Chapter 24 Reading Wata Soyayya Complete Hausa Novels by Maryam Ibraheem Aleeyu.txt Arewa Novels

Wata Soyayya Complete Hausa Novels by Maryam Ibraheem Aleeyu.txt

Author :  Maryam Ibraheem Aleeyu Category :  Hausa Novels 001

Chapter   24 / 31

69K to 72K   out of 90.9K words

faman ture turen baki tace
"Tashi ki maida min sak'ona bedroom d'ina idan su Hassana suka dawo su saisu kai".
"An fasa kaiwa Ammi?". Jauhar ta tambayeta, cikin gatse Ammi tace
"Eh tunda wanda yafi kowa iko dake ya hana ai dole ki hanu tashi ki maidamin abuna. Abdallah daya san dashi Ammi take baiyi magana ba sai sajenshi daya shiga shafawa yana tattare fatar goshinshi sama.
Tashi Jauhar tayi ta kalli Abdallah da shima yake kallonta wani irin kallo tayi masa sannan ta nufi upstairs dan maidawa Ammi sak'on nata, saida taje tsakiyar stairs d'in sannan ta waigo taci sa'a kuwa idanun Abdallah na kanta wata k'atuwar harara ta sakar masa tareda murgud'a masa baki, baki ya bud'e yana zaro ido kafin cikin hanzari ya haura ta bayan kujerar inda yake tsaye ya bita da gudu kan upstairs d'in da gudu itama ta kwasa, Ammi kam zaune tayi kan kujera tana kallonsu itada su Irfaan da suka shigo yanzu daga wajen Ayyah suna kallon mahaifinsu na gudu akan stairs 🤣 Ita ta rasa ma abinda zatace musu wllhy.
Da gudu ta k'arasa bedroom d'in ta banko k'ofar da k'arfi shikuma daidai lokacin daya k'arasa, tsayawa yayi cikin haki ya rik'e k'ugu yana kallon k'ofar, kai ya jinjina yana shirin barin bakin k'ofar yaji tace
"Kuma bazan yafe gudun daka sani ba Abdallah".
Murmushi yayi yana kad'a kai gamida cije lips d'inshi na k'asa yace
"Abdallah kai tsaye ko? Zan rutsaki ai kin kusa shiga hannuna, kwarkwar d'in yarinya kawai". Daga haka ya sauka downstairs, sumar kanshi ya shiga shafawa yana kallon Ammi da itama take kallonshi ya bud'ewa su little Janaan hannayenshi sun san ma'anar hakan dan haka da gudu suka nufoshi suka rungumeshi suna masa surutunsu irin na yara wanda abubuwa dayawa ba'a sanin abinda suke fad'a.
"Sannu, ALLAH ya shiryeka Modibbo ka gama gudun?".
"ALLAH Ammi yarinyar nan batada kunya kiyi mata fad'a".
Baki Ammi ta tab'e tace
"Matsalarku ce kuje can ku k'arata bazaku dinga sani magana ba kamar k'ananun yara".
Y'ar dariya kawai yayi ya sunkuyo ya sumbaci forehead d'insu sannan ya fice.

Mrs Salees Mu'az 💝
3/16/22, 20:39 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝

Page 40.
Paid book.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022.*

©Oum Hanan.


Tun daga ranar Jauhar bata k'ara bari sun had'u da Abdallah ba duk hanyar datasan zasu had'u kauce mata take har zuwa lokacin da y'an biki suka fara hallara a gidan.

Gidanshi da suka zauna da Janaan nan aka k'ara gyarawa sosai gaba d'aya kayan ciki fitar dasu akayi aka zuba wasu sabbi komai da komai wadancan kuma na Janaan d'in aka dawo dasu gidan Ammi aka zubasu a wani d'aki daba komai anan cikin compound.

Ranar alhamis da safe sukaje akayi musu gyaran gashi sannan akayi musu k'unshi.
Da yamma kuma akayi kamu anan compound d'in gidan wanda aka k'awatashi sosai inda ya cika da mutane mak'il kamar irin ranar yinin nan amare sun fito d'as inda sukayi kwalliya da kayan sak'i wanda amare kesawa kalar ja da adon bak'i a jiki light makeup akayiwa kowacce sai tashin k'amshi suke, an gabatar da kamu lafiya k'alau aka tashi daf da magreebah bayan anyi rabon abubuwa masu tafiya suka tafi masu shiga ciki suka shiga.

