Author : Maryam Ibraheem Aleeyu Category : Hausa Novels 001
ciki please karka b'oyemin Habeeb".
Gaba d'aya Habeeb saiyaji tamkar Yah Ameen ya d'aureshi da jijiyoyin jikinshi ne yana matuk'ar ganin girmanshi da k'imarshi musamman dayake zaune yanzu a gabanshi saiyake jin bazai iya masa k'arya ba.
Kai ya shiga gyad'awa tareda fad'in
"Hakane Yah Ameen A.B yana gidanmu kuma kosu Hajiyata bata saniba afwan please shiya nemi hakan daga wajena ayi hak'uri".
Ajiyar zuciya Yah Ameen ya sauke yace
"Karka damu laifinka d'aya daka biyewa wannan shashashan yaron kai kanka kasan tsiyar Abdallah fa bai kamata ka biye masa ba yanzu dai duk ba wannan ba yana gidan naku a yanzu haka?".
Kai kawai Habeeb ya gyad'awa Yah Ameen alamun eh, tsaye Yah Ameen ya tashi yana fad'in
"Thank you so much Habeeb bari inje gidan naku in tafi da d'an banza marajin magana". Dariya kawai Habeeb yayi yace
" Ayi masa a hankali dai yayanmu please nima akwai bak'in dazamu gana dasu yanzu dana biyoka mun tafi tare".
"Karka damu nagode". Ameen ya fad'a tareda fita daga office d'in ya shiga mota ya nufi gidansu Habeeb.
Kai tsaye side d'in Habeeb Ameen ya nufa bayan yayi parking a compound d'in gidan, a rufe yasamu k'ofar tsayawa yayi bakin k'ofar yafara knocking amma ba'a bud'e ba ya cigaba dayi amma shiru, saidaya b'ata mintoci masu d'an dama sannan yaji alamun antaho bud'ewa.
Three quarter din wando ne a jikinshi milk color mai igiyoyi a jikin aljihunan wandon sai farar riga mai hula mai yankakken hannu yayi baya da hular bai sata a kanshi ba sai farin slippers mai taushi sosai dake sanye a farar k'afarshi, sweet ce a bakinshi yaketa faman tsotsa kamar wani yaron goye, ido ya zaro sosai lokacin da idanunshi sukayi tozali da Yah Ameen dake tsaye yana wurga masa wani irin kallo da sauri yayi baya Yah Ameen yabi bayanshi, tsaye yayi a tsakiyar falon ya wani had'e rai yana kallon Ameen daya zauna kan kujera da shima d'in yake masa kallo mai kama da harara.
"Malam samu guri ka zauna magana zamuyi dakai". Yah Ameen yace
Ba musu kuwa ya zauna d'in a kujerar kusa da Yah Ameen d'in shiru ya biyo baya kafin Yah Ameen ya katse shirun da fad'in
"Meka aikata haka Abdallah? wane irin hukunci ne haka ka yanke batare dakayi tunanin meye zaije yadawo ba?". cewar Ameen yana k'urawa Abdallah ido.
"Haba Yah Ameen bakaji abinda suke shirin yimin bane for God sake taya za'ayi min haka saikace wata mace ko wanda yazo irin zamanin da d'in nan kum........"Hakan dakayi a tunaninka shine daidai? kokuma shine maslahar dakake ganin zata fissheka? Yah Ameen ya katse masa maganar daya fara, kasan irin tashin hankalin dasu Ammi suka shiga kuwa haba Abdallah kasan girman hakkin iyaye akan y'ay'ansu kuwa ya kamata ka tsaya kayi tunani su Ammi basu cancanci haka daga wajenka ba dan ALLAH ka karb'i tayin da sukayi maka na auren Janaan karka watsa musu k'asa a ido ALLAH ya gani nima inason aurenku da Janaan saboda yarinyar akwai hankali ga hak'uri please Abdallah". Cikin sigar lallashi Yah Ameen ya k'arasa maganar yana kallon Abdallah dayake ta faman had'e rai yana d'an tura baki, a marairaice yace
"To saboda ALLAH kuma sai ayimin haka Yah Ameen? nifa yarinyar nan matsayin k'anwa na d'auketa kuma yanzu sai ace za'a had'ani aure da ita". Murmushi Yah Ameen yayi yace
"Ai ikon dasuke dashi a kanka shiyasa har sukayi tunanin hakan, Abdallah iyaye ba abin wasa bane karkayi abinda daga baya zakazo kana dana sani ka amince?". Ga mamakinshi saiyaga Abdallahn ya d'aga kai alamun ya yarda, lallai dole yayi mamaki saboda sanin halinshi na taurin kan tsiya da shegiyar kafiya amma kuma harya yarda yanzu. Cikeda farin ciki Yah Ameen yace
"Masha ALLAH thank you very very much my brother yanzu ka tashi ka shirya muje kabasu hak'uri ka kuma fad'a musu ka amince da duk zab'in da sukayi maka shine daidai".
