Author : Mamuhagge Category : True Books
din wannan karon harda Anano Dan kuwa ta hangowa kanta masifa a idanuwan saheeb gameda Anano.
Tun bayan rasuwar rayuwarsa taqara canzawa miskilancinsa da shirunsa rashin son maganarsa ya qaru,
Gashi har lokacin lafiyarsa taqi dawowa gabaki 'daya.
Zayyan takira tayi Masa bayanin rashin lafiyar saheeb din Nan take yayi Masa booking appointment na ganin doctor 'dinsa dake new York yafara nemar musu visa.
Ita kanta Bata saniba Sai abakin nabeela dake tsokanarta tana cewa,
Honeymoon 'dinnan fa Yana burgeni musamman yanxu danasan Sai ranarda muka ganku tunda dama saheeb sbd Abba ne yake Zama anan.
Kallon rashin fahimta Anano tayi Mata tana cewa,
Honeymoon ana zaune qalau nida Zan fara zuwa makaranta tunda komai ya kammala registration kawai zanyi.
Miqewa nabeela tayi tana bu'de wardrobe dinta tace,
Kinyarda na qara shirya Miki kayan tafiya?
Da sauri ta taso tana cewa,
Aa banyardaba indai irin na wancen Karan ne.
Dariya tayi tace,
Amma dai koba komai na taimaka ko?
Harara ta watsa Mata tana cewa,
Eh ba laifi Amma dai kinsan ra'ayina.
Bata yarda da tafiya zasuyiba Saida zayyan yakirata yasanarda ita washe gari zasu wuce.
Shirya kayanta tayi zuciyarta na Mata tunanin 'danta sbd har cikin ranta tana tsananin buqatarsa kusada ita saidai Kuma batason Yana kusantuwa sosai da saheeb yanxu tafison Sai komai ya daidaita sbd tayi alqawarin insha Allah dasunje zata fadawa saheeb komai gameda su mum Asee
Saita fara ganin yanda zai kar6i zancen kafin ta sanar dashi maganar nafeesat da abdulshakur.
Gurinsu gwaggo tayi kusan Raba dare kafin tadawo tayi wanka Tai Shirin kwanciya.
#vote
#comment
#share
#and follow.
[10/17, 7:00 PM] +234 803 668 9121: *_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_
*39*
Shirin kwanciya tayi harta kwanta Sai Kuma ta taso ta fito Palo ta nufi bedroom dinsa ahankali ta murda handle ta tura qofar tana kallon cikin 'dakin sbd duhu ko Ina.
Cikin san'da ta Isa gurin switch ta kunna wutar 'dakin
Zaro idanuwa cikin wata matsananciyar kunya biyu sbd ganinsa zaune a sofa idanuwansa qyar akanta
Dama yasan zatazo shiyasa,
Cikeda kunya tayi qasa da kanta ai kawai saitaga kayan baccin dake jikinta a firgice ta 'dago takallesa taga oily eyes dinsa qur akanta da gudu tayi hanyar barin 'dakin cikin rashin sa'a ta bu'de qafarta da wardrobe tasaki qaramar qara tareda durqushewa cikin tsananin zafi.
Akaro na farko dayayi murmushi bayan tsawon shekaru Wanda har nafeesat tayi rayuwa dashi ta rasu bata ta6a ganin murmushinsaba.
Sam baisan sanda murmushin ya kubce Masaba Dan ta matuqar basa dariyar yanda tashigo da yanda taji kunya.
Tasowa yayi ya qaraso gabanta saiyaga hawaye na gangaro Mata Sai kawai abin yaqara sashi murmushi
Duk da tana cikin azaba hakan Bai Hana tsantsar mamakinta bayyanowaba karo na farko arayuwarta dataga murmushinsa
Tasaki Baki tana kallonsa..
Hannu ya miqa Mata daga tsayen
Ta Kama ta miqe har lokacin Bata daina kallonsa ba cikeda mamaki Dan har lokacin murmushin Bai gushe daga fuskarsa.
Bakin gado suka qarasa suka zauna tare ya juyo ya kalleta ganin takasa daina kallonsa.
Ahankali ya bu'de Baki murya akasance yace,
Kina mamaki ko?
Kai ta 'daga sbd bakinta ya mutu bazata iya maganaba.