Jauhar harta fara gajiya duk tayi tib'is da ita tana kwance saman gado bayan tayi wanka ta d'an tsakuri abinci y'an mata ne birjik cike da d'akin y'an uwansu. Hassana da Hussaina kam ansamu dama suna can wajen angwayen su dan Abdallahn Momy Maryam ma tun ranar yazo shida wasu daga cikin abokanshi sauran mutanen kuma sai ranar d'aurin aure zasu biyo baya.
Kan dole Habeeb yayi sallama da Hussaina ya tafi saboda kiran da babanshi yake masa, wajen shiga gidane Hussaina ta had'u da Abdallah yace ta kira masa Jauhar a cikin gida da sauri ta amsa da to ta wuce kafin ya tuhumeta fitowar datayi ta tsaya da Habeeb dan tasan sarai zai iya ba ruwanshi da amintakar dake tsakaninsu da Habeeb d'in.
"Auntie Jauhar angonki fa na kira a waje". Hussaina ta fad'a lokacin datake zama gefen gadon da Jauhar take.
"Waye haka kuma?". tace cikin yatsina tana b'ata fuska bayan ta d'ago kanta.
"Ke kuji min y'ar rainin hankali angon naki ne baki saniba?". wata y'ar uwarsu ta fad'a, tsaki taja ta maida kanta tana fad'in
"Kice masa bazanzo ba". kai tsaye.
Ido Hussaina ta zaro da wasu na kusa da ita da hankalinsu ke kansu da sauri Hussaina tace
"Bazakije bafa kikace?".
"Eh ki fad'a masa haka kedai ai y'ar aike ce". Kai Hussaina ta jinjina ta tashi tana fad'in
"Kin fad'i gaskiya ni y'ar aike ce amma Yah Abdallah ba lallai ya tuna da hakan ba shiyasa zan tsaya daga baya baya in fad'a masa". ta fita daga bedroom d'in.
Tana zuwa ta fad'a masa abinda Jauhar tace, kai ya shiga kad'awa kafin yace ta tafi, wayarshi dake hannunshi yana danne danne yafara nemo number ta ya danna mata kira, Itama wayar na hannunta lokacin kiran ya shigo dayake da wani sabon sim card ya kirata bata gane number shi ba tayi picking takai kunnenta tareda yin sallama saboda masifa dake cinshi da k'yar ya amsa sallamar datayi ya fara balbala mata bala'in ta rainashi har ya aiko a kirata tace bazata zoba saboda batada mutunci, itama a fusace take fad'in
"Wai to idan nazo me zanyi maka haka nan zaka damu mutane da jarabar aike".
K'wafa yayi yace
"Haka kikace ko to ki shirya zuwana yanzun nan kinsan ba gudun abin magana nake ba wllhy tsaf zan d'auko ki kowa ya ganki kafin in fito dake nan inci uwaki tunda bakida kunya".
K'aramin tsaki taja tace
"Ina jiranka idan kuma bakazo ba baka cika sunanka Abdallah Madugu ba". daga haka ta katse wayar.
"Kutt shikenan Jauhar kin kwanto mana kura bala'i da kanshi ai bakeba muma nan idan har yazo d'akin nan tamu ta samemu dan haka wllhy ba abinda zai zaunar dani a d'akin nan karku babbaka mu da ranmu gara tun wuri in fece". wata y'ar yayan su Ammi Aliya ta fad'a tana mik'ewa tsaye tareda kama hannun Hussaina suka fita daga bedroom d'in, dayake sauran bawani cikakken sani suka yimasa ba itama d'in wani zuwa ne daya tab'a yi Yola yakai musu ziyara aikuwa duk saida ya gallabi y'an gidan akwai yayyenta mata masu jida kansu marasa jin magana duk saidaya saita musu zama a lokacin tun daga nan suke shakkar shi, Abdallah case 🤦😂.