Tsaye ya tashi ya shiga bedroom d'in Habeeb bayan y'an wasu mintuna ya fito ya shirya cikin wandon jeans blue black da dark blue d'in riga mai dogon hannu, sai baza k'amshi yake a gaba Yah Ameen ya tasashi suka fito ya rufe part d'in maigadi yabawa key d'in ya shiga motar Yah Ameen suka tafi da niyyar zai dawo ya d'auki tashi motar dake gidan.
Suna tafe a hanya Yah Ameen na k'ara yimasa nasiha da nuna masa falalar bin iyaye da duk maganar da suka fad'a indai bai haura shari'ar musulunci ba, shidai yayi kwance kan seat d'in daya kwantar ya tallabe k'eyarshi da hannayenshi biyun yana sauraron Yah Ameen da haka har suka k'arasa gidan.
Sosai su Ammi sukayi murna da ganinshi amma duk da haka saidata nuna masa b'acin ranta akan abinda yayi ya kuma bata hak'uri hakama Ayyah da kuma Abbie daya dawo gidan bayan shigowar su.
Janaan kuwa tunda taji shigowar shi gabanta yake fad'uwa kasa fita ma tayi sam saisu Hassana ne sukaje suka masa barka da dawowa itadai tana d'aki tana faman sak'e sak'e a ranta.
Mrs Salees Mu'az ๐
2/24/22, 16:22 - Ummi Tandama๐: *WATA SOYAYYA* ๐
Page 24.
Paid book
Oum Hanan
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*
Gudu gudu sauri sauri haka ta dingayi yana binta, shidai Baba maigadi da kallo kawai ya bisu baiyi azarb'ab'in tare Abdallah ko dakatar dashi ba saboda yanayin yadda yaga Abdallahn duk da yana girmama shi da ganin mutuncin shi amma yasan tsaf zai iya fad'a masa wata maganar da zata dad'e tana masa ciwo dan bai iya saita kanshi ba yayin dayayi fushi.
Tana k'arasawa bakin k'ofar falon shima ya k'arasa ganin batada sauran wani gudu kuma kawai tayi surrender so take tayi masa bayani yadda zai fahimceta amma tasan bazai bata wannan damar ba.
"Ni zaki rainawa hankali Janaan? dan ubanki sa'anki ne ni ko abokin wasanki da har zaki tsaya da wani a waje bayan dasa ranata a kanki har kina masa dariya". ya k'are maganar yana nuna k'irjinshi da hannunshi d'aya d'ayan kuma rik'e da belt d'in, kai kawai take girgiza masa ta rufe bakinta da hannunta tana k'unshe kukanta, kyawawan mari biyu ya sauke mata a kuncinta na hagu dana dama wanda ya gigita tunaninta, belt d'in ya d'aga zai kai mata duka ta k'wak'ume k'ofar tamkar zata shige cikinta tareda sakin wata siririyar k'ara mai k'arfi wadda Ayyah da Ammi da suke zaune a falon sukaji ta da sauri kuwa suka taso suka bud'e k'ofar dan ganin abinda yake faruwa. Saboda yadda ta matse da jikin k'ofar hakan yasa su Ammi na bud'ewa tayi taga taga zata fad'i k'asa saida Ayyah tayi saurin rik'ota ta had'ata da jikinta, a rud'e Ammi ke fad'in
"Lafiya Modibbo meya faru meya had'aka da Janaan d'in?".
"Ammi wasu take kulawa a waje ayi mata gargad'i idan ba hakaba wllhy zan karya yarinyar nan".
"Kamar ya tana kula wasu a waje?". Ayyah ta fad'a cikin rashin fahimta tana d'ago kan Janaan datake kuka sosai ga bakinta daya fashe saboda marin datasha ga fuskar tata harta fara d'agawa.
