Author : Maryam Ibraheem Aleeyu Category : Hausa Novels 001
2, 2022 at 12:41 pm
REPLY
An educative piece of work.
Avatar
Zainab Abdullahi barde
March 2, 2022 at 1:29 pm
REPLY
Masha Allah summy Allah yakara basira
Avatar
Umaima
March 2, 2022 at 3:06 pm
REPLY
Allah ya biyaki takorinmu.
Avatar
Bilkisu Aminu usman
March 2, 2022 at 5:02 pm
REPLY
MashaAllah,lallai akwai chakwakiya bakadan ba,muna biyeda ke Allah ykara basira da daukaka
Avatar
Zainab ibrahim Makwashi
March 2, 2022 at 8:09 pm
REPLY
Masha Allah Aunty Allah ya kara basira da zakin hannu
Avatar
SUMAYYAH ABDULKADIR
March 3, 2022 at 1:11 pm
REPLY
Nagode muku bakidaya, jazakumullah bikhair
Avatar
Hadiza Adamu
March 3, 2022 at 10:18 pm
REPLY
Masha Allah, Allah ya Kara basira
Avatar
Fatima m
March 7, 2022 at 5:25 pm
REPLY
Ma sha Allah. Allah ya qara basira
Avatar
Hafsatmusajibrin
March 20, 2022 at 9:21 am
REPLY
Kai Allah ya qara basira I so much like ur write ups
Leave a Comment
Your email address will not be published. Required fields are marked *
Name *
Email *
Website
Comment *
Save my name, email, and website in this browser for the next time I comment.
Subscribe to weekly updates
PREVIOUS
Rayuwata | Babi Na Daya
NEXT
Ta Ki Aure | Babi Na Uku
© 2022 Bakandamiya
CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×
3/21/22, 20:59 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA*💝
Page 47.
Paid book.
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.*
©Oum Hanan
Sun dad'e a haka kowanne yana aikawa da d'an uwanshi sak'on dake cikin zuciyarshi ta cikin idanuwansu a tare suka k'ara kauda kansu suka kalli P.O.P d'in saman d'akin suna sauke numfashi a tare kowanne fuskarshi d'auke da murmushi, kiran wayarshi da akayi ne yasa ya tashi zaune ya karkace yana zaro wayar a aljihun wandonshi itama tashi tayi tana kallonshi yadda yake gyad'a kai yanata rangaji daga zaunen saboda dad'in wak'ar dayake ji wadda kuma itace akan ring tone d'in nashi wak'ar Nura M Inuwa wadda yake cewa (Wanda baiso ku tambayeshi dame yake more rayuwa abadan bana daina yin so gaskiya ko dame yazo mini). Yana son wak'ar sosai har wayar ta katse baiyi picking ba aka k'ara kira sai lokacin ya d'aga tareda rungumo Jauhar ta gefenshi ya fara magana cikin harshen turanci, yana wayar yana sakarwa Jauhar kisses a gashinta da goshinta zuwa fuskarta harya gama ya kashe wayar tashi yayi ya nufi wata speaker dake d'akin yayi connecting da wayarshi yasa wak'a speaker tafara dukan kid'a mai dad'i Jauhar dai na zaune bakin gado tana kallon ikon ALLAH taga me Yah Abdallah zaiyi kawai taga yafara taka rawa yana fad'in "kwana biyu bai d'an taka ba". wato duniyar dai tayi masa dad'i kenan😂 rawar shi yake bilhaqqi da gaskiya cikin kwanciyar hankali sai dariya Jauhar take masa. Hannu ya mik'o mata yana d'age mata gira alamun ta taho itama tayi kafad'a ta nok'e masa alamun a'a tana dariya har inda take ya k'araso yana rawarshi ya janyo hannunta ta taso ya fara malk'waya hannayenta yana juyi da ita irin na India tun tana nok'ewa har itama wak'ar tafara tsumata dan haka suka cigaba da takawa tare yana rawar amma bakinshi bai zauna k'alau ba sai kissing d'inta yake.