I'm also surprised, after so many years I've found my smile again,.
Sunkuyar dakai tayi batareda tace qalaba sai qafarta datake tabawa gurinda ta buge.
Kallon qafar yayi yakuma 'dauke Kai sbd ganin fararen santala santalan cinyoyinta a fili sbd rigarta iyakacinta kwatan cinyarta.
Lurada hakan yasa ta miqe ahankali cikin sanyin murya tace,
Saida safe.
Miqewa yayi tareda miqa Mata hannu ba musu ta miqa Masa suka fita tana 'dingisawa ya rakota har qofar bedroom'dinta ta shige ya juya Yana mamakin kansa.
Washe gari Sai qarfe takwas ta fito Palo taci adonta cikin Riga da skirt na turkie brown da lopas coffee brown ta nado gyalansu akanta Kar itama 'yar turkie dince.
Shida zayyan ta gani a palon suna maganar wasu takardu da ake buqatar saka hannunsa.
Gaisawa tayida zayyan yana tambayarta abdulshakur.
Mummunan fa'duwa gabanta yayi kusan atare suka saci kallon saheeb
Nantake taji hankalinta ya tashi da yanayin dataga fuskarsa tayi sum sum tabar gurin tabita kicin tafada gurin gwaggo.
Rungume abdulshakur tayi ajikinta tanajin qaunarsa data mahaifinsa na qara shigarta.
Koda mum asee ta Aiko Kiran saheeb fuskewa yayi yace ace yariga ya fita sbd yasan maganar Kamal ce zatai Masa wanda ita agurinta ba hakan bane wani mugun magani ne tasa aka kawo Mata daga nijar wanda zai ringa qone jininsa ahankali batareda kowa ya ganeba harsai yabi uwarsa da ubansa sbd yanxu shikadaine yayi saura Wanda yayi Mata shamaki da samun cikar burinta.
Da gwaggo kawai tayi bankwana taqi zuwa gurin mum sbd zayyan yafada Mata mum batasanda tafiyarba sbd zata iya Hana saheeb tafiyar.
Tunda suka ha'du da safiyar fuskarsa ta canxa jiyake zuciyarsa da kansa kamar zasu tarwatse sbd maganar 'dan da zayyan yayi Mata.
Koda suka shiga jirgi harsuka Isa fuskarnan a tamke take ko alamar fara'a Babu.
Already zayyan yayi musu booking komai motar hotel dinsu tazo 'daukarsu takaisu hotel din.
Lafiyayyan honeymoon suite aka Basu
Shiyafara yin wanka yayi sallolinsa yasaka kayan Shan iska ya kwashi wayoyinsa ya fice zuwa ganin Dr sbd a Daren ne yakeda appointment dashi.
Wanka tayi itama jiki asanyaye tareda yin sallah tasaka rigar baccinta ta kwanta Nan take baccin gajiya ya 'dauketa.
Bai dawoba Sai tsakar dare 'daukeda ledojin snacks da pizza daya siyo musu.
Jikinsa yaji ya mutu dayaga yanda tayi bacci atakure fuskarta na bayyana damuwar data kwanta da ita.
Ajewa yayi tareda qarasowa Bakin gadon ya shafa fuskarta ahankali.
Bu'de idanuwanta tayi cikin nutsuwa ta 'dorasu akansa suna cikowa da 'kwalla.
Tayarda it's zaune yayi Yana kallon cikin idonta ta rintse idanun
Ya jawo pizza ya bu'de tareda Ciro 'daya yakai bakinta.
Ba musu ta ringa ci haidaida taci slice uku kafin ta girgixa Masa Kai ya Bata ruwa tasha.
Tana zaune tana kallonsa yaci uku shima yatashi yaje yasako wanka da brush
Yana fitowa Tai saurin rufe idanuwanta.
Yana Gama shirinsa ya hawo gadon ya kwanta Yana kallon idanuwanta dake rufe dogayen eyelashe dinta daya kwanta.