D'an yatsanshi ya ciza lallai ma yarinyar nan baisan meyasa ta rainashi har haka ba bari ta shigo hannunshi zatasan da wanda takeyi, cikeda karsashi ya tashi ya nufi hanyar dazata sadashi da cikin falon zai nuna mata shi Abdallah Madugu ne, yana shiga falon yaga mata da yawa wasu na kallo wasu cin abinci yayin da wasu sukayi group sai zabga hira ake ta y'an uwantaka, bai tankawa kowa ba ya nufi hanyar dazai isa bedroom d'in Jauhar sukaci karo da Ammi itakuma zata fito baya yayi yana y'an kame kame ganin yadda Ammi ta tsura masa ido da alamun tambaya a fuskarta.
"Ina zakaje da daren nan Modibbo?".
Hannu yakai kan lallausar sumar kanshi ya shiga shafawa d'ayan kuma ya cusashi a aljihun wandonshi yace
"Ammi wajen yarinyar nan mana wai har in aiko a kiramin ita tace bazata zoba tsabar ta raina ni Ammi". galala Ammi ta tsaya tana kallonshi kafin tace
"To daka taho nan zuwa zakayi ka d'aukota kokuma dai me zakayi?".
Ba rissinawa ba komai yace
"Eh Ammi zan gyara mata zamane naga rainin hankalin nata ya wuce misali". Tsaki Ammi taja ta nuna masa hanyar fita tana fad'in
"Dallah malam wuce ka tafi harkar ka kiran uban me kake mata da daren nan harda tasowa wai kazo ka d'auketa saboda bakada kunya wai dan ALLAH Modibbo yaushe zaka girma ne ka daina abinda kake?". Baki ya tura yace
"Dan ALLAH Ammi ki k'yaleni da.......hanyar fita data k'ara nuna masa yasa yayi shiru ya juya ya fita daga falon, da kallo Ammi ta bishi tana girgiza kai tasan halin kayanta shi yanzu ba abin kunya bane a gurinshi ya d'auko Jauhar duk uban mutanen nan yazo ya keta ta cikinsu ba ALLAH dai ya zaunar dasu lafiya inba hakaba wllhy za'a ga kwamacala kala kala ita Jauhar rashin kunya shikuma ba hak'uri da rangwame ko yaya akayi masa abu saiya rama haka zaije yaita wahalar da ita a banza indai bata daina yimasa rashin kunya ba zata sameta kuma tayi mata magana rashin kunyar datake masa tayi yawa inzata gyara ta gyara idan kuma bazata gyara ba to itace a wahale.
Yana fita yaga har lokacin Abdallah da Hassana suna nan anata lobayya, wajen ya nufa a fili yake fad'in
"Kaima tashi zakayi dan ubanka tunda nima ban yiba, tunda Hassana taga ya nufosu gabanta ya shiga fad'uwa tun kafin ya k'araso ma ta mik'e tsaye dan tasan sauran zancen yana zuwa kuwa yace mata
"Ke dan ubanki wuce ki shiga gida". da sauri kuwa tabar wajen jikinta na rawa, harara Abdallahn Momy Maryam ya zabga masa yace
"Malam ya haka daga zuwa zaka korar min mata bayan bamu gama soyayyar mu ba".
"Ai yadda banyi ba ba ubanda ya isa yayi wllhy shima wancan d'an iskan daya nan wlhy saina koreshi". ya fad'a yana zama kusa da Abdallahn, tsaki Abdallahn Momy Maryam yayi cikeda jin haushin korar masa sweetie dayayi yace
"Banza d'an bak'in ciki wato yadda bakayi ba muma baza muyiba ance maka kowa ma irinku ne kullum bakuda aikin yi sai fad'a kamar wasu kaji".
"Da bakasan kajin bane". Madugu yace yana lallatsa wayarshi, k'wafa Abdallah yayi ya tashi yabar wajen Madugu ya tuntsure da dariya ya bishi yana masa magana yayi masa banza.


✓•✓•✓•✓•✓•✓
Washegari juma'a aka tashi da hada hadar d'aurin aure duk da dai na azahar ne d'aurin auren. Bayan an sauko masallacin juma'a aka d'aura auren ABDALLAH BASHEER MADUGU (MODIBBO) da amaryarshi HUSSAINA ISMA'EEL TURAKI (JAUHAR) saikuma na HABEEB UMAR MARAFA da HUSSAINA BASHEER MADUGU daga k'arshe kuma aka d'aura na ABDALLAH ALIYU ZAKEER da HASSANA BASHEER MADUGU kowanne akan sadaki naira dubu d'ari d'aurin auren daya tara d'aruruwan mutane da manya manyan mutane babu wanda babu malamai ne masu mulki ne rik'akk'un y'an boko ne da k'usoshin gwamnati da manya manyan masu kud'i wad'anda sukaci kuma suka tada kai nan fa marok'a suka samu abinyi musamman da sukaga anata musu b'arin naira tamkar ba'a san zafin nemanta ba.
Anko sukayi su ukun wato Madugu da Habeeb da Abdallah komai da sukayi amfani dashi iri d'ayane hatta wrist watch d'insu iri d'ayane na silver wanda shi kad'ai ma idan mutum yaji kud'inshi saiyayi mamaki, kowanne ka kalla fuskarshi taf da fara'a da farin cikin angwancewa sai gaggaisawa suke da jama'a ana musu fatan alkhairi.
A can Yola ma a ranar aka d'aura auren JA'AFAR ISMA'EEL TURAKI da amaryarshi HANNATU ALIYU ZAKEER, shima yayi mutane sosai na ban mamaki daga nan Ja'afar da Daddy da wasu y'an uwa na jiki suka nufo Kano.