Ammi da takaicinsu yasa ta komawa falo ta zauna saiji tayi kid'a na tashi daga bedroom d'inta ba k'akk'autawa da sauri ta tashi ta haura upstairs d'in dan duk zatonta ko Abdallah ne yake dukan Jauhar shine ya kunna kid'a saboda kar ajishi sarai kuma tasan zai iya amma abin mamaki da ban haushi tana bud'e k'ofar ta shiga ta samesu sunata rawa hankalinsu kwance tamkar su kad'ai ne a gidan tsaye tayi tasaki baki tana kallonsu dan duk basu kula ma da zuwanta ba amma dai yaran nan sun iya tsiya wllhy yanzu fa data fita ta barsu suna fad'a amma tadawo ta gansu sunsa kid'a sunata tik'ar rawa? lallai idan mutum ya biye musu zaisha kunya saisu sawa mutum hawan jini, Jauhar ce tafara ankarewa da Ammi dake tsaye bakin k'ofa tana kallonsu hakan yasa ta daina rawar shikam Abdallah da hankalinshi baikai kaiba sai juyi yake yana k'ara juya Jauhar ganin ta tsaya a hankali murya k'asa k'asa tace
"Yah Abdallah Ammi ce ta shigo fa tana bakin k'ofa". da sauri ya tsaya tareda kai kallonshi bakin k'ofar yaga Ammi kuwa a tsaye kai ya d'an sunkuyar yana shafa k'eya yana d'an murmushi sukayi tsaye a wajen, k'arasa shigowa Ammi tayi tana fad'in
"To kuzo ku wuce kutafi gidanku bada niba wannan kayan takaicin". ta k'are maganar tana nuna musu hanyar fita daga bedroom d'in da hannunta, marairaicewa Jauhar tayi tace
"Ammi shinefa yace saina biyashi wayarshi amma idan nayi rawa zai yafemin".
Ido Abdallah ya zaro yace
"Wllhy Ammi k'arya yarinyar nan take ita t......dakatar dashi Ammi tayi tace
"Koma dai meye ku kuka sani kuzo kubar gidan nan wllhy bazaku samin hawan jini ba ina zaman zamana wllhy maganar da kuke sani kosu Irfaan albarka kuma na k'ara ganin k'afafunku nan kusa a gidan nan saina b'ata muku rai kuzo ku wuce kuje can gidanku ku k'arata". A tare suka koma wajen gadon ya d'auki glasses d'inshi da P Cap da key d'in motarshi ya fita daga bedroom d'in yana cewa Ammi sai anjima bata kulashi ba sai kallo data bishi dashi itama Jauhar d'ankwalinta ta d'aura ta yafa mayafinta ta d'auki jakarta kanta a k'asa tazo tayiwa Ammin sallama ta fita sai yanzu take k'ara jin kunyar rawar da Ammi ta samesu sunayi duk Yah Abdallah ne ya jawo mata wllhy.
Sai bayan fitarsu nema abin yabawa Ammi dariya girgiza kai tayi ta shiga bedroom d'in tana murmushi cikin ranta tana k'ara binsu da managarciyar addu'a ta k'ara samun zaman lafiya da daidaito a tsakaninsu dakuma zuri'a dhayyibah mai albarka.
D'akin Ayyah sukaje Abdallah ya gaisheta yaga yaranshi daga nan ma tare suka fita dasu Janaan d'in yace Ayyah ta fad'awa Ammi zasuje sudawo yaran kuwa sai murna suke.
Suna tafe suna hirarsu irin ta masoya cikin nishad'i da annashuwa har tafawa suke idan abin yayi musu dad'i, ba zato kuma taji ya bige mata baki yana fad'in shine tayi masa k'arya a wajen Ammi ko tace shiya sata rawa.
Baki ta tura masa cikin shagwab'a tace
"ALLAH Sweetheart ka cika cin zali wllhy". Hannun da baya tuk'i dashi yasa ya matse mata hannu cikeda mugunta harda cije lips d'inshi ta saki k'aramar k'ara kuwa tana yarfe hannu tare dasa masa kukan shagwab'a saidaya k'ara matse hannun sosai sannan ya sakeshi yasa hannu ya rungumo kafad'unta yana d'an jijjigata gamida cewa
"I'm sorry RAYUWA TAH na yarda yau kibani punishment a gado yadda nake baki kinji y'ar albarka". ya ida maganar yana sumbatar goshinta, duk abinda suke hankalin yaran ma gaba d'aya baya kansu yana can wajen game da suke bugawa.
Wani irin kallo tayi masa na sama da k'asa kafin tace
"Lallai ma Sweetheart to nak'i wayon, kaima dakake min wannan punishing d'in ALLAH na ganinka kuma saiya sakamin". ta k'are maganar cikin tura baki kamar zatayi kuka tana jefa masa hararar wasa.