Ahankali wani irin sabo da shaquwa yafara shiga tsakaninsu musamman yanda ta sake take kula dashi sosai
Nan take rayuwarsa tafara canxawa sbd yanxu ko abinci sukeci sunyi sabon ciyarda juna,
Gurin kwanciyama tun ana kwana kowa gefensa Amma su farka sukagansu maqale da juna harsun fara sabawa.,
Abu 'daya data lura yafiso shine tsananin kulawa da riritawa tareda son rayuwar yanci kamar turawa kotace yatashi ciki yanason rayuwar
Saita tattara ta lalace gurin riritashi da basa wata irin kulawa ta musamman
Ga yawo da kullum suke fita yi idan ka gansu zaka dauka masoyan asaline..
Haryanxu baisawa zuciyarsa Wai sone yayi Masa mummunan kamuba sbd baitaba Jin wannan feelings din akan kowaba.,
Abu 'daya yasani zuciyarsa ta yarda da ita,
So da dama tanason sanar dashi komai sai Kuma taji batason 6ata Masa 'dan farin cikin dayake ciki zata Bari Sai sun dawo Nigeria...
A Nigeria kuwa tunda mum asee Kamal yasanarda ita tafiyarsu saheeb da ananon bindigewa ne kawai zuciyarta bataiba sbd baqin ciki da tsananin 6acin rai Wanda tayi alqawarin magance komai lokaci 'daya dasun dawo.
Yau watansu 'daya a qasar
Dukkaninsu sun sauya matuqa musamman mashi dahar wata lafiyayyar qasumba ya aje data qarawa lafiyayyar farar fuskarsa kyau da aji ga wani haske sosai daya qara.
Ita kuwa girma da cikowa ta qara tareda qarin wayewa tazamo mace Mai cikakken class musamman hips 'dinta dasuka baje daidai.
Tsaye take gaban mirror 'daure da towel fari tana waya da nabeela tana combing dogon gashinta Dan handsfree tasaka wayar ta aje gaban mirror.
Suna cikin wayar ne yashigo 'dakin sanyeda jallabiya fara qal da hular larabawa dawowarsa kenan daga sallar isha'i.
Kallonta yake Yana qarasowa gaban mirrorn.
'daukar wayar tayi tareda cire handsfree ta 'dora a kunne tace,
Nabeela gobe zankiraki.
Aje wayar tayi ta 'dauki comb zata cigaba ya riqe hannun Yana kallon cikin idanuwanta ta cikin mirror.
Sunkuyar dakai tayi sbd yau tun safe take ganin sauyi ataredashi Wanda hakan ba qaramin tayar Mata da hankali yakeba,
Har cikin ranta batason wani Abu yashiga tsakaninta da saheeb Dan zai gano Bata ta6a sanin wani 'da namijiba kenan Dole zai tsareta saita fa'da Masa abdulshakur 'dan waye.
Zame hannunta tayi tareda miqewa zata nufi wardrobe ya birkitota tareda matsota Yana jifanta da wani irin kallo daya karya dukkanin garkuwar jikinta.
Rufe idanuwanta tayi ahankali numfashinta na fita da sauri qirjinta na sama Yana komawa.
Qirjin nata ya qurawa Ido Nan take yaji abinda baita6a jiba na yawo cikin jininsa
Yakai hannunsa 'daya ya dafe Mata qirjin 'dayan hannun kuwa ya riqo qugunta yaqarasa matso da ita cikin jikinsa
Still idanuwansa dasukai wani laushi suna kanta
Ta qara rintse idanuwanta tana jan 'dauke numfashi.
#vote
#comment
#share
#and follow.
_*EZNAH*_🌹
_wattpad@mamuhgee_
*40*
Idanuwanta data rintse ya kalla tareda shafa dogayen eyelash nata Dan suna matuqar burgesa da 'daukar hankalinsa.,
Gangaro da hannunsa yayi zuwa lips dinta dasuke qyallin lipbalm ya lumshe ido ya bu'de cikin nutsuwa sbd nauyin dasuka fara Masa na rikidewar dasuke Dan kuwa zai iya cewa baita6a Jin wannan lafiyayyar sha'awarba.,
Ahankali yakai fuskarsa daf da tata tareda riqo Tata fuskar hancinsu na gogar juna ya qurawa idanuwanta dake rufe nasa idanun dasuka canza,
Ahankali ta bu'de idanuwanta dasuka fara canzawa itama
Idanuwansu suka shiga cikin na juna cikin sanyi ya 'dora bakinsa Kan nata Yana kallon cikin idanuwanta
Tanajin bakinsa cikin nata ta rufe idanuwanta ahankali sbd wani yanayi daya shigeta karo na farko arayuwarta.