Ranar ma amaren kaya iri d'aya suka sa wata dakakkiyar shadda fara dogayen riguna da akayi musu wani tsadadden aiki irin na y'an Senegal sunyi kyau sosai tunda aka d'aura auren kowacce jikinta yafara sanyi ganin yau dole ne subar gidansu da suka rayu tsahon lokaci a ciki shikenan kuma sun shiga wata sabuwar rayuwa kenan.
An cigaba da shan shagalin biki wanda gidan ya cika mak'il ba masaka tsinke harda wad'anda ba'a gayyata ba irinsu Mom sayyeed da Aunt jamila dasu haleemah d'ayyabu da wasu daga cikin y'an TOP TEN dai irinsu bazan kama suna ba dai 😝😅. Abinciccika gasu nan kaloli daban daban sai wanda mutum ya zab'a da kalar lemuka kala kala can na hango su Mom sayyeed da Aunt jamila a lungu sunata aswaki da naman kaji suna korawa da exotic ( bani na fad'a ba ango Madugu ne ya hangoku🤐).
Kasancewar bikin Ja'afar daya had'e lokaci d'aya yasa Mama batazo Kano ba tasan dai Ammi na tsaye akan komai na yaranta.

Tunda yamma aka fara shirye shiryen kai amare wad'anda tuni suka fara kuka saboda ganin dai da gasken tafiyar zasuyi ga kuma tsoro da fargabar shiga wata sabuwar rayuwa wadda basu saba da itaba dad'in dad'awa kuma nasihar dasu Abbie da Ammi da sauran y'an uwa sukayi musu hakan ya k'ara sanyayar da jikinsu musamman Hassana da zatayi nesa dan ita yola za'a kaita. Jauhar kam tuburewa tayi ita dole saidai a kaita dasu Irfaan ba za'a kaita ita kad'ai ba da k'yar aka shawo kanta da rarrashi akace idan tayi kwana biyu za'a kawo mata su, suma d'in kukan suke tayi ganin za'a rabasu da ita da k'yar da dabara aka fita da Jauhar aka shigar da ita mota aka tafi ana tafiya da ita itama Hussaina motocin da zasu d'auketa sukazo haka suka k'ank'ame juna itada Hassana.

Mrs Salees M
3/17/22, 12:10 - Ummi Tandama😇: *WATA SOYAYYA* 💝

Page 41.
Paid book.

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*.

©Oum Hanan.

Sunsha kukan rabuwa sosai da k'yar aka b'amb'are Hussaina daga jikin Hassana aka fita da ita sunata kuka tunda suka taso suke tare daidai da rana d'aya wata a cikinsu bata tab'a tafiya tabar y'ar uwarta ba komai zasuyi tare su kwana su tashi tare ayi fad'a a shirya yau ALLAH ya kawo rabuwarsu auren kenan ai kabar kowa naka iyaye y'an uwa da abokan arzik'i shiyasa masu karin magana sukace aure yak'in mata, koda aka fita da Hussainar ma Hassana bata fasa kukan ba kwanciya tayi kan gadon ta cigaba da raira kukanta.