Cikin kuka Janaan tace
"Ayyah Anas nefa wani d'an layin nan muke school d'aya shine yau na biyosu ban tsaya jiran driver ba shinefa na manta handout d'ina a motar ya fito ya kawomin".
A fusace Ammi tace
"Bakada hankali ne Modibbo, kan wannan abin zaka mata irin wannan dukan? mahaukacin inane kai? dan ubanka aure aka d'aura maka da ita dazaka yiwa mutane wannan haukan?".
"Ammi ninaga abinda nagani dariya fa yarinyar nan take masa wato ga banza mahaukaci ta ajiye a gefe na rantse idan na k'ara ganinta dawani abinda zan mata saiya zarce wannan dan ubanta". cikin huci ya k'are maganar yana k'ok'arin maida belt d'in k'ugunshi.
"Zoka kasheta Modibbo, nace zoka kasheta yanzu dan ubanka shashasha marar hankali kawai, inbanda hauka kawai daga ganinta da wani a tsaye saika hauta da duka ko kayi binciken abinda ya tsayar dasu? tunda akayi maganar aurenku ka tab'a kiranta koda na minti biyar ne kunyi magana da ita a matsayinta na wadda zaka aura? shine danka ganta dawani a tsaye zakazo kana nuna wani kishi na banza da wofi to wllhy ka kiyaye ni kaji na fad'a maka sakarai kawai ka dinga sassautawa ranka kana yak'i da zuciyarka tun kafin ta kaika ta baroka".
K'ala Ayyah bata iya tofawa ba tayi tsaye kawai tana kallon zafin rai da zuciya irin na Abdallah anya basuyi wauta ba kuwa dasuka had'ashi da Janaan? ashe da labarinshi kawai take ji wajen su Hassana na bala'in shi itadai nata Abdallahin ba haka yakeba sam bashida hayaniya ga hak'uri da kawaici shikuma wannan kowa ya d'ebo a zuciya? dangin uwa kona uba ALLAHU A'ALAM, ALLAH masani.
Hassana da Hussaina ma wad'anda suka fito tun d'azu saboda hayaniyar dasukaji na tashi a k'ofar falo, jikinsu banda tsuma ba abinda yake saboda tsoro, Janaan kam har yanzu hawaye take tana kuka k'asa k'asa Ayyah na d'an bubbuga bayanta alamun rarrashi.
Hannun Janaan Ayyah ta kama suka koma cikin falon Ammi tabi bayansu da sauri suma su Hassana suka take musu baya tun kafin yayo kansu su shiga uku.
Ido ya lumshe ya shiga sauke numfashi a hankali a jere a jere kafin daga bisani ya nufi part d'insa yana k'ara gyara zaman agogon hannunshi na fata daya karkace.
Zazzaune suke a falon bakajin sautin komai sai kukan Janaan k'asa k'asa, har lokacin tana jikin Ayyah.
Numfashi Ayyah ta sauke tace
"Yau naga bala'i ganin idanuna haka dama maigidan nan nawa yake Hafsat?".
'Hmm gara dai da kika gani da idanunki tsohuwa da idan muna fad'a miki halinshi ai gwasalemu kike kega mai sunan mijinki'. Hassana ce tayi maganar cikin ranta tana tuna lokaci zuwa lokaci idan suka kaiwa Ayyah ziyara a yola idan suna mata hirar Yah Abdallah bashida dad'in zama saita faman kareshi tana ita maigidanta ba haka yakeba. Cikeda damuwa Ammi tace
"Wllhy Ayyah lamarin Modibbo ya wuce duk yadda kike tunani abinda yasa na k'arfafa yin auren nashi kenan bansan ina ya kwaso wannan bak'ar zuciyar tashi ba iya sanina dai mai sunanshi ba haka yakeba yanzu dan ALLAH kuduba abinda yayi mata?".
Kai kawai Ayyah ta shiga jinjinawa tana shirin magana Janaan tace
"Ammi bafa ni kad'ai yayiwa haka ba".
Idanuwa duk suka zaro Ammi tace
"Ban ganeba me yayi masa Janaan?".
Sai data share hawaye sannan tace
"Ammi wllhy bakuga dukan dayayi masa ba da k'yar Baba maigadi dayaji hayaniya ya lek'o da kuma driver'n su suka k'waceshi suka sashi a mota".