Sam saheeb baya komai da zafi arayuwarsa
Cikin nutsuwa yaje komai shiyasa yake kissing 'din bakin nata ahankali yana zame towel 'dinta da hannunsa 'daya,
Jin saukar towel 'dinta a qasa yasa hawaye gangarowa daga idanuwanta dasuke rufe taja wani mugun dogon numfashi sbd numfashin dataji Yana qoqarin barin qirjinta sbd wani lafiyayyan ta6i daya kaiwa qirjinta
Ta zame ahankali tareda durqushewa qasa
Binta yayi qasa cikin nutsuwa ya 'dauketa
Tayi saurin qanqamesa tana qara rintse idanuwanta sbd kunyar batada komai ajikinta,,
Ahankali ya kwantarda ita a gadon Yana kallon face 'dinta ya zura hannu ya rage hasken wutar 'dakin sosai..
Gashinta daya barbazu ya shafo tareda Kai hancinsa ya shaqo qamshinsa ya lumshe idanu buqatarsa na qara tsanantuwa
Ya jawo ya 'dora Kan jikinsa idanuwansa qyar akan qirjinta farare tas
Ahankali yakai hannuwansa da bakinsa lokaci Yana fidda numfashi ahankali jikinsa na fara rawa
Nan take komai ya kunce Masa yafara 'daukar zafi zafi da al'amarin
Dan kuwa tun tana qoqarin dannewa harta kasa yayi mugun fitarda ita nutsuwarta tana Jan numfashi
Tanajin alamarin yayi zafi jikinta ya'dau rawa tafara qoqarin zamewa tana kuka ahankali
Shikuwa Sam jiyake bazai iya dakatawaba...
Qarar ringing na wayarsane yafara tashi
Harta katse Baima saniba
Nan take aka cigaba da danno Kiran
Cikin qarfin hali tasamu ta qwace tareda juyawa ta shige cikin bargo tana fidda numfashi da sauri tareda qoqarin daidaita numfashin.
Dafe kansa yayi Yana daidaita nasa numfashin shima kafin ya Kai hannu daqyar ya 'dauki wayar ya Duba...
Tashi zaune yayi Yana 'dan wartsakewa sbd ganin ogansu ne gabaki 'daya ke Kira.
Gyara muryarsa yayi ya 'daga wayar tareda gaishesa cikin nutsuwa da girmamawa,,
Dafe goshinsa yayi Yana karanto innalillahi cikin zuciyarsa sbd Jin abinda umarnin gaggawa dayake basa na ana nemansa a gaggauce qasar Romania gobe.
Yana aje wayar ya rintse idanuwansa dasuka qanqance sukai ja sbd urged,,
Ahankali ya miqe ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwan 'dumi..
Hawayene sabbi masu 'dumi suka gangaro Mata sbd taji wayarsa.
Koda yafito yitayi kamar tana bacci ya shirya cikin kayan bacci yazo ya kwanta bayan yayi booking flight 'dinda zaibi goben ta wayarsa ya kashe wayar tareda jawota jikinsa Yana sauke ajiyar zuciya har bacci ya 'daukesu.
Tunda sukai sallar asuba ta shirya Masa kayansa ta shirya nata sbd itama jirgin ranar zatabi takoma gida.
Jikinta duk a sanyaye takeyin aikin Yana lure da ita
Tana gamawa ya jawota jikinsa tareda zaunar da ita Kan qafafunsa ya riqo fuskarta Yana kallon cikin idonta yace,
Zaki bini?
Girgixa Kai tayi hawayen datake dannewa na gangaro Mata.
Hawayen ya kalla sbd Shi kullum yaga hawaye mamakinsu yake yanda shi basa fito Masa koda zai ringa rage ra'dadi da quncin zuciyarsa
Amma ita nata mamakin zafinsu yakeji sbd itace ke fitar dasu shikuma shine Mai Jin zafinsu cikin qirjinsa.
Hannu yasa yana goge Mata ta sunkuyar dakai tareda shigewa cikin jikinsa ta kwanta tareda zura hannayenta ta zagayosa ta rungume.
Ajiyar zuciya yasaki tareda sake shigewa da ita jikinta Yana rufe idanuwansa.