*****
Wad'anda suka kai Jauhar basu wani dad'e ba anga gida dai ansa albarka daga nan kuma motocin da suka kaisu suka juya dasu aka barta ita kad'ai, sai bayan tafiyar sune sannan ta bud'e kanta ta shiga k'arewa d'akin kallo ya matuk'ar yimata kyau duk da dai bawai yaune ganinta dashi na farko ba amma kasancewar ya k'ara shan gyara ga me sabbin furniture hakan yasa ya k'ara yin wani irin kyau na musamman ya burgeta sosai haka kayan ciki sunyi mata masifar kyau.
Abdallah shi kad'ai ya taho abinshi bayan dogon gargad'i da nasihar dayasha daga bakin Abbie da Ammi dakuma Ayyah, saida ya biya ya siya kazar amarci da fresh milk da ruwa saboda ba komai a fridge d'in sannan ya wuce gidan.
Da kanshi ya fito ya bud'e gate d'in gidan ya shiga da motar ya k'ara rufewa, ledar dake kan front seat ya d'auka ya rufe motar sannan ya wuce cikin gidan yana jin zuciyarshi wasai tamkar wanda aka yiwa albishir da gidan aljannah sai faman doka murmushi yake, tanajin motsin shigowa tayi sauri ta k'ara jan gyalenta ta rufe fuskarta ta cikin mayafin take kare masa kallo lokacin daya shigo cikin salon gayunshi daya saba tafiya da hankalin y'an mata shadda light coffee da hula kalar shaddar basai anyi maganar k'amshi ba dan wannan a zaune take tsadadden k'amshin shi dake masa rakiya a ko ina yauma yana biye dashi harya zarta na kullum, masha ALLAH Yah Abdallah badai d'aukar wanka ba wllhy koya yasa kaya saiya haskasu koda kuwa yasane bada niyyar kwalliya ba ya had'u tako ina idan ka ganshi kamar ya had'a jini da larabawa. Inda take ya nufa yana zuwa ya zauna a bakin gadon bayan ya ajiye ledar hannunshi yace
"Da zaki taimaki kanki ki cire wannan lullub'in na kanki kisha iska". ta cikin mayafin ta murgud'a masa baki, batare datayi zato ba taji ya fisge mayafin ya jefar akan gadon yana fad'in
"Malama ki cire wannan abinda kike ta fama dashi kamar matar liman". baki ta tura kawai batayi magana ba.
"Wow she's very very beautiful baby, kinyi kyau ba kad'an bafa". bata kulashi ba sai juyar dakai gefe datayi tana ta wani cin magani hakan saiya bashi dariya ma baki ya tab'e ya tashi ya d'auki ledar daya ajiye ya fita ta bishi da kallo tareda k'ara d'auko gyalenta ta k'ara lullub'awa saidai bata rufe fuskarta ba.
Kitchen yaje yasamu plate ya juye naman kazar ya d'auko cup biyu da fresh milk d'in yadawo d'akin cup d'in ya ajiye da madarar a bedside drawer ya haye da naman kazar kan gadon ya ajiye a gabanta yana fad'in
"Gyaramin zaman nan naki malamar k'arya shine saida kika k'ara yafa wannan gyalen ko? baki ya cije yasaki k'wafa yana murmushi yace
"Ki gama yafe yafen k'aryar naki Jauhar badai mayafi ba? dariya ya saka kafin kuma ya had'e fuskarshi tam yaci serious ya d'auki naman yakai bakinta, girgiza kai tayi ta kauda kai gefe tace
"Nifa na k'oshi Yah Abdallah bazan iya cin komai ba yanzu".
Cinyar kazar ya yaga ya fara taunawa yana fad'in
"ALLAH sai kinci kazar nan Jauhar bazan b'ata kud'ina a banza ba ko kici ko in yanka miki ta wahala yanzu nan".
Cikeda gajiyawa tace
"Wai ana dole ne dan ALLAH tunda nace na k'oshi basai a k'yaleni ba".
"Zakiga dole kuwa yanzu yanzun nan yarinya ganin idonki wllhy ko kici da arzik'i kokuma kici ta tsiya saiki fad'amin wanda kika zab'a". yace yana ajiye naman hannunshi yafara cire links d'in hannunshi yana tattare hannun rigarshi kamar wanda zaiyi dambe ido kawai ta zuba masa tana kallon ikon ALLAH taga abinda zaiyi, d'agowa yayi ya kalleta bayan ya gama tattare hannun rigar tashi yace
"Tsiya kikeso ko arzik'i? idan tsiyace kinsan na iyata harda ta siyarwa wllhy danneki zanyi in miki d'ura ta rashin arzik'i koda kuwa zakiyi amai idan kuma arzik'i kike nema shima na iyashi kwando kwando idan mutum ya nemi hakan". zab'i ya rage naki tsiya ko arzik'i?". ya ida maganar yana d'age mata gira, da kanta ta shawarci zuciyarta gara taci ta arzik'in dan tasan sarai zai iya aikata abinda ya fad'a d'in yayi ma wanda ya fishi sun gani, idanun daya tsura mata ne alamun

24 / 31