"Innalillahi wa inna ilaihi rajioun". Ammi ta fad'a tana dafe goshinta, Ayyah ma kai ta dafe tana girgiza kai, kai jama'a Abdallah kanshi d'aya kuwa? anya ba abinda ke damun k'wak'walwar shi kuwa?.
"Yaron d'an gidan waye?". Ammi ta tambayi Janaan.
Kafin Janaan tayi magana Hussaina tace
"D'an gidan Alh Hamisu ne Ammi". Kai kawai Ammi ta jinjina batace komaiba.
Kallon su Hassana Ammi tayi dasukayi tsuru tsuru tace
"Kuje ku rakata tayi wanka sai akai mata abinci taci ta kwanta ta huta".
Da 'Toh' suka amsa suka mik'e Janaan ma ta tashi suka nufi bedroom d'insu.
"ALLAH dai ya sanyaya masa zuciyarshi wannan masifa dame tai kama, irinsu ne suke d'aukar mataki cikin fushi daga baya suzo suna dana sani". Ayyah tayi maganar tana kallon Ammi datayi tagumi.
"Amin dai Ayyah, ni tunanina ma yaron nan bansan ya zamuyi dasuba hankalina duk ya tashi wllhy".
"Ah dole fa za'aje a basu hak'uri tunda anyi musu laifi bari baban nasu yadawo saiyaje yasamu mahaifin yaron".
"Shikenan Ayyah". Ammi ta fad'a cikin damuwa batasan yaushe Abdallah zai daina janyo musu magana ba kwanakin baya ma saida akayi wani case da iyayen wani yaro dawani abu ya tab'a had'osu ya masa dukan tsiya hardasu rauni yayi masa case d'in har police station saida akaje da k'yar dai Abbie yasamu case d'in ya mutu bayan yayiwa Abdallah gargad'in karya sake ya k'ara janyo musu fitina idan kuma ya janyo d'in zasu k'yaleshi da hukuma suyi duk abinda sukaga dama dashi babbar matsalar ma kuma shi baya tsoron hukumar a hakan ma kuma ana d'aga masa k'afa ne saboda mahaifinshi Alh Basheer wanda ake ganin k'ima da mutuncin shi a garin dama k'asar baki d'aya.
Wanka Janaan tayi ta fito ta shirya cikin doguwar rigar plain material mara nauyi orange color tasa hula orange tayi sallah, tana idarwa Hassana ta mik'a mata plate d'in abincin data zubo mata jallof d'in macaroni da kifi, kai ta girgiza cikin sanyin murya tace
"Bazan iya ciba bakina ba dad'i sanyi ma nakeji kamar zazzab'i ke son rufeni ga kaina yana min ciwo sosai". ta ida maganar tana k'ara rufe jikinta da hijabin jikinta datayi sallah.
Gaba d'ayansu tausayinta ne ya kamasu dama wannan uban marin datasha ai dole kai yayi ciwo gaskiya lamarin nan da buk'atar su Abbie su k'ara dubashi tun kafin fa ayi auren kenan inaga anyi ankai masa ita gidanshi?.
"Please sister kici ko kad'an ne dan ALLAH kinga fa haka kika fita d'azu ma da safe bakiyi breakfast ba". Hassana ta fad'a tana k'ara mik'a mata plate d'in, Hussaina ma baki tasa suka cigaba da rarrashinta da k'ara kwantar mata da hankali da haka suka samu ta d'an yafici abincin kad'an tasha paracetamol ta kwanta.
Bai kara shigowa gidan ba fita yayi ya shigo da motarshi cikin compound ya koma part d'inshi, wanka yayi, yayi sallah ya kwanta batare daya tuna da abinda yayi ba danshi da iya gaskiyarshi yayi hakan kuma bawai don yana sonta ko kishinta yayiba kawai gani yake ta raina masa hankali ne inba rainin hankali ba taya ansa musu date d'in biki kuma tazo kan layi tana kula wani harda yimasa dariya? sai yanzu yakejin wani takaici ma dabai lakad'a mata dukan tsiya ba ta yadda bazata k'ara marmarin kula wani ba.