Wanka sukayi sukai Breakfast daqyar suka ciyar da juna suka shirya mota takaisu airport.
Zama sukayi jiran kowa Akira flight 'dinsa tana kwance cikin jikinsa hakanan dukkaninsu bamai farin ciki,,
Jirginsa aka fara Kira ta 'dago ta kallesa taga kamar baida niyar tashi ta 'dago daga jikinsa tareda miqa Masa hannunta ya kama suka tashi tsaye ya juyoda ita suka fuskanci juna Yana jifanta da wani irin kallo daya qara karya garkuwar jikinta zata rufe Ido ya girgixa Mata Kai ta tsaya kallonsa
Ya matso da fuskarsa tareda riqo Tata ya 'dora red lips 'dinsa Kan nata tareda zura harshensa cikin bakinta.
Wani irin lafiyayyan kissing yayi Mata na tsawon seconds kafin cire bakinsa
Yakai bakinsa Kan kunnenta cikin wata irin kasalalliyar murya Mai sanyi yace,
Take care""""ya shafi fuskarta ya juya ya wuce Yana Sanya shade 'dinsa.
Kasa motsi tayi tana kallo harya 6ace Mata hawaye suka sauko Mata ta sulale ta zauna Kan kujera tana rufe fuskarta da hawaye ke cigaba da fitowa.
Jirginsu na tashi nasu ne next suka taso zuwa Nigeria.
Cikin dare suka sauka Dan haka Samuel ne yazo 'daukarta ba zayyan ba
Kodata isa kowa yayi bacci
Wanka tayi Tai sallolinta ta kwanta Nan take bacci ya 'dauketa.
Washe gari da safe su gwaggo na ganinta suka hau murna musamman ma abdul daya maqale Mata ko sakinsa yaqi yarda tayi Dan karta Kuma tafiya tabarsa.
Da kanta ta kamawa nuratu aiki sukayiwa ko'ina fes tareda kunna duka ac ac koina yadau sanyi da qamshi.
Abinci taci ta nufi gurin mum Dan tasan zuwa yanxu Kam haduwarsu ba kyau.
Da sallama ta shiga abdulshakur na riqeda hannunta,
Yakurah ce ka'dai a palon tana Shan babbar robar ice cream tana kallo hankalinta kwance Dan ita jira take su mum su Gama yaqin kar6ar dukiyar tafara nata yaqin sbd kar6arta hannunsu tafi Mata sauqi matuqa.
Wani kallo tabi ananon dashi daga samanta har qasa tsantsar mamakinta afili sbd ganin mugun sauyi atareda ananon,
Fatarta,dirinta,kyawunta da wani class duk tayi Kuma sun amsheta matuqa.
Wani irin 'daci taji cikin ranta ta maida kallonta gurin stairs sbd motsin dataji taga mum asee ce ta 'dauki robar ice cream 'dinta ta wuce room 'dinta tana qoqarin lallashin zuciyarta akan lokacinta yakusa zuwa itama.
Zama Anano tayi batareda ta saki fuska sosaiba tace,
Ina wuni mum?
Abdulshakur daya 'dale Kan cinyar Anano ta qurawa Ido ko kyaftawa batayi.
Fa'duwa gaban Anano yayi sbd ganin irin kallon datake Masa shaf ta manta tazo dashi.,
Miqewa tayi da sauri takaisa bakin qofa tace,
Sweetin mamah jeka gurin gwaggo kace ganinan zuwa ko.
Da gudu ya wuce cikin maganarsa da Bata qarasa budewaba Yana cewa,
Mommah kalkije yawo pa.
Murmushi tayi tana cewa,
Eh bazanje ko'ina.
Dawowa tayi palon tana kallon fuskar mum danta karanci yanayinta kozata iya gano idan ta gano wani Abu.
Ga mamakinta ko muguwar fuska mum asee batai mataba saima ya hanya datai Mata.
Mamakinta kasa 6oyuwa yayi tasake kallonta tace,
Mum ya Kamal kuwa anji labarin inda yake?
Wani mugun tsinannan kallo ta watso Mata sbd har wani 'daci takeji cikin bakinta sbd baqin ciki, takaici da 'dacin zuciyarta datake ji Kan saheeb da Ananon Amma sbd canza tsari datayi saita danne tasake fuska tana kallon tv tace,
Yadawo Yana gida.
