ta juya zata wuce mum asee ta riqo hannunta cikin wani irin mugun 6acin rai.





#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_





*28*
'dan fiddo da idanuwanta tayi tareda jujuyawa ko Ina tayi qasa da murya tace,

Mum yi ahankali Kar wani yagani cikin yaran saheeb su rainani inzo inason Basu umarni suna qin bi...

Wani mugun kallo mum asee tasakar Mata Saida taji gabanta ya'dan Fadi ta ha'diye wani yawu tareda sakin murmushin qarfin zatayi magana mum asee ta katseta cikin wani irin yanayi tace,

Kibi ahankali fa karkibari rawar kanki tasaki wuce wurinki Dan kuwa bazaki Kai wani dogon labariba,,,kisan dawa kike karkiyi gangaci da rayuwarki..

Sakinta tayi ta juya ta shige palonta Kamal da tuni yayi mutuwar tsaye sbd baqin ciki gashi baiji Mai suka tattaunaba yajuya yabar gurin Yana qissima wani mummunan nufi a zuciyarsa..

Sanyi taji jikinta na nemanyi sbd tabbas tasan waye mum asee tasan dawa take dealing amma itama dolece tunda ba wata hanya ko mafita yanzu idanba wannan dinba Kuma matuqar Bata fara da hakanba bazata samu su hada duk wata shaida dasuke soba ta tona su mum din
Dan ko sunso tonasu yanxu basuda wata qwaqwaran shaidar gabatarwa...

Juyawa tayi ta jiki ba qwari takoma gurin gwaggo ta 'dau Abdul suka koma..

Abinci ta 'daura musu itada Abdul din sukaci suna gamawa yayi bacci takaisa 'daki kwantar bayan ta rage Masa qarfin ac
Takoma kicin taci gaba da ayukanta
Ta gyare kicin din tadawo Palo tazauna tana kallon tashar cwtv.

Washe gari da safe zayyan zo tareda takardunta dayasa aka kar6o Mata na gama makaranta..

Drinks din data kawo Masa ta aje tareda Zama cikin sanyin murya tace,

Mum asee tafara tambayata akan nafara gaggawar aikata abinda yasa akayi auren.

Wayarsa dake ringing ya fitar Yana cewa,

Karki damu da wannan kicigaba da yanda Kika fara dinnan sbd rashin hakuri da zafin zuciyar Kamal agurin mum ya gado abinsa coz Sam itama batada hakuri.,
Idan Kika cigaba da kunnasu cikin qanqanin lokaci zasu fara fiddo da halayensu,

Yanxu dai kishirya gobe Ahmed zaizo yakaiki siyayyar Kaya da duk wani abun buqatarki saikuma maganar jamb dinki yau za'a cika komai insha Allah..

Miqewa yayi tareda miqa Mata kwalin wayar iPhoneX yace,

Bari natafi baby saheeb ne ke kirana Kar ya hasala kinsan halinsa...

Sunkuyar dakai tayi tana dariya cikin kunya sbd tasan tsokanar zancenta na jiya ne yakeyi.

Yana fita ta fiddo wayar ta kunna tayita dube dubenta kafin ta maqala charging Dan Sam Bata iya wayarba.

Da marairaice gurin gwaggo takai abdulshakur tasamu tagama aikinta sabuwar Mai aikin da mum takawo Mata tana tayata duk da tana zargin sbd saka Ido aka kawo Mata ita.


Washe gari

10 / 19