Dariya yasa sosai har yana d'an dukan sitarin motar da hannunshi yace
"ALLAH kinga gurin kwanana yarinyar amma bari mu koma gida zan saita miki zamanki sosai". baki kawai ta gatsina masa tareda kai hannu ta shafi sajen fuskarshi wanda yake matuk'ar burgeta shikuma yaja karan hancinta fuskarshi d'auke da murmushi kafin ya maida hankalinshi kan tuk'in dayake.
Yawo suka sha sosai a ranar sun zazzagaya park park na shak'atawa sunsha ice cream sannan suka tsaya a wani babban boutique clothing store ya jidar musu kayan sawa da takalma tamkar wad'anda suke fatararsu, daga kuma suka zarce wani babban super market ya dinga jidar musu uban kayan zak'i dasu biscuits kamar hauka har saida Jauhar ta gaza yin shiru da bakinta tace
"Kai jama'a Yah Abdallah dan ALLAH a dinga tausayin kud'i haba". harara ya dalla mata yace
"Ina ruwanki malama kud'inki ko nawa banason sa ido fa". yadda ta saba gatsina masa baki haka ma tayi masa a lokacin yayi k'wafa kuwa yana kad'a kai yace
"Ni kikewa haka ko? ALLAH ya kaimu gida lafiya saina kusa karkatar miki dashi ta yadda idan akace watarana kiyimin haka baza kiyiba". Gaba tayi tana fad'in itama haka zatayiwa nashi, duk dariya mutanen dake wajen sukayi kafin sukazo wajen biya ya biya kud'in suka tafi.
Bayan sun maida yaran ma gida ba gida suka nufa ba sunje gidan Aunt Deejah da gidan Aunt Jeeddah dakuma Aunt Mabrookah suka dire kuma a gidan Habeeb lokacin ma Habeeb d'in yana gida murna a wajen Hussaina kamar me ta rungume Jauhar cikin jin dad'in zuwansu nan ta shiga cika musu gabansu da lemuka da kayan ciye ciye ta tsuguna har k'asa tana gaida Abdallah amsawa yayi yana k'are mata kallo ganin yadda duk tabi ta rame sai dogon hancinsu irin na gado daya k'ara fitowa sosai apple juice ya d'auka yana bud'ewa yace
"Ke meya ramar dake haka? kai dan ubanka me kake mata?". maganar yana kallon Habeeb, kafin Habeeb yayi magana ya k'ara juyawa wajen Hussaina yace
"Fadamin gaskiya idan yana miki wani abu inci miki ubanshi yanzun nan, goshi Jauhar ta dafe tana d'an girgiza kai ALLAH ya shirya mata wannan mijin nata idan ba Abdallah ba waye zaizo har gidan mace ya dinga zagin mijinta a gabanta, k'asa Hussaina ta k'ara yi da kanta tace
"Ba komai Yah Abdallah banida lafiya ne wlhy". juyawa yayi ya kalli Habeeb yace
"Shege ai tunda naga idanunka nasan bakada gaskiya hala har ka d'irka mata ciki ne". wata masifaffiyar kunya ce ta kama Jauhar da Hussaina suka sunkuyar dakai Habeeb ma kunyar ce ta kamashi ganin ga Jauhar a wajen ya maze dai yana murmushin yak'e yana kallon Hussaina da kanta ke k'asa, shikam gogan baisan ma sunayi ba lemonshi kawai yake sipping hankali kwance ya bararraje akan kujera ko kunya bayaji gidan k'anwa ne 🤦.
'Gaskiya bakin Yah Abdallah bai gasu ba sam lokacin da yana jariri' Jauhar ta ayyana a ranta ta mik'e tsaye ta kamo hannun Hussaina tace tazo su shiga daga ciki kafin ya k'ara b'aro musu wata maganar datafi k'arfinsu.
"Kai dai kaji kunya wllhy, banza ko kunyata bakaji kake irin wannan maganar a gabana".
Kai tsaye Abdallah yace
"Ubana ne kai da zanji kunyarka? jiya ma munyi waya da Abdallah yace suna hospital Hassana ba lafiya itama nasan bai wuce cikin ba shegu jarababbu". Hararar shi Habeeb yayi yace
"Kai ubanwa yafika jaraba ma A.B Madugu fad'awa wanda bai saniba". dariya Abdallah yayi bai dai maida martani ba suka cigaba da hirarsu irin ta aminai da suka dad'e tare ayi fad'a a shirya kuma duk yawancin fad'an Abdallah ne yake janshi dayake Habeeb d'in ya karance shi kuma yaci maganin zama dashi abubuwa dayawa idan yayi masa ko d'aga kai bayayi bare ya kalleshi.