Da wuri yau Abbie ya dawo kamar yasan abinda yaronshi yayi, Ammi bataso sanar dashi ba lokacin so tayi saiyaci abinci ya huta sannan ta fad'a masa rashin mutuncin da Abdallah yayi amma ganin yadda yanayin ta yake alamun tana cikin damuwa yasa ya tambayeta abinda yake damunta haka tunda bai saba ganinta hakaba dan Ammi macece mai sakin fuska da fara'a ga mutanen gidan da duk wanda zama ya had'asu da ita.
Nannauyan numfashi Abbie ya sauke yace
"Wai dan ALLAH meke damun Modibbo ne Hafsat? inbanda shirme da shashanci daga zuwa saika hau mutum da duka batare da binciken abinda ya tsayar dasu d'in ba shi idan baiyi neman magana ba bayajin dad'i, tsaki ya k'ara saki yana sauke numfashi ya zaro waya a aljihu yafara laluben number Abdallah yana fad'in
"Bari in kirashi yazo muje yabasu hak'uri dan ubanshi tunda shi bayajin magana".
Baikai ga kiran number ba Baba maigadi yayi sallama daga bakin k'ofar falon, Abbie ya bashi iznin shiga.
Shigowa yayi ya tsuguna daga can bakin k'ofa yace
"Barka da hutawa Alh".
"Yauwa barka dai Baba lafiya dai ko?".
"Eh to Alh wannan mak'ocin namune yace ayi masa iso gurinka zakuyi magana Alh Hamisu".
"Okay, shikenan gani nan fitowa".
Tashi Baba maigadi yayi ya fita bayan ya amsawa Abbie.
"Kingani ko Hafsat? yanzu ina amfanin haka dan ALLAH". Abbie ya fad'a rai a b'ace yana kallon Ammi.
Kai ta girgiza tace
"Babu fa ayi hak'uri dai Abbie kaje ka sameshi d'in".
Tashi Abbie yayi ya gyara babbar rigar shaddar dake jikinshi sannan ya fita kiran da Alh Hamisu yake masa.
A compound d'in ya sameshi zaune kan fararen kujerun dake kusa da wasu shuke shuken furanni, bakinshi d'auke da sallama ya k'arasa wajen tareda mik'a masa hannu sukayi musabaha.
Mrs Salees Mu'az ๐
3/2/22, 08:19 - Ummi Tandama๐: *WATA SOYAYYA* ๐
Page 25.
Paid book
Oum Hanan
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*
Shima Abbie kujera yaja ya zauna suka shiga gaisawa da tambayar iyalai dakuma kasuwa duk a mutunce, shiru suka d'anyi nawasu y'an sakonni kafin Alh Hamisu ya katse shirun nasu da fad'in
"Wato Alh Basheer d'azu bayan nadawo office nakejin wani labari a gurin iyalina wanda sam banji dad'in shiba shine nace bari dai inzo inji yadda batun yake da kuma abinda ya faru tsakanin yaron wajena da naka yaron kar in yanke hukunci cikin rashin sani dan dukan nan saidaya kaishi ga asibiti".
"Gaskiya ne Alh Hamisu yaron wajenka bashida laifi ko kad'an babban mai laifin Modibbo ne kuma koda bakazo ba zan taso k'eyar shi muzo har gida mubaka hak'uri, anan Abbie ya zayyanawa Alh Hamisu abinda ya faru kamar yadda Ammi ta fad'a masa ya d'ora da neman afwarshi.
"Ba komai Alh Basheer ALLAH ya kiyaye gaba bari in koma". ya ida maganar yana mik'ewa tsaye tareda k'ara bawa Abbie hannu suka k'ara gaisawa Abbie yace
"Ya kamata mu shiga dakai ciki iyalina su k'ara baka hak'uri dan haka nazo nasame su cikin damuwar abinda yayi mahaifiyata ma har gida tace zataje".
Alh Hamisu ma cewa yayi basai ya shigaba komai ya riga ya wuce amma Abbie ya takura masa dole sai sun shiga haka dole yabi bayan Abbien zuwa general parlor na gidan.
Har lokacin Ammi tana zaune a falon cikin zullumi dan batasan da abinda Alh Hamisun yazoba, amma ganin yanayin fuskarshi a sake kamar ma wani abu bai faruba yasa taji tasamu nutsuwa, a mutunce suka gaisa dashi tabashi hak'uri Abbie yace ta kirawo Ayyah ma su gaisa.
Ayyah ma tazo sun gaisa itama ta bada nata hak'urin yace