Dum""gabanta ya buga Jin Yana gidan ta miqe ahankali tareda cewa ta tafi ta nufi qofa.
Kusan karo suka kusanyi harsaida takardun hannunsa suka zube ya 'dago da sauri suna ha'da Ido taga yayi saurin kallon takardun dasuka zube ya duqa cikin sauri yahau tattarawa rashin gskia qarara atareda shi.
Mamakine yakamata tayi Kai kallonta Kan takardun Amma yariga ya keashe ya ra6ata da sauri yabar gurin.
Shiru tayi cikin mamaki tace,
Wane takardune Kamal kewa wannan rawar jikin?
Wayarta ta 'daga ta Nemo numbern zayyan takira tana wucewa zuwa part dinsu.
Inada wata mahimmiyar hidimane agabana shiyasa naketa qoqartawa Naga nasamu na kammala kafin lokacin sbd akwai saura sosai agaba
Amma gskia idan bakwa voting da comments Zan ajiye harsaina Gama hidimata Wadda bansan ranar kammalata ba so now posting 'dina depends on your votes and comment.
Love you my people 😍😍😍😍
Mamuh💋
#vote
#comment
#share
#and follow.
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_
*41*
fasa wucewa gurinsu gwaggo tayi ta nufi part dinsu tana cigaba da dialling numbern zayyan
Yana dauka cikin sanyin murya suka gaisa ta sanardashi abinda yafaru na takardun hannun kamalu data gani yana boye matawanda ta tabbatarda na wani mugun qullin ne.
Kwantar mata da hankali yayi yace tabari zaiyi gaggawar bincikawa yagano kona meyene.
Suna gama wayar kiran saheeb yashigo wayarta gabanta yadan fadi ta qurawa screen 'din wayar ido tana kallon sunan data sakawa numbersa kkewarsa da marmarin ganinsa na shiga jikinta tana qara ratsa koina nata.
Cikin sanyi da taushin murya ta 'daga
Qasa qasa tajiyo muryarsa yana mata magana
Nan take taji tsikar jikinta ta tashi
Jikinta na sake mutuwa tace,
Kana lafiya kuwa?
Numfashi ya sauke mata cikin kunne ahankali sbd tsananin kewarta dake tsabanin cin ruhi da jikinsa yace,
I'm not Okay,i want to be home.
Murmushi tasaki tana zamewa ta kwanta kan kujera tayi qasa sosai da murya itama tanacewa,
Then come back soon coz the home is already missing you so badly..
Da wata irin murya yace,
Are you sure?
Yes hundred percent sure.
Sun dauki tsawon time suna waya batareda sun ankaraba har lokaci yaja kafin suka kashe.
Tundaga ranar basu sake wayaba sbd sunfara aikin daya kaisa tuquru ko waya bai kunnaba sbd kai yadau zafi.
Ta bangaren school kuwa tuni aka gama komai tafara zuwa hankali kwance tana karantar medicine ,
Zayyan kuwa duk yanda yaso gano wani abu kan takardun datace na hannun kamal yayi amma yakasa samun damar samun yin binciken yanda yakamata dole dai saisun samu sun sato takardun sungani kona meyene.
Yau tunda tadawo school da yamma taga fitarsa kuma batareda motarsa ya fitaba da motar mum yafita saitaji tanason dubawa motarsa kozataga takardun.
Wanka kawai tayi ko abinci bata tsaya ciba ta lallabo ta nufi motarsa sbd duhun magriba dayayi dan anmashiga masallaci.
Cikin saa tana bude motar tajita abude tayi saurin shigewa ta rufe tafara duddubawa cikin sauri.
Cikin dashboard taga wasu takardu cikin file anyi musu kyakkawan boyo tabudesu da sauri jikinta na rawa tafara dubawa amma sam bata gane kona meyeba saidai ta tabbatarda sune taga kamal na boyewa ta rufe dashboard din da sauri tafito ta nufi part dinsu ta shige.
Hotunan takardun ta dauka ta turawa zayyan cikin sauri kafin takirasa ta sanar dashi.
Cikin tsananin mamaki da tsoro yaqara zooming din hotunan bayan ta turo masa sbd ganin takardune na mallakawa wani dukiyarka da kadarorinka