Sai bayan sallahr Esha'e sannan suka bar gidan Jauhar tayi matuk'ar gajiya dan ba k'arya sun yawatu yau d'in nan ta langab'e a jikinshi zata masa barci yace sam bata isaba shi dayake ta garari yana tuk'in baice yagaji zaiyi barci ba sai ita aikuwa tashi zatayi dolenta ta tashin tana murza ido barci da gajiya sun had'e mata.
Suna komawa wanka sukayi tare sukayi shirin barci, ganin take takenshi yana neman wani abu a wajenta ya hanata sakat yasa ta marairaice masa tace
"Haba Yah Modibbo dan ALLAH ka tausaya min mana ka barni in huta bakaga yadda kayi min d'azu bane gashi yanzu munsha yawo duk mun gaji".
"Malama ki bani hakk'ina kawai, kedai kika gaji amma ban dani dayake yawone ai kin iya bina to saina fanshe ladan wahalar tuk'a ki d'in danayi". yace yana d'ora k'afarshi kan cinyoyinta dake mik'e samb'el ba abinda ya rufesu dan wandon kayan barcin da kad'an ya wuce pant.
"Please kibani ko d'ayane sai in hak'ura ko cikin dare ne na k'ara wani".
Shure shuren k'afafu ta fara lokaci d'aya tana sa masa kukan shagwab'a wanda ta k'ara rikitashi, shima k'asa yayi sosai da murya ya shagwab'e mata yace
"Please My sugar nine fa Abdallahn nan naki bawan ALLAH". Dariya tayi tace
"To saika fad'i wani abu daidai tukunna".
"Meye shi?". Ya tambaya yana k'ara nanik'arta kawai dai yana biye mata ne bawai dan idan ta hanashi d'in zai hanu ba.
"Fad'i Jauhar zaka fad'a daidai".
"Meye abin wahala a sunan naki? Nace Jauhar to". Ya fad'a da harafin 'R' d'inshi da bata fita daidai. Dariya tasa sosai tana fad'in
"Eyyah ka fad'i Yah Abdallah ba daidai ka fad'a ba kai yanzu Jauhar d'in ne yake maka wahala?". Ita a dole wayo take so tayi masa harya gaji yabar maganar kusantar ta, zabura yayi ya haye kanta gaba d'ayanshi yana fad'in
"Ke nabi Jauhar da.......Batare daya k'arasa ba ya zura bakinshi a nata ya cafko harshenta yafara masa wani salo daya hargitsa Jauhar wadda batare data saniba ta biye masa suka shiga farantawa juna rai.
Mrs Salees Mu'az 💝
3/22/22, 19:29 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝
Page 48. THE END.
Paid book.
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.*
©Oum Hanan.
Washegari da k'yar Jauhar ta iya tashi saboda tsamin da jikinta yayi ga gajiyar yawon da suka sha ga kuma wadda Abdallah ya tara mata dan barcinsu rabi da rabi ne a wannan daren duk yabi ya addabeta da fitinarshi. Langab'e masa tayi tace ba abinda zata iyayi wlhy jikinta ko ina ciwo yake dan haka da kanshi ya shiga kitchen safiyar ranar yayi musu breakfast duk da dai tea ne kawai ya dafa shima baiyi irin na Jauhar ba sai wainar k'wai daya soya wadda itama duk ta fara k'onewa ya shirya a dinning table ya shiga gyaran gidan duk tana lafe cikin bargo barci take so tayi duk ya hanata da uwar kwarafniya shi bai yadda ba aiki yake, tashi tayi ta sauko daga kan gadon ta fito falon.
Tsakiyar falon ta hangeshi daga shi sai bak'in gajeren wando yana mopping duk ya had'a uban gumi batasan lokacin data tuntsure da dariya ba harda tafa hannu tace
"Oh yau maza na aiki fa a gidan nan gaba d'aya an hanamu zaman lafiya".
D'agowa yayi yana cije baki tareda sakin k'wafa yace
"Idan ban sakar miki aikinki ba kice ba sunana Abdallah ba ya zan tak'ark'are ina miki bauta kizo kina min dariya ko sannu babu". Baki ta dafe tana k'unshe dariyarta da hannu d'aya d'ayan kuma tana d'aga masa shi alamun bada hak'uri saida ya saki wata k'wafar sannan ya cigaba dayi, d'aya daga cikin k'ayatattun kujerun dinning inda take tsaye taja ta zauna tana kallonshi tana k'unshe dariyarta dan karya ganta da anyi kad'an sai a tashi tsaye a rik'e k'ugu ana goge gumi abin dole yabaka dariya, ai gara dai kaji yadda akeji in ana aikin, nan akayi ta fama dashi ya yarda a d'auko y'ar aiki yace sam bai yardaba shi baya ra'ayin y'ar aiki ba yadda ba'ayi dashi ba yace bayaso kuma dama tun lokacin Janaan wani zuwa datayi tazo gidan taga yadda take shan aiki ga girki ga gyaran gida tace mata ya kamata a samo mata y'ar aiki wadda zata dinga tayata aikace aikacen gida koda batayi mata girki ba Janaan tace ai Yah Abdallah ne bayaso shiyasa bata d'auka ba tayi masa maganar yace bayaso, baki kawai ta tab'e a lokacin gani take idan itace bai isa yayi mata wannan mulkin ba dan dai yasamu Janaan d'in ne saigashi itama ya hana d'in kuma ta hanu d'in farko dai taso tayi masa bore taga dai ya fita bala'i dole ita ta rissina ta mik'a wuya dan a zauna lafiya, amma magana ta gaskiya dai tana shan aiki gyaran gidan ma kad'ai wani uban aikine amma idan ta tuna bautar aure take kuma ta hakane zata samu lada sai taji baya damunta. Magana ta gaskiya Janaan ba k'aramin hak'uri tayi da bawan ALLAHn nan ba sai yanzu take k'ara tabbatar da hakan datake zaune dashi musamman ita Janaan da batada baki bata iya masifa ba ita d'inma datake da tsiwa da masifa dole take shafawa kanta lafiya dan bazata iya da bala'in Abdallah ba.
"Ka manta da burner Yah Abdallah". ta fad'a cikin sigar tsokana bayan yagama mopping d'in, a gajiye yace
"Meye haka kuma? shima mopping d'in akeyi dashi?".
"No abin saka turaren wuta". ta bashi amsa, harara ya zabga mata ya jefar da mopper a tsakiyar falon yace
"Aini ba bawanki bane in miki ciki in miki goyo? kwankwaso na ciwo kawai yake dan mugunta kin sani aikin daba nawa ba salon anjima idan nazo raya sunnah in kasa tab'uka komai, wuceta yayi ya shige bedroom yanata masifa kamar ita tace dole saiyayi aikin, tashi tayi ta maida mopper inda take mopping d'inma gaba d'aya saita canza wani dan bawani yi yayiba bai mata yadda yakeso ba, itama bedroom d'in ta shiga danyin wanka.
Tare sukayi wankan suka shirya tare sannan suka fito yin breakfast tafara serving d'insu, tashin farko tana zuba tea d'in taji k'amshin ya bambanta da nata, kallonshi tayi ko zaiyi magana taga hankalinshi ma gaba d'aya yana kan wayar hannunshi yana danne danne haka dai ta zuba musu madara da Milo tasaka musu cube sugar tasa tea spoon a cup d'inshi ta tura masa gabanshi, again dai tana bud'e plate d'in taga waina bak'a tana kallonta ido ta zaro tace
"Yaa subhanallah". d'agowa yayi daga kallon wayar dayake yace
"Lafiya?".
Kallon plate d'in tayi tace
"Amma Yah Abdallah meye wannan dan ALLAH haka akeyin wainar k'wai dama?".
Wayar hannunshi ya ajiye yace
"To koyamin zakiyi? y'ar iya meye bamu iyaba a girke girken naku zakimin iyayi". baki ta tura tace
"Nidai to wllhy bazan ciba".
"Karki ci d'in yarinya". yace yana janyo plate d'in ya gutsura yasa a baki ido ya dinga zarewa yana kallonta dan tashin farko wani uban gishiri ne yayi masa sallama wanda ya gauraye duk ilahirin bakinshi mai uban yawa dan lokacin dazai zuba bada spoon ya zuba ba bakin robar ya karkata ya antaya shi, ido itama ta tsura masa duk yadda yaso had'iyewa ya kasa da sauri ya furzar da ita akan dinning d'in Jauhar dariya kawai take tana kallonshi tashi taga yayi duk zatonta zuwa zaiyi ya wanke bakinshi sai gani tayi ya nufota yana zuwa ya d'auketa cak d'inta ya d'ora